← Book details Kece Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Kece Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aykuwa tatashi tafita aguje sai faman haki take.
____d'an gefe da part d'in shi ta tsaya, ta goge hawayen fuskarta tareda gyara rigarta tanufi part d'in su.

Ab'an garen m.k kuwa, yadda ta hankad'ashin nan anan bacci mai nauyi yay awungaba dashi.

Saifaman zare i'do take, tana addu'ar Allah sa bakowa a parlour n.don i'ta a tunaninta za'a gane abinda M.K yay mata.

Aykuwa tai sa'a bakowa ciki. Da gudu tashi ge dakinsu, direct toilet tanufa donyin wanka.

M.k kuwa baitashi ba sai 4:00pm, ya gabatar da sallar la'asar.
Bayada yagama u'zurinsa ne yazauna yana tunanin abinda yafaru tsakaninshi da Neenah, ouucchhhh yadafe kanshi yana danasanin abinda yayi.
🤦🏻‍♂allah wadaran shan _beer_.
(Hmmmm tukun nama ai)

Sai 5:30pm yafito saka makon yunwar data adda beshi.

Neenah ce sanye cikin wata doguwar riga na atanfa _colour n Orange_ tai bala'in amsarta.

Gefe kuma fareeda ce kezaune akan sofa tana charting, da alamu da saleem takeyi, don irin k'aya taccen murmushin danaga tana dokawa.

Neenah ce tashiga kitchen don dafama kanta _indomie_.

After 8mins, m.k ko sallama babu, baiko kulada fareeda wanda take a parlour n ba, kaitsaye yashige kitchen abunshi yana shafa ciki.

_Manage wlloh agajiye nake_

*UrS QuEeN BEEE MaRaFa😘😘😘😘😘*
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRI NA7⃣*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

*♻€°W°F♻*

NA_______
Habeeba Muh'd Marafa *{HM²}*

________Neenah tajuya da niyyar d'auko plat , kwata2 tashafa'a daruwan data zubar a lokacin yin girkin nata, tsantsin gurin ya d'ebeta tatafi luuuu zata fad'i.
Yayi dai2 dashigowar m.k tafad'o jikinshi.
Yinyin da shima san tsin yad'eb'eshi duka suka zube a k'asan gurin.
(Ooo karona biyu Neenah a k'irjin m.k.)

K'amshin turarensa yatabbatar mata dacewa shine, dasauri tafara kiciniyar tashi .
Yayinda shikuma m.k gaba d'aya tunaninsa yafara sauyawa, sakamakon yadda jikinta ke goguwa da nashi, gawani shu'umin turaren dake jikinta.

Dasauri neenah tatashi donjin abinda ta d'aura yafara k'auri, gaba d'aya ta diririce tamanta dacewa abin yad'au zafi, wani k'ara tasaki yayinda tad'aura hannunta akan towan daniyyar saukewa, bashiri kuwa tasaki abun taja baya.
Hannun tarik'e tana yarfewa hawaye na malala.

M.k wanda ke ganin duk abinda ke going, mtswww! Aransa yakecewa kai anyi kid'i manmiya anan wllh mtsw.

Yaje yasauke indomien akan _gass cooker_n, plat da spoon ya d'auko ,indomie yajuye aciki yad'aura spoon din akai, copee n dake acikin dan cup a gefe yadau, yahada tareda indomien yay ficewsrsa dasu.

Neenah kam ikon Allah kawai take kallo, kan ubancan! Lallai ya moha yagama dani.
Gazafin hannunta daya dameta, gaya ya d'auke abincin, ga yunwa tadameta.
Gabad'aya sai haushin MUH'D yacikata.

Haka tafito tana yarfe hannu da'alamu k'unar tad'an shigeta.

Shiko gogan dining yanufa, yabaje yanaci yana zuba santi.

Kekuma dalla malama meye hakan?, kinzo kinama mutane iskanci kina wani yarfe hannu.
Cewa fareeda wanda neenah tazo wucewa tagefen ta.

Neenah, tawatsa mata harara tai wucewaita.

Fareeda ta balbale da uban dariya......cause taji duk abinda yafaru tsaka ninta da m.k.
Tak'ara shek'ewa da dariya tai d'akinsu aguye don meman tsokana.

Kamar kullum iyalen gidan *Alh kabeer madugu*ne , ke hallare a dining da zummar yin diner.
Yayinda neenah tai saving d'in kowa yakama nashi yanaci.

Alh kabeer naji yace """fareeda"".

""Na'am abba.....fareeda ta amsa.

Yazancenki da Salim?......kwanaki kuma yamatsa da zai turu zaituru so yauzu kuma naji shiru ko lpy?.

Fareeda tai k'as dakanta tace""""" am dama Abba bayada tafiyarka yakara cewa daddyn sa yamatsa mai.......shine na fad'ama ummi tace abari inka dawo koda yaushema sai su iso..............am yanzudai Abba kai akejira.

Tom masha Allah, tunda allah yadawo dani lpy inyaso kocikin week dinnan saisu iso insha allah.

Fareeda d'ad'i yabi yacikata, burinsu yakusa ciki i'tada salim namallakar junansu💃 .

To autata fa. Abba yafad'a yana kallon Neenah.

Neenah tasunne kai k'asa kamar munafuk'a.........caraf abdallah yaka ma""""" ay infad'ama kashirya, kakusa aurar da autar............fareeda ma tacafka.....wllh kuwa don neenah kam tayi nisa a soyayyar *KHALEEL* .....kuma wllh abba tsakani da allah yakesonta da aure.!!!!

Kalmar da taringa yawo a kwakwalwar m.k ......khaleel, yana sonta da aure!!!!!!.

Abba yace lalala shikuma a i'na yake?.

Aykuwa fareeda takwashe duk wani labarin datasani akan khaleel wanda neenah tafad'a mata a Abba........arda yadda suka had'u, da yadda suke soyayyarsu gwanin ban sha'awa duk ta I'darma Abba........ardama Ummi wanda batasan da zancen ba.

A to masha Allah abu yayi d'ad'i, indai har kinasonshi , kuma yayarda zaibarki kici gaba da karatunki, aishikenan kuma sai zancen aure!!.

(Abinda yake ta6a ran m.k)

Neenah da zuciyarta tamamaye da farin ciki, don harga allah tanason khaleel.

Ummi ma da d'ad'i yacikita, don a yanzu batta da wani buri dayawuce allah yabawa 'yanma tanta biyu miji nagari a aurar dasu......dakuma mataye nagari ga yaranta maza biyu.

M.k wanda zuciyarsa tacika da kishi, haushi tareda bak'in cikin wannan zance......baisan sanda yabuga wani uban tsakin da yasa duka hankalinsu yadawo kanshi.

Muh'd lpy kike tsoki haka???....cewar abba.

M.k dayarasa tacewa, dakyar ya tattaro natsuwarsa yahad'a """"am..am... wllh Abba kwata2 yau banjin d'ad'ine, abincin ma kwai inacine amma bawai inajin d'ad'insa ba .

Ummi tace sannu kaji son...Abba ma...kowa yay mishi sannu.

Ummine tarakashi har part d'in shi, tabashi magani yasha sannan tace yakwanta don yasamu hutu.

Kowa ya tafi d'akin baccinsa, neenah da fareeda kowacce ta duk'unk'una a blanket da'alamu kowacce soyewa take da habibinta.🤗

Neenah sai wani lankwasa murya take tanawani farrr da ido kamar tana gaban khaleel🤣.
Tana fad'amishi yadda Abba yaji zancenshi.
Bak'aramin d'ad'i khalel din yajiba, don ayanzu baida burin daya wuce ya mallaki neenah.

Haka dai sukaci gaba da hiransu cikin ji dadi da farin ciki , daga bisani sukayi sallama.
Neenah kam adda'a kawai tayi bacci ya d'auketa.

_____________*Taya family n Alh kabeer madugu yakafu*...........

_Kukasance tare dani donjin yadda abun yake.._

For any comments/correction
☎08104117749☎

*UrS QuEeN BEEE MaRaFa💋*
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRI NA8⃣*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

NA_________
Habeeba Muh'd Marafa _*{HM²}*_

*♻€°W°F♻*

*Taya _family_ n Alh _khabeer Madugu_ yakafu???.*
*____________________________*
*"""""""Alh Muhammad Madugu*, yakance mahaifi ga *Alh kabeer* tareda d'an uwansa *Muktar*, wanda shi khabeer yakance shine babba.

Suntaso cikin jind'ad'i da farin ciki, kasan cewa mahaifinsu *Alh Muhammad Madugu* babban attajirine agarinsu *GEZAWA* LGA kano.

Mahaifiyar su khabeer *Haj Nana khadeeja* , dattijuwar arziki, mace maikamala, gasanin yakamata. Wanda Allah yamata rasuwa tunsu kabeer na k'anana, hakan yasa Alh Madugu yad'au son duniya yad'arama 'ya'yansa, don ko aure yak'i yi gudun karya auri matarda zata azaftar masa da yara.

Hatta school acikin kano sukeyi, makaranta 'ya'yan manya2n masu k'ud'i. Kusandai rabin rayuwarsu acikin kano sukeyi, hutu kad'ai kedawo dasu _GEZAWA_.

Bayan gama secondary school d'insune muktar yasamu _Admission_ a _Germany_, bak'aramin farin ciki yayiba , don yana bala'in son rayuwa a _outside_.
Wanda ra'ayinsa yasha banban da kabeer donshi yafison yazauna a k'asarsa _Nigeria_. Haka rayuwar su tacigaba da tafiya cikin jind'ad'i da nasara.

Ranar da kabeer yake kammala _degree_d'inshi a *BUK*, ranar Allah yama *Alh Madugu* rasuwa. Sakamokon _accident_ d'in dayayi a hanyar zuwa kano don taya d'ansa murna.

Wannan ranar kam tazamewa khabeer Madugu ranar b'akin ciki, haka kuma bazai tab'a mancewa da i'taba.
Bak'aramin tashin hankali mukhar yashiga ba yayinda labarin rasuwar mahaifinsu ya riskesa.
Haka yasha jima minsa, daga karshe yabarwa Allah lamarinsa.

*______________________________*
*________*Alh kabeer Madugu, ne zaune tamfatsetsen parlourn sa, gefe kuma ga uwargidan sa *Haj A'isha* wanda sukayi aure da'i'ta lokacin yana aiki a kark'ashin _company_n mahaifinta.
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRI NA9⃣*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

*♻E.W.F♻*

N@____
Habeeba Muh'd Marafa _*{HM²}*_

Alh khabeer, sunyi aure da aysha tun lokacin da yake ayki a k'ark'ashin mahaifinta. Zama sukeyi da matarsa zama na soyayya da amana.

Shekara daya da aurensu Allah yabasu haihuwa yayinda ta haifo d'anta namiji, bak'aramin so sukeyiwa d'ansu Muhammad ba, yarone maishiga rai gashi gifted kowa sonshi yake tunyana yaronsa.

Abdallah k'ani ga Muhammad wanda haj Aysha tahaifesa bayan Mohammad nada shekaru 8.

*Alh khabeer*zuwa yanzu da Allah ya azurtashi yakuma daukakashi. yazama shararren mai kudi , yanada companies bila adadin.
Kuma yana aywatar da duk wani tarkokinsa a _chaina_, baifiye zama a Nigeria ba.

*Mukhtar*, wanda yakare karatunsa a Germany, acan sukabashi ayki haka yake rayuwarshi a can ,amma yakan zuwa gurin dan uwansa don sada zumunci.
Haka har Allah yahadashi da farisa a Germany sukafara soyayyar su tainisa har Allah yasa suka mallaki junan su tahanyar aure, bakaran zaman lpy sukeba.

Bayan shekara biyu da aurensu Allah yabasu d'iya mace wanda tacisunan ta *Nana Khadija* mahaifiyar su mukhtar, kai tubarkallah Allah yiyi wanan yarinya baiwar kyau da farin jini kowa k'aunarta yakeyi.

*Muhammad kabeer madugu*, da ga *alh kabeer madugu* jika ga *alh Muhammad madugu*. Yataso cikin jindadi da kulawar iyayensa, wanda kocikin abokai daban yake, jinkansa da k'asaitarsa ma kadai abin burgewa ne.
agarin kano yay primary school dinshi yay secondary school dinshi kuma a abuja, yayin da kuma yatafi Spain donyin doctoring degree dinsa.
Tofa! Acan Spain idon *M.K* yakara budewa yazama dan duniya, don hatta jikinsa tattoos ne. Acan yaywata girlfriend mai suna *Zuwairat* wanda ita ma yar kanoce tazo karatu nan. Haduwar m.k da Zuwairat ne takara hargutsa rawuyar m.k. gashan Bear.

Zuwairat takasance diya ga alh mustapha, alh mustapha mutunne maitarin dukiya, Allah yabashi 'ya daya wanda yadauson duniya ya dauramata duk abinda tayi maikyau da akasin haka daidaine agurinshi.
Wannan dalilin yasa Zuwairat ta fetsare bataganin kowa da mutunci, gabin maza tun a Nigeria barekuma a outside wanda bawanda zaice cikanka.

Zuwairat ce takoyama m.k iskanci , tunda suna dan tabawa kadai.👌🤗.....................
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRI NA 10🔟*

Dedicated to Khaleesat Haiydar

Abdullahi khabeer madugu kani ga Muhammad kabeer madugu, yaro kyakkyawa dan zamani, gasanin darajar mutane da faram faram da jama'a.
Yana karatunsane a garin kano don baison yin nisa da i'yayensa.
Sai k'anuwarsa FARIDA wanda wata shida tabama Neenah a haihuwa, yanzu haka takusa kammala secondary school dinta.
Yiyin da abdallah yake 200 lvl a BUK.

**********************
Yau Neenah saifaman murna take, alkawarin da daddy nta yadaukar mata nacewa """ saita gama secondary school dinta zata je Nigeria don ziyartar yan uwanta .
don saidai tagansu a photo ko taji muryansu.
Ahaka kuma take bala'in son umminta, don Ummi tana matukar ji daita.

______ yausu FARIDA saimurna da rawar kai akeyi, kawalliyarta zatazo daga Spain ( su farida anga 'yar fara za'a mak'alema ta lolz).
Chapter 3 · 0% Book details