← Book details Kece Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 20

Sashe 7

Kece Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fauzan yacigaba da cewa "yanzu kana i'na inzokaji komai har pic d'inta zakagani. "

"Inagida ".

"OK tau ganinan zuwa".

M.k yakatse wayarshi yana tsoki , za'azo ataiyar masa da wata damuwar.
Ba'fi 25mins saiga fauzan, direct part d'in m.k yawuce. A parlour yasamesa yana aiki da laptop d'insa. Da sallamarsa yashiga, yasamu guri yazauna yana washe baki.

M.k dakamar ana zuba masa ruwan zafi dan bak'inciki.

"Kai frnd wallh kayi dace kaganta kuwa wallh tahad'u."

Fauzan yaciro wani envelope a ljihunsa yamik'ama m.k.

" meye wannan kuma?."

"Kaidai karb'a kagani mana".

M.k fir yak'i karb'a saidai yanuna mishi.
Fauzan yaciro photo n ciki yanunama m.k.

" to ya kaganta?".

M.k yafara yamutsa fusku.
Fauzan yace "meye hakan ko bata maka bane?".
A yamutse m.k yace "yayi". Amma k'asan zuciyarsa kam saiwanda yagani.

"""""""Tou wannan i'tace summayya 'yargidan alh gaddafi, yarinya maitashe, daji dakai ga naira agun ubanta.'

A fudace m.k yace "saika fad'ama wanda basuda duk abinda ka lidsafo".

"Anyway yanzudai gashi nabaka brief history nata, yarage kafitarmana ranar dazamuje gidansu kufatinci juna, nd saikuma kafad'ama su abba a tsaida magana".

"Bayanzuba saina samu lokaci zanfitar randa zamu.".......... Daga nan yashige bedroom abinsa.

Fauzan ransa yad'an baci abinda m.k yamasa. "Banza maramutunci dole kai walak'anci tunda kasamu abinda kakeso."...... Fauzan yatafi abinsa.

°°•••°°••°°
Da sallamarsa yashiga d'akin, Ummi tana zaune bak'in gadon tana waya. Saida tagama wayar tajuyo cikin kulawa tadubeshi, " ya'akayi son?".

"Am Ummi dama maganane akan auren yafad'a mata duk yadda sukayi da fauzan.

" To alhmdllh tunda tamaka aishikenan, yanzu zansamu abbanku sai infad'a masa."..... Hakadai sukagama magannan nunsu after m.k yafito.

_____Yana sauk'owa daga upstair i'takuma tana hawa.
Waya take da sahibinta farin cikin ranta sai doka murmushi take. Ganin m.k ne yasa taisaurin cire wayan a kunnenta. Wani irin kallo yake binta dashi wanda nagagara gane ma'anarsa, so a'a k'ine sai Allah.
cangefe tamatse tatak'ure kanta a k'asa kamar muna fuk'a .
m.k yawuce tabi bayanshi da kallo sai a lokacin ta kulada irin ramar dayayi.
" kome yake damunsa yarame haka oho"..... Tai ciki abinta.....

_(Wehuhuhu💃💃💃💃💃mah fans kuzo🏄🏻‍♀ mutaya m.k murna😆😂🤸‍♀ uhhmmm baruwana 🏃🏻‍♀)_

Yaune ranar daza'a kaima m.k tambayar auren summayya................

*QuEeN BEE MaRaFa💋*
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRINA 18*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

*♻€°W°F♻*

NA____
Habeeba Muh'd Marafa _*{HM²}*_

Uhm su sumy ankusa zama matar doctor Muhammad khabeer madugu wanda'yantama kekai kansu dakabsu sai fad'i take a cikin frnds d'in ta .
"shine yakesona kuma zai aure ni wayyo Allah na dad'i."
gaban mirror taje tadubi kanta sosai " kai nahad'u ashe gawad'annan boos da hips d'in susuka rikirkitashi wooooo wani abu saina shiga gidan Dr sai juyi da rankwad'a take a d'akin i'takadai.

Tanijin dirin motici wanda da'alamu fita sukayi, tafito parlour aguje.
wasu arnan akwtinane wanda sukaci kud'insu guda shida. sai kud'in sadakinta 250k wani uban shoki sumy takwaso dataga wannan kayan,
"wannan akwatinan aurena gakuma sadakina 250k wowww".
tawani lumshe i'do d'auka pics d'in kayan tafarayi saida tayi tagaji sannan takoma d'akinta.
K'awayenta tafara Kira , in a few mins sukaci mata d'aki.
sai fasa matakai suke Sumy kam high high takejinta
wata frnd d'in ta tace "sumy dan nuna mana pic dinshi muga don ni kawai inajin sunansa ne ammana bantaba ganin shi ba, so kinga ko watarana in aka hadu za'a gaisa"......

Sumy taimata wani kallon rainin wayau .

" dawa d'in zakirink'a gaisawan?." "Da m.k din."

"Ke nifa bansan irin wannan munafircin ".

"wani irin munafirci kuma?".

" Wanda kikeyi..... inba munafirciba meye wani anuna mini pic dinsa kurinka gaisawa. To inma sokike kizagaye, m.k ba kulaki zaiyiba don yafi karfinki ".

taimata wani harara. "banza kema yakulaki bareni , wallh nasan nawuce ajinsa tunda har yakulaki".

Sumy tai wani dariyan rainin hankali.
"Wlh wllh uwarkima batakai ajin m.k ba bare tawucesa inakuma ke."

"Dakata karki kara samun uwa. banza shegiya mara mutunci. Tafice abunta.

"Woooo ajedai. bak"in cikinki ya kasheki kekadai".
Saurankan sukaci gaba da gashi.

_Gidan alh khabeer_
______daga dubai Abba yasa aka yomusu ordering na wasu mahaukatan furniture's Wanda ko gidan ubanwa za'a kaisu ansan bakarya.
Ummi, musamman tad'auko masu gyaran jiki daga Maiduguri, sokoto, niger don kyaran 'ya'yanta.

Su amarya farida sai faman rawar kai d i'yayi ake.

Neenah kam tunda aka yanke bikin 1mounth gaba daya tazama wata kala, batacin abinci sosai duk anrasa ganekanta tazama wata so silent da ita.
su abdallah saifama ake kamar shine angon.
M.k kokad'an bayasa aurennan a lissafinsa. Kullum yana kwance a d'aki.
In Ummi taimishi magana yace baida lpy. abokanan sa in sundameshi Yatafi gidansa Na GRA .

Dole dai fauzan da abdallah ne kekomai na bikin m.k.

_Ina labarin Zuwairat?._

tun ranar m.k baisake nai mantaba.
zury hankalinta yatashi don in tanemeshi a waya baya dagawa. Kwatsam taji labari wai m.k zaiyi aure bak'aramin Rud'u tashigaba.

'"" lallai m.k nizaiwa haka Dan boroubansa, gani nan anan shikuma zaije can yayi aure.
to wllh yayiwa uwarsa k'arya don narantse da Allah saina wargaza auren anan gatan durun uwa"...... Tashiga dealing number zeey .

zee tafito daga wanka kenan taji ringing d'in wayarta.

" hlo Mrs m.k ya akayi."

"Ke dalla banason buroubanci wani Mrs m.k?.
kinajin shegen nan zaiyi aure saura 3days".

"wace 'yar zee ta malmalo wani uban ashar tamaka zata kwacema frnd d'ina farin cikinta?."

"Kedai kawai yanzu kisameni agida nasan tuggun dazan had'a. wllh auren nan baza'a dauraba."

"OK ganinan zuwa karki damu."

Zury takatse wauar.

Zee tazauna abakin gado tana huci .
"Wllh wllh m.k bai i'sa yayi wannan aurenba! saida nagama d'aura burin rayuwata akanshi yanxu kuma yace.....hmmm.

zanhad'a Hanuda zury miyi wannan abun badon in taimaka mataba a'a don in taimakawa kaina zanyishi........ni zainab nice Dr Muhammad khabeer madugu zai aura....nice matarsa....nice uwar yayansa .....tare zamuyi rayuwa kuma mumutu tare!!!!.............!.

_UrS QuEeN BEE MaRaFa💋_

❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRNA1⃣9⃣*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

*♻ €°W°F♻*

NA____
Habeeba Muh'd Marafa _*{HM²}*_

_I'na godiya gareku *Ummu khausar,* *Ummu hauwart*, *X33NAT*, *Meenat pretty* tareda *Sweet khardehy😘*.kuna d'aya daga cikin manyan masoyan book d'innan Allah yabar *SO❤.*_ ```{AMEEN}.```

_*We will be together.*_
_*#one lurv.*_

*____________••°°°••°°°••________*
____Ba'a fi 1hour ba saiga zee ta i'so. zury daketa kai kawo a poluor n tagagara zama.
"Assalam".
" yawwa shigo shigo". Zee tak'araso suka zauna.
Zury tace "kinga yadda m.k yawatsamin k'asa a i'do ko shege munafiki."
Zee datakejin kamar tashak'e zury don haushin zagin m.k datakeyi.

"To yanzuke kina tunanin taya za'a katse auren?". Zee tatambayeta.

"Kawo kunnanki kiji".

Kome tafad'a mata oho. Jinai sunbuga wani uban shewa da tafi.
"Kai zury wllh ke mushance".
Tai wani farrr "ai wllh indai gun sharrine ko shaid'an."
Haka sukaita hada munafurcinsu har dare.

Wasu mata biyu nagani sun sauk'a a keke napep, duk sunsha zunbula zunbulan hijjabi har k'asa. D'aya da k'aton cikinta wanda zai i'ya kaiwa wata 6. Daidai wannan had'add'en gidan da'aka ajiyesu suka shiga.

Cikin mutunci suka gaisa da megadin gidan , suke tambayarshi ko mai gidan yana nan.

"Eh kam kunyi sa'a , don d'azunnan yadawo daga England saboda auren 'yarsa daza'ayi. Jibi."

Mai cikin azuciyarta tace " dama bai dawoba yayi aikin dake gabansa acan, don wannan aure baimai yayuwa bane."

"Kuzo inshiga daku ciki mana".

"Yawwa to mungode." Sukabi bayanshi .
da sallamarsu sukashiga parlour n, yayinda alh gaddafi da matarsa dakuma tilo'yar tasa summaya sai yayarsa wanda tazo daga Maiduguri da k'anwar matarsa, Sai hira sukeyi cikin nishad'i . alh sai tsokanan amarya sumy yake i'tako saiwashe baki take akace mata matar Dr Muhammad.

Aka amsa musu sallama mahaifiyar sumayya taimusu mazauni suka zauna. Cikin ladabi da girmamawa suka gaishe da duk wanda yake parlour n.
Suka amsamusu cikin sakin fuska.

Can2 zee tace "dama kwatancen gidannan aka mana Allah yasadai bamu b'ataba."

"Wani gida kenan?.".....mahaifiyar sumy ta amsa.

Zuwairat tace " gidansu *Dr Muhammad khabeer madugu!."*

Zuciyar sumy tace tatsatsatsatsa dataji ankira sunan mijinta.

Alh Gaddafi yaygara zama. "Ko lpy kuke neman alh khabeer ko d'annasa?."

Zee tace " eh to duka muke naima don shi Dr ne yazalunci k'awata shine mukakawo k'ara."

Alh yace "subhanAllah meye yamiki wani irin zaluntarki yayi?."

Zury tafashe da wani uban kuka mai bantausayi da tsuma zuciya. "Wllh yacuceni d'anku yacuceni ya zalunceni yagama da rayuwata.......

"Annalillahi wai meye yamikine?.
Mahaifiyar sumy tace " a'a alh adakata asanar da i'ta cewa Muhammad ba d'anmu bane . saifaman cewa take d'anmu yacuceta tomu bamuda wani d'a namiji ma bare yacuceki".

"Baiwar Allah kinatsu kisaurareni. Kinga Muhammad ba d'anmu bane, abinda yasa nace d'anmune shine saura kwana uku ranar juma'a za'a d'aura mishi aure da 'yata".... alh yanuna summayya .

"innalillahi wa i'nna i'laihi raji'un". Zury tadoka wani uban sallallami. Tararrafa gun suammaya. Tace
"Baiwar Allah inafatan baitab'a tab'akiba kuma ba'abinda yatab'a shiga tsakaninku?".

Sumy tabita dawani kallon raini "bangane mekike nufiba wani irin abu?.".... Tafad'a atsiwace.

Zury tajuyo cikin falourn tana shashek'ar kuka tace " bayin Allah don Allah karkuce nacimuku fuska. don Allah kukai 'yarku asibiti a dubata, kokuma kudubata da kanku wllh kuduba 'yarku."........ tak'ara fashewa dakuka harda d'aura hannu aka.

Alh Gaddafi yace "baiwar Allah don Allah kinatsu kifad'a mana meke faruwa wllh gaba d'aya kinsamu a duhu."

Sai da akarink'a bata baki sannan tanatsu tai shiru.
Zury tafara magana kamar haka. "Bayi Allah inaso kutsaya kuji abinda zan fad'a muku, kunga wannan cikin dake jikina banakowa bane saina *Dr Muh'd Khabeer Madugu* ."
duka suka d'au salati da sallallami.

"Keko baiwar Allah garin yaya haka tafaru?." .... Yayarda alh Gaddafi ta tambayeta.

Zury tashare hawayen dake kwaranya a i'don "munfara soyayya nida Muh'd tun a Spain gurin karatunmu , lokacin yanuna yana sona tsakani da Allah kuma da niyyar aure . yamin alkawarin cewa muna dawowa Nigeria zaitura magabatansa domin ayi maganar auren.
Chapter 7 · 0% Book details