← Book details Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba qarya ita kanta tayi masa baqin cikin rashin khalesah
To ya zasuyi qaddara ta riga fat
Taro na watsewa ya fada helicoptern da yazo a ciki,sannan ya d'aga wayarsa ,missed calls din matarsa ya fara karo dasu
A take ya saki murmushi,lallai da ita zan fara sharing farincikina ,nasan zata tayani murnar nasarana
" My excellency "
"Uwargidata ,kuma first ladyn Nigeria ,a nan kusa"
"Wow kasakani nishad'i mijina,da kana kusa da nayi maka kyautar lafiayye,kuma zazzafan kiss"
"Karki damu koyanzu na gamsu da zumudin zuciyarki,hajiyata ,abun tarairayar farincikin gidana..."
"My excellency kana cikin tsananin farincikin da ,da ace ba atabbatar maka da cewar ka zama president ba da tabbas na canka min lashe wannan kujeran ne..."
"Qwarai ina cikin farin cikin da yafi na samun kujeran ma,shiyasa nakira don Ku tayani farinciki, kafin in qaraso..."
"...wowohooo mijina ,kullum dama kai me sa'ane don Allah yi gaggawar shafamun wannan qasaitaccen labarin da yasa mijina cikin wannan nishadin?"
"...Alhmdllh naje azdajarz kuma na bada auren saudatun ki wa ngwandu PA dina,sannan kuma sarki mai adalci ya bani auren khalisah aure jumma'an nan inshaallah..."
Wani qara ta saki ta damfara wayar a qasa hakan ya saka wayar dagargajewa,hakan kuma yayi daidai da shigowar saudah da gudu d'akin
Saidai ganin ta tiska wayarta yasa taje gabanta ta tsaya ,ba tare da nuna wani zazzafan kulawa ba tace "lafiya kuwa....me ya sami mahaifina?"
Rikicin tashin hankali,yawun bakin saudah ne ya sarqe a take tari ya sarqeta sakamakon jin wannan baqin labarin yanzunnan a bakin ummanta,gabadaya sun fada mummunar tashin hankali,ita ummah zullumine gamida fargaban zaman kishi da khalisat ,a yayinda itakuma saudah baqin cikin auran sadakar da aka bayar da ita take yi ga mijin farida ,da ganin idonta taga suna fasikanci da qawarta latifa da ta rasu....

Wani kakkauran ajiyar zuciya tasauke ,takoma da6as ta zauna ,a take wani kauraran hawaye ya sirnano mata
Duk yanda ummah taso taji maganarta ,amma ta kasa furta ko kalma 1...
[8/19, 13:34] Bamalli: *JNS*
51-55
Ta 6angaren khalisah kuwa ,ana furta an bada ita wa Ahmad sannan an bada saudah wa Yusuf ,a take taji tamkar an zare mata kaso tamanin cikin Dari na damuwarta ,ko banza in auren tsohon ne ,dukkansu tsoffin zasu aura
Kazalika bazatayi zaman kishi da uwar aminiyarta ba a gaban idon saudanta,finally baza a hada auren aminiyarta da yaron ja'ira sanata baraka ba,ko yanzu ita alhamdullh tunda aminiyarta ta tsallake wannan bala'in da bata San dashiba.

Idonta ya kad'a yayi jajur ,sai safa da marwa take yi ,tama rasa tunanin da zata somayi ,,,,,,,Wani bubuuummmmm
taji qarar tashin ganga ,jauje gamida algaita ,suna tashi gamida tunkaro harabar cikin gidan....tsam tayi da ranta ,don sauraran,sanin qasaitaccen bafaden dake shirin shigowa gidan da wannan yammacin.

Kirarine maroqan suka farayi suna dukan gangunansu hade da busa farensu ,suna faman wasa gimbuya khalisa ....

Qarasawa gaban windonta tayi ,daidai nan jakadiyar gimbiya diyana tazo ta gurfana a gaban ta tana dunqula hannu gamida jinjina mata
"Ran jarumata ya dad'e ,matar gwamna tana nan falon ganawa da manyan baqin gimbiya ,ta taho takanas don tayaku murnan aurenki da shugaban qasan mu mai adalci...."
A qufule ta waigo ta kalli jakadiyar ,kafin ta taka ta d'age labulen windon yanda zata iya hango tun daga get d'in karshe da zai shigo da kai sasunan cikin gidan,mai dauke da wawakeken haraba ,an masa kawanya da fulawoyi masu kaloli na burgewa da daukan ido....ba bu ko keke bare wani mota a haraban sai fili tahhhtahh iya ganinka ,sakamakon wasu dika dikan garejin motoci dake manne da jikin ginin sasukan ,anan ake ajiye motocin mallakin fadan,don haka komun matsayinka ko muqaminka ,dole ka faka motarka ,A cikin rumfar ajiye motoci na get din farko zuwa na biyu ,kai kuma ka tako a qasa zuwa cikin gidan mamallakan izza!

Mulkin kenan
Don haka qwarqwar take ganin maroqan cikin tsimman bubbunan rigunansu ,sunyi layi suna zarya a tsakar wajen suna zuba kirari da banbad'anci
"Jakadiya bazan samu ganin kowata kalar maceba zuwa wannan lokacin ,ina buqatar in huta"
Kiki kaka...Magajiya tai masu burin tsuli,har sun fara lissafa yanda zasu yanyana ko dubu ashirin ashirin ne cikin kudin da matar gomnan zata basu kyauta.

Jin still bata futaba yasa ta juyo a qufule
"Baba ki fita ko zaman me kikeyi?"
"Afuwan ran shalelen masarautan nan ya dade,kiwa girman rawanin mai martaba ,ki je ku gaisa ko na sakwanni gomane ,cikin tsadaddun lokutanki,girmane Allah ya Baku kuna gudunta ,alkawarin Allah kenan bayi bawa Wanda yikeso"
Huro hanci tayi ta furzo numfashi mai huci ta baki
"Tom naji gani nan tafe"
"Godiya muke sarauniyar dudduniya ,a fito lafiya"
Haka ta fice tana murna kamar ta taka rawa ,don farin ciki
Waigawa ta qarayi tana kallon yanda maroqan ke ware iyakan karfin muryarsu suna waqeta amma tamkar sunsa speaker,jinjina kai tayi,Allah mai iko kowa Allah ya huwace masa hanyar cin abincinsa,ni kuma shikenan magana ta fantsamu zan auri shugaban kasa, anji labarin zuwan matar gwamna wajena ,kamar bata saba zuwa kawo gaisuwa ba ,anzo zaa fitineni da roqo ,ni me Nike dashi?

Banda komai sai salatin annabi,ni wallahi gidan sarautar nan akwai ginsa ,hayaniyar yayi yawa
Da hakan ta rataya alkyabbarta da ta war6ar akan kujera tun shigowarta,sannan ,ta fito zuwa asalin babbar falonta inda zai fitar da ita sassanda zuwa cikin gidan
Kuyanginta na ganin fitowarta sukayi saurin bin bayanta ,suna mata barka da fitowa ,sannan suka d'inguma zuwa inda matar gwamnan take zaune tare da gimbiya diyanah .

Gimbiya diyanah na ganin shigowarsu ta mike ta fita itakuma....
[8/19, 13:34] Bamalli: *JNS*
61-65
Yau JUMU'AH ,tun sassafe qaran jiniya da hawa da saukan jirage ya gama rikita garin azdajarz ,ko jariri yasan ana bikin 'ya'yan gata sauda da su'adah ,tun wajen karfe sha d'aya excellency ya shigo garin da danginsa da bakinsa ,shima ya zuwa wannan lokacin PA ya ware ,amma har yau d'aurin aure basu samu zantawa da amarya saudah ba...saidai wannan kyautar dannan haushin yasashi jin sanyi cikin ransa yasan an masa karamci ,ai dole yasan in ya bawa saudah kula khaleesa za tayi farinciki,to ko don hakan ya haqura ,ya rungumi matansa da zuciya 1
Zuwa qarfe biyun rana kuwa ,tun daga kofar gari ake ajiye motoci ana takowa da qafa tamkar idi, saboda Sam bama hanyar wucewar ko keke
Sai bayan da aka idar da sallar jumu'ah sannan limamin jumu'an ya daura auren khalisa da Ahmad ,Yusuf da sudha .bisa umurni da yarjewan mai martaba .....bindigan toka ,dogarai suka shiga saki,wannan ya tabbatar da an d'aura daga nan mutane kowa yashiga kokarin kutsawa don samun abun kai rahoto cikin gari
Kyauta kam Ahmad yayishi kamar mene, duk in da yabi mutanene fans d'insa ke jansa kowa burinsa ya d'auki photo da mai girma shugaban qasa
A tarikhin masarautar azdajarz bata ta6a kar6an mutane a lokaci gudaba kamar haka,daga kowani qusurwa na fad'in duniya ,dukda kasancewar bikin yazo babu shiri ,ko din zumudi da kasancewar sabuntansa na zama shugaban qasa ne ohoooo!...

Umman saudah kam itada sanata baraka suna zaune suna kallon komai live ta TV ,ranta na wani irin suya da tafarfasa ,alwashin tarwatsa wannan couples din kuwa tayi su kala da iri,gidan tsit ko tarin quda bakaji
Don a na damun ta da kwarafniya zakiga ta fito tace ta sallami mai aiki
Gabakuwa take yi da Ahmad jarumi qaqas ,impact tunda ya yi mata albishir din kishiya ta waya har yau basu ga junaba
Tadai siya sabon waya ta saka sim dinta ,shima saboda mutanen tane bawai don shiba,amma ko ya kira bata d'agawa,kuma haduwa ta haramta masu shi.

Kuka ta fashe wa sanata baraka "shikenan ya kashe ni hajiya, ya kashe ni,ya aikawa zuciyata saqonnin bamabamai biyu a lokaci guda ,na fada maki bayasona ,hajiya ya tsaneni"
Shafa bayanta ta ringayi taa rarrashinta tana bata yankin azaban da zata ganawa khalisan in ta shigo ,itakuma saudah ta nuna mata bakomai,tunda duk sonka da Abu sai Allah yayi ,kuma uba shi yikeda iko da d'iyarsa ba itaba
"Hajiya kishi da farida ba qaramar hadari bane a rayuwar baby ,da tasan sirrina muka saba qwaqulan juna, daga baya na gujeta..."
"....mtsew abun kiyi murna ne,kuma ki yardarwa kanki, baki kai 'yarki gidan me kishiyaba ,tunda kinsan duk er mad'igo bata damu da namiji ba,kuma haka zaki kaita baki tsimataba?

Wai inama yarinyar tawa take ,mije daukanta zanyi in barda ita qasarnan a kimtsa mun ita sosai sai dab da tarewa zamu dawo"
Ajiyar zuciya ta saki ,sannan ta mike jiri na dibanta suka haura dakin saudan
A zaune suka tarda ita akan kayanta baje baje akan gado ,littafai anan takardu a can ,laptop anan ,kan gadon bako tsari,bare kuma filin dakin
tunda akayi mata maganar ta daina magana da kowa,ta kashe wayarta,ta daina cin abinci daga ruwa sai lemo
Haurawa gadon sanata barakan tayi tana karkauda komai gefe ,ta kamo kafadarta ta tadata zaune,sai sannan taja wani doguwar ajiyar numfashi,kamar ranta zai fita kuma sai ya dawo
"Momy sun d'auramun aure dashi ko?"
Girgiza mata kai tayi cikin tsananin tausayawa
Haka Al'amura sukaita faruwa a yayinda gimbiya khalisa ta cire duk damuwa ,saboda ganin yanda damuwarta ke Neman affecting mamanta,saidai ta lashi takobi da d'amarar rashin zaman lafiya da Ahmad bayan anyi aure
Da haka gimbiya saratu ta taho qasar da masu gyaran jiki irin na qasarsu ,hakama momy farida(matar PA) ta aiko da mata nijar da zasu had'a gimbiya khalisa har zuwa satin tarewa
Sosai ta cirewa ranta wani zafin kishi akan saudah ,don haka tayi ruwa tai makar6iya dukda khalisa ba a hannu ta takeba ,itace tamkar uwa kullum tana zarya tsakanin Dubai ,jiddah zuwa Nigeria,had saida taga komai na d'iyarta ya zama to d pick ,daidai nunawa tsara naira kam yayi kuka a sashen khalisah don kaya ta 6angaren PA kawai to bacin gidane mai part da yawa da an rasa wajen zubawa,bare gana gayya uban tafiya mai martaba
Don dole sashen baqi aka hadewa khalisat inkikaga falukanta tamkar fadojin sarauta.
Chapter 9 · 0% Book details