← Book details Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'an madaidaicin Akwatin daloli ta umurci wata mata da sukazo tare da ta ajiye a kasan gefen karkashin kafar gimbiya khalisan
"Ga tawa gudunmawar nan babu yawa sannan na dauki nauyin souvenirs na bikin gabad'aya "
Wasu almaran hawayene sukai ma idona flashing"Da gaske kenan aurena da abbah ya tabbata?"
Tsunkayar kuyangina nayi suna zuba ruwan godiya ,itakuma ta mike tana gyara lafayan da ta nad'e jikinta dashi ,da shirin tafiya....bayan ta umurci da a basu bindir biyu na en d'ari biyar biyar su raba,aikuwa godiya kamar su kwanta mata a qasa.

Daga nan muka d'ingumo zuwa farfajiyar ,inda wainnan maroqan suka haukace da kirari muryoyinsu ya qara d'agawa
"Yooo ko yau nakkoma ga ubangiji ban yarba.....eh bamuyarba....ganin magajiyarmu dacene...eh dacene....tauraruwa mai haske ,dariyar ki fitar nairorine ....eh nairorine....sarauta gadonkune,mulki damarkice....qasaita ajininku take ,kyauta daga hannunku ta qare, nasha rawa don murnan kyauta ban ta6a kuka don kyautabaa....eh jaruma sadauki tauraruwa shalele,Allah yaja da yawan raiiiiii..ehhhh " wani ya dad'a d'aga kai zai cigaba da waqeta a hankali ta d'aga masu hannu
D'if kaji kamar mutuwa ta gifta
Kallon matar da suke tare da ita tayi kosassu ajin karshe,kowa ka kalla naira ta tsumata tawagar matar gwamna hajiya karima
"A raba masu kujera goma,motoci goma,da miliyon biyu susha mai"
Wani gigitaccen sowa suka dauka ,gidan ya rikice kasa waqan sukayi kawai sai suka d'auka da cewa
"Yaro nemo tsaranka ,yaro nemo tsaranka"
A take hajiya karima ta tuttulo ido waje,shifa tsiyar zuwa fada kenan duk isarka sai sun sattar maka da gwuiwa,yanzu jiba ta siyanwa kanta girma ni kuma da basu wainnan gagaruman kyautan
Saida ta furzo da wahalallen numfashi kafin ta kalli wannan matar na dazu da ta bada akwatun daloli
A basu kujerun hajji goma,a fitarda miliyon talatin cikin wannnan fund d'in a bada motoci goma ,da miliyon biyar ,tukwuicin kirari wa gimbiya
Zaman en bori marokan sukayi ,saiga shi suna shesheqan kuka ,lallai dole suyi raki,Allah ya kashe ya basu yau sun tako arziki ,gasu ga matar gwamna ga matar shugaban kasa ,kuma hamshakiya magajiyar fada
Murmushin dole gimbiya khalisa tayi ,don sosai taso ganin iyakan hajiya karima don ta lura ita din irin matan nan ne masu dagawa da qaryan arziki,ga shishigi da zulwajahaini,bata San shi fada bayason izzah ba ,a duk inda sikaje girmamawa auke buqata ba kyautar kashe kaiba,saidai bakomai in halin tane zasu had'e a gaba .....
[8/19, 13:35] Bamalli: *JNS*
71-75
Ina zaune dani da kuyangina a babban falon qasan ,a zuwa yanzu na mallake falon ya zama wajen fadancina ,inkin ganni a sashena to barci yakaini,don ko sallah anan Nikeyi da cin abinci,gashi duk na siye en aikin gidan da kyauta na,har masu aikin gidan haduwa da kuyangina sikeyi aita fadanci da banbadanci,Abu dayane ban jura kawo tsegumi
Kamar ko yaushe ina kishingide akan lallausan tafkeken carpet din falon gabana akushine shashaqe da kayan marmari ,na shimfid'e kafafuwana da sukasha Jan lalle,wannan na matsamun su wannan namun furfita majestically a yayinda sauran ke kewaye dani a zazzaune wata tana bani labarin ban dariya ,nikuwa in anyi abun dariya sun qyalqyale da dariya sai inyi murmushi
Kurum cikin rashin zato sai gata ta shigo dakin cikin takun issah ,ta kalli dukkanmu ta watsar
Kallon sheqeqe tayi mun sannan ,a wulakance tace "tashi...tashi maza kubar nan wajen duk kun ishi mutane da shirme da shiririta bakuba ba shashashar wacce ta tarakuba"
Tsam na mike zaune ,raina na azalzalata
Na dad'e ina shanye damuwar rashin mutuncinta amma nayau yafi na kullum 6atamun rai,ai wannan sai taja su rainani
"A'ah anty tsaya akan 'yan aikin gidan mijinmu,amma ki qetareni da kuyangina"
"Har kenan banzan bazara cikon bencin tarkacen sharan kasuwa,mijinki ko mijina ,mijin da baisan da zaman kiba ,da kwananki da nawa kina kallo zan had'e su zama nawa,ba yanda kika iya saboda dolanci"
Dariyar rainin wayo na bita dashi ,kafin in umurci duk 'yan aikin su fita ,sannan nasa hannuna a baki na dauki ihu "wooowooo,andai aure mata miji wiooooo"
"Ke ni tsararkice?

Bakisan ganin damata bane ,na bari presdo ya aureki,ko ya taimaka ya daga sunan fadanku,dabadin hakanba saidai ki qawarewa ngwandu ,dake qarqashin ikonmu,soooo auren miji daya bashine zarran kwacen mijinba,shashasha"
"Sorry anty ai kinrigada kinyi sake ,don kuwa tamkar yanda ake qwace goruba a hannun yaro haka zan qwace excellency a hannun ki ,idan nayi ra'ayi...

Saidai ina tayaki murna ,kuma inason miki kyakyawar albishir cewar har yanzu excellency baya cikin jerin kalar mazan da na ke so kuma zan iya aura....so plz aje a qarawa boka kud'iiiiiyy..."
Ta fad'a tana ca6e baki,tana naqishe hanci tana girgiza qafa
Ayayinda ummah ta mike ta fiddo mata da duk idanuwarta sannan ta doka mata wani gigitaccen tsawa
"Ke er iska fitsararriya,marar mutumci,karamar ja'ia..."
"Shishhhhh
..." Ta fada sannan ta gyara zamanta ,ta kunbura naman kasan ha6arta,ta d'aura hannu a kasan kwai6i,ta ca6e baki tana daddallaro ido
"...hmmm anty ni kika kira da er iska,bla ...bla...bla ko?

Fine.

Amma tunda nayi maki kara ta hanyar qyale maki miji kin kasa ganewa ko,to zamu canja wasan, saina nuna maki iskanci da salsalolinsu ke kika koyamun ,ni kuma na daura daga kan inda kika tsaya ,nazo na shafeki....zaki ga iskancin akan gadon barcinki ,tsakanin ni da mijinki in bakiyi wasab...."
Da gudu ta taho ta daga hannu zata sharareta da mari.

A daidainan excellency ya turo qofa,a take ya shigo da sauri yina rawar baki "keyyy key...hajiya lafiya kuwa ya mari da girmanki"
Sunkuyar da kai nayi da sauri ina gyara d'aurin ture kaga tsiyar da na turo gaban goshi ,zuwa qasan tuntun gashina...kafin na mike da gudu naje na d'ane bayarsa,na sa hannuna ta wajen qasan mararsa na cukuykuyesa ,ina jin yanda duk jikinsa ya amsa, ha
kan yasani lekowa nayi mata gwalo kafin na fara magana cikin murya irin na sangartattun yara
"Barka da zuwa ubangidana,gatana ,farincikina...abbah gwara da kai gaggawar dawowa,qila da baka dawo da wuri ba da kazo kaga gawar amaryanka"
Na qarasa ina dudulo ido ina huro mata ido cikin izgilanci,sannan na dad'a shafo saman mararsa kamar ban saniba d'innan
A take ya fara rawar murya ,kundai San tsoho a hannun qwaila
"Ahh...ammm...eh tooo, hajiya baki kyautaba,yakamata ki daina kula khalisa ,matsayin 'ya fa take a wajenki fa"
"Aah Ahmad bansan hakafa,in ita ta maida kai hamago Toni bamzama shashasha ba....(daga nan ta waiga ta kalleni tayi qwafa ) tabbas lokaci yayi da zanbi shawarar da kika bani yanzu ,don na lura yanzu kinason zama er hannu ko?"
Lafe kaina nayi akan bayansa ,ina Jan ajiyar zuciyaa kamar ina cikin tsananin tsoro a wajensa ,amma ita saina lumshe ido na Watso mata su,ina nuna mata bayansa Dana kwanta akai
"Shegiya 'yar iska saina yi maganin karuwancinki mu zuba"
Ta juya zata fita....

"Ashsha ashsha ,ya da cin zarafi kuma ,to gaskiya bazan dauki hakanba, ki kiyayeni fa,ni ba mugun miji bane,in ita bazata iya ramawa ba ,zan iya yin hukunci da kai na"
Tsaki tayi kurum ta haura dakinta dondai batada lokacinsu,don tasan zasu iya zaraar da ita,musamman yanda taga idonsa yina shanyewa ,ai ita tasan alamomin tashuwar sha'awar mijinta....
[8/19, 13:35] Bamalli: *JNS 3*
76-80
Ina ganin ta juya na fara kiciniyar janye jikina, saidai tsam ya riqeni
A kunne ya rad'amun "Yau wa na kama?

Kin gama gudun nawa ,wato yau kinga giwar gidan zata zauneki shine kika rugo waje ko?"
Noke kunnena nayi akan kagad'ana yanda naji muryarsa na dukan dodon kunnena yasani jin wani Yarr yamm,readers karkuga laifina ,ni ba ma'asumiya bace I've feelings
Tuno baki nayi "Wallahi nidai ban gudunka ,kawai kewar gida nikeyi da kuma karatuna"
Riqe duk kafad'una yayi sannan ya d'an sakko daidai tsawona ya manna mun kiss a saman le66an da Nike cunowa
Kautar da kaina nayi da sauri ina goge bakina da bayan hannu
"Abbah bari inje sallah"
"Hahhh lokacin sallah baiyiba ,so kije ki huta ,sannan ki jiraceni anjima ,ke ke dani"
Zambad'awa nayi da gudu bayan ya cikani.

Sai da na shige d'akina sannan na qanqame jiki na qwalla qaran murna ,harda er tsalle
Ina tuno yanda Nike hango idanuwar ummah ta cikin glass tana leqenmu
Wohoho Allah ya isana tsakanina da kunyar da ke damu na da wallahi yau sai na kusa haukata umma,na tabbatar na zawwatar da mijinta ganin idonta kamar yanda nayi mata alkawari
Gabana ne yace dam! _"ki shirya yau ke kike dani"_
Me yike nufi?

Wai ni zan kwana a sashen shi yau?
kirane ya shigo wayata Wanda tabbas bansan ko wanene ba saboda baquwar numberne ,amma haka nan naji bazan iya d'aukaba saboda yanda gabana ke bugawa
Saida aka kira kusan sau uku kafin text ya shigo
Cikin sanyin jiki na d'aga
*Na gamsu wa kaina duk yanda zan 6illo don ganin mun samu magana dake bazaki bani goyon bayaba,Aminiyatah don Allah kar kiyi ignoring message dina ,inason in fahimtar dakene cewa ina mugun jin farinciki na kasancewarki cikin family dina ,sannan ina roqonki ki tsaya ki bawa abbahna kula ta musamman fiye da Wanda zakiba saurayinki da kike mugun qauna,domin a halin yanzu abbahna yafi buqatar wannan taimakon...kamar yanda akayi auranki bisa tirsasawa haka nima ,saidai ni ban shiga gidana da makaman yaqinaba ,don haka ina Shiga na fara fafitikar Neman gurbi a zuciyar mijina ,kuma alhmdllh na ga canji tun yanzu ,a halin yanzu ina farinciki da godema Allah da ya bani dadynki a matsayin mijina ,banbi qyalqyal banxaba,Mijina yasan yanda za'a sarrafa mace har tasoshi ,kuma dukda anyi mana auren hadine ,yina bani kula da nake jinjina masa ,finally ina muki albishir da momynki ta zama ta gari kuma ta tungumeni tamkar ke a wajenta,so plz ki maida gidanmu tamkar gidana inkin hakan zaki sanya abbahna farin cikin da baisamu ba a baya ...ngd qawata*
Hawayene ya shiga mun karakaina a kuncina ,bansan ina mugun qaunar dady na ba ,sai yau da naji kishin saudah ya kama ni,lallai dadyna jarumine wajen iya soyayya ni kaina sheda ce,maiyasa ban za6i dady ba ,nayiwa kaina za6en abbah matsayin miji?

Kuka sosai nikeyi na dumbin nadama da tunanin mafita.

Ban jima a kwanceba saiga abbah ya shigo dakin
Yina ganina kwance ya hauro da sauri donjin abunda ke damu na
Kamoni yayi ya d'aura akan cinyarsa yina shafa bayana
"Baby lafiya meke damunki?
Chapter 11 · 0% Book details