← Book details Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lahaula fi shaatul lah ,jakar brief case ya aiko Wata kuyanga dashi ta kawo mata,tana zaune tana yarfe qananu kalban kanta ,tana shaidawa Anty Habiba yanda sukayi ,kurum saiga yarinya da jakar wai yace a kawo mata
Tsaki taja "this is nonsense, waya Fada masa ana siyan soyayya da irin wannan abun,to meye a cikin jakar ya Fada maki?" Girgiza kai tayi
"To maida masa kice Angode"
Dakatar da ita Habiba tayi da hannu ,kafin tace "Ke jeki abinki" ta kar6a ta bud'e
Ja da bata Habiba tayi a tsarace tareda dafe kirji
kudi ne tsaban daloli sababbi katakal shishirye a bandur bandir dinsu ,ciki FAM
Da sauri taje gaban dinning ta suri wayarta ta kira Dr
"Hello Qalby akwai matsala fa..." Katseta yayi "Nima anan akwai matsalar ,da na gani Wanda yafi ko me zaki fad'amun so ki jirani ina zuwa,ki kuma dakatar mun da Khalisah"
"Tom Allah yasa muji alkairi"
"Khalisah kinason wannan baqon da yazo wajenki?"
"Yah me yasa ka tambayeni?".

" Gargadine da hangen nesa,kawai ki Fada min in kinajin 6ir6ishin wani abu a ranki game dashi"
"Eh inaji"
"Ai da gaske?

Har kenan kinsan so?"
Tashi tayi taga kumbure kumbure
"Yah tambaya ta fa kayi" daure fuska yayi
"Khalisah inaso yanzunnan ki blocking number wannan a wayarki ,kuma ki tsamesa a ciki ranki"..

Zaburowa Habiba tayi " Ko e yasa?".

"Habiba mutumin nan ba na gari bane kurum tabi umurnina"
Wasu siraran hawayene suka zubo mata da batasan ko na menene ba,saidai tasan na takaicine,duk saurayin da zatayi sai ace bashida hali
"Shikenan yah na fitar dashi shima a raina ,na kumasan *Wanda ya fishi ma zaizo*" daganan ta zura takalminta zata fita
"Khalisah" cikin murtukakken fuska ta kallesa
"Karkice na rabaki da masoyini,ki sani nine masoyinki na gaskiya ,kuma bazanso ganin abunda zai cutar dakeba....zauna infada maki hujjata da na ke son rabaku da wannan mutumin....da fari sunansa *Adamu salansa* d'an asalin garin qauyen Anchau,ya kasance mai zuwa gida gidan jama'a yina sallama da mazan mutane ,da zaran sun futa wajensa to matansu baza su sake ganin sa ba har Abadan ,kenan *D'an mafiya ne* Na samu rahoton nan ne bayan an kamasa yayi nasaran yankewa wani magidanci mazakutansa,a garin Abj. akayi referring case din asibitina a lokacin mutumin bai mutuba saida ga baya .....

Naso bin case dinsa bansami sarari ba,kinga gashi ynx an sakesa ya dawo cikin Al'uma ransa a kwance yina Neman aure...."
"Allah ya kyauta toh muma kaga sununan kudin da ya kawo mana"
"Hhh to qila nima ya siya nawa abarne
" ya radawa Habiba a hankali yina kashe mata ido
"Ba na ganiba ,barmuna fatan tsiya"Cesar Habiba
"Hmmm to kadai sallamesa ko?" Tambayr khalisah ya dawo d hankalinsu kanta
"Aah inajiran inji amincewarki".

" amincewata?

To in amincewata ne ban yarda ba ,tunda ba abun nawa mijin za a cire ba
A guje yayo kanta ta fice tana masa gwalo
"Hahaha kin ci bashi"
Oum Aphnan
A tayani share Albarkacin so da qauna don Allah
[8/19, 13:32] Bamalli: *JNS*
6-10
Duk abun da ya faru bai dameta ba saida taje kwanciya barci,damuwa ya fara bijiro mata,na yanda duk saurayin da zatayi da nasa kalar damuwar,amma Wanda zai biyo bayansa sai yafi wancan girman matsala,bata manta shu'aib da yazo da qudurin aurenta ya 6arar da nairori a fadan,saida yaja kafatanin ra'ayoyin Al'umman gidan harta mai martaba, saboda simplicity dinsa ga kuma uwa uba kyautansa,shine Wanda in yayiwa bafade kyauta saidai kaga bafade na kuka ya rasa bakin kuzuzutawa ,akansa ne sarki ya fara bada makullin gidan shaqawarsa don gimbiya khalisah suje zance yanda zasufi samun sakin jiki,amma kamar Wanda ya shammaci jama'a ba Wanda ya iya sanin usulinsa ko ya damu da yasani,har sai bikin Anty lubnah kanwar Anty zahra ,lokacin ne zasuje dinner yazo ,anan take shaida mashi ita motar gida zatabi amma ya kafe, sannan suna tare da Saudah itace ta roketa da ta barsa yazo ya kaisu ,inyaso sai ta rakata su tafi tare
A lokacin ne yayi masu kyautar da ya gigitasu ,daloline sababbi katakal masu uban yawa cikin wani abu me kama da drawer a cikin motarsa,haka ya bude ya diba ya baiwa Saudah tayi liki ,yadada diba ya baiwa khalisah, sosai Saudah ta furgita dashi ,kuma a take ta saka masa kwalelen alamar tambaya ,saidai tayi shiru har saida biki ya watse kafin ta tunkari abbanta (VP) da maganar kalar kyautan da saurayin bestynta yayi masu ,kumawai shi haka yike kyautarsa .sosai shima ya tsorata da kudaden da yaga ya basu,ko da suke yaran manya bai kamata ana basu sunanan kudi irin wannan ba,saidai ya 6oye damuwarsa a ransa har sai yayi bincike ,hotonsa ya nemi ta Tura masa aiko ta sa ta turo mata ta WhatsApp ta turo masa ,a take ya fara ciccila hotunan a wajajen binciken masu laifi
Kwal din farko aka bayyana masu sunansa tukur na gaskiya dan asalin garin kogi state ne,yayi aure aure da dama saidai da ya auri mace bata sati uku a gidansa take mutuwa anan zargi ya tashi kodai shidin dan mafiya ne?

Asirinsa bai Tonu ba saida ya auri Wata yarinya er talakawa mai tsananin riko da addini ,kullum azumi da nafila ,tunda ya kusanceta sau daya ranar biki ,ya tafi da ita a jirgi zuwa portakwat da nufin zai aiko da wani jirgin zaa kwashi En uwanta suga matsugunin diyarsu saidai unfortunately to them ,walqiyansu ko labarinsu basu kuma jiba
In ankira wayarta baya tafiya,a hakan ne ya dimbirawa yarinya ciki saidai ya kasa aiwatar da nufinsa na baiwa dodonsa jininta saboda addu'arta saidai yayi nasaran goga mata qanjamau Wanda ya roro garin barikinsa,har Allah ya bata ikon tserewa a gidan shine ta fito wajen En sandan garin tana bada labarinsa amma baa sake jin duriyars ba ,sai a wannan karon da ya 6iullo a gidan sarautar yina nemanta da aure
Hankalin vp kuwa ya tashi haka ya taso ya labartawa mai martaba abunda ke faruwa ,don haka aka rabasu,don an gano auran kyawawan mata yikeyi yina baiwa gunkinsa shikuma yina basa dukiya .

Murginawa gimbiya khalisah ta dad'a yi a gadon tana sharar qwallah a daidai nan messages suka fara karakainan shigowa wayarta ,kamar bazata daukaba saidai na qarshen da bataga sunaba shi yaja ra'ayinta.

A nutse ta bude ta fara karantawa
If I get the opportunity to describe you in a word, it would be life, Yes that is true you are my life!_
_You are my light in darkness,_
_You are the smile in sorrow_,
_I would pleasantly give away_ _everything to be with you tomorrow,_
_I love you! ,have a wonderful Night_
Ur secret crush
Ta maimaita yafi sau uku ta kasa fahimtar komai ,to waye wannan kuma?

Ni yanzu nama fara tsanar duk Wata mu'amala da mutane musammam maza,kife wayar tayi ta janyo pillow ta rungume tana kallon sama ,so takeyi ma tayi tunani amma ta kasa ,kiririm wani saqon ya dad'a shigowa
Nasan dole zan saki d'imuwa da tunanin koni wanene?...karki damu zan fayyace maki anan kurkusa, saidai kullum ni mai sa'a ne banso akanki in zama kishiyar hakan,na tura maki saqo ta WhatsApp in kin bude datanki zaki gani
Tsaki taja zuwa yanzu ta fara jin haushin al'amarin kawai ja bargo tayi ta runtse ido da qarfi saita kora barci yazo ya sureta.

Asubahin farko ta mike cikin muguwar kasala a hakan tayi sallah tana zaune tana lazumi kiran PA ya shigo ,murmushi tayi har yau har kullum tana girma ma babanta "Hello dadynah....ina kwana" "dady yayi fishi da daughter dinsa Sam twinkle dina ta manta dani" "Anya dadynah kana nan cikin raina afuwan ya momyta" "momynki gata a gefena amshi itace tace inkira zakuyi magana"
Sallamartane ya fara mata amsa kuwwa a kunne ,da sauri ta rumtse ido, bazata ta6a manta sanda ta wattakata ba taja mata silar karyewan hannuba.

"Hello daughtern dadynta kina jina?"
"Inajinki momy ina kwana "
A takaice ta amsa kafin ta daura da bata bayanin dalilin kiranta
"Su'adah ta ,magana zamuyi dake ta fahimta ,wallahi wannan maganar da zan maki ,na ratse wlh PA baisan wannan maganar ba...don haka inaso ki natsu muyi magana dake ta kyakyawar fahimta fatan kin fahimce ni"
"Eh ina jinki momy"
"Suada ki ceceni ki ceci dadynki ,ban ta6a kuka akan wani lamari ba yau gani sanye da guiwoyina a qasa ina roqonki ,kinsan munyi rashinki a gidan nan ,kece sayin idanuwarmu sannan har ynx bamu samu wacce ta maye gurbinki ba a zukatanmu musamman mijina dake tsananin kaunarki,saidai iyayenki na asali bazasu bamu keba ,kinga hakan yina nuna kin mana nisa kenan sai gani daga nesa ,a don haka na yanke shawaran rokonki a maimakon mijina ,don Allah su'adah badon ni ba ki auri mijina "
Dam !

Gaban su'adah ya buga, bakinta ya kama rawa ,tayi saurin cire wayarta a kunne ta kalli screen din wayan din ta tabbatar da wa take magana tabbas dai number PA ne
"Momy wallahi banjiki da kyau ba,me kike nufi kenan?"
"Nasan kin fahimce ni su'adah wallahi kullum dadynki bayida lfy kuma soyayyar ki shi kadai ne zai zamar masa warakansa"
Murtsuke ido tayi ,sannan ta bashi zaune
"Hmm Anty Farida kike ko wa?

A gaskiya saidai cutar ta kashe mijinki ,domin kuwa azaban da nasha a sa'ilin xamana dake bani fatan in koma don wannan khalisah take ba su'adah kanwar salah ba,kikayimun za ayi Wanda babu kyau ,don haka ina Baki shawara karki gayyatoni gidanki matsayin kishiya don zamu qona gidanne...."
Da sauri ta datse wayar tana rera wani irin marayan kuka
Ni to yanzu da wanne zanji ga VP ya taso ni a gaba kullum waya ,tsofai tsofai bayi jin kunyar furta mun Kalmar soyayya ,in masa rashin kunya ace nayi butulci,kuma ma bazan iya ba albarkacin besty ,Ni ga samarina ba daya na gari dake zuwa bare inyi wuf daga ciki,kwatsam yau kuma ga Matar PA da gumtun munafurcinta Wanda nasan damacan sharen fage takewa mijinta ,don tuntuni na lura da take takensa ....
Chapter 2 · 0% Book details