← Book details Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 18

Sashe 17

Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sati biyu
Muka wuce yawon shaqatawa qasashe biyar na za6a ,mun kuwa wataya sosai daganan muka sauka a saudiyya mukayi umrah ,aikuwa acan na fara 'yan qananun zazza6i ,gwajin farko akace ciki,oh my god nan gatan duniya ya kara ,saukemun ,na dai barmuku sugar daddy a hannun er qwaila ,haka na zauna muka cigaba da rainon cikinmu ,banda matsalar kewar gida duk muna chart da waya dasu ,don haka koda na warke cemasa nayi ya barni a qasar london atmosphere dinsu yafimun dad'i....itakuwa tafiyarmu dad'i ya dad'a yiwa ummah haka ta saki jiki har kwarata ake kawo mata gida,Nikam a d'ebe d'ebe saida muka kwashe kusan wata shida don ni a gidansa na England na tare ,har dawowa Nigeria yikeyi ya barni acan, inkika ganni na murje nayi fresh nazama damfareriya ina juyawa da qyar ,karatu kam nace tunda na samu certificate din secondary a barni saina haihu yarona yayi qwari.

Mr.president kam shida kansa yaringa terere cikina a dangi kowa kam yayi murna barekuma masarautar mu ,da sukeda qishin yara ,PA kam takanas ya taho shida saudah itama da nata matashin cikin sukazo dubani,naji kunya sosan gaske saboda rabon da mu hadu da saudah tun kafin ayi bikinmu ,wai yau gani da cikin abbanta,saidai kuma mazewa nayi don nima ai cikin dadynah ne a jikin ta
PA yina kirana Anty amarya ,acewarsa aini surukuwarsa ce ,nikuma ina kiransa my big dady ,sunyi kusan sati a London sannan suka koma ,dukda basu so komawa ba sai sanadiyyar ciwon anty farida da yayi tsanani ,dama kuma shine dalilin da ba'azo da ita ba
Sun koma nijeria amma hankali na a tashe yike duk mintoci saina kira su donjin halin da momyna take ciki ,A asibitin da take aiki suka sauka ,saboda nan taje koda batada lafiyar dukda yanzu tayi resigned
Daddadar albishir akayiwa PA cewan wannan kumburin cikin da take fama dashi da fari sun dauka fibroids ne ,cikine saidai yaso yazo da matsala ne amma yanzu komai normal don cikin ya shugarma wata biyar a kowanne lokaci dan cikin zai iya fara motsi
Murna da tsalle kamar zan hauka dajin wannan daddad'an labarin nikam zuwa yanzu ba abunda nikeso ,illah inzo indafa cikin antynah kuma momynah ,cikinda akayi ittifaqin bazata sameshiba ,saidai ganin yanda nima duk na fara tattasawa yasa likitocina sukayi cautioning din excellency kar a barni inbi flight,a dole na hakura saidai an dakko anty rabiyya tazo ta zauna dani ,shikuma excellency hankalinshi na London yina Nigeria
Har saida cikina ya shiga wata bakwai ,a lokacin kuwa gabad'aya cikin a qafa ya zauna mun ko tafiya ban iya yi ,duk d'an uwanda ya kira ni a waya to da kuka zamuyi sallama ,ina roqonsu gafara a cewana na qunshi ajalinane ,tunda yanzu ban iya tafiya saidai Jan jiki ,wanka ban iya dirje jiki na ya fita saidai excellency yayimun ,haka shaving da sauransu ,ga wani baqi da nayi a wajen goshi da wuya na musamman
Duk wannan abun ummah ko a jikin ta bata damu ba ,don ita yanzu shedan ya gama kad'a mata ganga a ka ,to din me ake haihuwar?

Ba don gado bane?

To ya sakar mata komai bata bukatar d'a namiji ma ,ko sha'awarsa balle har tayi sha'awar yara
Sheqe ayarta take yi ,tayi suna sosai a Nigeria har kalar style din wankanta manyan mata ke kwaikwaya ,shikuwa my Romeo ya dawo ya taremun ,dukda sex d'inma andaina ,kuma shima acan Nigeria umman bata yarda ,don haka yazama tamkar sufi, in baya tare dani to yina masallaci yina mun addu'ar rabuwa da cikina lafiya ko allah yasa shima rayuwar mu ta dawo irin Nada ,kujerun hajji kuwa da umrah d'ururu ya bawa malamanmu don kawai suje suyimun addu'ar sauka lafiya ,a gidama haka iyayena ke aikomun da magani sosai kuma nikejin dad'insu ....Asibitine nace kawai mu haqura da zuwa don duk in mukaje aka jagwalgwalani to ranar na me barci ,to menene tindadai anyi booking aiki za ayi mun nanda sati takwas gwara kawai inzauna in jira lokacin.

Nigeria
A davil club dake garin ikko ,excellency ce zaune gefenta wasu irin goggagun kafiran enmatane suna romancing dinta a filin mutane ,itakuma tana buqan shisha ,sun yi nesa cikin masha'arsu saiga wata budurwa da ganinta inyamurace ta nufo inda suke
Akanta ta tsaya ,kafin ta cire tabarau din idonta "Hajiya magana nikeson yi dake"
Cikin tsawa ummah ta hauta da masifa
"Ke !

Bakiganin am busy ne ki jira sai sun gama gamsar dani " ta qare maganar ta tana jawo wata budurwa tana tsotson fatan qasan kunnenta
"Hmmm to karki damu in kin gama ,dama alarting result ne ,na kawo maki nasan inkin bude da wuri zai maki amfani ...na barki lafiya " ta fad'a tana jefa wani qaramun envelope akan tebur din da ta d'aura bututun shishan
Kamar zata share ,sai kuma ta dakatar da ita ,sannan ta yage envelope din ta fara karantawa ,saida takai qarshe sannan ta yaga takardan ta zubar ,sannan ta waigo ta kalleta
"To meye damuwa na anan"?

" bakiga abunda ke ciki bane?"
"Yes nagani,mercy akawu na d'auki da qwayar cutar sida a cikin jininta ,toh kinzone in maki taimako da kudin jinya ,sakamakon quruciyarki Dana Mora a watannin baya ko mene?"
Kallonta tayi tana murmushi
"Humm hajiya kenan,ni tuni nariga na cira rai da rayuwa, tunda a halin yanzu ba HIV bane ke gareni yayi chronic ya zama AIDS ,so am waiting for my corpse ne...kece Nike bawa shawaran kije a gwadaki don kema tabbas kina dashi "
Wani muguwar tsawa ummah ta daka mata "ke ni tsarar kice?

Ta ina zan samu qanjamau ?

Me mukayi dake?

Tsotsan duri ko shan baki?

Ke din namijine da zan samu qanjamau sanadiyyar ki?"
Dariyar raini tai mata "Hajiya karki maida kanki daqiqiya ,ina tabbatar maki kin kamu da qanjamau wata kusan hudu baya tun had'uwarmu...."
Ai bata qarasaba tayi mata wani irin mugun shaqa ,sannan ta kafa qumbunar robanta a murfin maqoshinta ,a take jini ya fara tsatsafo mata ,kiciniyar kwatar kanta tayi ta kasa kurum ta miqa hannunta akan wani tebur dake d'auke da kwalaban giya ,ta rarumi d'aya ta buga da teburin a take ya fashe ruwan giyar ya watse, wani qarfine ya zo mata daidai lokacin da taji ummah na cewa
"Gwara inga gawarki tunda na lura abokin mutuwa kike nema ,kafin kiyi mun sharri kija mijina ya rabu daniiiii..."
Burum!!! ta nitsa mata fasashen kwalban a ta bayanta Wanda saida ya nitsa cikinta,wani razananniyar qara suka saki,ita mercy ta zube a sume, itakuma ummah ta fad'i nan raiga hannun allah wani irin jini ya fara gangara kamar an yanka sa
Tsorone ya kama en wajen kowa ya fara arcewa ,sai wasu mutanene suka kira polis ana zuwa aka taras ummah har ta cika ,haka aka kinkimi gawarta had'e da mercy Wanda duka ya farfad'o da ita ,cell aka wuce da ita itakuma ummah aka sakata a ambulance, zuwa babbar asibitin Lagos
Tuni labarin ya fantsamu a duniya ,Saudah dake zaune da anty farida suna shan fruit ,suna ta6a ,hira tana shaidawa anty farida wai duk jikinta a mace yike ga gabanta dake yawan fad'uwa ,bata yanki tayi da haka mata ke tsintar Kansu a ciki in cikinsu yakai wata bakwai haka,"to ai ke anty gashi har cikinki yakai na Tara bakiji hakan ba" "in naji ai bazan fad'a makiba saudah saboda ni babbah ce" PA ne ya turo qofa yina yakace zufa,yina addu'ar allah yasa basuga abunda yake gani yanzu a labarai ba.

A tsorace suka miqe kowa da tsireren ciki "lafiya" sambatu ya farayi "bakomai ina zuwa " kurum sai ya fita waje yina nanata innalillahi...da qyar aka tausheshi ya dawo ya saka kaya securities suka wuce dashi airport zuwa Lagos
Ha'ahhh hankalinsu bai gama tashi ba saida sukaga dangin saudah suna tittid'owa gidanta ,ana ke6e anty farida ganin ita saudan bata saniba ana bawa anty faridan haquri darokonta ta tsareta tunda tanada ciki, cikin kuka anty farida take nanata "dolena tunda yanzu saudah ta rasa mahaifiyarta nice zan zama bangonta allah sarki allah ya jik'ankiii...."
Qaran fad'uwar saudah ya ankaran dasu da sauri aka kwasheta sai near by asibiti, tun kafin sukai ta fara bleeding don haka ,ana zuwa d'akin tiyata aka wuce da ita don fidda bakwainin cikinta don ceton ransa, saidai inah bai fito daraiba ,sakamakon amniotic fluid dinda ya dad'e da tsiyayewa kafin jinin ya 6alle
Excellency hankalinsa yakai qarshe wajen tashi a ranar da yamma ya dirku a Nigeria a can azdajarz akayi jana'izarta ,saidai shi abunda ke basa mamaki ,mai yakai ummah club har fad'a ya had'asu da arniya ta Burma mata kwalban giya ta mutu?

Wannan tambayar a bakin yarinyar kadai zai samesu ,saidai bayan kwana uku aka je cell don a fidda mercy aka taras itama tayi mushe ,sanadin hadiyar guba da tayi, saboda tsoron hukuncin da zata kar6a sakamakon kashe matar shugaban kasa da ta yi.

Duk bidirin nan saida saudah ta kwana bakwai sannan ta farfad'o ,shikenan na rasa uwa na rasa d'an cikina ,Allahu Akbar allah ka musanyamun da d'an da na rasa ,ka kuma jiqan ki mahaifiyata....shesheka ta cigaba dayi, excellency na Mirza hannunta yina tofeta da add'ah
A hankali ta bud'e ido akan abbah ta saukesu
"Abbah dagaske shikenan na rasa ummahta rasawa na har Abadan?
Chapter 17 · 0% Book details