← Book details Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 18

Sashe 1

Jinin Sarauta Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
[8/19, 13:32] Bamalli: *
JININ SARAUTA
_Buk 3_
Oum Aphnan
Page 1-5
*Alheri Writers Asso.*
_Bismillahir rahmanir Rahim_
Zaune take a kan stool din dressing mirror tana qara gyara zaman d'aurin dankwalin kanta na wani nannauyan tsadadden leshi da kudinsa sun haura 250k ,tana cikin maqala dan kunnen fashion dinta na silver ,kalar kwalliyar les din saiga kuyanga zubaina ta turo qofa,bakinta na rawa ta soma koro ma gimbiya khalisah zance bayan ta gurfana a qasa cikin tsananin firgici.

"Ranki shi dad'e, yanzun nan mahaifiyar Deen ta bar gidan nan,ta sami mai martaba ,tanata kuka wai a raba d'anta dake, wai yaronta ba ruwansa amma saboda azaban son da yike gwada maki ,ya kaisa da soma yi mata sata ,kama daga gwalagwalanta,manyan gidajenta da sauransu yina saidawa don kawai yayi maki hidima ko zaki soshi..."
Kallon kanta tayi a madubi,ta d'an jujjuya jikinta,kafin ta dauki gira brush,ta Dad'a gyara cikakken giranta,tana wani murmusawa har haqorin gwal dinta na fitowa yina dad'a qara mata wani sihirtaccen kyau da aji .

Saida ta tabbatar kuyangar ta amayar da duk kalamanta kafin ta mike a qasaitance ,ta dauki turare tana yiwa kanta wanka dashi
A hankali ta tako gabanta cikin takalminta half cover silver colour,sauke idonta kuyangar tayi akan takalmin har yanxu jikinta na rawa don tana tausayawa gimbuya khalisat saboda tsananin son da take gwadawa Deen
"Oh kenan mamarsa ta gwada kishinta a kaina ko?

Har take claiming ni na 6ata mata yaro....karki damu *Wanda ya fishi ne zaizo*"
Dago ido da sauri tayi don ta ga sirrin fuskarta don duk zatonta kuka zata fashe da shi,amma a sa6anin hakan,sai kurum taga ta taqarqare tana selfie fuskarta fal nishadi.

Tsam ta miqe ta fita cikin tsananin mamaki,anya gimbiya khalisah batada Aljanu kuwa?

Wannan fa na uku kenan.

Daga Fada airport suka wuce don d'auko Dr Khalid da Matarsa Habiba da suke shirin sauka a wannan lokacin.

Sun isa jirginsu bata samu qarasowa ba,a don hakan ta umurci driver daya budeta tanaso zata dan miqe qafa kad'an
A nutse take tafiya barorinta biyu suna take mata baya cikin atamfarsu da mayafi iri d'aya, wani snacks and ice cream joint ta gani mai kyau well decorated
A nishadance ta qarasa wajen kafin ta sami waje ta kame,qarqashin wani laima mai kyau da kujeru biyu da tebur a tsakiya ,sukuma barorin sukayi tsaye a kanta ta baya.

Er qaramar Jakarta ta ajiye akan tebur din ta zaro chocolate dinta daga jakar ta soma gutsura a hankali tana motsa dan ficilin bakinta dake walainiyar lip balm,tana taunawa,hannunta riqe da rafkeken wayarta tana game tana d'an murmushi..

Can kamar an tsikareta ta kalli daya daga cikin kuyangin nata
"Ke jekice a kawo mana roba uku, musha in da dad'i inyi guzurin na gida"
Rankwafawa tayi kamar me shirin yin ruku'u sannan ta wuce ciki.

Itakuma gimbiya khalisah ta cigaba da shafa wayarta fuskarta da d'an murmushi
*Attahir* dake zaune tun shigowarsu ya Lula duniyarta,komai nata na fuzgarsa ne ya mike da nufin qarasowa inda take.

Guards dinsa da suka kasance cikin Ash din kwat ne suka dafe masa baya da nufin su biyosa.

Da sauri ya dakatar dasu ,sannan ya makala tabarau din fuskarsa ya gyara zaman suit dinsa ya qaraso a hankali inda suke
"Barka da hutawa manyan mata" kallon uku saura kwata tayi masa kafin ta maida hankalinta kan wayarta
"Barka"
Tace a gimtse
Murmusawa yayi ,sai yaji tama Dad'a burgesa
"Allah yasa bazanyi laifi ba inna maye gurbin wajen nan da babu kowa a kai"
Wannan karon saida ta yamutse fuska kafin tayi masa nuni da wayarta ,alamar zai iya zama
A qasaitance ya ja kujeran ya zauna "Nagode mai kyau".

Walai tayi masa da ido ,sannan ta Dan karkace le6enta na sama
" really?

"Karki cemun ba'a ta6a Fada maki cewa kedin kyakyawa bace ba"
Murmushi tayi tareda dafe kai ,a duniya tanaso ace mata kyakyawa kai a madai zuzutata ko a yabeta
"Ko naji,ai dai dole in yaba Wanda yafito daga bakin Wanda ban wayesa ba"
"Nagode da kika tinasar dani kuskurena ,am sorry ,da fari sunana Attahir Ishaq jingim ,ni mazaunin plateau ne,sannan ni dan kasuwane dawowata kenan daga qasar China ,inajiran jirgin da zai wuce dani gida plateau...sai kuma kwatsam daga sama Allah ya kawo min kyautar kyakyawa"
Muskutawa tayi a hankali ,ta lankwashe bakin ledar chocolate din hannunta ta rufe tareda mikawa kuyangar dake kanta"Ina buqatar ruwa"
Rankwafawa tayi kafin ta tafi amso mata ruwa,ba qishi takejiba tayi hakan ne don su ke6e da Attahir
"Barka da zuwa sir,Attahir "
"Kefa ya sunan gimbiyar tawa?"
"Correct
sunana gimbiya khalisah magajiyar masarautar wannan yankin"
"Fatan zamu zama abokai "
"U welcome"
Sukayi musayen contacts ,aka kawo masu ice creams dasu Snacks, debit card dinta ta mika mata da nufin a cire kudin
"Ance wancan mutumin ya biya mana ko me zamu siya "
Ca6e baki tayi
"En asara a haka nemanku ke qare anga kyakyawa" ta mike suka bar wajen
Suna qarasawa jirginsu Dr.na sauka, yina sakkowa sa6e da little diyanah da ita ya fara tozali.

Aikuwa nan fara'arsa ta ninku,ya ringa keto mutane bai kallon masu masa Barka da zuwa saida ya nufo gabanta
Dage kanta sama tayi tana kallonsa qerere akanta ya zama wani rusheshe ga tsawo ga qiba...xaman Spain ya chanja sa entirely
Cuno baki tayi cikin sigar shagwa6a ta mika hannu don ta kar6a lukutan babyn hannunsa
Qyar ya kafeta da ido yina kalon yanda ta cika ta batse,Ashe duk kallon da yike mata a photo raihune ,ji yanda ta zama Wata babbar mace
"Zamu fara fad'an ne daga zuwata ko d'an oyoyon nan bazan samu ba?"
Noke kafada tayi kamar Wata small baby
"Uhm uhm,bayan....bayan da zanzo in rungumeka ne in Fada maka how much nayi missing dinka sai naga ka zama wurtumemen wulli gaskiya kaimun girma ,ni bani little dinmu" leqa ta bayansa tayi ta kalli Anty Habiba
"...Anty me kike ba wannan bujumin ,baya damunki da nauyi"
Dariya ta fashe da shi ,ta zo ta rungume ta "Mai zaisa ya dameni er kwanwata ji shifa cas dashi kalan yayi"
Huro hanci tayi
"Ahhh
da wannan tumbin,gaskiya matan aure kuna fama ,nifa shiyasa banson auren mai kiba"
Lakuce mata hanci yayi ,yaji xancenta zai sauka akan layi a waje,lallai girma ba hankali
"Hmmm to sannu sai ki nuna mana bolanmu"
Dariya tayi ta kar6e little sannan suka rankaya wajen motocinsu fadawa na masu barka da qarasowa.

Attahir kam ya gigice a soyayyar khalisaht don haka fasa tafiya yayi ,ya shiga cikin gari ya kama hotels gwara ya nemeta da zafi zafi,tun kafin ya tsaya sanya ayi wuf da ita
_*Jinin sarauta* bana kyauta bane,ki biya kudinki kalilan ki kwashi labarinki,just #200 via this account 7782217014,Mohammed Hassana ,Fcmb ko ta wannan layin Mtn 09065990265 don Allah a bar fitar da shi,kema sis ko an fitar ki rintse idonki karki karanta ki biyo ki siya na halal,nagode makarata da masoyana Wanda suka biya suka karanta damasu na er sibare ,nasan duk cikin kaunace still nima inasonku_
A sassan Dr.Khalil yau zir gimbiya khalisah ta yini,suna tareda Matar Khalil tana koya mata salo salo na kula da miji,tare sukayi girkin dare,bayan sun hadu a sashen nannah sunci abincin tarban baqi duka,shine ta roki abarta zat iya na dare in sun huta, itace ta tayata shirya baby,sukuma kuyangi suka gyara abubuwan da aka 6ata...kira kam a waya Attahir baya had'a awa d'aya ,tun tana daukar abun wasa har ta fara gajiya tahau qorafi ,Habiba kam sai dariya take mata.

A ranar kuwa bayan magriba tana zaune tana add'ua gefenta wayarta ne,so take in tayi isha'i barorinta suzo ,su rakata cikin gida...wayarta ne ya fara 6urari,tsaki taja ,ta danna abun gefe saman power bottom nan ya daina ringing ta cigaba da abunda takeyi
Yina yankewa ta kuma shigowa
A fadace ta d'auka "Haba wannan wani irin bala'ine Ibadan ma baza'a barka kayi ba ,wannan wani irin mutum ne ?

Anya yamayi nasa sallahn kuwa?"
Dariya Dr.

Khalil yayi ,ya kasheta da ido, sosai yikejin dadin yanda take qorafi akan samarinta ,symbolize basa kanta
"To kidauka mana kin San kowa da kalar soyayyansa".

" Allah ya ,ya isheni ne"
A lokacin kira na uku ta shigo
"Hello Assalamu alaikum ya akayi kuma?"
"Sorry gimbiyata Allah yasa ba barci gimbiyata ta soma ba"
Waro ido tayi kamar yina kallonta,a ranta tana ayyana anya wannan yasan addininsa kuwa
Amma saita kanne "Barci kuma ?

A yanzu bayan magriba".

" oh yes yes,to gadai baqon naki a daga wajen Fada yina bukatar ayi masa iso zuwa ciki ,Allah yasa gimbiyar tanada lokacina"
Kautar da wayar tayi a kunnenta ta ja siririn tsaki ,tareda babbanka ma wayar Harara
"Hmmm y not,barkanku da zuwa ,bara insa a shigo dakai" ta katse wayar tana kallon Dr.Khalid
"Ya nayi baqo ,bari in wuce gida"
Cikin tsananin kishi "No!

Yazo nan,Sitting room dina,sannan in kun gama inason ganinsa"
_My sister ba lallai ki iya gane inda labarin ta sa gababa,zaifi miki dauki ki biyo wannan Layin 09965990265 don jin samin farhinsa da samun na daya zuwa na biyun a sassauqan farashi_
A Wata hatsabibiyar mota ya cunno kanta cikin doguwar hanyar da zai sadaka da sashen Dr.kafatanin fadawan da masu tsaron qofar sun gigita da ganin motar,amma duk zatonsu wajen Dr yazo,ma'ana baqon sane
Sosai akayi masa tarba mai kyau,saidai hira sama sama sukayi aka kira isha'i
"Yayanah yinason kuga juna,so,in kaje sallah zan Fada masa sai Ku hade kaga va sai na sake fitowa ba"
"Kina nufin kin gaji da ganina, duk zumudinki da na yi"...

" sallah a jam'i bata wajabta a kaina ba,amma kai ta hauka ,kenn zan iya samun rabon zunubi kuma ban kyautawa soyayyah ba in na bari ka rasa jam'i"
"Shiknn in na gama zan dawo".

" a'ah fa ,ni ina sallah lokacin barcina ya shiga,ammm muyi waya gobe inshaallh ...bye"
Dole yaja sahu ya fita yina taune le6e zaki shigo hannune yarinya.
Chapter 1 · 0% Book details