← Book details Jinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 27

CHAPTER 8

Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Gidan bahaushe, gida ne da zaka tarar da mace fiye da daya wato kishiyoyi. Kishiya kalma ce dake girgiza da yawan mata. Hada miji da wata matar, ko kuma ma wasu matan, hakan ba kowacce mace bace keda wannan jarumtar. Wadansu suna kallon haka a matsayin cin amana daga mazajensu idan suka ce zasu kara aure wanda har ta kaisu ga sun nemi saki. A wannan lokacin ma da muke ciki wasu matan kawo karshen rayuwarsu suke ko na mazajensu. A wajensu kishi wani abu ne da bai dace ya wanzu ba a duniya.

Sai dai a wajen wasu matan ba haka bane, koda za'a auresu suna sakawa a ransu "namiji mijin mace hudu" ne dole wata rana mazajensu su kara aure.

Zaman kishi yana iya zuwa da matsaloli, makirce-makirce, surkulle... kamar yanda zai iya zuwa gidan ya zama wani babban ahali, kishiyoyi su hade kansu, su zauna cikin kwanciyar hankali...
Bangaren Malan Shehu baban Dauda yayi sa'ar samun mata da suka kawata masa gida da kwanciyar hankali, kuma shima yana yin adalci a tsakanin matan, a wurin matan ya kasance miji na kwarai. Sai dai matsalar tana wurin 'yan'yanshi ne, ba kamar mazan, dan ya gaza a matsayinsa na uba. Kuma hakan ta fara faruwa ne, wata rana lokacin Dauda yana cikin mahaifiyarshi, ziyara suka samu ta wani abokin mahaifin Dauda, mutumin babban malami ne, wanda yayi kaurin suna wajen warkar da cututtuka da yin duba. A ranar da malamin yazo yayi ta kallon mamar Dauda kafin yace
«Wannan yaron da yake cikinki, shi zai zamo arzikin wannan ahali, yana tafe da alkhairai masu yawa, zai zamo yaro mai farin jini, ki kula dashi kamar tilon kwan kazar da ya rage a duniya.» Wadannan kalaman da ya fada, su suka yi tasiri a kunnuwan kowa dake kauyen, kowa a kauyen ya yarda da maganar malamin.

Lokacin da aka haifi Dauda, malan Shehu ya samu wannan masana'antar da tayi sanadin daukaka ahalin aka sansu kowanne lungu a kauyuka. Nan fa kowa ya kara gasgata maganar malam ana fadin "lallai wannan yaron da sa'a yake tafe." Daga ranar Malan Shehu ya dauki son duniya ya dorawa Dauda, ya fifitashi kan sauran ya'yanshi. Matan sun fahimci fifikon da yake nuna ma Dauda amma basu saka komai a ransu ba, dan sun san dagaske Dauda alheri ne garesu tinda gashi yayi sanadin arzikinsu. Sai dai ga yaran wani abu ne daban, Idrisa da Isa da suka kasance diyan fari a gidan suka dauki karan tsana suka dorawa kaninsu Dauda, gani suke uban kamar ya daina sonsu tinda aka haifi Dauda. Shi kuma Dauda natsuwarshi da kyawawan halayensa suka sa yake da farin jini ga sauran mutanen gidan da ma kauyen baki daya. Kiyayyar dake tsakanin yan uwan gashi yanzu tayi sanadin mutuwar Idrisa da Isa, Dauda kuma kwance cikin jini rai a hannun Allah.

Jinah zaunawa tayi kusa da mijinta jiki na mata rawar tsoro, tallabo kanshi tayi da sauri ta mayar dashi ta kwantar ganin yanda jini ya wanke mata hannuwa, ta saki wani razanannen ihu, ihun da ya yayi sanadin fito da wasu daga cikin yan gidan.

Mahaifiyar Dauda ce ta fara shigowa dakin, daskarewa tayi waje daya ganin abinda ke faruwa, kafafuwanta kasa daukanta suka yi da rarrafe ta karasa wajen danta, kuka ta fara tana kiran sunan Dauda. Wata razananniyar kara tare da jan Innalillahi wa inna ilaihi raji'un suka ji a bayan su, Malan Shehu ne ganin danshi mafi soyuwa a wajenshi kwance cikin jini ya saki kara tareda faduwa kasa. Sauran mutanen gidan dake biye dashi suka yi kanshi, suka ciccibeshi zuwa dakinshi kafin su dawo dakin Jinah. Lokacin da mutanen suka lura da Isa kwance, daya daga ciki ya tabashi yaji baya numfashi tuni ya mutu, umarni yayi da kar a bar mahaifiyar Isa din ta shigo dakin, mutuwar 'ya'ya biyu a rana daya, kwalwarta ba zata iya dauka ba, amma kuma ko ba dade ko ba jima dole ta sani. Kawun Dauda, koda ya taba Dauda yaji yana numfashi yace a daukeshi zuwa wajen makocinsu mai magani.

-Yana numfashi!

Kawun ya fada, wata nauyayyiyar ajiyar zuciya Jinah da Mahifiyar Dauda suka sauke a tare. Lokacin da aka tambayi Jinah abinda ya faru, kasa cewa komai tayi sai hawaye da take, dan ba zata iya jure tuna abinda ya faru ba a cikin kanta, ba kamar idan ta tuna itama saura kiris ta mutu sai tsoro ya kara shigarta, sai dai tsoronta yayi yawa akan halin da mijinta yake ciki. addu'a ta fara Allah ya tashi kafadun Dauda. Kamar daga sama Kanwar Isa ta fado dakin lokacin har an dauke Dauda zuwa wajen mai magani, ganin jini a malale ga kuma gawar dan uwanta kwance, kara ta saki, ta fita a guje zuwa dakin mahaifiyarsu, sauran yan dakin da basu san meke faruwa ba suka dugunzuma dakin Jinah dan gane ma idonsu. Tashin hankali ne shimfide a fuskokinsu ba kamar Habi mahaifiyar Isa, mutuwar 'ya'yanta biyu maza wadanda take tunanin zame mata madafa a kingin rayuwar da zata yi gaba. Habi taci kuka har ta godema Allah, neman mijinta ta shiga yi bata ganshi ba, dakinsa ta nufa da shigarta ba'a fi mintuna biyar ba ta fito tareda kecewa da wata mahaukaciyar dariya da ta jawo hankalin yan gidan. Ganin abinda ke faruwa mahaifiyar Dauda da gudunta ta nufi dakin mijin nasu, tarar dashi tayi rai yayi halinsa, sai dai ita ba kamar Habi ba fitowa tayi tana jimamin rashin mijinsu. Wannan ba abu bane da ahalin zasu iya jurewa ba. Kafin kace me gida ya cika da mutane da koke-koken mata. Sai bayan wasu awanni mutane suka farga da dariyar da Habi take, mutuwar 'ya'yanta biyu da kuma ta mijinsu ya haddasa mata tabin kwakwalwa.
Mahaifiyar Dauda fita tayi daga gidan, itama hankalinta a tashe na mutuwar mijinsu, abin kaunarta, mahaifin ya'yanta. Duk da tasan irin wannan ranar zata zo, sai dai bata shiryawa hakan ba, haka ma mutuwar ya'yan kishiyarta ta tabata, yaran da suka tashi a gabanta, tana son yaran duk da diyan kishiyarta ne. Ga kuma danta Dauda kwance rai hannun Allah. Gidan mai maganin ta nufa ta tarar da Dauda kwance, komawa tayi kusan kanshi tana kuka.

Jinah kuwa a tsakiyar gida ta samu wuri ta rakube, tana kallon matan gidan sai rizgar kuka suke. Kukan da Jinah taci da hawayen da ta zubar yasa idanunta yanzu suka kafe babu alamar hawaye tana son yin kuka amma ta kasa. A cikin kanta kuwa tunani take yi, tana yiwa kanta tambayoyin abubuwan da suke faruwa wanda ta kasa samun amsarsu, alhali ita ya kamata a yiwa wadannan tambayoyin ta bayar da amsarsu, domin itace komai ya faru gabanta.

Bayan wani dan lokaci, Jinah taji kamar ana kallonta, dagowa tayi taga daruruwan idanu a kanta. "Me nayi kuma?" tambayar da ta fara zo mata a kwanya kenan.

-Itace, komai ya faru ne sanadinta, muna zaune lafiya kafin zuwanta, babu wata masifa irin wannan da ta konkwasa mana kofa.

Wata 'yar uwar Dauda ce ke fadar haka tana nunen Jinah da yatsa.

-Kwarai kuwa, ya za'a yi ace Isa ya mutu a dakinta kuma Dauda gashi cen rai a hannun Allah.

Wata daga cikin yan uwan Daudan ta kara da hakan.

-Wai ya aka yi kuka zama kamar makafi, baku ga yanda take kama da aljanu ba. Mayya mai cin kurwar maza.

cewar wata makociyarsu.

-Ina yawan ganinta a mafarki, duk lokacin da naso fada sai wani abu ya tokare min makoshi.

Cewar wata yar uwan Dauda.

-Rannan a tsakiyar dare na ganta tana magana da wani kare...

Nan fa kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa na yiwa Jinah sharrin maita. Ita kuma Jinah ji tayi kamar tana gaban tv, dan binsu kawai take da idanu. Bata ko taba ganin da yawa daga cikin matan ba, amma gasu sai bada shedarta suke yi akan mayya ce kamar sun santa.

Kuma hakane a duniyar nan tamu a yanzu, mutane suna jin dadin nuni da yatsa, yanke hukunci ba tareda sani ba, wato yiwa mutum sharri.

Jinah bata ankara ba, taga matan sun yo kanta, wasu na kara daure zani, wasu kuma da makami irin su tabarya, itace, ludayin miya. Jinah kasa motsawa tayi dan razanar ganin wannan al'amari da yake shirin faruwa da ita. Matan na karasowa gareta, da sauri ta runtse ido tana jiran saukar duka a jikinta. Har wani dan lokaci ya shude shuru bata ji saukar dukan ba, kuma bata jin muryoyin matan, kamar ma nesa da ita suke. A hankali ta bude idonta, mamaki abin ya bata ganin kamar an tara al'amarin zuwa baya. Abun kamar ya faru mintuna goma baya (time travel). Wani makahon mari ta yiwa kanta, ta mitsiki kanta wai ko mafarki take amma kuma zahiri ne ba mafarki ba. Ganin komai tayi yana faruwa kamar a baya, sai dai lokacin da matan suke ta fadar maganganu a kanta ne aka cire a lokacin. Matan ko kallonta ma basu yi ba, bare kuma suyi mata magana. Tunani ta fara ko dai ta fara haukacewa ne, da sauri ta mike ta nufi dakinta, ji tayi ta fada kan gado, sannan ta fara wani nauyayyen bacci da bai wuce mintuna kalilan ba.

Kiyi hakuri Jinah, na kasa cika alkawarina na kula dake da na daukarwa mahaifiyarki, babu yanda zanyi, nima tawa tazo karshe. Ki bar wannan gidan Jinah, kiyi nesa dashi, ba zan iya kareki ba... Ki gudu! ki gudu Jianh!

Jin wannan kalaman cikin baccinta, Da sauri Jinah ta farka tana zufa, zuciyarta na dukan uku uku. "Me hakan ke nufi? Wayyo Allah me yake shirin faruwa dani?" tambayoyin da Jinah ke ta maimaitawa cikin tsoro. Tana cikin wannan halin taji wani mugun ciwon ciki ya turnuketa, wata yar karamar karar wahala ta saki, sai kuma ta fashe da kuka... Gashi ta kasa sauka daga kan gadon.

Bayan tsawon lokaci da Jinah ta dauka cikin wannan matsanancin ciwo, cikinta ta gani yana kara girma, ta fara kurma ihun wahala, ji tayi a tsakanin kafafunta kamar zai kama da wuta tsabar azaba. Bayan dan lokaci kafafuwanta suka bude, saka yatsunta tayi a cikin katifa, ta cije labbanta na kasa, ta runtse idanunta. Lokacin da ta bude taga jariri ya fito daga cikinta, kara runtse idanu tayi, tana budewa taga wani ya kara fitowa.

"Wannan wanne irin mummunan mafarki ne nake yi?" Ta fada cike da tsoro tana kallon halittun dake gabanta.

---------------------------------

Fatan dai wannan chapter zata kayatar daku? Zaku yi saurin samun cigaba ne, idan naga adadin comments yafi na ko yaushe 🙁

My watty : @El_Ashtar
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story
Chapter 8 · 0% Book details