CHAPTER 21
Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Esperanza, ban sani ba ko kun taba jin wannan sunan, duk da ba suna bane na hausawa, amma masu karance karance da kuma kallon fina finan kasar Italia ko na kasar Spain ba zasu rasa jin wannan sunan ba. Akwai mutanen wannan kasashen da dama dake da irin wannan sunan Esperanza, wanda a hausance zamu iya bashi ma'anar "Sa rai". Wannan kalmar Sa rai, tana karawa mutum karfin gwiwar rayuwa, muji mun kaunaci mu rayu, sa ran cigaba da al'amuranmu na yau da kullum, da sa ran jiran gobe mai kyau. Dan haka komai yanda yau taki yimana dadi, mu sa ran gobe zata zo da dadi. Wannan kalmar tayi tasiri sosai a gun yan tagwaye, yanda basu fidda ran ganin samun lafiyar iyayensu ba, yau gashi cikin ikon Allah sun gani.
Aya da Ayu ne kwance kusa da mahaifiyarsu, tana shafa sumar kansu. Farin ciki ne marar misaltuwa akan fuskokinsu, tunda Jinah ta farfado suke like da ita ta yanda basu ma yi kokarin sanar da sauran yan gidan ba. Ganin abun nasu ba mai karewa bane, Jinah tace masu suje su kira Sarah, babu wanda ya motsa cikinsu, kowanne jiran dan uwanshi yaje yake. Jinah cewa tayi Ayu yaje, ba tare da yana so ba ya tashi zuwa aiken.
-Sarah, Abdul, Nafi! Mama ta tashi!
Yana fadar haka ya juya da gudu ya koma wajen mamarshi. Sarah sakin kwaryar dake hannunta tayi, kwaryar kuwa ta fashe abinda ke ciki ya watse kasa. Ko rige rigen shiga suka yi ita da 'ya'yan nata zuwa dakin Jinah.
-Alhamdulillahi!
Abinda suke ta firtawa kenan tsananin murna. Babu wanda ya iya tambayar ta yaya aka yi ta warke, ko ta yaya gashin Jinah ya sake fitowa wanda hakan aikin yan tagwaye ne. Dawowarta a Jinah da suka sani shi kadai ma ya ishesu.
Sarah da Nafisa har da kukan murna suka yi, shi kuwa Abdul rungume Jinah yayi kamar ba zai saketa ba. Suna ganin wannan wani ikon Allah ne.
Shuru dakin yayi na wani lokaci kafin Sarah tace :
-Abdul, ka raki yar uwarka kasuwa ta siyo wani abun da za'a gyarawa Jinah nasan dole tana jin yunwa.
Ta fada tana mikawa Nafisa Jika biyar (5000fcfa).
-Yanzu kuwa Aunty!
Nafisa ta fada da hanzarinta na son zuwa kasuwar. Fita tayi Abdul yabi bayanta.
Bayan Tafiyarsu Jinah ta fara kuka.
-Ki daina kuka mama.
Cewar Aya.
-Kiyi shuru Jinah, ki daina kuka! Sarah ta fada.
-Na tuna komai Sarah, komai ya dawo min. Yarintata, dangina komai...
Rungumeta Sarah tayi tana cewa :
-Kiyi hakuri komai zai wuce, yanzu dai ya kamata ki kwanta ki huta.
-Ba zan iya ba, ba zan iya ba Sarah!
Take ta maimaitawa tana kuka, abubuwa da yawa ke ta dawo mata. Tana cikin farin ciki amma tunawa da rayuwarta ta baya ne ya sanyata kuka ba kamar ranar da ta rabu da dangin nata. Abinda yafi daga mata hankali shine rashin sanin halin da iyayenta suke. Yan tagwaye sun fahimci halin da mahaifiyar tasu take ciki, shi yasa da Sarah tayi masu tayin su fita su bar mamarsu ta dan huta yasa basu yi musu ba.
Tana zaune ita kadai cikin daki, tun daga nesa take iya juyo alamun zuwan Fally, rarraba ido ta fara ko zata ganshi, ba bata lokaci sai gashi ya bayyana kusa da ita. Duk da ya canja hakan bai hana ta kasa ganeshi ba.
-Fally! Tsalle tayi ta fada kanshi. Shima cike da murna yace :
-Jinah! Masoyiyata! Nayi tunanin na mutu, ba zan sake ganinki ba, ba zamu taba dawo da soyayyarmu ba. Nayi kewarki sosai!
-Ni kuwa, ban ma iya tuna rayuwata ta baya ba, amma ina jin kewarka sosai a cikin raina. A baya na dade ina jin akwai abinda na rasa, wanda ya zama tamkar cikon barin jikina.
-Ba zamu kara fadar haka ba, babu abinda nake so da ya wuce ki kasance kullum a cikin hannuwana har na sauran kwanakina. Har abada, ba zamu sake rabuwa ba. Ina tabbatar maki ba zan jure ba, idan haka ta kasance, zan mutu ne anan take.
Haka suka zauna tsawon wani lokaci, Jinah ta manta da abinda take son ta tambayeshi. Shi kuwa Fally, ji yake da ya matsa ko na yan dakiku ne, to zai kara rasata. Da wannan tunanin, har lokacin da su Sarah suka dawo dakin bai tafi ba amma su basu ganinshi.
Kowa na gidan na nan amma banda Dauda, a take Jinah taji ba dadi, tanada wani auren da wani mutumin, anya kuwa Fally ya sani. Tambayar da take wa kanta kenan. A take kuma taba kanta amsa, Wata kila bai sani ba, tunda bata ga wata alama da ya nuna mata ba.
Haka gidan suka zauna anata hira har dare ya raba tsakiya kafin kowa yaje ya kwanta. Sai dai Fally da Jinah cigaba da hira suka yi kamar ba zasu kare ba. Kamar zasu ba junansu labarin duk abinda ya faru tsayin rayuwarsu. Zuwa cen Jinah ta jero masa tambayoyi :
-Wai me ya faru bayan bani nan? Ta yaya aka yi na dauki tsawon wannan lokacin ban tuna rayuwata ta baya ba? Ina su mama?
Fuskar Fally juyewa tayi zuwa ta damuwa. Sai kuma ga hawaye sun zubo masa.
-Mama ce, ita ce ta mantar dake komai. Domin ki rayu nesa damu kuma kar kiyi tunanin dawowa. Domin rayuwa a cikin mu hadari ne gareki. Ranar da kika tafi? Kin tuna?
-Eh, a ranar da muka yanke zama na har abada tsakanin mu.
-Rana mafi dadi a garemu.
Murmushi kowannensu yayi. Kafin kuma fuskar Fally ta sauya.
-A ranar ne kuma duk wani bakin ciki ya shigo rayuwarmu.
Labarin duk abinda ya faru ya bata, har zuwa lokacin mutuwar iyayensu. Dakatawa yayi yana kallon Jinah da ta kasa dena kuka jin labarin halin da masoyinta ya shiga. Hankalinsa ne ya tashi, baya son ganinta cikin wannan halin. Sai dai yafi shiga tashin hankali da ya tuna yanda zata ji idan taji mutuwar iyayensu. Katseshi kuwa tayi da tambayar :
-Su mama fah, suna ina?
-S..un..sun..
-Ka fada min Fally!
-Sun mutu.
-A'aaaaa ba gaskiya bane! Ka fada mani ba gaskiya bane Fally! Mama tayi min alkawarin ba zata taba barina ni kadai ba, zata kasance dani har tsawon rayuwata. Kuma ita da baba zasu ga jikokinsu da zana haifa...
Jin labarin mutuwar iyayenta duka biyun a lokaci guda ba karamin tashin hankali bane gareta. Taci kuka sosai kamar hawayen nata zasu kare. Fally kasa jure kukanta yayi, ya hade bakunansu wuri daya, wani zai dauka kissing dinta ne yake a'a, yana kokarin zuke duk wani zafin da Jinah take ji ne yana mayar dashi jikinsa. Jinah ta gane hakan sai tayi kokarin ta kwaci kanta amma kuma shi ya hana. Fally, har sai da ta kai zafin yayi masa yawa, kasa jurewa yayi ya kwanta kan gadon. Jinah zata yi magana ya dakatar da ita da hannu, shuru tayi tare da kwantowa kan kirjinsa, a hankali a hankali yaji zafin yana ragewa, ya gama fahimtar Jinah maganin duk wata cuta ce gareshi.
Bacci ne ya dauke Jinah, shi kuwa ya kasa bacci, domin wani sabon tunani ne ya takurashi.
Shin ko zata iya yafe masa idan tasan abubuwan da ya aikata mata domin memory ta ya dawo?
------------------------------------------------------
Alooooooooooooors, ya kuka ga wannan chapter?
Ayi ta hakuri da typing error. See u next chapter abokai 😍
©Al_Ashtar
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story