← Book details Jinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 11 OF 27

CHAPTER 11

Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Rayuwa akwai dadi, kasancewa a raye, shakar numfashi, kasancewa cikin koshin lafiya, abubuwa masu dadi da ban sha'awa a cikin rayuwa da kudi basu iya siya. Mai kudi a shirye yake ya sadaukar, a lokaci daya, duk wata dukiya da yasha wahalar tarawa shekara da shekaru, kawai dan ya kasance a raye. Haka ma talaka yana iya kokari ganin yayi fafutukar yakin kasancewa a raye. Wasu kuma duk dukiyarsu, adadin kwararrun likitocin duniya ba zasu iya kubutar dasu daga wata cuta da Allah ya dora masu ba, haka zaka ga kullum suna fadi tashin neman lafiya da tunanin idan sun kwanta bacci ba za'a wayi gari dasu ba. Sannan akwai wadanda a kullum cikin koshin lafiya suke kuma a kullum fatan dawwama a haka suke.
Duka wannan nau'i hudun na mutane mun kaddarantu ga mutuwa ne ko ba dade ko ba jima. Amma duk da haka muna fatan masu tsayin rayuwa, domin kamar yanda nace rayuwa wata aba ce mai ban sha'awa, kasancewa a raye wani iko ne na Allah kuma dole mu kasance masu yi masa godiya a kowanne hali. Iska daya ta numfashi da muke shaka ya fiye mana adadin dukiyar Karuna, mu kwanta da dare, mu wayi gari da safe wannan duk iko ne na Allah.
Sai dai Rayuwa takaitacciya ce, lokaci yana gudu ne tamkar haske. Kuma kowanne cikinmu yanada takaitaccen abin kirgen lokacinsa, dan haka muyi anfani da wannan takaitaccen lokaci namu, mu tunkari kaddarar dake gabanmu, mu kasance masu komawa ga Allah, dan mu kamar matafiya ne da muka yada zango a wannan duniyar.

A bangaren Fally a yanzu ya fahimci mecece rayuwa, domin halin da ya shiga da ganin mutuwa a kusa dashi. Yanzu kuma gashi ya kubuta, ya zama mai 'yanci sannan ya gujewa mutuwa a halin yanzu. "Nasan iyayena zasu yi farin cikin ganina idan naje gida." Ya fada a zuciyarsa cike da zumudin zuwa gida.

Sai dai da karasawarsa gida, yanayin kamshin gidan ya sauya, kamar akwai abinda ke faruwa, dan ba kamar yanda yake a baya ba. A kasalance ya karasa shiga gidan, mahaifinsa ya tarar zaune cikin yanayin bakin ciki. Ido suka hada, Fally yayi mamakin rashin ganin farin ciki ko mamakin ganinsa a fuskar mahaifinsa.

-Baba!

Cewar Fally.

-Kada ka kara kirana da wannan sunan! Kaga inda taurin kanka ya kaimu ko? Mahaifiyarka babu gwagwarmayar da bata yi ba ganin ta fiddoka, ganin cewa baka mutu ba. Gashi yanzu ta... A'a babu abinda ma zan iya fada maka dan bani da wannan karfin. Jeka! je ka kwanta kan gado.

Fally ya fahimci abinda mahaifinsa ke nufi, domin idan aljani ya mutu to yana barin wasiyyarsa ne kan gadon baccinsa. Kallon mahaifinsa yayi, bai ce dashi komai ba, ya nuna yatsa a take gadon marigayiyar ya bayyana a gabansu. Tafiya Fally yake kamar wanda kwai ya fashe ma, karasawa yayi kan gadon ya kwanta tare da rufe idonsa....

Dana, da farko, bana son ka dorawa kanka laifi akan abinda ya sameni, sam ba laifinka bane. Nayi kawai abinda ya dace ne. Naje naga Hindu... Nasan me zaka ce, kamar yanda mahaifinka yace min. "Bakida hankali ne, kinsan wannan matar shedaniya ce, kullum idan aljani yaje mata da neman taimako sai ta nemi wata sadaukarwa gareshi, ke kuma shine zaki je ki nemi taimakonta?" Itace aljanar da tafi kowanne aljani tsufa a wannan duniya tamu, ta rayu tsawon zamani da yawa, mace ce mai dogon sani da kuma karfin tsafi. Da yawan aljanu idan suka samu matsala suna zuwan wajenta ne neman taimako. Ban nemi taimakonta ba har sai da na tabbatar babu wata hanya ta kubutar da kai. Domin na kubutar da kai ka rayu, dole ni na kashe kaina, eh, na kawo karshen rayuwata. Lokaci mai tsawo kenan da take son taga mutuwata amma bata samu dama ba, ita da kuma da yawa daga cikin aljanu. Ba don komai ba, sai domin nice mai gadin Jinah kuma nice wadda uwarta ta bani amanarta kafin ta mutu. Shi yasa indai ina raye to basu taba cimma burinsu akan Jinah ba. Amma nayi imanin kai da mahaifinka zaku kare min 'yata Jinah, shi yasa na yanke ni na mutu dan kai ka rayu. Nasan mahaifinka zai yi fushi da kai, amma komai zai wuce.
Sannnan ina tayaka murna Dana, ka zama uba yanzu, Jinah ta haifi yan tagwaye kuma ta saka masu sunanmu, ni da mahaifinka. Yaran sun rayu, wannan wani ikon Allah ne dan hakan bai taba faruwa ba, idan irin haka ta faru yaran mutuwa suke. Wadannan yara suna tattare da wani karfin sihiri na aljanu, dan haka yanzu ba sai an jima ba rayuwar Jinah tana cikin hadari. Zasu bi kowacce irin hanya ganin sun mallaki waddan yara. Hindu ta dade da ganin wannan al'amari dake tattare da yaran shi yasa take son na mutu. Kar kayi bakin ciki dana, zan kasance kullum a cikin zuciyarka, ina yi maka ban kwana, ka kula min da 'yata Jinah da kuma jikokina. Mahaifiyarka mai kaunarka.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo ma Fally lokacin da ya gama jin wasiyyar mahaifiyarshi, hannuwa yasa ya dafe zuciyarsa sakamakon wani zugi da take masa. Mikewa yayi ya sauko daga kan gadon sannan ya nufi mahaifinsa tare da fadawa jikinsa yana kuka kamar wani karamin yaro. Yana ji da ba dan taurin kansa ba da har yanzu mahaifiyarsa na raye.

-Yanzu tunanin Jinah da ya'yanka zaka yi, ka daina kuka.

Take kuma wani farin ciki ya lullubeshi jin abinda mahaifinsa ya fada, yanzu kenan shi uba ne. Ana yawan basu labarin idan aljani da mace mutum, ko kuma aljana da namiji mutum suka samu haihu tare, yaron ba za'a taba haifarsa da rai ba. Amma gashi cikin ikon Allah nasu yaran sun rayu.

-Bamu da lokacin batawa, ya kamata muyi saurin tafiya kafin su farga da mutuwar mai gadin Jinah.

Cewar Ayu mahaifin Fally. Goge hawaye Fally yayi tare da daukar wata jaka ya saka wasu kaya da zai bukata, suka dauki hanya shi da mahaifinsa. Ba suyi tafiyar wasu kilomitoci ba, aka harbo wani mashi ya ratsa cinyar mahaifin Fally da tayi sanadiyar faduwarsa kasa.

-Baba!

Fally ya kwala kara tare da durkusawa kusan mahaifin nasa.

-Ka gudu! Suna nan!

Cewar mahaifin nasa da ya ankare da an biyosu.

-A'a baba a tare zamu je!

-Guba ce, ba zan iya anfani da tsafina ba.

Motsi Fally yaji, yana juyawa yaga mayakan aljanu sun kewayesu ta ko'ina.

-Ka ceci kanka dana!

Wasu kibiyoyin aljanun suka kara sakawo kafin Fally yayi saurin bacewa. Sai gashi ya bayyana a tsakiyar wani jeji, durkushewa yayi kasa tare da dafe kai, yana ji kamar yayi kuka, yayi kara ko kuma gurnani kamar zaki... Yanzu shi daya ya rage, shi daya, kuma dole ya kare matarsa da kuma 'ya'yansa...


(.....)


Jinah, Sarah, Dauda da kuma 'ya'yan Kimba ne zaune a tsakiyar gida, kowanne ya fada duniyar tunani. Duk wannan ta faru ne lokacin da Kimba ya furta shine ya yiwa Jinah fyade.

-Wannan ba fa zai taba yiyuwa ba, ba shi bane. Tagwayen da ba'a dade da haifa ba, lokacin da ya kamata a samu cikin yaran, Kimba yana Nigeria.

Sarah ce ke magana, kowannensu daga kai yayi yana kallonta, kamar tana maganar ne da niyyar kare Kimba, domin har yanzu kalaman mijin nata suna mata yawo a kwanya, sai dai ba yanda za'ayi ta gasgata hakan, abu ne marar yiyuwa ace Kimba ya yiwa Jinah fyade.

-Ba abu ne mai yiyuwa ba ace babana ne.

Cewar diyar Kimba. Jikin jinah yayi sanyi, ita kanta bata yarda shine ba, shi da ma baya cikin Nijar din, kuma bama tada hujjar cewar fyade aka mata.

-To me yasa zai ce shine idan ba shi bane?

Cewar Dauda.

-Gashi yayi tafiyarsa ba tare da ya bamu hujja ba.

Cewar dan Kimba.

-Bama shi bane, na tabbata.

Cewar Jinah.

-Kenan ke fyade aka yi maki?

Cewar diyar Kimba.

-Nima ban sani ba!

Jinah ta bata amsa.

-Mu manta da wannan yanzu, idan ya dawo, shi zai yi mana bayanin komai. Cewar Sarah tare da juyawa ga diyan mijin nata. Baku fada mana sunanku ba?

-Ni sunana Abdul.

Cewar namijin, ita macen kin magana tayi. Ya cigaba.

-Ita kuma Nafisa sunanta, amma muna ce mata Nafi zararra ko kuma kuce Nafi yar mahaukaciya.

Dariya dukansu suka yi, banda Nafi dake ta hararar yayan nata, shi kuma yayi kamar bai gani ba.

-Ina maku barka da zuwa gidan nan, kuma ina maku jajen rasuwar mahaifiyarku. Allah ya jikanta, yayi mata rahama.

-Ameen.

Fira suka cigaba da yi, kafin Jinah da Dauda su kebe zuwa daki. Da shigarsu daki ke da wuya Jinah ta fada jikin Dauda tare da fashewa da kuka.

-Kayi hakuri dan Allah Dauda, na haifar da abubuwa da dama cikin danginku. Naji dadin ganinka ka warke. Ka yafe mani dan Allah, da cutar da kai da danginka da nayi. Mutanen nan suna da gaskiya, ni may...

-Shiit, yi shuru ya isa haka...

Shiru dakin yayi, babu abinda ke tashi sai sheshekar kukan Jinah. Dakatar da shurun Dauda yayi bayan wani dan lokaci.

-Ko kin san lokacin ne nafi bukatarki, abinda yafi min ciwo, lokacin na dawo hayyacina ban ganki ba, da na tambaya aka ce mani kinyi tafiyarki, naji ciwon haka marar misaltuwa. Bai dace kiyi tafiyarki ba Jinah, haka nayi ta nemanki domin yayan Sarah bai so fada min inda kike ba. Yi tunani idan da ban ganki ba, halin da zan shiga.

-Kayi hakuri, ka yafe mani.

Jinah ta fada tana kara shigewa jikinsa.

-Ban yi fushi dake ba, amma kiyi min alkwari ba zaki kara tafiya ki barni ba.

Murmushi tayi, taji dadin ganinsa da tayi cikin koshin lafiya, ya warke sumul.

-Ina sonki!

Dauda ya fada yana kallon fuskar abar kaunarsa da ta kasa cewa komai, kallonsa kawai take itama. Kukan jariran Jinah da suka tashi bacci ne ya katse masu yanayin da suke ciki.

-Ya Allah! Wai sune haka?

Cewar Dauda cike da mamaki ya nufi inda jariran suke.

-Wow masha Allah, kyawawa dasu!

Kallon yaran yake yana murmushi, yana ji tamkar nashi. Wasa ya fara yi da yaran da har ya fara manta damuwar da ke tare dashi. Jinah ce ta katse masa nishadin da tambayar da tayi silar kawo damuwa a fuskarsa.

-Dauda, me yasa ka nuna min kamar akwai aure a tsakaninmu?

-Ban gane ba?

-Akwai wata rana da muka je ni da Sarah wajen wani waza'i, nan naji malamin yana fadar, ba'a yin aure idan macen na da ciki, idan kuwa aka yi to auren bai halatta ba. Nasan ka sani, dan ina lura da yanda baka son tabani. Me yasa kaki fada min?

Wani yawu Dauda ya hade kafin yace

-Eh hakane, ina ganin wannan ita ce damar da zan samu ta kasancewa a kusa da ke. Kiyi hakuri da karyar da nayi maki.

-Taimakona ne kayi, nagode sosai.

Shiru ya dan biyo baya kafin Dauda yace

-Jinah!

-Na'am?

-Zaki aureni, auren gaske a wannan karon?

-Eh sosai ma!

Wani kayataccen murmushi tayi tare da gyada masa kai. Ta amince zata aureshi, dan ya cancanci komai, kuma tana fata itama wata rana ta soshi. Sungumeta Dauda yayi yana ta juyin farin ciki da ita a cikin dakin.

-Ba zaki san wane irin farin ciki yau nake ciki ba, ina cikin matukar farin cikin da yafi kalmar farin ciki. Nayi maki alkawarin ba zaki taba nadama ba. Gobe kenan za'a daura auren?

-Gobe?

Ta fada tana fiddo ido.

-Eh mana gobe, ko yayi nisa?

Fashewa da dariya Jinah tayi.

-Dauda, ba fa guduwa zan yi ba, dan haka ka kwantar da hankalinka! Gobe yayi kusa!

-To naji nan da kwana uku?

Nan suka fara jayayya har dai ya yarda akan nan da sati biyu.

Daukar Ayu Jinah tayi, shi kuma Dauda ya dauki Aya, suka fita dan sanar da Sarah labarin auren.

-Sarah, aure zamu yi nan da sati biyu ni da Jinah!

Dariya Dauda yaba Jinah ganin yanda yake maganar kamar yaro.

-Ah madallah, nayi murna kwarai!

Cewar Sarah tana tafa hannu.

-Na tayaku murna!

Cewar Abdul.

-Nagode nawa (abokina)

-Zan iya daukar yaron?

-Eh, me zai hana?

Cewar Dauda yana mai mika masa Aya dake hannunsa.

-Woww! Mace ce ashe, kyakyawa masha Allah! Zo ki gani Nafi!

Ko kallo bai samu ba daga yar uwar tashi, ya cigaba.

-Wayyo dubi idanunta kamar Barbie, dubi lebenta duka kalan pink, har da ma dimples idan tayi dariya, masha Al...

Duk yana yin hakan ne dan jawo hankalin yar uwar tashi dan ya santa da masifar son yara kanana. Ai kuwa yayi nasara, tashi tayi ta nufi wajen Jinah ta karbi Ayu dake hannunta.

-Ai daman nasan ba zaki iya jurewa ba.

Cewar Abdul yana mata dariyar keta.

-Ni kyaleni!

Nafi ta fada tana turo baki, dariya sauran sukayi.

-Oh ni bari na tashi na hada mana abinda zamu ci, dan nasan kun fara jin yunwa.

-Wallahi kuwa, dan cikina har ya fara yaren Chinese.

Cewar Dauda.

-Ai bai kai nawa ba.

Cewar Abdul.

-Ai kai dama cin tsiya ne da kai.

Cewar Nafi, dariya dukansu suka yi.

-Ba sai kin wahalar da kanki ba Sarah, zamu je ni da Jinah mu siyo abincin a waje.

Cewar Dauda.

-Eh bari sai muje mu siyo dan na rogo. Fatan dai kunsan meye haka?

-Sosai ma, a cen akwai wata yar Nijar dake soyashi kusa damu.

Cewar Abdul.

-Ai na fada maku ba abinda ya sani sai ci.

Nafisa ta fada. Kowa ya kwashe da dariya. Bayan wani dan lokaci Jinah da Dauda suka nufi kasuwa.


(.....)


Dare yayi sosai, Jinah ce daga ita sai yan tagwayenta kwance akan gado. Juyi take ta yi idanunta rufe amma ba bacci take ba. Tana jin kamar mutum a kusa da ita amma bata ganinsa.

-Jinah, abar kaunata, kalleni nine Fally!

Eh Fally ne, mutumin nan dake kusa da ita wanda ta kasa ganinsa. Fally ne a gabanta, farin ciki ne fal a ransa gashi ga rabin ransa, cike da zumudi ya kai hannunsa kan gashinta yana shafawa, ganin idonta a rufe hannun nasa yakai kan fuskarta yana shafawa, ita kuma Jinah ji take yi tamkar ana shafa mata wani narkakken karfen da aka sanya a wuta. Abun bai ishi Fally ba, duko kansa yayi yana sumbatar wuyanta, a hankali ta bude ido. Baki Fally ya wage kai kace gonar auduga.

-Jinah abar kaunata!

Ya fada, ita kuma dube dube ta fara kamar wadda hanya ta bacewa. Anan ya fahimci ba ganinsa take ba. Wani haushi ne yaji ya turnukeshi, sai dai bai ida gasgata abinda zuciyarsa ke fada masa ba, yanke sharawar ya bayyana mata kansa yayi. Tsalle daga kan gado Jinah tayi, tare da kwala wata gigitacciyar kara... Tsoro duk ya kamata, jikinta sai rawan mazari yake.

-Jinah nine fa! Fally naki!

-Dan Allah kar kayi min komai, kar ka cutar dani dan Allah! Dauda! Dauda!

Ta shiga kwalawa Dauda kira.

-Kinyi alkawarin fa ba zaki manta dani ba!

-Dan Allah ka tafi, bana son ganinka!

Jinah ta fada, da alama bata jin ma abinda yake fada. Kofar dakin ce ta bude da karfi, ba kowa bane face Dauda. Sai dai Fally tuni har ya bace, ko Jinah bata ganinsa.
Ran Fally yayi matukar baci, ta yanda yake ji tamkar ya ciro zuciyarsa yayi jifa da ita nesa. Cikin awowin da basu wuce 48 ba, ya rasa uwa da uba, gashi kuma wadda dan ita komai ya faru wai ta kasa ganeshi.

"Kawai zan kyaleta da sauran aljanun su cutar da ita ma, me yasa zan kare wadda tayi sanadin wargajewar rayuwata? A'a ba zan iya ba, taci amanata!!!!"


---------------------------


Salam, miss u many, realy lol.

Bon, ina fata zaku ji dadin wannan chapter. Kar kuyi tantamar fadin kowanne ra'ayi naku game da wannan chapter, haka idan ma kalamai sunyi maku karanci zaku iya bina da stickers marar iyaka. 😂

Merci de toujours vous retrouver même si je tarde a publier, je vous adore 💘 vous êtes les meilleurs.

Sai mun hadu a wata chapter. 🤗

Kusha ruwa lafiya 🎈

@El_Ashtar

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story
Chapter 11 · 0% Book details