← Book details Jinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 27

CHAPTER 19

Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

A wurin mutane soyayya ba wani dogon nutsatsen kogi bane a'a, a wurin mutane soyayya dogon kogi ne mai cike da igiyoyin ruwa masu saka kogin yayi sama yayi kasa. Haka a wurin aljanu, banbancin ba mai yawa bane, sai dai akwai muhimmanci mai tsauri a soyayyarsu, suna tsananin yarda akan wanda suke so, ta yanda zasu iya sadaukar da komai akan wanda suke so, nuna kulawa da muntuntawa da gujewa duk wani abu da zai cutar dashi, wannan kenan a cikin soyayyar aljanu. Amma kuma idan aka samu akasin haka daya daga cikin masoyan wani ya cutar da dayan, alakar dake tsakaninsu zata wargaje kuma dukansu biyun da wanda aka cutar da wanda ya cutar kowanne zai biya bisa laifin dan uwan nasa. Hukuncin kuwa ba komai bane face mutuwa.

Abinda Fally yayi kenan, bayan yayi magana da 'ya'yanshi, ya gano rashin lafiyar Jinah shine sila amma sai yace ai abu ne mai kyau domin dan ya gyara gobenshi ne. Bai san abinda yake aikatawa ba, a hankali yana wargaza muhimmiyar alakar dake tsakaninshi da Jinah ne kuma idan har ya cigaba dukansu zasu rasa rayukansu.

Hindu tana sane da hakan, kuma wannan shine plan dinta, da kanta ta tsara komai daki-daki, kuma abinda zaifi kayatar da ita shine yayin da Fally da Jinah suka mutu haka zai sa yan tagwaye suyi rauni, ta yanda ba zasu iya anfani da karfinsu ba. Daga nan zata sa a kamosu ta barka kirjinsu ta ciro zuciyoyinsu ta cinyesu danyu. Daga wannan lokaci babu wanda zai iya kwatanta karfinsa da nata, karfinta zai karu, kuma zai mayar da ita gagara badau ki mutuwa (Immortelle).

(...........)

A gidansu Sarah, alfigir ya keto, duka mutanen gidan idanunsu biyu tun awowi 3 da suka shude, suna kan Jinah, sakamakon farkawa da tayi da kara, ciwo mai tsanani da kuma sambatu, wanda yayi sanadin taso Sarah, diyan mijinta da kuma yan tagwaye. Kowannensu cikin tashin hankali yake, basu san me zasu yi ba, su kaita likita? Sun riga da sun san abinda likitoci zasu ce. Sarah bayan tayi iya kokarinta na ganin ta rarrashi Jinah. Da gudunta taje ta jiko ganyen maganin da wani mai maganin gargajiya ya bata, lokacin da ta bata ta sha, Aya da dan uwanta ta dalilin karfinsu, suka saka uwar tasu bacci, su kuwa sauran sai suka dauka ganyen maganin ne yayi aiki.

Fita suka yi suka barta ita kadai domin ta samu hutu. Yan tagwaye wajen babansu suka je, suka ce ya dakatar da abinda yake. Ce masu yayi, zata warke ne kawai idan ta tuna dani, a yanda na kusa cimma burina, ba zai yiwu na dakatar ba. Abinda ya fadawa yaran kenan.

-Ka cika son kai baba.

Cewar Ayu, kafin yaja hannun yar uwarshi su bar wurin. Shiga dakin mahaifiyar tasu suka yi, suka tarar har yanzu tana bacci. A bangare daya kuma na dakin, Dauda ne zaune a kasa hannuwansa dafe da kanshi. Matsawa suka yi kusa dashi, anan suka ji yana ta wasu sambatu. Aje hankalinsu suka yi domin fahimtar abinda yake fada. Anan suka ji yana fadar :

-Ba zan iya cutar da ita ba! Me yasa nake yin haka? Amma kuma ba ni bane! Zan yi fada domin ta! Ta dalilina ne ka dawo, zan fadawa shugaba, zata batar da kai har abada! Daga nan kuma wannan karamin ahalin naka zai biyo baya. Ba zan barka ka aikata hakan ba! Ba zan barka ka cutar da...

Maimata kalamansa na karshe yayi ta yi kafin ya fadi sumamme. Kallon juna yan tagwayen suka yi, ba tare da dayansu yace kala ba. Ayu ne ya saka hannunsa cikin rigar Dauda tareda dora hannun daidai kan zuciyar Dauda, shuru yayi na dan lokaci bayan ya janye hannunsa kafin yace :

-Bansan ko menene shi ba.

-Kamar yaya?

Yar uwar tashi ta tambayeshi da mamaki.

-Ban sani ba ko shi mutum ne ko aljani.

-Me kake fada ne? Mutum ne mana!

-Eh, da gani mutum ne, amma jin bugun zuciyarshi zai tabbatar maki da ta mutum ce kuma ta aljani ce.

Kasa yarda yar uwar tashi tayi, sai da itama tayi da kanta ta tabbatar.
Dukansu cikin rudu suka fada. Kokarin tayar da Dauda suka yi domin yayi masu bayanin meke faruwa dashi amma kuma yaki tashi. Kalaman Dauda ne ke ta lugude a kwakwalan yan tagwaye, kafin dukansu tunaninsu ya basu aljani ne ya shiga jikinshi. Daukar Dauda suka yi suka bace daga dakin nasu. Anan suka shiga bin duk wata hanyar da Dauda zai farfado, sai dai basu suka samu nasara ba sai da sanyin safiya. Kokarin karantar tunaninsa suka yi amma hakan ya faskara, wannan ya tabbatar masu shi ba aljani bane kuma shi ba mutum bane.

-A zahirance kai waye?

Ayu ne ya fara magana.

-Ruhina aljani ne, gangar jikina mutum.

-Ta yaya haka zai yiwu?

Cewar Aya.

-Ta karfin tsafin shugabata Hindu.

-Wacece Hindu kuma meye dalilinta?

-Hatsabibiya ce ita, Aljana mai karfin tsafi marar misaltuwa, kuma tana son kara zama gagarabadau ta hanyar samun naku karfin.

-Me? Ta yaya?

-Ta riga da ta fara, kuma sai ta karasa.

-Tanada alaka da ciwon mahaifiyarmu?

-Eh.

-Kuma da abinda babanmu ke yi?

-Eh. Zai yi sau 10 ne, a dare goma, daren jiya shine na dare na karshe.

Zuciyoyin yaran ne suka buga duum.

-Me zai faru bayan hakan?

-Iyayenku zasu fada doguwar sumar da zata dauke su tsawon wasu kwankaki kafin su mutu. Kuma da hakan ta kasance zata juyo kanku. Zaku fara yin rauni, ku kasa amfani da karfinku, daga nan zata kamaku ta ciro zuciyoyinku ta cinye.

Da gudu Aya ta nufi wajen iyayenta domin tabbatar da abinda Dauda yake fada, sai dai kuma da zuwanta ta tarar dasu sumammu, wurin mahaifiyarta ta durkusa ta fashe da wani azabataccen kuka wanda yayi sanadin jawo hankalin Nafisa, Abdul da Sarah. Ganin Jinah taki farkawa kuma bugun zuciyarta kadan kadan yake yi, yasa suka nufi asibiti da ita duk sun san ba lallai bane likitoci su iya yin wani abu.

Shi kuwa Ayu tsayawa yayi wurin Dauda domin sanin yadda zai iya wargaza plan din Hindu.

-Amma ta yaya zamu dakatar da ita?

-Ba zaku iya ba, amma akwai hanyoyi biyu da zaka iya daidaita wannan matsalar.

-Wanne hanyoyi ne?

-Zaku iya cire zuciyar Hindu kafin ku rasa karfinku, hakan zai sa kai da yar uwarka ku rayu, amma Iyayenku zasu mutu. Ko kuma hanya ta biyu, daya daga cikinku yaci ganyen Fula, itaciya ce dake kashe aljanu. Wannan itaciya guba ce da zata sa yayi rauni, daga nan sai yaje ya nemi Hindu, ganin halin da yake ciki zata dauka ko plan dinta ne yayi aiki, daga nan zata cinye zuciyar mai guba sai ta mutu shi ma mai zuciyar ya mutu.

Hakan zai sa Iyayenku su tsira, sannan mahaifiyarku zata tuna da babanku da duk wata rayuwa da tayi da aljanu.

Hawaye ne suka kwaranyo daga cikin Ayu kafin yace bana son mama ta mutu.

-Kuka kake yi Ayu?

Cewar yar uwarshi data bayyana kusa dashi. Jin bai bata amsa ba, ta cigaba :

-Ba zasu mutu ba, ba yanzu ba.

Goge hawayen fuskarsa yayi tare da rungume yar uwar tashi. Yaji dadin kalamanta sosai.

-Nayi miki alkawarin babu abinda zai faru.

---------------------------------------------------------

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story
Chapter 19 · 0% Book details