← Book details Jinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 27

CHAPTER 26

Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Lokacin da Jinah ke kallon Fally a kwance, jini na malala, gangar jikin sa na bankwana da ruhin sa. Wani zafi taji da yafi duk wata azaba zafi na kwanakin da suka shuɗe.

-A..a'a Fally, ba zaka mutu ba, nayi nadamar abinda na faɗa maka, na yafe maka, amma kar ka tafi dan Allah.

-Ki daina mama, ya riga da ya mutu.

-Ku tashe shi! Kuyi duk abinda zaku yi, ina son ya tashi!

-Su tashe shi? Ai wannan ba mai yiyuwa ba ne!
Cewar Infa cike da mamakin abinda Jinah ke kokarin sanya ƴan biyu.

-Saboda me? Nasan zamu iya yin hakan da karfin mu!
Cewar Aya.

-Koda muna iyawa, ba zamu yi ba, domin abinda yayi wa mama! Ba...
Cewar Ayu, wanda da alama mutuwar mahaifin nasa bata taba shi ba. Kallon da mama tashi ta watsa masa ne yasa yayi shuru.

-Ko ma me ya aikata, shi ne kuma zai cigaba da kasancewa mahaifin ka. Kada ka bari kiyayya ta rinjaye ka. Ka..kada ka maimaita kuskuren mahaifin ka. Shuru tayi kafin ta cigaba. I..idan da kun san wani lokaci a baya, lokacin muna yara. Ni nasan shi a wancen lokacin, babu wani mai zuciya mai kyau irin mahaifin ku.

Ta faɗa da alamun ta tuna abubuwa da dama.

-Sai dai kuma yau, babu mugu irin shi, kalli fa irin azabtar dake da yayi mama!
Cewar Ayu cike da wani yanayi mai kama da tsana. Sai dai akasin haka ne, bangaren yar uwar shi, mutuwar mahaifin ta ta taɓata sosai, ita ma tana son ya dawo, domin ba zata so rashin mahaifi ba, a irin wannan yanayin, duk da mintuna kadan baya da yana raye, babu abinda take fata face mutuwar sa.

-Ni ina son ya tashi!
Cewar Jinah.

-Jinah, cewar Infa. Ina tunanin baki san wannan ba, tayar da aljanin da ya mutu abu ne da ba'a taba yin sa ba. Domin ba zai koma kamar yanda yake a baya ba, kuma a yanda zai tashi, hakan ba zai yiwa kowa daɗi ba. Domin zai iya tashi a sheɗani.

Kamar bata ji ko kalma daya daga abinda ya faɗa ba, Jinah ta umarci ƴaƴanta da su tashe da baban su. Kokarin tashe shi suka shiga yi, ba irin karfin da basu yi aiki dashi ba, ganin sun tayar da shi amma sun kasa. Bayan ɓata lokaci mai yawa da suka yi, daga karshe suka ce mata ba zasu iya ba. Cigaba da rizgar kukan ta tayi. Daƙyar suka iya bamɓare ta, suka bar wurin.

Jikin Dauda yayi sanyi, tun lokacin da yaga Fally ya mutu. Da farko saboda bai fahimci abinda ke faruwa ba, na biyu kuma ganin halin da Jinah take ciki. Sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa bai taɓa samun soyayyar da yake fata ba daga gare ta, ashe wani take so, kuma ba kowa ba face Fally. Kuma yaga irin girman soyayyar da take nunawa Fally : ta yafe mishi duk da irin cutarwar da yayi mata.

Murna marar misaltuwa sai gida gun Sarah. Kuka take yi ba kakkautawa, ta yanda duk wanda ya gani zai yi tantamar anya na farin ciki ne kuwa, amma sai dai ganin irin murmushin da ke shimfiɗe a fuskar ta zai bayyana maka kukan farin ciki ne. Haka take ga sauran yan gidan. A ranar farin cikin su ya kasa boyuwa.

Zamu iya cewa Jinah ta manta da duk wata wahala da tasha a bayan nan, ganin yanda take cikin farin ciki.

-Nagode Dauda, ban san da me zan biya ka ba, kayi min alkawarin zaka nemo min ta, gashi ka cika.

Cewar Sarah kafin hawaye su kwaranyo mata. Murmushi Dauda yayi mata, ko kuma mu ce yake mai kama da kuka, wanda ba kowa na wurin ba ya lura. Zarewa yayi daga wurin, ya shige ɗaki, hankalin sa duk a tashe.

-Ta yaya har ka iya gano inda Jinah take? Faɗa mana gaskiya!

Infa da ƴan biyu ne suka yiwa Dauda wannan tambayar. Ba tare da yaga shigowar su ba, kamar ma sun rutsa shi.

-Zan faɗa maku komai.
Dauda ya faɗa a fusace.

-Nayi yarjejeniya ne da Hindu.

-Ni fa na sani, ba yanda zata iya barin ka, ka taho haka.
Cewar Infa.

-Sati ɗaya ta bani, na kawo mata ɗaya daga cikin ƴan biyu, ta barni a raye.

Mamaki ne ya dabaibaye fuskokin su, suna bin sa da wani kallo.

-Kuma ma ba shikenan ba, lokacin da naji labarin Jinah ta ɓata, na tambaye ta, ta faɗa min yanda zan ga Jinah, tare da yi mata alƙawarin duka ƴan biyun...

-Innalillahi!

Jinah ta faɗa a gigice jin abinda kunnen ta ya jiwo mata daga shigowar ta. Kwalar Dauda ta shaka tana faɗin :

-Me..me ka aikata ne Dauda... ƴaƴa na?!

-Kin manta wani abu Jinah, ni dolo ne! Kuma dolonci na, shi ne son da nake miki, fiye da kowa. Har abada ba zan taba cutar dake ba da sani na. Kuma ni ba sakaran Fally'n ki bane, da bansan me nake yi ba. Nayi wannan yarjejeniyar ne da Hindu saboda...

-Saboda me? Me hakan zaya haifar, kai kasan irin son da nake wa ƴaƴana kuma nafi ƙaunar mutuwa ta da na rasa su! Toh saboda me?! Saboda me kuke son cutar da ni?

Fushin Dauda raguwa yayi ganin halin da Jinah ta shiga. A hankali yace :

-Nayi wannan yarjejeniyar ce kawai dan na gudarwa Hindu, kuma dan na karashe sauran kwanaki na a tare da ku, idan da ban yi wannan ba, da ba zata taɓa bari na na dawo ba, ko kuma ma ta kashe ni, har abada ba zan taba bayar da ƴaƴan ki ba, suna cikin cikin ki lokacin da na muka fara haɗuwa, ƴaƴana ne nima Jinah, soyayyar da nake musu ba mai ƙirguwa bace, zan iya bada rayuwa ta domin su, domin ke.

-A'a..a'a..Dauda.
Jinah ke faɗa tana riƙe da fuskar Dauda.

-Idan har lokacin da ta ɗibar min ya cika, kuma ban kawo mata ƴan biyu ba, to zata kashe ni. Ni kuma abinda ba zan taɓa yi mata ba. Shi yasa na zaɓi nazo na ƙarashe kwanaki na da ku cikin farin ciki. Wannan shi ne kawai buri na.

Jinah, ƙafafuwan ta kasa ɗaukan ta suka yi, sai gata ta durƙushe a kasa.

-A'a kada kayi min haka Dauda, bana son kai ma na rasa ka.

Jinah ta faɗa cikin wata ƙaramar murya. Ƴaƴanta kuwa tsabar sun girgiza, sun kasa motsa koda bakin su, domin basu shirya zuwan irin haka ba.

Dauda ya kasa cewa komai, shi ma zauna yayi a kasa, ita kuwa Jinah ta haɗe kai da gwiwa. Shuru wurin yayi kamar na wasu mintuna kafin Infa ya katse shurun da cewa :

-Bai zama dole sai ka koma wajen ta ba, ni da ƴan biyu zamu yi ƙokarin kare ka.

Kowa a wurin sai da yasa rai a kan plan din Infa kafin Dauda ya sare musu gwiwa da cewa :

-Tana controlling duk wani motsi na ne daga nesa, sau da yawa nasha kokarin guduwa, amma bansan ta yaya ba, sai na ga na kara komawa gare ta.

-Shedaniya! A hannun ta kake!
Cewar Infa.

-Lokacin da baba na ya mutu, ban ji wata damuwa ba domin nasan ina da kai, a gare ni, kafi baba na, kar ka tafi ka barmu baba.

Cewar Ayu, cikin yanayin nuna tsantsar kaunar da yake wa Dauda. Shi ma Dauda cikin bakin cikin zai rabu da su yake, amma ba yanda zai yi. Dauda rungume Ayu yayi, sannan yayi wa Aya nuni da ta taho. Ita ma kamar mahaifiyar ta, tashin hankalin da take ciki marar misaltuwa ne, ta yanda daƙyar ta iya buɗar bakin ta tace:

-Bana son ka tafi, kar ka barmu dan Allah.

Kara ƙanƙame su sosai Dauda yayi, shi kanshi baya son rabuwa da su.

-Jinah! Jinah! Jinah!

Suka yo kan Jinah gaba ɗayan su, ganin ta zube kasa bata motsi. Cak Dauda ya ɗauke ta, ya kwantar da ita kan gado, su kuwa yaran suka yi waje kiran Sarah da sauran.

Dubawa suka yi, suka ji tana numfashi. Kumatun ta ya dan tattaɓa, a hankali ta buɗe ido.

-Sannu Jinah, duk wannan mai wucewa ne wata rana. Nasan kin gaji, kin sha wahala sosai, amma ina son ki sani komai yana da karshe.

Dauda ke faɗa mata haka, yana mai shafar fuskar ta. Wahala ta rayuwa dai Jinah ta ganta, kuma fiye da haka na tafe.

*****

-A ina nake? Kuma ke wacece? Sannan ni waye?

Farkawa yayi, ganin wata mata da bai san ko wacece ba, Gashi shima kuma bai san ko waye shi ba.

-Ni shugabar ka!

Ta bashi amsa a taƙaice.

-Ina jin ƙishi!

Ya faɗa yana taɓa makoshin sa. Miƙo masa tandu biyu tayi, dayan ɗauke da ruwa, ɗayan kuma da jini a ciki domin ta tabbatarwa kanta a yanayin da ya tashi. Eh Fally ya dawo daga duniyar matattu, ƴan biyu sun ɗauka karfin su bai iya tayar dashi ba, amma ba haka bane, domin da sun ƙara hakuri na wani dan lokaci toh zai tashi a gaban su. Hindu kuwa tana laɓe lokacin da suke ƙoƙarin tayar dashi, kuma tasan sun iya, sai ta ƙyalesu, suna bada baya tazo, anan taga zuciyar sa na bugawa. Farin ciki ne fal a ranta. Idan aljani ya mutu, sannan aka yi kokarin tashe shi, toh fa yana tashi ne tamkar jariri, babu komai cikin kan sa, toh daga nan zai fara daukar sabbin abubuwa, walao sharri ko alkhairi.

Fally mika hannu yayi, ya karbi tandu mai dauke da jini, ya shanye a take. Hindu kuwa daɗi ne ya lulluɓe ta.

-Zamu je mu ɗauki fansa!
Hindu ta fada cikin karaji.

-Fansar wa?

-Ta makiyan mu, da suka cutar da mu, kuma dole su biya.

-Dole zasu biya!
Shi ma ya sake maimaitawa.

-Ina son ka san wani abu, ni shugabar ka ce, kuma dole ka bi umarni na.

-Yanda kike so Shugaba, zan iya samun ƙari?
Ya faɗa yana nuni da tandun jini.

-Zaka samu, kuma sai ya ishe ka, mu je lokaci na ƙurewa! Jinah da dangin ta zasu ji daɗin ganin mu.

Cewar Hindu da sigar sheɗanu.

Kamar kyaftawar ido, suka bayyana a ƙofar gidan su Jinah. Sai dai basu shiga ba, suka tsaya bakin ƙofar, domin tasan ko su waye ƴan biyu. Don haka dole sai sun yi taka tsantsan.

-Infaaa! Infaaa!
Fally ya shiga ƙwalawa Infa kira bisa umarnin Hindu. Kiran kuwa ya isa kunnen Infa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya bayyana gaban su, ba tare da ya fahimci meke faruwa ba. Fally ne a gaban sa, bai gama mamakin ganin Fally ba, sai ya tsinkayi Hindu a bayan Fally, nan ya gama yankewa kansa wannan ba alamu bane mai kyau.

-Fally...am..amma ta..yaya..

-Kai Fally bamu da lokacin yi masa bayani ka kashe shi!

Hindu ta umarci Fally, murya cike da karaji. Ba tare da wani tunani ba ya cika umarnin ta. Infa bai samu lokacin maida martani ba, bare kuma ya kare kansa, sai lokacin da yaga jinin sa na zuba sannan ya fahimci meke faruwa, Hindu nada babban makami, kuma Fally ne makamin nata.

-Mun gama da wannan! Ɗauke gawar ka jefar, sannan ka dawo.
Cewar Hindu.

Ƴan biyu ne suka karaso wajen, ganin mahaifin su yasa suka kwaso a guje suka nufo shi, ba tare sun yi tunanin ta yaya mahaifin nasu ya tashi ba, har da Ayu da tuni mutuwar baban nashi ta fara taɓashi. kafin su karasa jikin sa, tuni Hindu ta tsikarawa kowannen su, wata allura a gadon baya, fadawa jikin baban nasu suka yi summamu.

-Yauwa! Yanzu ka shiga gidan, kaji daɗin ka, kayi yanda kake so da mutanen gidan, ka sha jini iya son ran ka.

Bata jira jin amsar shi ba ta ɓace da ƴan biyu.

Ɗaki na farko da Fally ya tarar shi ne na Jinah, tana kwance ita kaɗai bisa gado, idanun ta a rufe, da alama sauran sun fita ne sun barta domin ta huta.

Matsowa Fally yayi sosai kusa da Jinah, santin kyawun ta ya shiga yi, kasa motsawa yayi kamar bai taɓa ganin halitta mai kyau ba irin Jinah. Yatsun sa, ya tura cikin gashin kanta, sannan yabi tsawon gashin, tare da janye wani daga gashin da ya rufe mata fuska, anan ya kara shaida kyan da take da shi. Kasa controlling kan sa yayi na son taba jikin ta, anan ya shiga yawo da hannun sa kan fuskar ta. A hankali ta bude idanun ta, idanun ta cikin idanun sa, numfashin su ya hade, shuru ya mamaye ko'ina, ba tare da bata lokaci ba, Fally ya tsinci laɓɓan sa cikin na Jinah, ita ta fara sumbatar sa, kafin shi ma ya biye mata. A hankali sumbatar ta kara karfi, daga nan suka lula wata duniyar, sun sha soyayya kamar ba zasu dena ba. Duk wasu sassan jiki na Fally magana suke, yana jin tamkar ana saka masa lantarki. Bai fahimtar meke faruwa, amma yana jin abun da karfi sosai da haɗuwa iya haɗuwa, zuciyar sa na wani irin bugawa da za'a iya jiwowa daga nesa, numfashin sa na yin sama-sama. Yanayin ya dauke su wani dogon lokaci, dukan su biyun suna jin su tamkar a wata duniyar da su biyu kaɗai zasu iya rayuwa a ciki, kuma domin rayuwa a cikin ta, dole sai sun rayu tamkar a gangar jiki daya.

Ƙarar da Jinah ta kwalla ne ya kawo karshen yanayin da suke ciki, Fally ne ya gatsa mata wani cizo a gadon baya, ba da gangan ba. Jin ɗanɗanon jinin a bakin sa ya dawo dashi duniyar mu. Jinah tambayar kanta take :
-Me yasa nake jin zafi alhali mafarki nake?

************************


💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story
Chapter 26 · 0% Book details