← Book details Jinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 27

CHAPTER 18

Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Cikin kankanin lokaci, Jinah duk tabi ta lalace, ko ina a jikinta kasusuwa ake gani, rama ta ban tausayi tayi ba tare da tasan wace irin cuta ke damunta ba, eh cuta mana me zuwa ba tare da sanarwa ba ko dalili, abar da kullum muke takatsantsan wajen ganin mun kare kan mu daga kamuwa da ita. Cuta bata bamu zabi. Muna iya wayar gari lafiya amma mu kwanta da ciwo, mu dinga jin wani yanayi da zafi da ba zamu iya misultashi ba wanda hakan zai sa muje asibiti domin a fada mana abinda ke damunmu. Sai dai ita tata cutar Jinah, har likitocin sun kasa ganota, sakamakon ganin abu yaki ci yaki cinyewa Sarah ta dauketa zuwa asibiti sedai an kasa gane sahihin abinda ke damunta. Gashi dai a jikinta da ka gani kasan batada lafiya, amma kuma sanin ciwon nata ya gagara. Ganin haka likitocin suka bata shawarar kawai taje birni domin a kara dubata amma taki a cewarta idan har likitoci sun kasa gane abinda ke damunta wata kila ciwo ne mai wucewa, ba babba ba.

Sedai kuma kullum ciwon nata kara ta'azzara yake, wannan ma ne yayi sanadin jinkirin tafiyar su Abdul.

Halin da take ciki ya tayarwa da kowa hankali ba kamar ma yan tagwaye da suka kasa yin komai har da karfin tsafinsu, a tsorace suke sosai.

-Me kake tunanin shine sanadin rashin lafiyar mama?
Aya ta tambayi dan uwanta.

-Ina tunanin baba ne!

-Me? Hakan ba zai yiwu ba, baka ga shima ya damu sosai ba, kuma shima yana iya kokarinshi ganin Mama ta warke.

-Eh, amma idan fa shine sila ba tare da ya sani ba, baki lura ba hakan ta fara faruwa tun lokacin da ya fara abinda tonton Dauda ya fada mashi zai yi domin mama ta tuna dashi.

Shuru yar uwar tashi tayi alamar tunani kafin tace:

-Kuma fa kanada gaskiya.

-Ya kamata muyi masa magana.

-hakan za'a yi.

Neman mahaifin nasu suka shiga amma basu ganshi ba, yanke shawara su jirashi suka yi. Kafin nan suka wuce wajen mahaifiyarsu.

-Nan da ba da jimawa ba zaki warke mama.
Cewar Aya.

-Nayi kewar fadanki.
Cewar Ayu.

-Karya ne, Mama bata yi mana fada.

-Eh gaskiya ne, Tanti Sarah ce ke yi mana fada.

-Amma ita mama idan muka yi laifi, kawai zata ce : a'a rabin raina, ba kyau abinda kuke yi, ku daina kunji kuma kar ku kara sakewa.

-Sannan sai ta kara da ina sonku sosai, kyawawan diyana.

-Kuma abinda zamu yi matsayin hukunci, shine mu rungumeta.

-Kuma ba zamu saketa ba har sai taso hakan.

-Muna sonki mamamu !

Duk da halin da jinah take ciki, sai da ta jawosu jikinta ta kankamesu, sosai kalamansu suka tabata ta yadda hawaye suka kasa tsaya mata. Zuwa cen kuma ta fashe da kuka, sedai kukan nata kuma da nashi dalili, ba komai ba ta tuna face yanzu idan ta mutu a wanne hali zata bar 'ya'yanta, duk da ta tuna hakan hankalinta na matukar tashi ganin irin shakuwar dake tsakaninsu.

Jinah bata daina kuka ba har lokacin da Dauda ya shigo dakin. Tagwayen fita suka yi suka barta daga ita sai mijinta.

-Ni fa wannan koke koken naki sun fara isata!
Cewar Dauda a fusace, idanu Jinah ta fiddo cike da mamaki.

-Gaskiya na fara gajiya.

-Me.. Me yake damunka? Tsawa fa kake min?

Jinah ta fada tare da kara fashewa da kuka, ko sau daya mijinta bai taba yi mata haka ba.

-Kiyi hakuri, ki yafe min, ba a son raina ba, ki yafe min dan Allah. Kinsan ina sonki fiye da komai.

Mamaki ya kara dabaibaye Jinah ganin yanda ya koma yana bata hakuri. Zuwa cen Dauda kamar an bangajeshi yayi baya ya bugu da bango, yanayin fuskarshi ya fara canjawa, da ta nuna suffar mugun mutum sai kuma ta sauya zuwa ta nutsatsen mutum. Jinah bata ankara ba taji Dauda ya shaketa kamar zai kasheta, kokowar kwatar numfashi ta shiga yi, zuwa cen kuma ya saketa sannan ya rugumeta yana kissing dinta. Sosai Jinah ta tsorata da lamarin Dauda. Mikewa Dauda yayi, sannan ya fara buga kanshi jikin bango yana fadin :

-Ka mutu ! Eh amma kuma gangar jikina ce ! Ni kuma ruhina ne ! Ba zan barka ka cutar da ita ba ! Ni ban damu da ita ba !...

Juyawa Dauda yayi wajen Jinah sannan ya shiga juya kanshi hagu da dama, kuma duk lokacin da yayi hakan sai kamannin fuskarsa sun canja daga ta salihi zuwa ta mugu. Daga karshe dai ta muguntar ce tayi nasarar tsayawa, cike da mugunta ya dunfari Jinah kafin ya nausa mata wani naushin da yayi sanadin sumanta.

A wancen ranar Aljana Hindu da mataimakinta makabarta suka je, sunje da niyyar kawo karshen rayuwar wannan aljanin ne domin taso da Dauda. Tayi anfani da ruhin aljanin a gangar jikin Dauda. Hakan yasa aljanin ya koma mutum ba tare da ya manta da tunaninsa na aljanu ba. Hindu tasan idan ta aika aljanin directly, tagwayen zasu iya halakashi. Amma yanzu wannan hadin da tayi shine kadai hanyar da zata iya samun cikar burinta ba tare da wata matsala ba, sedai kuma wata barazana da zasu fuskanta a yanzu shine, tsananin soyayyar da Dauda yake wa Jinah, da kuma zaman gangar jikinsa a kusa da ita, yasa kwalwar asalin Dauda ta fara aiki, a hankali a hankali yana dawowa Dauda. Gangar jikin ta fara kokowa da ruhin, da ganin ta hanashi yin duk wani abu da bai dace ba.

A yanzu haka dai Aljanin ne ya dauki control din jikin ta yanda har ya sumar da Jinah, yanke shawarar zuwa ya samu uwar gijiyarsa yayi sai kuma ya tuna da yanda Hindu take ba zata yi jinkirin kasheshi ba domin bata son duk wani abu da zaya kawo mata cikas a cikar burinta.

Bayan wasu lokuta Jinah ta farfado taga Dauda kwance a gefenta yana ta sharar bacci, a tunaninta mafarki tayi, ajiyar tayi tare da cewa : wannan wane irin mummunan mafarki ne nayi.

(.....)

Sarah ce ta shigo gidan a kasalance, Nafisa da gudunta tazo ta taimaka mata ta zauna kan tabarmar dake shinfide a tsakar gidan, dan kishigidawa Sarah tayi.

-A ina kika je aunty Sarah ina nan duk na damu ?

Nafisa ta fada cike da nuna kulawa. Tsantsar nuna kulawar da Sarah ke yi masu yasa a kullum take kara sonta, kuma tana damuwa idan ta ganta cikin wani hali.

-Ganin likitoci sun kasa yin komai game da rashin lafiyar Jinah, shine na tafi neman mai maganin gargajiya.

Sarah ta fada da muryar damuwa.

-Kuma shine zaki tafi cikin wannan ranar, kema bakya tsoron wata rashin lafiyar ta kamaki ?

Abdul ne ya karaso wajensu, ba tare da ya yarda ya hada ido da matar babanshi ba. Duk da abinda ke faruwa tsakaninshi da ita ba zai so ganinta cikin wani hali ba. Yar uwar tashi ce tayi masa bayanin inda Sarah taje, shiga yayi cikin kayansa ya dauko magani doliprane, da taimakon Nafisa Sarah tasha maganin, kafin wani dan lokaci taje tayi wanka, sannan Nafisa ta danyi mata massage kafin ta kyaleta tayi bacci.

Haka gidan ya kasance tsit, kowa yayi bacci banda yan tagwaye dake jiran dawowar babansu. Bayan tsawon wasu awanni sai gashi ya dawo.

-Ina ka tafi baba ?

-Ina tunanin ai zaku iya sani.

-Ai ka hanamu anfani da tsafinmu ga mutanen dake cikin gidan nan, idan ba ya zama dole ba.

-Hakane.

Yau tsawon watanni kenan Fally yake son ko ta yaya yaga ya dawo da matarshi, yanzu kuma da ya samu hanyar ance masa duk cikin aikin ne matar take fama da wannan ciwon.

-Idan mama ta cigaba da rashin lafiya, ba zan taba yafe maka ba.

Ayu ke fadawa mahaifinsu da alamar kashedi, kafin ya bar wajen yar uwar ta rufa masa baya.

Shi Fally a tunaninsa ciwon nata na wani dan lokaci ne daga nan komai zai koma masu daidai. Abinda Dauda yace masa yayi shine : Sake yin wani alkwarin aure tsakaninsa da Jinah kamar a baya «Wata yar karamar wuka Fally ya dauko tareda yanka babban yatsanshi, itama haka Jinah tayi, sannnan suka hada yankakkakun yatsun nasu gu daya inda jinin nasu ya garwaya. Bayan sunyi hakan sannan Fally ya dauko wata kwarya mai dauke da wasu koren ruwa, ya fara sha sannan ya ba Jinah itama tasha.

Jinah cire zanin dake daure kugunta tayi, sannan ta kara cire wanda yake daure a kirjinta. Kwantawa tayi akan wani jan kyalle dake shinfide a gurin babu komai a jikinta. Shima Fally dama wani gajeren wando kadai a jikinshi ya fiddashi, sannan ya zuba wasu ruwa a jikin Jinah, bayan wani dan lokaci sai ga wani maciji ya bayanna a hannunshi, sakin wannan maciji yayi yanata bin jikin Jinah, ita kuwa ko a jikinta, dan ta san wannan yana daga cikin siddabarun alkawarin nasu, kuma daman ta iya sarrafa dabbobi kamar sauran aljanu, kuma kasancewar kyawun dake gareta irin na aljanu yasa tana iya yin wasu abubuwa sosai wanda cikakken dan mutum ba zai iya ba.

Macijin ya bace bayan wasu yan lokuta. Bayan wannan, cikin farin ciki Fally suka raya wannan rana kamar kowanne ango da amarya. Hakan zai nuna sun dau alkawarin zama na har abada a tare.»

Wannan shine abinda ya faru ranar aurensu, ranar alkawarinsu. Sai dai yanzu da yake son ya sake yin haka a cikin mafarkin Jinah, komai sai ya jagule, domin ita Jinah, ta kasa fahimtar komai, ta tsorata da ganin wannan mutumin yana tursasata shan wani abu da bata san ko meye ba, da kuma yanda taga maciji na tafiya a jikinta, kuma ta firgita sosai na ganin mutumin nan ta karfi yana yi mata fyade. Komai da ya kamata suyi cikin soyayya ita gani take ta karfi ne yake mata. Shi kuma ganin yake komai zai daidaita daga baya zasu zamo a tare kuma hakan shine muradinsa. Sam ya kasa bude ido ya farka ya kwaci kansa daga tarkon aka yi masa, ya gane wannan ba soyayya bace yake nunawa Jinah, kawai yana cutar da ita ne. Dadi da kari ma, kusan kullum sai ya bayyana akan idanunta sannan kuma ya bace, hakan ma bai san dab yake da haukatata ba.

A zahirance Fally bai san hakikanin abinda yake kokarin yi ba, bai san yana sanya rayuwarsa, ta Jinah da kuma ta 'ya'yansa a hadari bane.

Yayi nisan da ba zai iya gane abinda Dauda ya fada masa zai kaishi ga rasa duk wani farin

ciki nasa, kuma a hakan zai cigaba ba tare da yasan wadda yafi tsana a duniya wato Aljana Hindu yake taimakawa da kokarin cika mata burinta ba.

----------------------------------------------

Domin sanin abinda zai biyo baya kan abinda Fally yayi. Mu hade a Chapter na gaba.

Fatan wannan chapter ta kayatar daku ? Zan yi farin cikin ganin ra'ayinku.

Sannan ina bada hakuri akan kuskuren typing.

*©El_Ashtar*

Allez à la prochaine Readers 💪

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story
Chapter 18 · 0% Book details