CHAPTER 20
Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Aya da Ayu sun shiga rudin tashin hankali na ganin halin da iyayensu ke ciki, babu wata hanya da ta rage masu ta ceton iyayen nasu. A tunanin Aya kenan, domin dan uwanta tuni ya yanke hukuncin abinda zai yi, ya yanke hukuncin tafiya ya sadaukar da rayuwarshi akan iyayenshi da yar uwarshi.
-Je ki ga mama, sannan ki tsaya kusa da ita.
Ayu yaba yar uwarshi umarni. Ya kara da cewa :
-Ni zan je wurin baba.
Sai dai karya yayi mata. Gyada kai yar uwar tashi tayi ba tare da bata lokaci ba tabi umarninsa. Shi kuwa sai ya dauki hanyar zuwa wurin Hindu tare da rakiyar Dauda. Kafin su karasa sai da suka biya ta cikin bakin tsibiri wanda mutane basu iya ganinsa, suka debo ganyen Fula, a take Ayu ya saka a baki ya tauna kafin ya hadiye. Bayan yayi hakan, suka dauki hanyar gidan Hindu.
Suna zuwa kusan gidan, Ayu yayi kamar ya galabaita. Koda Hindu ta tsinkayesu tayi wata kururuwar jin dadi. Ayu sai ganin yayi ta dira gabanshi. Kyakyawa ce sosai, ba za'a kwatanta gashinta da na mahaifiyarshi ba wajen kyau. Hakoranta har wata walkiya suke tsabar haske da kyau, batada siffar miyagun aljanu. Katse masa tunani tayi ta hanyar tambayar Dauda.
-Amma abin yayi sauri kuma ina yar uwar tashi?
Bata samu amsar tambayarta ba, sai dai wata mahaukaciyar dariya da Dauda yayi. Hindu da Ayu cike da mamaki suke kallonsa.
-Kayi tunanin na kawoka nan ne domin ka kashe shugabata? To ba komai nayi ba face saukaka mata shirinta.
Ayu ya fahimci tarko ne ya fada, kokarin amfani da karfinsa yayi amma ya kasa sakamakon gubar dake jikinsa. Aljanin bayani ya yiwa Shugabar tashi da dalilinsa na yin haka, ita kuwa ta kara kecewa da mahaukaciyar dariyar jin dadi. Kawai zuciyar Ayu zata cire daga nan zata wanketa da wasu ruwan tsafi shikenan zata iya cinta ba tare da wani lahani ba.
-Toh idan har na mutu iyayena zasu tsira?
Ganin dariyar da suka kara kecewa da ita, ya gane zai mutu ne ga banza ba tare da ya ceci iyayensa ba. A zahirance ganyen Fula da yaci, ya kama duk wata hanyar jini ta jikinsa, sannan ya raunanar dashi ta yanda ba zai iya amfani da karfin tsafinsa ba. Kuma idan gubar ta dauki kwanaki cikin jikinsa zai mutu.
-Da gaske akwai hanyar da za'a iya cetonsu?
-Sosai ma.
-Fada mini, ina saurare.
-Babu abinda zai amfaneka domin ba zaka fita nan a raye ba.
-Na sani kawai ina son na sani ne.
-Kawai tasan ko shi waye kuma ta yafe masa.
-Ban gane ba.
-Ba amfanin ka gane. Manfa kawo min wukar nan.
Cika umarninta aljanin yayi, sai dai kuma ya tsaya cak yana waswasin ba shugabar tashi wukar, a wannan karon ma, ruhin da gangar jikin suka shiga dambe, Dauda na kokarin hana aljanin dake jikinsa bayar da wukar ga Hindu. Kiran sunan Aljanin da Hindu tayi, yasa aljanin yayi nasarar daukar control din gangar jikin.
-Me yake damunka ne?
Hindu ta tambayi aljanin a fusace.
-Babu komai shugabata.
Amsar wukar tayi, ta juya kan Ayu da yake ta kallonta ba tare da karfin kokarin kare kansa ba. Kwantar dashi tayi tare da dauko wani farin gari kamar hoda ta shafa masa kan kirjinsa, sannan ta dauki wukar ta kai daidai kan bakinta a take ta huro wuta daga bakinta zuwa kan wukar, ba ita ta dakatar da wutar ba har sai da taga wukar ta koma jawur. Sannan ta nufo kirjin Ayu da ita, da ganin haka shi kuwa ya runtse idanunsa, yana takaicin mutuwar da zai yi ba tare da ya ceci iyayensa ba....
-Ki dakata!
Cewar wata murya cikin karaji, Ayu ya gane mai muryar, bude ido yayi tareda ajiyar zuciya. Ba kowa bace face Aya yar uwarshi. Kallo daya ta yiwa wukar dake hannun Hindu, wukar ta fadi kasa. Ajanin dake jikin Dauda ya dauki wukar ya dumfaro Aya da ita, ganin haka Hindu ta ari wannan damar ta gudu, sosai take shakkar karfin yan tagwayen nan. Sumar da Dauda Aya tayi ta hanyar nunashi da yatsa, yayi sama ya fado kasa. Daga nan ta bace dasu duka zuwa gidansu.
-Ya aka yi kika gane inda nake?
-Zan iya sanin inda kake a kullum, ba kamar idan kana cikin hadari. Wannan ba shi bane mai muhimmanci a yanzu, zaka sani a duk ranar da na shiga hadari nima. Yanzu fada min ya aka yi ka tsinci kanka a cikin wannan halin?
Labarin duk abinda ya faru dan uwan nata ya bata.
A'a...a'a.. take maimaitawa tana girgiza kai.
-Kana..kana.. kana nufin kaima zan rasaka. Da kai nake tunanin zamu ceci iyayenmu kuma shine kai ma zaka tafi ka barni. Kada ka yimin haka dan uwana.
-Ki yafe mani Aya. Wannan gubar tana daukar lokaci kafin ta kashe mutum. Kar ki damu zamu samu mafita kafin lokacin. Abu mai muhimmanci dai a yanzu, mu ceci iyayenmu. A yau wannan muguwar aljanar ta bayyana mani, babu abinda ba zamu iya ba da karfin mu.
-Amma ta yaya zamu san abinda zamu yi?
-Dauda, ko kuma nace aljanin dake jikinsa, bawanta ne shi, dole zai san yanda zamu yi.
Ruwa masu sanyi Aya ta zuba masa a jiki, firgigit yayi ya tashi tare da mikewa tsaye. Kokarin guduwa yake, amma yaji kafafuwansa kamar an saka masa siminti.
-Zauna!
Aya ta umarceshi, ba bata lokaci yabi umarninta, bayan ganin shugabarsa da yayi, wadda duk duniyarsu ake tsoronta ta gudu gaban wannan yarinyar, waye shi da ba zai ji tsoronta ba.
-Ta yaya zan iya ceton dan uwana da kuma iyayena?
-Na...na rantse miki, ban sani ba!
-Kasan yanda za'a dawo da tunanin mamarmu?
Cewar Ayu.
-Me hakan zai amfanar ne?
Aya ta tambayeshi da mamaki.
-Hindu tace, domin cetonsu, kawai sai ta tunashi sannan kuma ta yafe masa. Da farko ban gane me take nufi ba, amma da nayi tunani na gane da iyayenmu take.
-Kanada gaskiya. Maza muna sauraronka! Ta yaya zamu yi hakan?
-Dole sai kun rushe alakar dake tsakanin mahaifiyarku da kuma uwar rikonta wato kakarku wadda ta haifi babanku. Kakarku ta mutu, naji wannan ne daga bakin Hindu. Indai har Jinah ba zata iya tuna rayuwarta ta baya ba, to saboda alakar dake tsakaninta ne da kakarku.
-Ta yaya zamu iya gane menene ya hada alakar tasu?
-Wannan mahaifiyarku ce kawai zata iya sani.
-Amma bata cikin hayyacinta, kuma ma ba zata iya tuna rayuwarta ta baya ba.
-Zaku iya bincikawa a cikin kwalwarta.
-Da gaske?
-Eh to ina tunanin haka, domin shugabata tace min ba abinda ba zaku iya ba.
-Ta yaya zamu yi haka?
-Ban sani ba.
Ba tare da bata lokaci ba, Aya ta nufi inda mahaifiyarta take. Ganinta yasa taji wani abu mai radadi yabi duk ilahirin jikinta, a kwance take tamkar gawa.
Tsoro ne ya kamata, na kar taje ta tabata taji babu rai a jikinta. Daurewa dai tayi, ta runtse idanunta kafin ta dora duka hannuwan nata biyu kan goshin mahaifiyar tata, da farko kasa ganin komai tayi, kafin daga baya kamar walkiya taga tunanunnukan mahaifiyarta na baya. Cigaba da dubawa tayi har ta kai ga wani wuri inda taga wata karamar yarinya zaune tare da wata mata suna magana. Tabbas wannan mamata ce da kakata. Ta fada cikin ranta.
-Ina so na fada maki wani abu, domin nasan yanzu kinyi girman da ya kamata ki gane.
Cewar Matar.
-Menene mama?
-Ni ba asalin mahaifiyarki bace, mahaifiyarki ta rasu yayin haihuwarki, kuma ita ta bani amanarki. Kuma ita bil'adama ce mu kuwa aljanu ne.
Kuka yar karamar yarinyar tayi kafin tace :
-Na dade ina jin sauran yara na ce mani bil'adama amma ni na kasa fahimta. Kenan shikenan daga yanzu ke ba mahaifiyata bace?
-Sam ko alama, ni mahaifiyarki kuma zan cigaba da kasancewa mahaifiyarki har abada. Ke 'ya ce da banyi tunanin samu ba, ke komai ce gareni 'yata Jinah.
-Nima mama, ina sonki kuma ina son na zama aljana kamarki.
Murmushi uwar tayi.
-Ai ba mai yiwuwa bane 'yata, sai dai zaki yi kama damu, kuma ma kyanki ba kasafai ake samunsa ba ga bil'adama.
-Da gaske?
-Sosai ma, matso ki gani.
Matsowa yarinyar tayi, matar ta debo wani dogon gashi daga gashin kanta ta dora kan na yarinyar tare da shafa shafa gashin. Cikin dakiku kadan gashin kan yarinyar ya kara tsawo har kan mazaunanta. Yarinyar tana ta murna ganin gashinta ya koma irin na sauran 'ya'yan aljanu.
Aya kara ganin wani tunanin tayi, matar dai ce da kuma karamar yarinyar. Wannan karon, matar fidda zobenta tayi sannan ta dunkuleshi a hannunta, tana budewa sai ga zoben ya zama biyu kuma iri daya. Sakawa Yarinyar tayi daya, sanann ta sakawa kanta dayan.
Wani tunanin Aya ta kara gani. Sai dai wannan karon ta gane mahaifiyarta ce. Tana kwance kasa da alamun bacci take, wannan matar ce tsugunne gefenta.
-Idan kika tashi ba zaki tuna komai na rayuwar da kika yi damu ba, sannan zaki rayu da bil'adama yan uwanki.
Cewar matar kafin ta bar Jinah a gurin.
Bayan wannan Aya bata kara ganin wani tunanin ba. A nan ta fahimci wannan tunanin su ke nuna alakar dake tsakanin Jinah da kuma uwar rikonta. Ta fahimci abinda ya kamata tayi, anan take tayi kokarin yin kudirinta. Sai dai a daidai lokacin sai ga su Sarah sun shigo dakin. Ta so ta jira har su fita, amma kuma sai tayi tunanin yanzu duk wani minti da zai shude barazana ne ga rayuwar iyayenta. Fita tayi daga dakin sannan ta sake dawowa amma wannan karon su Sarah basu ganinta. Shiga bincikar gashin mahaifiyarta tayi wai ko zata ga na kakarta, amma sai dai da yake gashin kala daya ne sai ta kasa tantancewa. Daga karshe dai yanke shawarar ta yanke gashin gaba daya tayi. Kara Nafisa da Sarah suka saki ganin gashin kan Jinah yana ta zubewa kasa.
Shi kuwa Abdul fita yayi da sauri ya kira likita. Lokacin da likitan yazo, kiransu yayi duka ukun zuwa ofishinsa. Nan Aya ta samu dama ta cigaba da aikin da take. Tana gamawa ta cire zoben dake dan yatsan Jinah. Yanzu abu na uku ya rage masu, abinda ta kasa fahimta a cikin tunanin kuma bata san ko meye ba.
A cikin ofishin likitan, su Sarah sun zura masa na mujiya domin jin abinda zai ce.
-Ina mai baku hakuri. Ya fada, tuni Sarah taji zuciyarta kamar zata fito daga kirjinta.
-Likita me yasa kake bamu hakuri, ba abinda fa muke son ji bane.
Cewar Abdul da kaguwar jin dalilin likita.
-Muna tsare da ita ne a banza. Babu wani abu da zamu iya yi mata. Abun yi anan shine ku mayar da ita gida ta karasa sauran kwanakinta. Domin kunga nan karamar asibiti ce mu kan mu muna da bukatar gadon domin wani majinyacin. Kuyi hakuri dan Allah.
Ba tare da tace uffan ba, Sarah ta juya ta koma dakin da Jinah take su Abdul na biye da ita. Ba karamar razana suka yi ba, ganin gashin kan Jinah zube a kasa iska na dauka, kanta babu komai kamar wadda aka yiwa sabon kolo. Durkushewa Sarah tayi, ta shiga rera kuka mai ban tausayi haka ma Nafisa ta kama mata suna tayi. Abdul ne yayi karfin halin tsince gashin ya zuba a leda, da taimakon wasu ma'aikatan suka bar asibitin zuwa gida. Haka su Sarah suka cigaba da kuka har suka kai gida.
-Kalleki, yarinya dake, da kuruciyarci kike shan wannan wahalar. Gashi yanzu zaki tafi. Wayyo Jinah, me zan yi ne domin ki tsaya. Ta dalilinki nasan me ake cewa samun 'ya. Kada ki rabani da wannan farin cikin tun yanzu, kiyi tunani akan yaranki Jinah. Suna bukatarki a kusa dasu...
Kuka yaci karfin Sarah ta yanda har makoshinta ya fara yi mata ciwo. Haka Sarah ta zauna kusa da Jinah har lokacin da Abdul ya shigo dakin.
-Na samu tayi bacci.
Bayanta Sarah take dubawa domin ta tabbatar idan da ita Abdul yake. Domin sam Abdul ya daina yi mata magana.
-Wa..wa kenan?
-Nafisa
-Ah hakan yayi kyau, ai dole tana bukatar bacci.
-Ke ma ya kamata ki kwanta.
-Ba.. ba zan iya ba, ina tsoron na kwanta na tashi naga bata a raye.
-Nima wannan nake tsoro.
-Su kuma yan tagwaye baki gansu ba?
-Ah suna dakina, Ayu yayi bacci ita kuma Aya tana zaune kusa dashi. Ina tunanin basu fahimci halin da ake ciki ba.
A kusa da ita ya zauna, suka cigaba da gadin Jinah kamar hakan zai hana mutuwa tazo daukanta.
A bangaren yan tagwaye kuwa. Aya ta bayyanawa dan uwanta duk abinda tayi sannan ta fada masa abu na ukun da bata san meye shi ba, kuma dole sai ta ganoshi ta lalatashi kafin iyayensu su rayu.
-Gara da kayi kamar kana bacci lokacin da Abdul ya shigo. Hakan zai kawar da hankalinsu daga garemu.
Cewar Aya ga dan uwanta.
-Toh me kika ce masu game da Dauda?
-Ce masu nayi ya tafi nemo wa mama magani.
-Makaryaciya!
Ayu ya fada cikin sigar zolaya, murmushi Aya tayi.
-To yanzu me zamu yi? Bansan meye cikon abu na uku dake da alaka da mamarmu da kuma kakarmu ba. Kawai abinda na sani ta tattare kayan mamarmu, sannan ta dauketa ta kaita nesa kafin ta sumar da ita sannan ta barta a wurin.
-Kar da ki damu zamu gano ko menene.
-Amma kuma lokaci tafiya yake, idan bamu sameshi ba fah, zasu mutu Ayu, shikenan zamu zama mu kadai muka rage.
-------------------------
Voilaaaaaaaaaa ! Anan zan dakata sai kuma wata chapter idan Allah ya kaimu. Fatan kunji dadin wannan chapter, idan kuwa hakane ku nuna min ko da stickers ne 🤓 A tunaninku meye abu na karshe da yayi saura a alakar Jinah da uwar rikonta? Sai naji daga gareku!
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story