← Book details Jinah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 27

CHAPTER 10

Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Hankalin Sarah yayi matukar tashi lokacin da ta tabbatar Kimba ya rigata dawowa gida. Tsoron nata kasa boyuwa yayi har Jinah ta fahimci halin da take ciki. Kokarin kwantar mata da hankali tayi.

-Babu abinda zai yi maki, ba ce maki yayi, idan yaje cen zai dade bai dawo ba? To kenan ban ga dalilin tada hankali ba ganin ba wani dadewa yayi ba sosai.

-Eh, amma...

-Ba wani amma, ki kwantar da hankalinki, ni nan nasan me zan yi.

-Me zaki yi?
Sarah ta tambayeta tana kwalalo ido.

-Ke dai ki jira zaki gani.

Jinah ta fada cike da tabbatarwa, dariya Sarah take wanda har tsoron nata ya gushe. Ita kuma Jinah fuska tayi, irin yanayin ita fa ba da wasa take ba. Ta tsani mutumin nan duk da bata taba ganinsa ba, kuma lallai ya cancanci a koya masa hankali. Kokarin shiga gidan suka yi ta baya, sai dai ganin kowacce da yaro a hannunta, so ba zasu iya shiga da kayan baki daya ba. Goya Aya Jinah tayi a bayanta sannan ta dauki Ayyu a hannu, ita kuma Sarah ta shiga da kayan. Duk wani taku idan tayi zuwa cikin gidan, sai taji tana kara kusanto muryoyin dake magana cikin gidan, muryar mijinta da wasu da ta kasa gane su waye take ji. Su waye wadannan mutanen? Wata kila daya daga cikin kishiyoyina ne. Ta fada cikin ranta. Dakinta ta nufa a maimakon ta nufi inda mijin nata yake, domin ajiye kayan nasu, sai dai...

-Sarah!

Muryar Kimba taji ya kwala mata kira. Wani bugawa zuciyarta tayi, taji yin numfashi na shirin gagararta, Sakin Jikunan dake hannunta tayi. Kamar wata sakago, ta juya a hankali suna fuskantar juna.

-Ina son magana dake, ki sameni a daki.

Ya fada cikin wani yanayi da ta kasa fahimta.

-Ina..ina zuwa.

Kayan ta fara kaiwa daki, sannan ta yiwa Jinah da tagwayen masauki kafin taje amsa kiran mijinta.

-Ina yini?

Ta fara gaidashi.

-An zo lafiya? Ya gajiyar hanya?...tun yaushe kazo?... Me kake so na hada maka, ko na kai maka ruwan wanka?...

Duk ta rude, tambayoyi take ta yi masa ba kakkautawa, ita dai kar dai yace tayi laifi. Cike da mamaki da daurewar kai taga Kimba ya nufota tare da rungumeta.

-Ta mutu Sarah, ta mutu!

Kimba ya fada cikin kasa da murya, amma kuma taji abinda yake fada. Karon farko kenan da taga Kimba cikin irin wannan yanayin gashi kuma har da hawaye. Tausayinsa ne ya kamata, a take ta manta da duk wani abu da yayi mata a baya, shafa kansa take da sigar lallashi. Bayan wani dan lokaci, bakin gado suka zauna, dora kansa yayi bisa kafafunta, ita kuma a hankali take shafa sumar kanshi. Bayan ta tabbatar kamar hankalinsa ya dawo jikinsa, ta tambayeshi:

-Kimba, waye ya rasu?

-Aisha, Matata ta farko.

Wani abu taji ya tokareta a kirji. Kenan nima irin wannan halin zai shiga idan na mutu? Tambayar da ta yiwa kanta kenan, da sauri kuma ta kauda tunanin. Fuskarta cike da damuwa, taji babu dadi na mutuwar kishiyar tata duk da basu taba ganin juna ba.

-Allah yasa kwanciya hutawa ce a gareta kuma Allah yasa aljanna ce makomarta.

-Ameen

Shuru na dan wani lokaci ya biyo baya, kafin Kimba yace:

-Akwai wani abu da nake son fada maki.

-Ina sauraronka.

-'Ya'ya uku muka haifa ni da Aisha, babban yana karatu ne a wajen kasa, su kuma biyun a tare muka zo. Ina son su zauna a nan, ina fata zaki kula dasu kamar ya'yan da kika haifa.

Kasa gasgata abinda kunnuwanta suka jiye mata tayi, duk matan da ke gareshi, a ce ita zai zaba ta kula mashi da 'ya'ya. Wata kila yana ganin ita daya ce zata rike masa su da amana, abinda bata sani ba, sai da ya kaisu wajen sauran matan amma suka ki karbarsu.

-Allah ya bani ikon rike amana, kuma naji dadin tunawa dani da kayi.

-Ameen, na sani Sarah ke yar halak ce. Nagode sosai.

Murmushi tayi jin wannan kalaman na yabo daga mijinta. Wata kila mutuwar matarshi ce tazo masa da shiriya.

-Zan je inyi wanka, sannan na hada maku wani abun ci.

-Ok, nima ina son yin wankan, amma kar ki wahalar da kanki, bana jin yunwa.

-Yaran fa?

-Eh, duka a koshe muke, kar ki damu.

-Ok, bari na kai maka ruwan wanka.

Kamar yanda tace, haka tayi, jawo ruwa tayi a rijiya dake tsakar gidan sannan ta kai masa bayi. Zuwa tayi ta tarar da Jinah da har ta fara bacci. Ta manta bata yiwa mijinta maganar Jinah ba. Sai dai akan wa zata gabatar da ita? Bata yi wannan tunanin ba ga kuma wadannan tagwayen. Zaune tayi tana tunani kafin Jinah ta bude ido.

-Lafiya dai? Me ya faru?

-Daya daga cikin kishiyoyina ce ta rasu, uwar gidan Kimba dake a Nigeria.

-Ayyah, Allah ya jikanta, ya kyautata makwancinta! Bata lafiya ne?

-Ban sani ba, amma rasuwarta ta taba Kimba sosai, dan nayi mamakin canjawarsa, wata kila dalilin rasuwarta ne, amma dai yau naga asalin Kimba da na sani kuma naso a baya.

-Masha Allah, Allah ya kara dorashi bisa hanya.

-Ameen, yazo tare da 'ya'yan marigayiyar, yace anan zasu zauna.

-To ya kike gani?

-Kema kin sani dole na karbesu hannu biyu sannan na kula dasu. Zan je in gansu, ko zaki rakani?

-Eh, me zai hana?

Fita suka yi daga dakin, suka bar tagwayen kwance suna bacci. Suna shiga dakin suka tarar da matasan zaune, macen ba zata wuce shekaru 15 ba, sai namijin saurayi ne da ba zai wuce 20 ba.

-Sannunku, kun wuni lafiya?

Sarah ta gaishesu, sai dai basu amsa ba, ko kallon tsiya bata samu ba. Kallon Jinah Sarah tayi da ta daga mata kafadu. Kara maimata gaisuwar tayi amma shuru basu amsa ba. Tashi suka yi, suka fita da tunanin wata kila har yanzu firgicin mutuwar mahaifiyarsu ne bai gama sakinsu ba. Bayan Sarah tayi wanka, itama Jinah ta shiga tayi. Kwantawa Jinah tayi gefen jariranta, ita kuma Sarah sai da ta tabbatar da diyan mijin nata sun samu wurin kwanciya sannan ta wuce dakin mijin nata.

Tarar da mijin nata tayi a kwance bisa gado, tunani tayi ko har yayi bacci. Kwantawa itama tayi gefenshi.
Cen cikin bacci taji hannunshi na shafa bayanta. Lebenta na kasa ta dan ciza, tana son ce masa a gajiye take, sai dai ba zata iya ba, ga halin da mijin nata ma yake ciki, kuma wannan shine karon farko da dadewa rabon da yazo mata cikin kwanciyar hankali. Juyawa tayi suna kallon juna, idanunta cike da sha'awa. Bata tsaya dogon tunani ba, ta biye mashi zuwa wata duniyar.

Washe gari, Sarah ta riga kowa tashi, gyara gidan tayi. Bayan ta idar ta nufi dakin da Jinah ta kwana domin tasheta tayi sallah. Kusan suman tsoro tayi, lokacin da ta tarar da yan tagwayen zaune suna kallon juna kamar wadanda ke tsaka da hira alhali ita uwar tasu bacci take ta yi abunta. Ido Sarah ta zuba masu, suma kuwa suka zubo mata nasu.

-Idan da ban sanku ba, to zan iya rantsewa aljanu ne ku!

Sarah ta fada tana kallon yaran dake ta yi mata murmushi.

-Gaskiya kuna da abin tsoro.

Ta fada kafin hankalinta ya koma kan Jinah da ta farka. Bayan ta fito daga dakin Jinah, ta nufi dakin yaran mijinta, tayi mamakin tarar da su suna sallah domin tuni suka tashi.
Fita tayi ta nufi tsakar gida inda ta ajiye gumba domin dama kokon karin kumallo.

(...)

Sarah na tsakar gida tana raba kokon da ta dama, sallama taji ana yi a bakin kofar gidansu. Amsa sallamar tayi tare da duba mai sallamar, da mamakinta taga Dauda, wani farin ciki ne ya lullubeta ganin Dauda a tsaye kan kafafunsa ya warke sumul. Tashi tayi da niyyar yi masa iso sai ga mijinta Kimba ya fito sanye da lafiyayyun kaya da jaka a hannu. Zuciyarta ce ta buga, ganin alamar tafiya zai yi.

-Kimba, ina kuma zaka je haka?

Ta fada da alamun tambaya a fuskarta.

-Ina ruwanki da inda zan je! Yaushe kika fara samun dokar sanin inda zan je?

Shuru tayi, domin ta tsorata da lamarin Kimba, mutum jiya take lafiya lau dashi, har ta fara tunanin zasu fara sabuwar rayuwa ganin kamar ya shiryu, ashe ba haka. Hawaye ne suka kwaranyo mata.

-Ina zaka je Baba?

Cewar 'Yarshi.

-Ba fa zaka tafi ka barmu a wannan gidan ba!

Cewar danshi.

-Ban son shirme, ba jimawa zan yi ba zan dawo. Kuma kar ku kuskura ku bar gidan nan. Kai kuma Samaila ka sake yi min magana haka, kaga yanda zan fasa maka baki, marar kunya kawai... Sai a yanzu ya lura da bakuwar fuska a wurin, yace: Kai kuma waye? Me kake nema anan?

-Sunana Dauda, kuma nazo wajenta ne, wato matata!

Dauda ya fada yana nuna Jinah da ta fito daga daki. Inda hannun Dauda ya nuna Kimba yabi da kallo, kwalalo ido yayi cike da tsoro, baki hangame kamar wanda yaga fatalwa. Duk wannan kallon ba kowa yake yiwa ba face Jinah. Sakin jakar dake hannunsa yayi, ya nufo inda take.

-Am..amma..ta..ta yaya.. kika dawo kyakyawa haka, ku..kuma kika mike tsaye kan kafafuwanki?.. Ya..yaya aka yi kika samu kafafuwa?..A'a ba haka kike ba, rarrafe kike yi a lokacin da nayi maki fyade.

"Nayi maki fyade" ita ce kalmar da kowannensu ya iya rikewa. Kimba jinsa yayi zube kasa sakamakon wani lafiyayyen naushi da Dauda ya aika masa a fuska. Sarah, kasa motsawa tayi, ita kuma Jinah ba ma zaka gane yanayin da take ciki ba...

(.....)

Kwance yake yana kallon sama, ya lula duniyar tunanin abubuwan da suka faru, yarintarsa, iyayensa, Mahaifiyarshi, Jinah... Tunaninsa tsayawa yayi ranar da zai rabu da Jinah, kuma a ranar ne aurensa da Jinah, murmushi yayi, murmushi mai ciwo. Zai iya cewa wannan ranar ita ce rana mafi dadi da ciwo a rayuwarsa, saboda bayan an rabashi da matarsa abar kaunarsa, mahaifinsa ya umurceshi da yaje ya dakatar da alkawarin da suka yi da Jinah, amma yaki yin hakan. Irin wannan umarnin sarkin aljannu ma yayi masa amma yaki yin hakan, wanda hakan yasa dole ya biya kin bin umarnin da yayi. Auren mutum babban kuskure ne a kabilarsu, mahaifinsa yace masa yaje ya dakatar da alkawarin shi kuma zai yi kokarin ganin ba'a turashi kurkuku ba. Fally shi bai shirya yin hakan ba, dan shi a ganinsa ba wani abu bane dan aljani ya auri mutum, sai dai bai san akwai kalubale da dama a cikin auren ba...

Fally yana ganin idan har ya karya alkwarinsu to dole Jinah zata auri wani, shi kuma abinda bai so kenan, yafi son Jinah tayi ta kasancewa tashi shi kadai. Kuma ma idan yayi hakan kamar yaci amanar Jinah ne, kuma ya karya alkwarin da suka dauka a tsakaninsu. Bayan awa 24 sun wuce wanda ya kamata ace cikinsu zai dakatar da alkawarin, Kaddararsa ta sauya, ya rasa duk wata kima irin ta aljanu.

Sarki ya aiko a kama Fally, a duniyarsu idan aljani yayi laifi ana zuwa kamunsa ne da wata azababbiyar sarkar wuta mai dauke da kananun kwari masu cin nama, idan wannan sarkar ta taba jikin aljani, shiga take har cikin naman jikinsa, ta sakar masa kwarin sun dinga cin naman jikinsa. Lokacin farko da ta taba jikin Fally, hannuwansa a daure suke ta yanda ba zai iya anfani da siddabarunsu na aljanu ba, Babu abinda ya iya yi face ihu. Bai taba jin matsanancin zafi a rayuwarsa irin na lokacin ba. A karo na biyu da za'a lafta masa ita, runtse ido yayi yana shirin jin saukarta. A maimakon yaji saukar bulalar, sai yaji an rungumoshi ta baya. Yana bude idonsa yaga bulalar ta sauka a bayan mahaifiyarsa da ta dantse hakori tare da runtse ido tsabar zafi. Ganin abinda mahaifiyarsa tayi yace:

-Me yasa kika yi haka mama? Me yasa kika zo nan? Me yasa kika bari bulalar ta tabaki?

-Kiyi hakuri ranki ya dade bamu ganki bane... kiyi hakuri.

Cewar Aljanun da suke bugun Fally cike da firgicin ganin bulalar ta sauka a bayan AYA mahaifiyar Fally. Domin babu aljanin da bai san da kwanan mahaifiyar Fally ba.

A wahalce mahaifiyar Fally tace:

-Idan har bakwa son ganin fushina, to ku gaggauta daina dukan dana, idan ba haka kuma kun san abinda zai biyo baya.

-Mun daina ranki shi dade, yanzu zamu maidashi cikin kurkuku.

-Karka damu Dana, zan fitar da kai daga wannan gun, nayi maka alkawari.

(...)

Girgiza kansa yayi domin dawowa hayyacinsa, a yanzu babu abinda ya rage masa face yin tunani domin kwanaki kadan suka rage masa. Kullum yana ji kamar ana cire wani bangare a jikinsa da wata wuta, da haka aljani ke fahimtar karshensa yazo. Juyawa yayi ya kalli inda abokin zamansa yake, tuni ya dade da mutuwa har wurin ya zama kamar sahara, babu komai da yayi saura a gawar sai kasusuwa. Shi ma lokacinsa kawai yake jira, duk da mahaifiyarsa tayi masa alkwari, amma ya riga da ya sare ba makawa sai ya mutu. Lokaci guda, idonsa suka fara yi masa nauyi, rufe idon yayi.

_Lokacina yayi Jinah._
_Ina matukar kaunarki Jinah._
_Na sani bayan mutuwata, zaki zama mai 'yancin kasancewa da wani, ni kuma idan haka ta kasance, zuciyata zata zama tamkar kwalbar da aka jefo daga kan bene mai hawan dari biyu._
_Nayi imani da soyayyarmu Jinah kuma zan cigaba da yin imani, tare da fatan kasancewa da ke a wata rayuwar._
_Ki cigaba da tunawa da ni, kamar yanda ba zan taba mantawa da ke ba, kema kar ki taba mantawa da ni, kar ki manta da ni Jinah!_

Fally ke fadar haka da tunanin maganarsa ce ta karshe. Domin ya gama sarewa cewa babu abinda zai hanashi mutuwa. Sai dai kamar almara, Fally yaji wani karsashi na kara bayyana a jikinsa, fatarsa na komawa daidai, wani karfi na kara shigarsa. Kasa yarda yayi, dan ya tabbatar, gwada bacewa yayi sai gashi ya bayyana a tsakiyar dokar jeji, Fally ya kubuta, Wani ihun farin ciki ya saki, ihun da yayi sanadin tsorata duk wata dabba dake cikin jejin.

*Libéré, délivré!*

A rayuwa, komai yanada dalili, a bayan kowanne al'amari akwai boyayyen sirri. Idan da Fally yasan me yayi sanadin fiddoshi to da zai gwammaci mutuwa.


--------------------------------

In cigaba ne? To na fara ganin likes da comments 😁

@El_Ashtar

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story
Chapter 10 · 0% Book details