Gabatarwa
Jinah Part 1 Complete Hausa Novel · about 26 min read
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
_Sabon labarin soyayya_
Na Malik al-Ashtar
*PROLOGUE*
Motsi take ji, takun sawun kafafu na kara tinkaro inda take, a jikinta tana jin ko meye ke nufota zai cutar da ita ne. Amma ta yaya zata iya guduwa, ta yaya zata iya guduwa domin ta buya? Alhali ba zata iya ba, domin sai da kafafuwa ake gudu, ita kuwa bata da su. Abinda kawai take iya yi shine tayi rarrafe. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta fara rarrafawa iya karfinta, duk da haka ba zata iya kubuta daga wannan mutumin da tuni ya nufo gurinta yana tangadi. Namiji kakkausa mai girma, jiki ne ya fara yi mata rawan tsoro koda ta hada ido dashi. Kallonta yayi tare da yin wani shu'umin murmushi, ita kuwa ganin hakan ma ya kara mata tsoro, kara kusanto ta yayi tare da durkusawa daidai kafafunta. Murya na mata rawa ta tambayeshi "Me kake so dani?" Ba tare da bata amsa ba ya kara kokarin riketa ita kuwa da sauri ta kara ja baya daga zaune bisa mazaunanta. Kara yunkurawa yayi ya rikota tareda fincike mataccen zanin dake jikinta. Tayi ta kokarin ta kwaci kanta, amma hakan ya faskara domin akwai banbancin karfi tsakanin su. Wani masifaffen wari ne ke fita daga jikinshi, warin giya ne, alamar yasha ya bugu ne. Cikin muryar kuka da ban tausayi take rokon wannan mutumi "Dan Allah kayi hakuri ka kyaleni! baka ganin yanda nake? Mumuna kuma gurguwa? Kayi hakuri ka kyaleni kar kara min wata najasar!"
"Ke kike ganin wannan a jikin ki, dan abinda nazo nema wajenki bayada wata nasaba da kazantarki ko gurguntarki." Kalmomin da kawai suka fito daga bakinshi, ya cigaba da abinda ya kawoshi. Bai rabu da ita ba har sai da yaga ya samu biyan bukatarshi, yayi mata fyade.
Sunanta Hauwa, ita kadai ke rayuwa cikin bukkarta nesa da wani kauye mai suna Kumana dake a wata kusurwa a kasar Nijar, kauye ne da kowane gida yake rayuwa cikin farin ciki amma banda ita, kauye ne da kowane makoci yake zaune lafiya da makocinsa amma banda ita. Sanadin munin da take da shi ga kuma kasancewarta musaka na rashin kafafuwa duka biyu yasa mutanen garin suka koreta a cewar su Mayya ce. Ta kasance ita daya ke da irin wannan halittar a kauyen, ita kanta ba zata iya tuna ina mahaifanta suke ba, kawai ta tsinci kanta korarriya kamar kare daga wannan kauye tun tana yar karamarta.
Bayan ya gama abinda yake so, ya fito ya barta a sume yayi tafiyarshi ba tare da ya waiwaya ba balle ya duba ko tana raye. Bayan wasu awanni Hauwa ta farka, matsanancin ciwon da zugin da tsakanin cinyoyinta ke mata yasa ta fashe da kuka mai tausayi, gashi babu wani da zai kawo mata dauki, ba dangin kusa balle na nesa.
BAYAN WATA TARA (9)
Wannan rana ta banbanta da sauran ranakun, Hauwa tana jin wani abu, tana jin wani abu da itama ba zata ce ga asalin abinda take ji ba. Ta tashi ne tana jinta cikin wani farin ciki, komai lafiya lau. Katon cikin dake jikinta ta shafa, jin alamar yanda dan cikin nata ke motsawa yasa ta saki murmushi. Sanadin wannan fyaden da wannan mutumi yayi mata watanni 9 da suka wuce yasa ta samu ciki,duk da ba wai kamar kowane da bane, shi ga sanadin yanda ta sameshi amma tana cikin farin ciki, ko ba komai yanzu tasan ba ita daya bace tanada mai debe mata kewa, wanda take samu tayi fira dashi duk da tasan ko dan cikin nata na jinta ba zai iya amsa mata ba. Tana jin dan cikin nata har cikin ranta, domin shine haske yanzu a gareta.
Fitowa tayi da rarrafe ta nufi cikin dajin domin samo abinda zata saka ma cikinta. Bayan taje ta samu 'ya'yan itatuwa da suka fado kasa taci ta koshi, komawa tayi gindin bishiyar wani mangoro dan ta dan huta kafin ta juya zuwa gida. Bacci ne mai nauyi ya dauketa har dare yayi, sheshekar kuka ne ya tayar da ita. Inda take jin sautin kukan ta nufa tana yi tana buya. Wata matashiyar mata ta gani sanye da zallan fararen tufafi ta gani a durkushe a kasa. Kasa dauke idanunta tayi daga kan wannan mata, don wannan shine karin farko da taga irin wannan halitta. Ta raya a zuciyarta "dan mutum ba zai iya samun irin wannan kyau ba haka, gaskiya wanann Matar tanada masifar kyau." Kasada ta dauka na karasawa kusa da matar tare da tambayarta "Baiwar Allah lafiya kike kuka?"
Cikin sheshekar kuka ta bata amsa "Yarona... yarona mutuwa zai yi idan ban bashi Yattaba ba, ganyen shuka da shine zai iya warwakar dashi!"
Cikin tausawa Hauwa tace "Ayyah, ai kuwa akwaishi a cikin killatacciyar fadamar kauyen nan." Matar tace "Ai ba yanda zan yi na shiga fadamar domin ni Aljana ce." Gaban Hauwa ne yayi wani mumunan faduwa, tsoro ya mamayeta, cikin ziciyarta take cewa : Na shiga uku ni Hauwa, yau kuma na taro abinda yafi karfina, aljanu wadannan dai masu karfin sihiri da shan kwalwar mutum, yau gani ga daya daga ciki. Me zan yi yanzu? Idan nace zan gudu, rarrafe nake kafin nayi wani yunkuri zata kamani. Ganin yanda jikin Hauwa ke mazari aljanar ta fahimci ta tsorata ne "Kar ki damu ba zan cutar dake ba, zaki iya tafiyarki ki kyaleni na cigaba da kukan mutuwar dake tunkaro yarona (Dana)." Hauwa juyawa tayi, tayi tafiyarta sedai ba gidanta ta nufa ba, wannan fadamar mai tsaro ta kauyen ta nufa, guri da dan Adam ne kawai zai iya shiga gurin, Idan har aljani yayi kuskuren shiga wurin to fa ba zai fito da rai ba, dan fadama ce da mutanen garin suka gada daga kakanin su mai cike da tsaro na tsafi.
Hauwa tana son ta taimaki wannan aljana, dan ita daya ce ta taba yi mata magana ba tare da ta nuna mata kyama ba. Cikin sanda da kulawa Hauwa tayi nasarar debo ganyen. Cikin kuka mai hade da farin ciki aljanar take ma Hauwa godiya, ta amshi ganyen da dan gudunta dan taba danta.
Lokaci na farko da Hauwa ta fara jin wani mummunan ciwon ciki ya turnuketa, da alama lokacin ne yayi, Haihuwa. Har awanni masu yawa suka shude Hauwa na cikin wannan hali, har lokacin da aljanar ta tardota.
"Na zo ne in maki godiya, ta dalilinki dana ya samu lafiya, ki fada min duk abinda zan yi maki ni kuma zan yi ma..." Tsayawa tayi da maganarta sakamakon ankara da tayi da halin Hauwa take ciki.
"Wayyo.. ci..kina, da alama ya..ro..na ne ke zuwa...!
Aljanar ta fahimci haihuwa ce zata yi, anan ta fara kokarin taimaka mata, bayan wani lokaci kadan ta haife 'yarta mace.
Aljanar ta rike 'yar tana murmushi tare da sanar da Hauwa abinda ta haifa. Murmushi da hawayen farin ciki ne suka kwacema Hauwa. Wuka aljanar tasa ta yanke cibiyar yarinyar sannan ta nadeta da zani.
"Ina rokonki da ki kular min da 'ya ki rike min ita,ki kawatata da kyau kamar naki, bana son ta wulakanta kamar yanda na wulakanta, ina son ki saka mata suna JINAH, ma'ana aljana da yaren mu..."
Sai yanzu aljanar ta fahimci kalar kalamin da Hauwa take, alama ce ta mutumin da karshensa yazo, domin bata karasa fadin abinda take son cewa ba rai yayi halinsa.
Aljanar daukar yar jinjirar mai suna Jinah tayi zuwa gidanta, kafin daga bisani taje ta bizne gawar Hauwa.
"Daga ina kike da dan Adam? Kinsan hadarin da ke tattare da kawota nan da kika yi?" Cewar mijin aljanar bayan ganin Jinah da yayi. "Yar matar nan ce da ta ceci dan mu, bayan ta haifeta ne ta mutu kuma ta bani amanar 'yarta ne kuma na dauka." "Amma kin sani sarai cewa,sauran dangin mu (Aljanu) ba zasu karbi dan Adam ba a cikin mu, kuma zamu fuskanci babban hukunci idan suka gano hakan." Sanin mijinta nada gaskiya yasa bata kara cewa komai ba, dan tasan ta riga da ta dauki alkawari kuma dolenta ta cikashi. Tuna alkawarin zata mayar mata da 'ya kyakyawa yazo mata, sedai tuni Jinah mai kyau ce dan tsabar kyau itama kamar aljanu take.
Jinah girma take yi a hankali a cikin wadannan halittu (aljanu), sedai ta ganin tsana a gun sauran aljanu, duk da su marikanta suna kaunarta sosai, suna jinta tamkar 'yar cikin su, kuma suna kareta daga dukkan wani sharrin aljani da yake son cutar da ita, tana samun kulawa haka daga wajen dan uwanta (dan marikanta wanda mahaifiyarta ta ceta) mai suna Fally, Fally yana matukar son Jinah dan a kullum sai yayi fada da yan uwanshi aljanu idan suka ce zasu taba Jinah. Son da yake nuna ma Jinah yayi tsananin da har iyayensa sun sanar dashi illar yin hakan, dan babu aure tsakanin dan Adam da aljani, kuma hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi kokarin taka wannan doka a duniyar aljanu, amma ina shi Fally bai san wannan ba dan tuni har yaga Jinah ta zama matarshi, kuma itama haka sosai take sonshi.
Wata rana Fally ya dauki Jinah zuwa wani kebataccen guri wanda wannan guri ya kasance anan aljanu wanda suka kasance masoya, suke alkawarin zama tare na har abada a tsakanin su. A lokacin Fally na da shekaru 18 ita kuma Jinah na da 16.
"Jinah kin shirya zama dani, zama dani har abada?" cewar Fally rike da hannuwan Jinah suna masu kallon Juna.
"Sosai ma, ina kaunarka kuma zan kasance koda yaushe a tare da kai." Ta bashi amsa cikin farin ciki
Wata yar karamar wuka Fally ya dauko tareda yanka babban yatsanshi, itama haka Jinah tayi, sannnan suka hada yankakkakun yatsun nasu gu daya inda jinin nasu ya garwaya. Bayan sunyi hakan sannan Fally ya dauko wata kwarya mai dauke da wasu koren ruwa, ya fara sha sannan ya ba Jinah itama tasha.
Jinah cire zanin dake daure kugunta tayi, sannan ta kara cire wanda yake daure a kirjinta. Kwantawa tayi akan wani jan kyalle dake shinfide a gurin babu komai a jikinta. Shima Fally dama wani gajeren wando kadai a jikinshi ya fiddashi, sannan ya zuba wasu ruwa a jikin Jinah, bayan wani dan lokaci sai ga wani maciji ya bayanna a hannunshi, sakin wannan maciji yayi yanata bin jikin Jinah, uta kuwa ko a jikinta, dan ta san wannan yana daga cikin siddabarun alkawarin nasu, kuma daman ta iya sarrafa dabbobi kamar sauran aljanu, kuma kasancewar kyawun dake gareta irin na aljanu yasa tana iya yin wasu abubuwa sosai wanda cikakken dan mutum ba zai iya ba.
Macijin ya bace bayan wasu yan lokuta. Bayan wannan, cikin farin ciki Fally suka raya wannan rana kamar kowanne ango da amarya. Hakan zai nuna sun dau alkawarin zama na har abada a tare.
Waje kuwa, sama tayi mugun baki, wanda hakan na nuna ba alkhairi a yau, eh babu alkhairi don saduwar mutum da aljani baya haifar da abu mai kyau. Lokacin da suka zo tafiya gida, Jinah da Fally sun lura da canjawar yanayi na garin, su kuwa ko a jikin su dan yau ta kasance masu ranar farin cikin da ba zasu taba mantawa da ita.
Fally daukan Jinah yayi suka nufi gida, tin daga nesa suke jiyo kukan Mahaifiyar Fally wato uwar rikon Jinah. Fally aje Jinah yayi suka nufi dakin mahaifiyar tasu. Mahaifiyar karasowa tayi wajen Fally kafin ta sakar masa wani masifaffen mari. Dafe kunci Fally yayi kafin ya dago ya kalli mahaifiyarsa cike da mamaki.
"Mama me ya faru? me nayi kika mareni?" Fally ya tambayi mahaifiyar tashi cike da mamaki. "Me ya faru mama?" Ita ma Jinah ta kara jefo ma uwar cikin mamaki.
"Baku ga yanda sama tayi bane? Ko baku ji kukan dabbobi bane? Ku a ganin ku lafiya a wannan lokacin mahaifin ku baya gida?" Kallon Juna Jinah da Fally suka yi dan su har yanzu basu fahimci komai ba.
"Ke Jinah tun tuni na fada maki, mahaifiyarki ta mutu, kuma mutum ce, kuma kema mutum ce, mu kuwa jinsin aljanu ne. Kuma akwai banbanci tsakanin duniyat mu da taku, wanda dole watara zaki nemi ki zama uwa, ki yi aure ki haihu, kuma hakan zai faru ne kawai idan kin auri mutum dan uwanki. Sai da na fada maki kar ki kuskura wata alaka ta hadaki da aljani!"
Yanda mahaifiyar take magana zaka fahimci ranta yayi matukar baci.
"Ni..Ni.." cike da i'ina Jinah ta fara kokarin ta kare kanta amma sai ta sunkuyar da saboda kunya.
"Mama kinsan muna son junan mu kuma..."
"Kai kuma ka rufa min baki, ai komai ma laifin ka ne! idan ba sakarci ba me ya kaika yin alkawari da ita? To ku sani abinda kuka yi babu wanda bai samu labari ba, dan yanzu haka mahiafin ku yaje amsa kira. Dama dangi sun jima suna son su ga bayan Jinah, yanzu kuwa ta sanadin abinda kuka yi kun basu hujjah kwararra da zasu batar da Jinah. Gashi bansan me zasu yi maku ba..."
Tsoro ne fal ya cika fuskokin matasan, dan Jinah har ta fara zubar da kwalla. Fally ne ya riko hannunta dan tabbatar mata da ba abinda zai samun su.
A take mahaifiyarsu ta fara hada kayan Jinah, dan bata son wani abu ya samu Jinah saboda ba zata yafe ma kanta ba, na rashin cika alkawarin da ta daukar ma mahaifiyar Jinah. Kuka Jinah ta fara, rabuwa da wadanda take tunanin sun zamar mata yan uwa abu ne mai ciwo garesu, mafi ciwo ma shine a rabata da abin kaunarta Fally.
Wanda tun tasowarta shine abokin rayuwarta kuma dan uwanta. Gashi yanzu har sun yi alkawarin zama na har abada a tare.
Shi kuwa Fally ya fada duniyar tunani, dan hankalinshi ya guje, ya kasa gane abinda ya kamata yayi. Kukan da yaci karfin Jinah ne ya dawo dashi hankalinsa, rungumeta yayi sosai sannan ya rada mata a kunne
"Ina sonki Jinah, ina makk son da ba zan iya rabuwa da ke ba, son da ba zan iya samun madadinki ba. Zasu rabamu amma na maki alkawarin zan samo mana hanyar da zamu zauna har abada. Mun riga mun yi alkawarin zama na har abada. Kada ki taba mantawa da hakan Jinah, Ke tawa ce, kuma tawa ni kadai!"
"Eh ni taka ce Fally, taka ta har abada."
"Ki min alkawarin ba zaki taba mantawa da ni ba."
"Nayi maka alkawari ba zan manta da kai ba, koda kuwa na so haka..."
Mahaifiyar su ce ta rabasu, da sauri ta finciki Jinah tayi sama da ita. Fally yayi kokarin ya bisu amma mahaifinsa da ke shigowa yayi sauri rikoshi.
"Ya kamata ka barta ta tafi Fally, idan ba haka ba zasu kasheta. Yanzu kaje ka dakatar da alkawarin da kuka kafin awanni 24 abun ba zai yi kyau ba."
Shiru Fally yayi bai ba mahaifin nashi amsa ba. Mahaifin ya dafashi yace "Kana jina Fally kayi sauri kaje yanzu!"
Juyawa yayi ya tafi, mahaifin nashi na tunanin ya tafi ya dakatar da alkawarin nasu ne. Sai dai shi a zuciyarshi ya kudura Jinah tashi ce har abada ba zai taba rabuwa da ita ba, alkawarin da yayi mata kenan kuma yasan itama ba zata taba mantawa dashi ba. Kuma dole ya nemota duk inda mahaifiyarsa ta kaita. To me zai sa yaje ya dakatar da alkawarin nasu?
Inaaa! wani masifaffen ihu ya saki wanda yayi sanadin tarwatsewar manyan itacen dake kusa dashi.
A bangaren su Jinah kuwa, wani nauyayyen bacci ne aljanar ta saka Jinah, Nisa sosai tayi da Jinah kafin ta kawota bakin wani kauye. Wani siddabaru ta yiwa Jinah wanda zata manta da duk wata rayuwarta ta baya, wadda tayi da aljanu, ta cirewa Jinah duk wani karfi dake gareta na iya sarrafa wasu abubuwa kamar yanda aljanu suke yi, har karfin dake ga Jinah na ganin aljanu shima ta cire mata, wanda indai ba shi aljani yaso Jinah ta ganshi ba.
Jinah ya dawo kamar kowanne mutum, kuma ko ba komai zata koma tayi rayuwa a cikin yan uwanta bil'adama. Jinah ta manta da Fally, ta manta da alkawarin da suka yi, ta manta da ita matar aljani ce.
---------------------------
Wannan shine prologue na sabon labarina mai suna Jinah (matar aljani), zan cigaba ne kawai idan kun ga yayi maku kuma naga comments sosai.
WhatsApp Contact : +22794203632
💞 *JINAH (Matar Aljani)*💞
by _Malik al-Ashtar_ ✒️
*You'd like this New ❤️ Story*
*CHAPTER 1*
Sanyanyar iska ce mai dadi ke kadawa, Bishiyu ne ke rangaji daga dama zuwa hagu. Tsintsaye sai shawagi suke a sama, ga kukan dabobbi iri iri sai tashi yake a wannan jeji. Wannan yanayin ne ya kara dada wa baccin da Jinah ke yi dadi. Baccinta take cikin kwanciyar hankali bisa babbar bishiyar kuka. Haka ta cigaba da bacci har lokacin da surutun da ake yi mata a kunne ya tasheta.
- Jinah! Jinah!
Wani karamin yaro ne ke maimaita hakan da alama so yake ya tasheta.
-humm...
cikin muryar bacci Jinah ke amsawa
-Ki tashi Tanti Sarah na kiran ki (Tanti na nufin kanwar uwa ko ta uba, ko matar uba a Nijar wanda haka ya samo asali daga yaren French kamar dai yanda wasu ke cewa Aunty da yaren English).
Ba tare da Jinah ta amsa mashi ba ta sauko daga kan bishiyar, tare da janyo babban zanin da ta shinfida bisa reshen bishiyar, sannan ta rufe duka jikinta dashi har da fuskarta.
-Tanti Jinah me yasa kike bacci kan bishiya? Baki tsoron wani abu ya sameki a wannan daren? Mama tana yawan ce mana akwai hadari zuwa cikin jeji da dare. Tsoron mutane kike yasa baki magana gaban su? Me yasa kike boye fuskarki...?
Tambayoyin da yaron ke ta aiko mata ne ba kakkautawa. Da sauri ta dakatar dashi :
-Dan Allah ka yi mana shiru, kai bakin ka ko gajiya baya yi irin wanann Tambayoyi haka!
-To kiyi hakuri na dena...
Bata tankashi ba, suka dauki hanyar zuwa gida, Gida ne wanda aka yi da bulo da siminti, hakan ke nuna mai gidan yanada dan abin hannu, dan sauran gidajen duk na kara ne a kauyen, Gidan Lasaini shi ne taken da ake yiwa gidan. Jinah ba wanda ta sani a gidan da kauyen bayan matar da ta kawota, sai kuma wannan yaron mai suna Bukari wanda shima tasu tazo daya ne sakamakon wayonshi da kuma shegen surutu dake gareshi.
Lokacin da suka karaso gidan, shigewa daki Jinah tayi ta fada akan gado, kamar kullum yau ma shiru take ba magana.
Tanti Sarah ce ta shigo dakin tare da yiwa Bukari da ya fita da gudu godiya.
-Sannu Jinah, zaki ci wani abu? ko na kai maki ruwan wanka ne?
Duk wadannan Tambayoyi da Tanti Sarah ta yiwa Jinah, Jinah girgiza mata kai kawai tayi.
-Jinah! Wai sai yaushe zaki fara yimin magana, yaushe zaki fada min abinda ke damunki? Tun lokacin da na fara ganin a cikin jeji, kika ce min na taimaka maki baki iya tuna komai da dalilin da ya kawo ki cikin jejin, kawai abinda kike iya tunawa sunanki ne, tun daga ranar baki kara bude baki kin yi min magana ba, bakya magana da kowa idan ba Bukari ba. Ki je jeji kiyi kwanciyarki idan kika dawo sai ki shige daki ki ki fitowa. Yau tsawon wata daya kenan da na kawoki gidan dan uwana, amma babu wanda ya taba ganin fuskarki idan ba ni da Bukari ba. Na yiwa kowa karya akan ke diyar kawata ce ta bani rikonki.. Ki yimin magana Jinah! Ki fada min damuwarki? Kar ki sa nayi nadamar taimakonki da nayi. Ni ina daukan ki ne tamkar kanwata, kuma hakan na mani ciwo ganin halin da kike ciki.
Cikin Sanyanyar murya Sarah ke fadawa Jinah haka. Jinah ta fahimci Sarah tana son tayi mata magana ne. Kuma tasan wannan matar ta cancanci ta sanar da ita duk wata damuwarta. Tasowa Jinah tayi daga inda take tareda durkusawa a gaban Sarah, kafin tace
-Kiyi hakuri Sarah, ba wai nayi hakan bane, don in bata maki rai ko rashin yarda ba, abin yana min ciwo ne na rashin tuna rayuwata ta baya, ina jin kewar wasu mutanen da na kasa gane su waye, ina jin nan ba a muhallina nake ba, ina jin kamar wannan shi ne karon farko da nake rayuwa a cikin mutane kamar ku, Na kasa fahimta, na kasa fahimta Sarah. Ina son na san ta yaya hakan ta kasance, wata kil 'yan uwana basa sona ne suka jefar dani, kin fa sameni ne da kayana a cikin jaka da kuma makuden kudade a ciki, wata kil kuma guduwa ce nayi, ba zan...
Kuka ne yaci karfinta, tabbas da alama tana jin abun sosai a ranta, sai dai ba yanda zata yi.
-Na fahimce ki Jinah, wannan yanayi ne mai rikitarwa, shi yasa ni da ke muka kasa fahimtar komai. Amma ki ragewa kanki damuwa kar ki haifarwa da kanki wani ciwo. Ke yarinya ce, kuma akwai rayuwa mai tsawo a gabanki.Ya kamata ki fita kiyi abokai, ki sake sabuwar rayuwa kafin ki tuna komai, domin ta yiwu zai dau lokaci kafin ki tuna rayuwarki ta baya.
Fadawa Jinah tayi jikin Sarah tare da fashewa da wani sabon kukan.
-Ki bar kukan haka yanzu, tashi kiyi wanka sannan ki zo ki ci abincin ki.
-Nayi wanka tin dazu...
Jinah tayi mata karya tare da sunkuyar da kai
-Oh na tuna ashe baki yin wanka sai tsakiyan dare kowa yayi bacci, me yasa kike tsoron mutane su ganki?
-Kafin na hadu dake, duk wanda na gani na nufeshi da niyyar ya taimaka min sai ya gudu. Shi yasa nace wata kila akwai wani abu ne a fuskata da yake ba mutane tsoro, ko kuma kawai munina ne ke tsorata mutane. Ku kadai ne ke da Bukari baku ranci na kare ba ranar da kuka fara ganina.
Abin da Jinah ta fada ne yasa dariya ta kwacewa Sarah.
-Allah Sarah da gaske nake, mutumin da na fara gani, rokona yayi tayi akan dan Allah kar in cutar dashi in kyaleshi, ai kuwa ina bashi hanya ya fece kamar mashi.
Dariya Sarah take tace
-Ni kaina na so guduwa lokacin da na fara ganinki.
Cikin mamaki Jinah ta kalleta tace
-Me yasa?
Hannu Sarah ta dora akan fuskar Jinah tana shafawa tace
-Jinah, kina da wani masifaffen kyau ne, fuskarki har wani sheki take, ki duba ko ina a jikinki daidai ga gashin ki har ya wuce mazaunan ki. Gaskiya kyanki ba irin na mutane bane, sai dai ko na aljanu. Idan mutum ya fara ganinki dole yayi tunanin ke ba mutum ba ce, dan ko ni ban taba ganin mutum mai irin wannan kyau ba.
Cikin jin dadi Jinah tace
-Allah da gaske kike?
-Da gaske nake Jinah, ki bari duk randa kika je bakin kogi ki duba fuskanki a ruwa zaki gani.
-Kenan babu wani dalili da zan boye kaina?
-A'a, zo bari in gabatar da ke ga mutanen gidan nan ba tare da kin boye fuskarki ba, daman sun sha tambayata wai don me yasa kike boye fuskarki.
Kama hannun Jinah tayi suka fita zuwa tsakar gida, inda kowa sai aikin gaban sa yake. Ganin Jinah yasa kowa ya tsaya da abinda yake, suka zura mata na mujiya.
Ganin haka Sarah ta katse shirun da cewa
-Sunanta Jinah, itace yar kawata da ta bani riko.
Wurin shiru yayi, mutanen gidan na bin Jinah da kallon tsoro.
Sarah ta kara katse shirun da fahimtar dasu cewa Jinah mutum ce kamar su, kuma tana boye fuskarta ne dan ganin yanda mutane ke yawan kallonta da jin tsoronta.
Ajiyar zuciyoyi ne ke tashi a wajen, wasu da yawa tsoron su ya rage, amma wasu har yanzu suna ganin wannan kyau na Jinah yayi yawa. Wasu kuwa tasowa suka yi suna ta taba jikin Jinah, wasu kuma na shafa dogon gashinta suna al'ajabin wannan abu. Ganin Jinah duk ta tsargu yasa Sarah ta janyeta. Rungume Sarah Jinah tayi tana hawayen farin ciki, domin Sarah tanada kirki, gashi dai basu hada komai da Jinah ba amma ta dauketa tamkar wata yar uwarta. Tin daga ranar komai ya koma daidai tsakanin Jinah da Sarah, suka koma tamkar wasu shakikan kawaye, duk da Sarah zata fi Jinah da kusan fiye da shekaru 10, domin Jinah tana shirin shiga shekara ta 17 ne ita kuma Sarah tanada shekaru 33.
Kauye kowa ya dauka ana ta yadawa cewa ai gidan Lasaini akwai wata kyakyawar yarinya mai kama da aljanu. Mutane na ta tururuwar zuwa ganin Jinah, hakan ya dauki lokaci sosai, har ta kai idan Jinah ta fito a hanya mutane na kallonta har suna nunanta suna cewa ita ce mai kama da aljanu, har ya kai Jinah na tsarguwa da abinda suke mata. Shi yasa koda yaushe tafi son taje cen cikin jeji tayi ta wasa da dabbobi, kuma tafi jin dadin kwanciya kan reshen bishiya da kwanciya kan gado. Sai dai yanzu bata boye fuskarta kuma tana magana da mutane. 'Yan matan kauyen da dama kishi da ita suke, ganin samarin su nata rawar kafa gunta wasu har zuwa tambayar aurenta suke. Ita kuma Jinah ko a jikinta don wannan bai ma gabanta. Sarah ta fahimci hakan har wata rana take tambayar Jinah
-Me yasa baki kula samarin dake zuwa wajenki?
-Kawai haka nan, naji bana da ra'ayin soyayyar ne.
Jinah tace a takaice.
-Jinah ya kamata ace kina kulasu, dan idan da ta nice ba zan bari ki ma fara ba, domin aure shine babban kuskuren da na taba yi a Rayuwata. Amma sanin aure shine darajar kowacce mace, yasa nake son ki fidda gwani a cikin masu neman aurenki.
Cike da mamaki Jinah ta kalleta tace
-Amma me yasa? Ina mijinki yake? Sai yanzu wannan tunanin yazo min dan tinda nazo gidan nan ban taba ganin mijinki ba...
Sarah ta katseta da cewa
-Ke nifa kar ki sauya mana magana, ya maganar da muke yi amma ke kina so ki canja zancen ki kamo wani babi. Bansan daga inda kike ba amma mu nan a kauyen Mambila muna aurar da yarinya ne da wuri...
Ita ma Jinah katseta tayi da cewa
-Kece dai kike son canja maganar!
Ita ma ta kara musawa
-A'a ke dai kika canja maganar!
Musu ne ya barke a tsakanin su kafin daga bisani Sarah tace
-To shikenan wata rana zan fada maki.
Jinah tace
-Me zai hana ki fada yanzu?
Sarah tace
-Ke dai nace ba yanzu ba...
Mikewa Jinah tayi tana kakkabe zaninta tace
-To shikenan, ni dai na tafi cikin jeji.
Tabe baki Sarah tayi tace
-Aikin kenan!
Cikin shagwaba Jinah tace
-Ina jin dadin zaman ne a cen, kuma ko ba komai ina kallon yanda dabbobi ke kai kawo...
Kara tabe baki Sarah tayi tace
-Ina guje maki kar ki je wani aljani ya ganki, ya makale maki, kin ga sai ki dawo gida ki zauna.
Fita Jinah tayi daga gidan tana dariyar maganar Sarah.
Tana isa cikin jejin, kamar kullum bishiyar da take hawa tayi kwanciyarta ta dale, cikin zurfin tunani ta fada, tunani take ko zata iya tuna wani abu na rayuwarta ta baya, kamar kullum dai tana jin kewar wasu mutane da ta kasa gane su waye, tafi jin kewar wani wanda tana tunanin nata ne na kusa da ita sosai, da ta fara irin wanann sai zuciyarta ta rinka bugawa da sauri da sauri. Tana cikin wannan tunanin ne taji wata murya tana cewa
-Ni fa ba zan koma gida yanzu ba, kawai kuyi tafiyar ku!
Lekawan da Jinah zata yi sai ta ga wasu samari su uku ne a kasan bishiyar da take kwance.
Daya daga cikin samarin ne yace
-Ka dakata da taurin kan nan naka Dauda, dare fa ne ke shirin yi, kuma kaga nan jeji ne bamu san me yake dauke dashi ba na cutarwa.
Dayan saurayin kuma yace
-Musa fa na da gaskiya Dauda, bamu san meke akwai na hadari ba anan...
Dayan saurayin mai suna Dauda wanda yake ta yiwa yan uwan nashi taurin kan ba zai koma gida yanzu ba, ya katseshi da cewa
-Ku rabu da ni kuyi tafiyar ku! ku wane irin masu naci tsiya ne? na fada maku ni ba yanzu zan koma gida ba, ta yaya zamu fito farauta ko fara bamu kama ba, sannan mu koma gida haka hannu rabbana? Kuna tunanin wani abu zai same ni ne? Ai bansan cewa abokaina matsorata ne ba.
-To mu kaga tafiyar mu zaka iya tsayawa, ruwanka ne wannan. Muje Mahadi idan ya gaji ya iskemu gida.
Tafiya suka yi suka barshi anan, shi kuwa ko a jikinsa.
Duk abinda ke faruwa Jinah na saman bishiya tana kallon su. Wata dabara ce ta fado mata, tace bari na koyama wannan dan rainin wayon hankali. Shi kuwa Dauda zaunawa yayi karkashin bishiya ya dauko Kwari da bakanshi yana gyarawa. Koda ya ida tashi yayi wai da niyyar kama wata kurciya da ya gani. Cikin Sanda Jinah ta bishi a baya ba tare da ya sani ba, boye fuskarta tayi da gashinta sannan ta dira gaban Dauda, Dauda kamewa yayi guri daya ya kasa motsi, ita kuma Jinah ta kara nufoshi... Ganin haka Dauda ya fara kyarmar tsoro yana cewa
-Dan Al..lah ki..yi hakuri ki kya..leni kar ki cutar dani... Mamata zata damu sosai idan na mutu, nine dan autanta. Kiyi min rai!
Dariya ta so kwacewa Jinah, kamar ba shi bane yake ta cika baki dazun. Dauda kokarin guduwa yayi ai kuwa sai ga maciji kuma gabanshi, kasa motsi yayi ya fasa ihu
-Wayyo Allah! yau lokacina ne yayi!! wayyo!!
Taku daya Jinah tayi gaban macijin, ta durkusa tana kallon macijin cikin ido, koda macijin ya hada ido da ita sululu ya juya ya koma daga inda ya fito. Duk wannan dramar da ake yi Dauda yana tsaye a kame yana kallon ikon Allah, dan yau ya tabbata tashi ta kare. Jinah kasa rike dariyarta tayi, ai kuwa tayi ta dariya har ta gaji dan kanta ta dena, amma har yanzu Dauda ko motsi shi kawai gani yake tashi ta kare. Jinah ta matso kusa dashi tana mai dauke gashin da ke kan fuskarta tace
-Ni ba aljana bace, mutum ce kamar ka.
Har yanzu shiru Dauda yayi yana kallon ikon Allah. Jinah ta kara cewa
-Kamar ba kai bane kake ta kurari dazu ba, wai duk ina jarumtar taka?
Kallo dai kawai Dauda ke bin Jinah dashi. Abin ya fara ba Jinah haushi tace
-Tsaya da yimin wannan kallon, na fada maka nima mutum ce!
Ajiyar zuciya Dauda ya sauke tare da cewa
-Na kasa yarda ne...
Jinah tace mashi cikin zolaya
-To kayi hakuri da tsoratar da kai da nayi, kawai ina son na gwada jarumtar ka ce, ganin yanda kake ta cika ma abokanka baki dazun.
Juyawa tayi da niyyar tafiya. Dauda ya dan dawo cikin hayyacinsa, tsoronshi ya ragu. Cikin zuciyarsa yace "Kuma da ita Aljana ce ba yanda za'a yi ta ceceni a hannun wannan macijin, kuma ba yanda za'a yi ta kyaleni tayi tafiyarta." Tsayawa yayi yana kallon Jinah da tayi nisa, yana kallon irin halittar da Allah yayi mata kamar wata aljana. Kuma da ya tuna yanda tayi ta kori macijin nan sai ya kasa yarda cewa ita mutum ce. Dauda bai san lokacin da ya fara bin Jinah a baya ba, lokacin da Jinah ta fahimci ana binta a baya, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace
-To kuma yanzu me kake so? Ka dakata da bina.
-Nima..nima bansan me yasa nake binki ba, kawai dai ina son nayi maki godiya akan cetona da kika yi, kuma ina son nasan sunanki...
A tsawace Jinah tace
-Wannan kuma ba zai yiwu ba, maganar godiya kuma ni nayi haka ne dan nishadi, shikenan zaka iya tafiya.
Juyawa tayi da sauri da niyyar tafiya, tuntube tayi ta fadi kasa, da gudu Dauda ya nufeta da niyyar taimaka mata
-Sannu ba kiji ciwo ba?
Kwalla a idonta tace
-Wayyo Allah zafi!
Anan Dauda yaga ya kara tabbatar ma kanshi lallai wannan mutum ce kuma akwai kurciya a tattare da ita. Lokacin da yazo da niyyar tabata, da sauri Jinah taja baya dan bata so ya tabata. Kuma me yasa zata yi haka alhali taimakonta zai yi? itama kanta bata san dalili ba.
Dauda ya dan ji ba dadi yace
-Kawai ina son ganin inda kika ji ciwo ne.
Da sauri Jinah tace
-A'a kar ka tabani!
Dauda bai tsaya saurarenta ba ya kama kafar tata, dole ta kyaleshi, kaya ce yaga ta taka a kafarta ta hagu.
Jin laushin kafarta da Dauda yaji yace
-Masha Allah, gaskiya kinada fata mai laushi da dadin tabawa... oh yi hakuri.
Kafarta kawai Dauda ya taba yana wannan sambatun ina ga...
Wata bishiya Jinah ta nuna mashi tace ya debo kunnuwanta, dan ta canja maganar, dan ta fara lura dan saurayin ya fara fita hayyacinshi.
Dauda yace
-Shit, barni nayi aikina, ba abinda zaki nuna min dan nima haihuwar kauye ne.
Cikin shagwaba Jinah tace
-To kayi a hankali.
Murmushi Dauda yayi yace
-Kinga shi yasa raina mutane baida kyau, ki duba yanda kika nemi kasheni da tsoro kema gashi yanzu Allah ya saka min.
Kallonsa Jinah tayi tace
-Kana nufin dan na tsorata ka ne yasa naji ciwo?
Dauda ya kara yin murmushi yace
-Ni dai ban ce ba..
Turo baki Jinah tayi a shagwabe tace
-Haka kake nufi ba gashi da bakinka kake fadi ba..
Fashewa da dariya Dauda yayi, kafin daga bisani wajen yayi shiru. Ciro ganyen bishiyar Dauda yayi sannan ya nika ganyen da taimakon wasu duwatsu biyu sannan ya saka dadai inda Jinah ta taka kayar. Keta zaninta tayi kadan ta bashi ya daure mata ciwon. Kamata Dauda yayi da niyyar taimaka mata ta mike, wani zafi ne yaji ya sauka a jikinsa kamar an kunna masa wuta. Ihu Dauda ya fasa kafin ya fadi sumamme ko matacce.
---------------------------
To Fans ku biyo mu domin jin abin da zai faru da Dauda sanadin taba Jinah da yayi.
---------------------------
Please comments dinku suna da matukar anfani domin suna karawa Marubuci karfin gwiwa...
Ga link sabon Group da zaku rinka samun updates na wannan sabon labari : https://chat.whatsapp.com/JGjb07Du5N45rzy8gfOCOV
Note : Amma fa ku sani Group ne wanda admin ne kawai zai iya posting, dan bamu son wani labari in ba na wannan labarin ba.
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story