← Book details Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 13

Sashe 8

Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Al’adun Xhosa Game da Bautar Kakanni

*Amadlozi / Amatongo*
A tsarin Xhosa, kakanni wadanda suka mutu (ana kiransu *Amadlozi* ko *Amatongo*) suna da matsayi mai girma. Ana ganin cewa ruhin su na ci gaba da rayuwa a wani yanayin ruhaniya kuma suna iya kare iyali, taimakawa wajen waraka, da kuma bada jagora idan aka bukata.

*Qamata / UThixo*
Xhosa suna kuma da akidar wani “Kirki mai girma” wanda ake kira *Qamata* ko UThixo wanda ake ganin shi ne wanda ya halicci duniya. Amma yawanci ba a kira wannan Allah kamar yadda Musulunci da Kiristanci ke kira ba; ruhin kakanni ne suke kusantarwa ga mutane fiye da Qamata.

Rituals da bukukuwa
*Imbeleko* (greeting newborns to ancestors), *Intonjane* (rite of passage ga matashiya bayan ta fara haila) da sauransu.

wannan shine takaitaccen tarihin KABILAR XHOSA.
Joseph yace '' ki ɗena damuwa duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa yake doka.''
gyara kwanciyar ta , tayi a jikin sa tace '' Hakane wallahi.''
Joseph fara yi mata kiss yayi yana zame mata sleeping dress ɗin ta wacce da ita gwara babu, kama hannun sa tayi tana kautar da kan'ta tace '' Joseph yunwa nake ji.''
mai da nakin da yayi kan breast ɗin'ta ba tare da yayi mata magana ba.
wayar tace tayi ringing da sauri ta ture shi ta dauki wayar ta , tamkar wani mara laka haka yayi flat a kan gado tana dauka kiran ya katsai number ba damar bi prevent number ce.
ɗogon tsaki taja ta ajiye wayar akan drawer.
hawa kan gado tayi tana kwanciya a jikin sa haɗe bakij su tayi wani irin zazzafan saƙo suke aikawa junan su.
a bangaren AFIYAH tun da sukai sallama da asim ta kasa komai ganin har 1:30 tashi tayi, ta cire rigar jikin ta da sauri ta juyo jij motsin Joseph cikin mamaki tace '' Joseph daman kaman kana cikin gidan nan?.''
wani mugun yawu ya haɗiya sosai girman sa ya tashi ganin afiya a haka.
dakyar ya isa saita ƙansa yace '' eh wallahi tun safe ina nan.''
Ya faɗa haka yana kafe ta da muci mucin idanunsa sheɗan na kawata mai isa dan dai yasan afiya tafi karfin sa , ba zai taɓa samun taba.''

far tayi da idon ta tace '' Ohkay.''

Joseph yace '' ya nagan ki, a haka..?.''
wanka zanyi zan tafi gurin asim
ta faɗa tana shiga toilet ba tare da ta tsaya taga me zai ce ba.
bathroom ɗin ta tamkar ka zauna kaci abinci komai na gurin luxury ne ,
tiles dark bue ne da fari hakan ba karamin kawata bathroom ɗin yayi ba shiga cikin bathtub tayi kan fanfon ta murɗa a hankali ruwa ya fara cika gurin, wani daddaɗan kamshi me sanyi yana tashi.
limshe ido tayi ta dade a haka ba tare da ta buɗe idon ta ba , abubuwa da yawa suna dawo mata dakyar ta iya tashi tayi wanka.
bayan ta gama ta ɗauro towel ta fito tana tsane kan'ta da towel zama tayi akan gado tana kwalawa Charity kira.
da sauri ta shugo tana cewa afiya lafiya me ya faru.
kan'ta ta ɗaga sama tana kallon ceiling tace '' dauko min kayana.''
to tace ta ƙarasa shugowa ta buɗe wardrobe, abaya yar gidan *HAAL INC* ta dauko mata dark grey colour buɗe bangaren da taka ajiye inner wear ɗin ta tayi ta dauko mata bra da pant ta ajiye mata turare ta dauko ta feshe su da shi tace '' shikkenan nan..?.''
ɗan murmushi tayi tace '' a'a sauran ki takalmi da jaka wanda zai yi matching da wannan kayan.''

okay ta faɗa tana juyawa inda taka ajiye takalman ta ta buɗe kofar Glass ce takalma ne sunfi guda ɗari a jere sai kace shagon sai da takalma ta buɗe, ɗauko wani purple colour tayi da adon grey kamar dai yadda adon rigar tata yake ɗab gidan *Prada pointy toe heel* ajiye mata tayi sannan ta rufe kofar Glass ɗin ta tafi ɗaya ɓangaren da jakunkuna suke kamar yadda tsarin takalma yake haka ma tayi wa na jaka daukar wata jaka tayi itama purple ce da ratsin grey colour yar gidan yar gidan Hermes birki bag.
ajiye mata tayi ta fita tashi afiya tayi tana jin kan'ta yana rasa mata ko dan yau bata yi chaji bane , shi ya saka damuwa take neman jefa ta a wani hali,
tashi tayi ta fara tafiya buɗe lokar ta tayi ta dauko wata roba cike da magani na kwaya, zazzagowa tayi ita kanta bata san iya adadin da ta zazzago ba ta watsa a baki ruwan da yake kan bedside lamp ta ɗauka ta kora magungunan da ta sha,
riga da wando ta fara sakawa sannan ta saka a baya. ta feshe jikin ta da tsadaddun turarurruka mayafin rigar ta daura akan ta , kalbar ƙarin gashin da akai mata ta zubo gadon bayan ta jakar ta ta dauka ta saka wayar ta da key din ta.
ta kalmin ta ta saka me dan matsakaicin tsayi, yau fuskar ta ko kwalliya bata tsaya yi mata ba ban da lipstick da ta shafa domin ita kwalliya sai da kwanciyar hankali ake yin ta.
cikin ƙasaita irin na cikakkun matan nan masu aji da ji da kansu haka take takun ta kai kace dole akai mata ba son tafiyar take ba.
ko da ta fito parlour ba kowa bata tsaya yiwa Charity magana ba ta buɗe kofa ta fita, motar ta da take harabar gidan ita ta buɗe ta shiga,
sakin kiɗa tayi a motar a hankali tana bi ta fara tafiya horn tayi wa me gadi ya wangale mata gate din ta fita a guje sosai take sharara gudu domin bata da wata bukata da ta wuce ta gan'ta agaban asim.
a gabaƙin get ɗin makarantar, ta tsaya aka soma checking ɗin ta , wata mota ce ta tsaya white colour ƙirar Bugatti la voiture noire zoge glass ɗin motar mamallakin motar yayi.
baki ne amma jikin sa irin chocolate colour ne kansa babu gashi ko ɗaya sai tarin ƙasunba da gemu da ya tara.
ƙurawa afiya ido yayi da take tsaye ranta duk a ɓace kamar basu saba ganin ta ba amma duk lokacin da zata wuce sai sunyi checking ɗin ta sai kace zata shigo da mugun abu cikin makarantar.

jikin tane ya bata ana kallon ta ɗago idon ta tayi, four eyes sukai dashi ɗauke idon ta , tayi tana yiwa me mara checking ɗin motar ta magana tace '' ka gama zan iya tafiya?.''
be bata amsa ba sakamakon hannu da wannan mutumin ya ɗaga mai jikin sa na rawa yace '' ina zuwa shugaba yayi kira?.''

taɓe baki tayi bata ce mai komai ba ya tafi da gudu ɗurƙusawa yayi yana cewa oga gani nan ranka ya dade Allah ya ja zamanin ka ,
Abdulwahab yace '' wannan irin ta mu ce?.''
ƙasa ƙasa yace '' tab gurin dr ASIM nake ganin tana zuwa kuma sau tari ina ganin su tare ranka ya dade daga ganin wannan za tayi maiƙo komai gashi nan a ciki dam dam?.''

cikin mamaki yace '' daman shima yana yi amma yake kallon mutane tara tara saboda shi ne babba ba me iya tsawatar mai kana ga kwana ki wata shegiyar doka da ya kafa wao duk malamin da aka kama ya lalata yarinya sai an kore daga makaranta kuma sai ya auri yarinya.''

wani ashar jallo ya lailayo yace '' yace kyale dan kan uba shi waliyi ne da zai ga irin wannan a kusa dashi ya kasa taɓa ta karya yake ai tuggu za ku haɗa mai wallahi gwara yayi gaba nima fa ina tunanin bincike yake akai na ya fara lura ina daukar yan mata ana kai wa oga su.''
Abdulwahab yace '' hmmm jallo wannan wanne irin sharri ne bamu kulla mai ba sai ya fita ya iya takun sa wallahi yadda kasan me gani har hanji ita dai wannan kwantenar a san yadda za a yi a kawo min ita yau na huta da ita domin wallahi jallo ganin ta da nayi , ji nake ina tsiyaya dole ko dan na baƙanta mai rai na fara soyayya da yarinyar nan yasan abin da yake mun sani.''

baka da damuwa yallaɓai cewar jallo.

kudi ya ciro daga aljihun sa ya miƙa mai godiya ya shiga yi yana komawa da sauri kallon afiya yayi yace '' kin yi babbar Sa'a ranki ya dade oga ya ƙyasa.''

haɗe rai tayi ji take kamar ta zabga mai mari, dauke kanta tayi ta buɗe motar ta , ta shiga da gudu ta shiga Cikin Makarantar har tana neman taka jallo.
bata tsaya a ko ina ba sai a bakin office ɗin asim parking tayi.

ta fito tana tafiya dakyar ji tayi taci karo da mutum a bakin kofar shiga office ɗin nasa da sauri ta ja baya tana ƙare wa mardiyya kallo yawu ta tofa mata a fuska yana matsawa gefe ya tsuna fuska tayi ganin takalmin kafarta da be wuce naira biyar ba domin irin slipper ɗin nan ne cikin tsawa da bala'i tace '' ke wacce irin dabba ce da bakya lura da hanya zaki bige ni?.''

SUHAILA da taji wulakancin da tayiwa mardiyya yayi mata zafi ta zabgawa afiya mari kafin ta ƙara wani yunkuri ta ƙara zabga mata hagu da dama tace ''ke a gidan ku ba a koya miki, sanin darajar ɗan adam ba ? gaki nan dabba a cikin jakuna kina abu na dabbobi kin tawo kina rangwada to ba wanda zaki birge sai dabba irin ki.''
ASIM da jin ana cin mutunci da kuma jin hayaniya da sauri ya fito ganin abin da yake faruwa ya harde hannuwansa a kirjin sa suhaila da sauri ta juyo gaban ta na faduwa ita kuwa MARDIYYAH ta kasa ko da motsi ganin irin kallon kaskancin da yake jifan su dashi.
juyawa yayi yana cewa ku shigo.
mardiyya kuka ne kawai bata saka ba idon ta har ya fara kawo kwallah daman akwai fanfo a gurin wanke fuskar ta , tayi ta bi bayan su ganin yadda office ɗin nashi yake a share a goge gudin kar yayi musu faɗa sai suka ajiye takalmin su a waje afiya kuwa tuni ta dade da shiga.
Chapter 8 · 0% Book details