← Book details Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 13

Sashe 3

Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani kallo ramsi tayi mata , tace '' tab gaskiya na gaji ku kamar baku san a ina kuke ba , to ai yan cikin hostel din nan , kusan rabi suna cikin ta, baki ga bular hancin su guda biyu ba , kasan leben su ma akwai bula, wasu kuma ring ne a cibiyar su ai duk wa'yannan alamomi ne , da ke nuna mutum dan kungiya ne.''
MARDIYYAH tace '' to ina amfanin me take musu..?,

kinga ko na faɗa miki ba ganewa za kiyi ba , dan haka kudai ku kiyaye, duk da na ga baku fiye cin abin mutane ba , to kuci gaba da wannan dabi'a

ramsi ta faɗa tana saka riga me hannun shimi.

to suka ce jikin su a sanyaye, mardiyya da , ta ƙara jin hankalin ta ya tashi gwara kawai ta amince da wannan auren, ko ta matsa daga cikin makarantar nan , wannan bala'i haka daga wannan sai wannan

SUHAILA kuwa shiru tayi, ta zuba uban ta gumi, abubuwa da yawa suna yi mata yawo a tsakiyar ka,

Ramsi wayar ta , ta ɗauka tana kunnawa ta fara charting tana sakin dariya, chips ta dauko tana ci ta kalle su tace '' bismillah..,

kai suka girgiza mata dan murmushi tayi tace '' kun yiwa kan ku wallahi, ni ban ce ku dena cin abin hannu na ba, kowa ya sani, ni bana shiga kungiya in dai harkar a marke ce , to ina ciki.,nice sahun gaba.''
banza sukai mata ,

AMBASSADOR EL'BASHIR MANSUR TURAI.

sunan da naga an rubuta da rubutu me launin gold a jikin wani kyakkyawan mansion.
a guje wata mota baka kirar G wagon tayi horn security din gidan ya buɗe wa motar nan ta shigo ko parking be bata tsaya yi ba , ta fito daga cikin motar nan wani arnan English wears ne a jikin ta , dukkan wata suffar da Ubangiji yayi mata ita, kayan nan ya bayyana ta ko dan kwali babu a kanta sai ma kalba da ta zubo da ita har gadon baya.

da alama sauri take kasancewar yadda take tafiya cikin sauri duk da uban hil din da yake kafar ta.

gaba wats kofa ta , tsaya nan da nan kofar tayi wani juyi ta buɗe kan ta shiga tayi da sauri tana cewa mom mom mom.
Mommy da take zaune a parlour yar aikin ta na yi mata tausa ta amsa dakyar tana kallon ta.

bawai zafin ciwon da take ciki bane, ya saka ya amsawa da kyar a'a kawai tsabar isa ce , gaba ki ɗaya hannayen ta , sanye suke cikin zoben gold ajiye glass cup din hannun ta , tayi tana zubawa diyar yar uwar' ta ido.

Aneesah ƙarasa shigowa parlour tayi ba ta cire takalmin kafarta ba , ta , taka kan carpet zama tayi tana cewa mom wai daman big bro be rabu da wannan shegiyar arniyar nan ba.

da hannu mom tayiwa me yi mata , tausa ta matsa ta basu , guri tashi tayi da sauri mom tace '' aneesah wa kike nufi...?.''

Aneesah da ranta yake ɓace tace '' Linda mana ke kinga birthday din da tayi hmmmmm wallahi idan kika ji miliyoyin kudin da ya , bata a matsayin gift sai kin yi mamaki.''

Mom tace '' zai zo ya same ni ne ya su mama dafatan kowa yana lafiya..?,

Aneesah tace '' lafiya qalau Please karki faɗa mai ni ce na faɗa miki, bana so yasan na dawo hutu kasar nan,

Mom tace '' okay ba zan faɗa masa ba.''

yauwa mom ta faɗa tana rungume ta tare da yi mata kiss a kumatun ta, shafa kanta mom tayi tana murmushi.
sallamar ASIM ce ta saka ta juyo da sauri, kallo ɗaya ASIM yayi mata , ta dauke idon sa yace '' ba dai a haka kika fito ba, baki san nan ba Oxford bane da zaki dinga yawo yadda ranki ya ga dama bakya kishin jikin ki da addinin ki...?,,

wani abu ne ya tsaya mata a maƙogaro ga wani rainin hankali, kafura yake son aure me shigar banza rabin jiki a waje me makon yake can yayi mata wa'azi shine ya zo nan ita yana yi mata kasa tayi da idon ta , tace '' sannu da zuwa..,
ASIM da yayi banza da ita ya durƙusa kusa da mahaifiyar sa ya riƙe hannayen ta yace..,,

Reacting sharing

za kuga read more me yawa kuyi following channel dina domin samun wannan littafin da zarar na ɗora

JAMI'A...

Only arewa book.

Episode 3

''Mommy barka da yamma.?''
ɗauke kai tayi tace '' asim baka rabu da wannan yarinyar ba ko..?.''
gaban sane ya faɗi amma sai ya danne yace '' mommy wacce yarinya..?.''

Mommy tace '' Asim, I didn’t know you as a liar. Don’t start lying to me today. If she were truly a good woman, I swear I wouldn’t care about her tribe just choose a good mother for your children.''

wani kallo ya juyo yayi wa aneesah domin yana kyautata zaton ita ce ta kawo mata wata magana, kan'ta ta sunkuyar ƙasa kirjin ta na dukan uku uku bata san me yaya ya gani a jikin arniyar can ba , bata san da me tafi ta ba da ko kallon mace baya yi mata , Allah ya ɗora mata son sa bama kamar bema son tana yi ba cije lips din ta , tayi tana ayyana abubuwa da yawa a ranta da ace wata, ta aure shi ba ita ba gwara kowa ta rasa.

ASIM jikin sa a sanyaye yace ''Please be patient, Inshallah I’m about to bring you the woman I will marry."

kan'ta ta ɗago ta kalle sa tace '' kai ko kunya baka ji kannen ka duk sun yi aure sai kai da auta ne a cikin gidan nan to kafin na yi tafiyar nan inshallahu nake so kai aure asim ban san ko zan tashi ba ina so naga ya'yan ka ina so naga matar ka .''

ƙasa yayi dakan sa a hankali ya furta insha Allahu ya faɗa yana tashi, mommy kallon sa tayi tace '' abincin ka dakin ka za'a kawo maka ko anan zaka ci..?''

anan ya faɗa yana juyawa fita yayi daga part din nasa ya shiga nasa iya tsaruwa ya tsaru komai na jin dad'i akwai shi a ciki zama yayi akan luxury sofa ɗin sa yana tura hannun sa cikin gashin kansa besan ya zai yi da soyayyar AFIYAH ba mahaifiyar sa bata son ta besan mene dalili ba
kamata yayi ta so abin da yake so musamman ma data musulunta saboda dashi amma har yanzu ta kasa cire sunan ta daga arniya.

tabbas da wannan yarinyar ya kamata ya buga game , idan ya aure ta yana da yaƙinin mom zata yarda ya auri AFIYAH.
tashi yayi ya shiga bedroom din sa toilet ya shiga ya cire kayan sa ya sakarwa kansa shower rufe idon sa yayi, yana jin soyayyar afiya na huda mai zuciyar sa kamar yadda ruwan da yake zuba daga shower yana sauka a jikin sa wanka yayi ya fito daure da towel.

tsane jikin sa yayi da towel tare da ɗaukar hand dryer ya busar da gashin kansa sumar kansa luf luf tabi ta kwanta kallo ɗaya zakai mai kasan shi din ruwa biyu ne ko dan yanayin yadda fatar sa take da kuma sumar kansa da har kanannaɗewa take saboda tsabar kyauhun sumar tasa.
zama yayai akan stool daukan acqua di parma Colonia body cream matsa kansa yayi ya zubo a tafin hannun sa ya fara shafawa.
bayan ya gama ya shafa body cream oud. tashi yayi a wani irin kamshi me dad'i ya gauraye bedroom din.
riga da wando ya saka yan gidan gucci wayar sa ya dauka ya fito daga dakin dai-dai lokacin afiya ta kira shi da sauri ya ɗaga tare da karawa a kunne, yace '' Assalamu alaiki.
Afiya da ta ƙasa amsa sallamar sa , saboda wani irin kasala da muryar sa , ta saka ta , tace '' my man please kazo gidana wallahi anji kewar ka...''

zama asim yayi ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yace '' afiyaah kinsan dalilin da ya saka bana som zuwa gidan ki be kamata ke ba muharrama ta ba ina zuwa gidan ki kuma ke kaɗai karki manta fa na ukun mu sheɗan ne..,

Afiya shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya hannun ta yana kan prevent part din ta , ta rasa gano sirrin asim magana kaɗai suke yi dashi saka ta yake yi a cikin wani irin yanayi me wuyar fassarawa.

Asim yace '' kiyi hakuri bawai ina rejecting din zuwa gidan ki bane..,

marairaice murya tayi tace '' Please yau kaɗai wallahi ji nake idan ban ganka ba zan iya mutuwa asim ka tausaya min na baro kowa nawa na dawo gurin ka be kamata , kana yin nesa dani ba ..''

Asim jikin sa ne yayi sanyi yace '' okay zuwa anjima zan nemi ki ina da ayyuka ne wallahi da yawa kinga yau ko A.E.M ban je ba.,,

wani irin dadi ne ya kamat tashi tayi ta fara rawa tana cewa thanks you i love you so much.
kashe wayar tayi tana zama taɓe baki Charity tayi tace '' l swear, I don't know why you gave in to that man while he's just playing with you .''

a'a Charity asim abu ɗaya ne kawai bana so tare da shi kasancewar sa musulmi bana kaunar musulunci wallahi amma ke kan ki, kinsan asim ya haɗu.

Charity tace '' yanzu kenan auren sa za kiyi ya zakiyi duk randa ya gane wasa da hankali kike mai ke ba musulma bace ba..? wannan tattoo na jikin ki ya za kiyi dashi. ?.''
Chapter 3 · 0% Book details