← Book details Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 13

Sashe 7

Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sannan suka fita daga cikin hostel din gaba ki ɗaya theatre da zasu zauna zana jarabawa nan suka je suka zauna a waje tun da malaman ke bawa mutum set number da zai zauna kullum cikin canza set number suke.
ci gaba sukai da karatun su har lokaci yayi gaban tane ya fadi ganin motar asim ta zo dab dasu,

yan mata da samari da suke gurin sosai hankalin su ya karkata akan sa, iya dukiya da ilimi Ubangiji ya ba shi uwa uba kyau da tarin ilimin addini dana boko shi ya saka yan mata da yawa suka mutu akan son sa.
driver sa ne ya fito da sauri ya buɗe mai kofa ya jima be fito.
da alama wani abu yake me mahimmanci a cikin motar, fitowa yayi yana sanye da ɗanyar shadda up white gezna an mai aikin monogram Black colour harta takalmin sa da hular da agogon sa duk black ne wayar sa ce a kunnen sa da alama waya yake yana kallon a gogon hannun sa.

cikin isa ya soma taka stair case din da zai shiga cikin theater.

mardiyya tashi tayi domin ta bashi hanya ƙirjin ta , na dukan uku uku.
ko kallon inda take beba balle ya nuna yasan da mutum a gurin.

sauran malaman department din sune suka tawo da booklet da kuma question paper a hannun su cikin wata leda an rufe ta sai a lokacin zasu buɗe ledar iya matakan tsaro sun zuba shi a gurin.

ajiyewa sukai yi a lokacin suka kafe set number kowa yake ya duba tasa ya dauki number sa mardiyya ita ce number ta farko gaban tane ya ci gaba da bugu shiga cikin theater tayi checking din ta wata mata tayi, ciro wayar ta , tayi ta bata ta ajiye mata da yake haka suke yi , Sannan ta zauna a gurin ta suhaila yana can karshe.

fara rabon booklet suka yi asim miƙa mata tata yayi tana tunani bata san ma ya zo kanta ba cikin ɓacin rai ya daka mata tsawa.

da sauri ta kalle sa gaban ta na faduwa fuskar'sa a haɗe kamar ko da yaushe yace '' get are out.''

da sauri ta buɗe baki za tayi mai magana yace '' karki sake ce min komai fita baki shirya yin jarabawa ba tun da har kina da lokacin tsayawa kiyi tunani.''
jikin ta a sanyaye ta tashi idon ta duk ya ciko da kwallah gaba ki ɗaya kowa kallon su yake ji tayi tana neman faduwa ko ganin gaban ta bata iya yi fita tayi ta zauna a kofar theater.
kifa kan'ta tayi akan gwuiwar ta , ashe ma kuka harama ne a wannan karon kukan yaƙi zuwar mata shikkenan yanzu tana ji tana gani jarabawa biyu ta rasa su.

Mukhtar ne ya ƙaraso yana cewa baiwar Allah me kike yi nana..?''

da sauri ta ɗago kan'ta cikin sauri yace '' mardiyya ba jarabawa kuke ba me ya fito dake..?.''

bakin ta na rawa tace '' doctor asim ne yace na fita ban shirya zana jarabawa ba wallahi ba i na sane nayi mai banza ban san ya zo bani booklet ba wallahi ban masan an fara rabawa ba dan Allah ka bashi hakuri.''

tausayin tane ya kama shi yace '' okay taso.''

tasowa tayi jikin na rawa ashe har an bada izinin fara rubuta jarabawa, magana yaje yayi wa asim dakyar ya yarda ya barta ta zauna mukhtar ne ya bata booklet da question paper amsa tayi tana dubawa asim harde hannunwansa yayi a kirji ya kafe ta da ido.

amina alhsan Muhammad opay 1k

8141785374.

ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785375

*JAMI'A*

*Episode 5*

Ƙasa tayi da Ƙan'ta zuciyar ta na faman bugu, ajiyar zuciya ta sauke ganin abin da, ta karanta shi ya fito.
fara rubutu tayi hannun ta yana rawa saboda tana jin kaifin idon sa a jikin ta.

ASIM mamaki yake gata dai ya ganta a hotel amma babu alamar jin dad'i a tattare da ita slipper ne ma a kafar ta.

da sauri ya yi istigifari yana kautar da ƙansa , bakin glass din sa ta mayar kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannun sa yayi goma da rabi dai-dai mukhtar ya matso kusa da shi ƙasa ƙasa yace '' malam kabar yarinya ta rubuta jarabawar ta lafiya , ka dena kallon ta , bata zama mallakin ka ba ka bari idan ta zama sai ka kalle ta.''
ji yayi kamar ya dunƙula hannu ya naushi bakin mukhtar ya zubar mai da haƙora yace '' wallahi mukhtar ka fita s ido na , na rufe.''

dariya yayi yana matsawa daga gurin fita yayi daga cikin theater gaba ki ɗaya wayar sace ta fara ringing ganin sunan afiya ɗagawa yayi yana karawa a kunne cikin sanyin murya tace '' beb barka da safiya.''

jin muryar ta ba ƙaramin sanyi yaji ba a cikin zuciyar sa yace '' Barka dai kin tashi lfy?.''

hmmmm lafiya ba lafiya ba
AFIYAH ta faɗi haka Muryar ta na rawa.

cikin nuna tsantsar damuwa asim yace '' innalillahi wa'inna ilaihir raji'un me yake damin ki..?.''
kwallar da ta taru a idon ta , ta share tace '' kai ne asim abin da kake min wallahi bana jin dad'in sa nunawa fa kake kamar baka yarda dani ba, asim son da nake maka ne ya janyo haka, da ace kaga ban damu da kai ba wallahi ba zakai min haka ba , ni dakai yanzu mun zama ɗaya a nawa tunanin.''

asim buɗe motar'sa zai yi sai ya fasa ya jingina a jikin'ta yace “Please be patient, I’m about to get into the car now. Once I park, I’ll call you.”

AFIYAH jikin ta a sanyaye tace '' to ba damuwa.''
kashe wayar tayi zuciyar ta na faman nawa wani irin ciwo ba wanda take burin da son haɗa shinfiɗa dashi sama da asim har yanzu tana mamakin sa bashi da wata buƙata akan'ta shi ko soyayyar zamanin nan ba ruwan sa da ita kamar ba wayayye ba.
tashi tayi zaune ta kalle Charity da take bakin kofa ta , tsaya tace '' Charity anya kuwa asim yana so na?.''

taɓe baki tayi ta ɗaga ƙafaɗun'ta tace '' waya sani.''

dafa kan'ta tayi tace '' Charity yaushe kika fara juya min baya ne ? ada duk abin da nake so kema kina son sa.''

shigowa za tayi sai kuma ta fasa ta tsaya a inda take tace '' saboda kina kaunar Musulmi shi ya saka ni kuma bana kaunar ki dashi Linda ga maza nan a gari da yawa wanda sun fi shi komai a cikin Christian babu masu kyawun da suka fi shi ne ?.''

ɗan murmushi tayi wanda iya labɓanta ya tsaya zuciyar ta cike take da wutar sha'awar ASIM ko tunanin sa take , sai taji ta , a cikin wani irin yanayi na feeling babban burin ta be huce ta gan'ta kusa da ita, tace
''Wallahi, there's no one like Charity ASIM is unique among men. Till today, I haven't seen anyone better than him wallahi Charity asim ya haɗa komai sai dai ƙiyayyar sa ta saka ki kasa gani ga iya kula da mace ga tarairaya.''

hmmm kawai tace ta juya ta fara tafiya zama tayi a kujera ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya limshe ido tayi ranta duk a ɓace bata san taya akai ta faɗa wannan tarƙon ba ? bata da me bata amsa cije lips ɗin'ta tayi wayar ta , ta ɗauka ta shiga cikin Instagram gaban ta har wani dukan uku uku yake , ta shiga cikin inbox ɗin'ta duk da bata ga alamar shugowar sako ba, gaban ta ne ya faɗi ganin ko alamar ya ga sakon babu, to wanne ne account din sa na gaskiya ko dai fake account aka buɗe da sunan sa ?.
ganin zata wahalar da kan'ta ta , tashi ta shiga daki ajiye wayar ta , tayi ta kwanta akan gado da sauri ta ɗago jin ƙarar buɗe kofa.

ganin Joseph ta ɗauke kan'ta, tace '' Joseph kai ne haka da sassafe?.''
ɗan murmushi yayi ya shugo yana rufe kofa yace '' wallahi kuwa kun tashi lafiya?.''
charity miƙa tayi tana turo kirjin tace '' lafiya sai godiyar Ubangiji.''

hawa kan gadon yayi yace '' me ya faru?.''
kwantar da kan'ta tayi a cinyar sa tace '' AFIYAH bata gane wa soyayyar wannan mutumin maƙiyin mu ta rufe mata ido, bana son abin da zai saka Murphy's wallahi Allah zai iya kashe ta duk da tana taƙama yana ungiyar Spreaders of the dark spell kasan Murphy's besan me tazo yi nan ba ta rufe masa gaskiya tace ta , tazo yin wani bincike da yasan asim ta biyo ta ɓaro *EASTERN CAPE (South Africa)* wallahi da sai ya hallaka su domin har ita ba zai bari ba.''

Joseph yace '' bata san irin tsaurin ƙabilar ta ba ? da zata dauko kwangilar da tasan zata iya tarwatsa rayuwar ta Xhosa kabila ce da take da ƙima da daraja da take mutunta ɗan cikin ta , amma bata duba wannan martabar da kabilar mu ta bata ba shi ne take ƙoƙarin rusa mu tabbas duk lokacin da Murphy's yasan har ta canza addini saboda wani ta canza suna ranar sai dai tayi kwanan rami.''

wai waye adon tafiya.
KABILAR XHOSA

Tarihin Xhosa:
Xhosa ƙabilar Bantu ce dake kudu maso gabashin Afirka ta Kudu. Sun samo asali ne daga tsofaffin mutane masu amfani da harsunan Bantu waɗanda suka fara zama a wannan yanki tun shekaru aru-aru da suka wuce. Xhosa suna da tsari na kabilanci mai zurfi, da shugabanci na sarakuna da manyan mutane.
A tarihinsu, suna da al’adu da yawa na gargajiya, ciki har da imani da ruhun kakanni da abubuwan al’ajabi. Suna da kyakkyawan tsarin zamantakewa da nishadi kamar rawa, waƙa, da labarai.
Addinin Xhosa:
Yawanci Xhosa sun rungumi addinin Kiristanci tun lokacin mulkin mallaka na Turawa, musamman Anglican da Methodist. Sai dai kuma, har yanzu akwai wasu da ke ci gaba da bin addinin gargajiya na kabilarsu wanda ke da alaka da imani da ruhun kakanni da kuma wasu abubuwan sihiri na gargajiya.
Saboda haka, addinin Xhosa ya haɗu ne da Kiristanci da addinin gargajiya na kabilarsu.
Chapter 7 · 0% Book details