← Book details Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 13

Sashe 10

Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ASIM yace '' okay Ina ne garin ku..?.''
MARDIYYAH tace '' Timbuktu a dajin GOURMA rugar harɗ'o Bello.''
da sauri ya kalle yace '' Mali..sahel tun daga nan kike zuwa birmu ?.''
A' sanyaye tace '' eh daga nan nake zuwa.''
kai ya jinjina yace '' za ki iya rubuta min sunan rigar ku da number wani wanda iyayena zasu nema?.''
mardiyya tace '' eh zan iya .''
biro ya bata rubutawa ta fara, wayar sa ya ɗauka ya kirawo mukhtar yace '' kana ina?.''
daga can ɓangaren mukhtar yace '' ina bakin kofar office ɗin ka.''
tsaki yayi ya kashe wayar ban da iskanci, me makon ya shigo sai ya tsaya ya ɗaga mai waya tun da yaga kiran sa ai yasan nemansa yake yi.
mukhtar dariya yayi ya shigo da sauri suka ɗago suka haɗa baki gurin gaishe shi amsawa yayi yana zama tare da tambayar su ya jarabawa alhamdulillah suka ce mai.
kallon asim yayi yace '' kai yanzun nan wannan matar ta huce ta office ɗina wai uban me ya ke kawo ta makarantar'nan?.''
Asim da ya lura neman magana mukhtar yake sai yayi mai banza ya nuna be ma san me yake faɗa ba gama printing paper yayi har guda biyu yace '' ungo idar har kun yarda da sharuddan da yake cikin takardar nan na'amin ce zaku saka hannu na saka mukhtar ya saka hannu ku riƙe copy ɗaya na riƙe ɗaya sannan zata karanta a fili kowa yaji.''

jikin ta a sanyaye mardiyya ta , tashi ta amsa ta ajiye mai paper da ya bata.

zama tayi kusa da suhaila tana ƙurawa rubutun ido, ganin rubutun bibbiyu take takasa fahimtar komai dakyar ta iya saita kan'ta, cikin sanyin murya tamkar ana busa sarewa saboda daɗin Muryar tata, tace '' contract marriage rubutu ne ɓaro ɓaro a sama manya sai kasa ta fara da cewa.
ni ASIM EL'BASHIR MANSUR TURAI zan biya wa MARDIYYAH HARUNA JAURO kuɗin makaranta har na tsawon shekaru uku za muyi contract marriage na shekara uku idan shekara uku tayi zan sake ta , taje ta auri wanda taga ya dace da rayuwar ta , zata kula da mahaifiyata duk wani aiki da masu aikin gidan mu suke yi za tayi wannan shine aikin ta bayan shi babu wani abu da zata ƙara yi min , idan Shekara ukun bata cika ba ta ce baza ta iya ba na sake ta zata biya ni kudin dana kashe mata .''
wani mugun yawu ta haɗiye , aiki kuma wanne irin aiki ne ta zata kawai aure ne za suyi shi zata zauna a matsayin matar sa kawai kenan a matsayin yar aiki ya ɗauke ta , tayi mai aiki ya biya mata kudin makaranta, kallon suhaila tayi, SUHAILA da jikin ta yayi sanyi amma bakomai addu'a ba abin da ta bari tace '' saka hannu na saka.''

tamkar wata ɗoluwa ko sokuwa haka ta saka hannu zuciyar na yi mata wani irin bugu hannun ta na rawa ,
miƙa wa SUHAILA tayi, itama ta saka hannu mukhtar ya saka shima ya saka sannan yace '' kuje na sallame ku , ku riƙe wannan copy ɗin zan riƙe wannan a hannu na.''

to tace , tana ninke takardar fita suka yi jikin su a sanyaye da sauri mukhtar ya kulle kofar ya dawo ya zauna yace '' asim wannan wanne irin cin mutunci ne yar aiki ka ɗauke ta kenan ma?.'''
ASIM cikin halin ko in kula yace '' to bayan wannan wanne amfani za tayi min aikin ma dana bata share share ne da goge goge karta sake ƙafafuwan ta su shiga hanyar kitchen din mu.''

Hmmmm wallahi akwai ranar da zan maimaita maka wannan maganar asim ba'a raina mace ko wacce da irin baiwar da Allah ya bata karka zo kana neman hanyar da zata amince dakai nace maka nima ban san hanyar ba.
Cewar mukhtar.

ASIM yace '' wa Ni...? Allah ya kiyaye gaskiya mukhtar ka cuce ni me zanyi da wannan kwailar wallahi har ka saka zuciya'ta tana tashi ni na haɗa gado da wannan nace na haɗa gado da wa ?.''
mukhtar yace '' kayi nisa baka jin kira wallahi, amma lokaci yana nan zuwa inshallahu da za kayi amai ka lashe zancen ka , bana fatan ku rabu da mardiyya fata nake naga har jikokin ku.''
ASIM dogon tsaki yaja ya ci gaba da aikin da yake gaban sa.
wannan kenan

aginɗin wata bishiya ta zauna domin tafiya ma , ta ƙasa yin ta , zama tayi tana sauke numfashi tace '' SUHAILA gaskiya bazan iya ba , cimin mutunci zai ɗinga yi yana hulakanta ni, bani da wani gata yan uwana ba anan suke ba shekara uku fa ba kwana uku bace ba..?.''

dan Allah mardiyya ki tashi ki dena wannan zance wallahi ba ayi namijin da zai hulakan ki ba inhar ina raina, ki kyale sa ba sai kin shiga sabgar sa ba , sannan zai hulakan'ta ki ba

Cewar suhailah.

tashi tayi tana dafa ta da sauri mardiyya ta rufe idon ta sakamakon motar afiyaah da ta , tawo a guje ta fallatsa musu ruwan , da ya kwanta a gurin da suke a hankali ta buɗe idon ta kayan ta duk ya ɓaci haka kayan suhaila afiyaah ganin basu gane wace tayi musu wannan aikin ba dawowa tayi ta tsaya tare da zuge bakin glass ɗin motar ta , tace '' talakawan banza ku da kusan a kafa kuke yawo, kuka fara faɗa dani..?'' nonsense.''

Mardiyya da zuciyar ta , ta kawo har wuya bata san lokacin da ta dauki dutsai ba ta buga a glass din motar afiyaah wucewa yayi ya sauka akan goshin ta anan danan jini ya balle glsss din gaban motar ta ya gashe domin dutsai da ta dauko ba ƙarami bane.

Ihuuuuuuuuuu afiyaah ta saki tare da rufe bakin ta domin tuni bakin ta ya kumbura , har ta leɓen ta sai da ya fashe.
da sauri mardiyya ta fita a guje haka ma suhaila sai dai kafin suyi wani yunkuri security sun riƙe su, Abdulwahab da yake kusa da gurin da sauri ya ƙara so yana cewa maza ku kai su gurin police.
da yake akwai police station a cikin makarantar.
mardiyya da ranta ya ɓaci ta ture hannun mutumin da ya riƙe ta , tace '' cika ni da kaina zan kai kana?.''

cikin tsawa abdulrazak yace '' wato ke ce mara kunyar ko to za kici ubanki yau za mu nuna miki shegen birni yafi na ƙauye.''

AFIYAH fitowa tayi dakyar da sauri Abdulwahab ya riƙe ta yana cewa duk ɓarnar da sukai miki sai sun biya ki bara na kai ki asibiti.
kai kurum ta gyaɗa masa domin bata da bakin magana.
riƙe hannun ta yayi suka shiga cikin motar sa mardiyya da suhaila security suka tisa ƙ'esar su, suna tafiya da sauri mukhtar da yake kokarin buɗe motar sa yace '' officer me yake faruwa ne...?.''
Bala officer yace '' wa'yannan da kake gani yan ta'addane tsagerun makarantar nan yau to kashin su ya bushe barin wannan mara kunyar wata suka fasawa kai.''

da sauri mukhtar ya rufe motar sa yace '' subhanallahi suhaila me ya saka kukai wannan gangancin...?.''

SUHAILA tace '' wallahi tun a office din doctor take ci mana mutunci, yanzu muna tsaye nida mardiyya ta fallatsa ruwa kuma ta faɗa magana bakaken maganganu shi ne ran mardiyya ya ɓace ta jefa mata dutsai wallahi itama da tasan haka zata faru ba za ta jefa mata dutsai ba..''
Suhaila ta ƙarashe maganar ta , tana matsar kwallah.
Mardiyya kuwa ban da dana sani ba abin da take yi mukhtar yace '' a OFFICE din asim kuka haɗu?.''

Kai mardiyya ta ɗaga mai mukhtar yace '' office ka sake su wannan da kake gani bata da kirki halin tane wallahi duk abin da aka ce min zata aikata, haushi taji dan yaji asim zai aure shine ta huce akan su.''

Hadi yace '' gaskiya malam mukhtar ba za mu iya sakin su ba domin iya Abdulwahab ya san wannan maganar yana tafi kai ta asibiti amma idan zaka biyo mu ka biya duk abin da ya kashe mata shikkenan idan ta hakura a kashe case din idan bata hakura ba mi hukunta su, Saboda da hukuma a cikin makarantar nan , duk girman mutum duk ɗaurin gindin mutum idan aka kawo mana kar'ar sa zamu hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata.''

okay muje mukhtar ya faɗa yana zaro wayar sa a aljihu, number asim ya lalubo ya dannawa asim kira har ta katsai be kira ba mai da wayar aljihu yayi ya bi bayan su.
har office din yan sanda ya bisu a bayan kan'ta suka zuba su mardiyya sai a lokacin kuka ya subbuce mata bata da gata sai Allah bata da madogara sai Allah yau ita ce a hannun hukumar makaranta , mukhtar a waje suka ce ya tsaya.

Wani dan sanda ne yace '' kunga wannan duk ba abin tashin hankali bane inhar zaku iya fansar kanku ai shikkenan kuna mata ku bari kanku ya kulle musamman ma ke yar fillo komai yaji ya ƙarashe maganar sa yana lasar bakin sa.

da sauri mardiyya ta ɗago kwata kwata bata gane yaren sa ba suhaila tace '' auzubillahi muna neman tsari da wannan bakar rayuwar wallahi idan baka iya bakin ka ba sai mun tona maka asiri mun maka kama da yan iska?.''

sai a lokacin mardiyya ta dauki hasken abin da yake nufi jikin tane ya fara rawa ta shiga uku karo na biyu kenan da aka taɓa yi mata wannan abu tsoro da farga ba duk suka cika mata zuciya

tsawa ya daka musu ya bar gurin ransa yana ɓaci beyi tsammanin ba wayayyu bane su.
Chapter 10 · 0% Book details