Sashe 6
Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
knocking kofar motar sa tayi tana sakin wani killing smiles.
ƙasa yayi da glass din motar sa, wani kallo yayi mata ya ɗauke ƙansa yace '' afiyaaaah wannan ba suttura bace kije ki canza kaya ko ki saka hijabi ga kanki babu dan kwali bakya tsoron aljanu?.''
turo baki tayi cikin shagwaɓa tace '' to ka shigo cikin gidan mana ka zauna a cikin mota .''
Mukhtar yayi saurin datakar da ita yace '' Hajiya afiya ba magana..''
dafa kanta tayi tace '' mukhtar ya gari ya aunty tawa take.?''
alhamdulillah yace yana dauke kan sa , marairaice murua tayi tace '' Please ku shigo ciki mana.''
ASIM yace '' kiyi hakuri sauri nake kinga dare yayi daga nan zan sauke mukhtar na huce asibiti.''
ji tayi wani abu ya tsaya mata a maƙogaro, saboda tsabar takaici bata san lokacin data dunkule hannun ta ba har farcen da ta saka ya ji mata ciwo bata damu ba , ta matsa daga jikin motar sa tace '' okay bakomai Allah ya kai ku lafiya.''
Amin yace yana zuge glass din motar sa .
dafa bangon gidan ta , tayi tana ɗibar ta , cire talmin ta tayi ta shiga cikin gidan ta da gudu bata tsaya a ko ina ba , sai a tsakiyar hamshaqin parlour ta fashewa tayi da kuka
Charity fitowa tayi jin kukan ta da gudu shigar ta toilet kenan ya gama cire kayan taji kukan ta cikin tashin hankali tace '' ina asim din yake me ya faru..?.''
lokaci ɗaya ta jero mata wa'yannan tambayoyin.
AFIYAH tace '' sun tafi wallahi sun tafi shiri na ya tashi a banza anya kuwa asim yana da lafiya...?.''
Charity zama tayi a kusa da ita ta kama hannun ta tana , shafa mata tafin hannu tana mata messaging hannun ta , tace '' gaskiya bashi da lafiya kawai ki, ki kirawo Samuel ku kwana tare zai ɗeɓe miki kewar guy nan.''
Cikin kuka haɗe da ɗaga murya tace '' Charity bana son kowa sai asim bana sha'awar ko wanne namiji sai shi wallahi shi nake so shi nake so mu kasan tare da shi,
takaici ne ya kama Charity amma sai ta danne tace '' okay to ke yanzu dai Kinsan duk wani lafiyayyan namiji ya ganki sai, hankalin sa ya tashi sai ya ji yana so ya kusance ki, amma gaskiya dole na faɗa miki gaskiya ko da zaki ji haushi zuciyar asim kaɗai kika mallaka bawai jikin sa ba , yana da iko da jikin sa kuma asim yayi nisa bazai taɓa kusantar zina ba dan haka ki canza salo inhar kina so aikin mu ya ci gaba da tasiri akan ki, dole fa wata ran yayi aure ko da baya so kuma zai haihu ke kuma me makomar ki..? ki canza tunani idan har kina so ki mallaki komai na rayuwar asim sai kin aure shi inhar fa kenan yana da lafiya idan bashi da lafiya to fa ba iya ke kaɗai ba ko wacce mace ba zata taɓa burge shi ba ki zauna yi tunani.''
charity ta faɗa tana saurin barin gurin.
shiga toilet tayi ta kifa kan'ta a jikin bango tana sakin wata ajiyar zuciya hawaye suka shiga sintiri akan fuskar ta.
cikin parlour kuwa sosai maganganun Charity suka ratsa ta , ta shiga auna su da sigar ma'aunin magana , tana son tantance gaskiya ta zabe hanyar da taga zata fi mata saurin isa ga burin ta..
Wannan kenan
kallon sa mukhtar yayi lokacin da ya gama dai-dai ta parking din sa yace '' gaskiya inhar zan baka shawara ka dauka asim be kamata kamar kai, ana ganin ka da mutunci da ƙima ba a cikin ƙasar nan , ka ɗinga mu'amala da wannan yarinyar wata ran fa wallahi ba wanda ya isa ya kankare ka daga zargin mutane, wannan asim ba matar aure bace kalli mardiyya yarinyar kirkir ko ba ma ita ba akwai mata wa'yanda gidan su gidan tarbiyya ne , be kamata dan ba ran mahaifin ku ba , ace kai da kake babba ka kasa samo mar kwarai ka aura.''
Asim yace '' daga anyi magana kace mardiyya to ka aure ta mana kai ni bana son village girl ba abin da suka sani ba abin da suka iya gidadawa ne me zan yi da mace ba wayayyiya ba , wannan yarinyar da bata fi yar ciki na ba.''
Mukhtar yace '' hmmm gaskiya kayi nisa baka jin kira ni kai nake yiwa sha'awar ta , wallahi da ba dan ina maka kwaɗayin auren ta ba , da tuni ni zan aure ta na jima ina bincike akan yarinyar da dabi'un ta.''
ASIM buɗe kofa yayi ya fito domin idan yace zai tsaya jin maganganun mukhtar tofa ransa ne zai ta ɓace , ai ta magana ɗaya da ba dan yasan asalin mukhtar ba sai yace maye ne wannan magana taki ƙarewa, shifa tun da yaga yarinya ƙarfe 11:30 na dare a waje wata mota ya sauke su ita da kawar ta yaji ya tsane ta ta tsani mazinaci gwara wanda zai fito da halin sa amma masu saka hijabin nan mafi a kasari yan iska ne fakewa suke da hijabi.
dariya mukhtar yayi yace '' asim wallahi kana son yarinyar nan akwai abin da yake danne maka son ta a cikin zuciyar ka.''
cikin hassala yace '' mukhtar dan Allah zo ka tafi gida na gaji magana kaɗan mardiyya idan bata yarda da contract ɗin nan ba ka samo min wata, inshallah zan cikawa mommy burin ta.''
zama ta yarda tana da buƙatar kudi.
mukhtar ya fadi haka yana fitowa daga cikin motar.
ASIM yace '' macen da take yawon dare ai bata da wata bukatar kudi saboda tana samun abin da take so.''
Mukhtar yace '' asim dan kaga mace a hotel an sauke ta hakan baya nuna cewa ita yar iska ce inhar bakai ne ka gani ba da idon ka a gaban ka sukai iskancin in haka ne muma sai suce mana munje kamawa karuwan room.''
wallahi Allah mukhtar kana da kafiya ni kaga sai da safe ina da abin yi.
Mukhtar yace '' kai da kake gauro ma kace kana da abin yi balle ni da nake da mata.''
dariya asim yayi yace '' rai dai.''
Mukhtar yace '' oni jikan rufa'i dan balaraben nan yaji hausa har da su ƙarin magana.''
banza yayi mai ya fara tafiya ganin haka mukhtar yace '' ka gaishe da mommy kace mata sai da safe ni gida zan tafi.''
''TO.'' kawai asim yace.
juyawa zai yi sai yaci karo da tukunyar da aka saka flowers, kaucewa yayi yana dariya ya buɗe motar sa ya shiga.
wannan kenan.
MARDIYYAH kwana tayi tana neman zaɓin Allah bayan ta gama sallah ta zauna tana karatu idan ta tuno da jarabawar asim za su yi gaban ta faduwa yake bayan anyi sallar asuba bacci ya kwashe ta.
karfe bakwai daidai ta tashi cikin sauri ta shiga toilet cire kayan ta , tayi shaf shaf tayi wanka ta fito sanye da hijabi har ƙasa ramsi da take kwance kamar bata san da yau suna da jarabawa ba.
SUHAILA da ta gama dafa musu taliya da manja da yaji daman tabar mardiyyah ne tayi baccin da jiya bata samu tayi ba , tun da jarabawar karfe tara ce da rabi.
akwatin ta ta buɗe ta dauko manta ta shafa bayan ta gama shafa mai ta dauki bra din ta da pant ta saka sannan ta dauki riga ta atamfa robber ta saka sannan ta cire hijabin ta.
SUHAILA tace '' tab kalli yadda kanki ya tsofa kamar ba shekaran jiya nayi miki wannan kalbar ba.?.''
Ramsi tace '' a yanayin kan mardiyya wannan kitsom ma ai ya dade tunda gashin ta yana da santsi.''
SUHAILA tace '' Hakane wallahi.''
MARDIYYAH janyo plate din taliya tayi gaban ta tace '' ramsi bismillah.''
zaro ido ramsi tayi tace '' Ni a'a rabani da kayan ulcer.''
hararrata suhaila tayi tace '' kema ke kikai mata tayi kim manta ita yar gayu ce kayan gwangwani ta iya ci..?.''
mardiyya murmushi tayi bata ce komai ba da yake ita bata fiye son yin magana ba sau tari mutane me girman kai suke kallon ta ,
gama ci suka yi, suka wanko hannun su, turare ta fesa wanda idan ba kusance suka samu da mutum ba , ba me iya jiyo kamshin turaren nata.
fuskar ta , ta wanke ta saka hijabin ta jakarta ta dauka da yar ƙaramar wayar ta kirar nokea me madanne sakata tayi a aljihun rigar ta exam card din ta , ta dauka da biron ta sai takardar da take karatu.
suhaila ma tuni ta shirya cikin abaya Egypt ash colour ta yi roiling da mayafin ta , agogo ta daura ta dauki jakar ta yar gidan dior ta rataya.
da yake mahaifin suhaila yana da rufin asiri haka ma yan uwan ta ita ce mace kaɗai dan haka suke nuna mata gata ta ko ina tafi mardiyyah da iyayen ta ba yau babu gobe, wata ran ma sai su kwana basu ci ba , yan shanun da suke dasu sun ƙare yanzu sauran guda biyu kuma duk maza balle suce zasu tatsi nono su sha, gwara yanzu ma da baffa yake amsar kiwo yana fita dasu shine har yake samun wanda zai aiko mata.
shi ya saka bata biye shigewa suhaila ba duk da ita , take janta a jiki kuma ba ta nuna mata banbanci so tayi ta samu daidai da ita.
dafa ta suhaila tayi tace '' tunanin me kike yi..?.''
da sauri ta kalle ta , tace '' bakomai mu tafi ko?.''
Ramsi tace '' lokaci yayi ne?.''
Suhaila tace '' a'a 9:30 zamu shiga.''
okay inama da lokacin ci gaba da bacci na ba ma lallai na shiga ba ni wallahi bana kaunar jin sunan jarabawa.
banza sukai mata suka fita.
kan'ta a ƙasa jikin ta duk yayu sanyi haka suka sauko ƙasa lokacin har ma'aikatan da suke aiki a reception sun zo gaisawa sukai da madan Sophia.