← Book details Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Jami'a Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a waje kuwa mukhtar ne yake ta kiran asim amma sam wayar bata shiga , mai da wayar yayi ya zura wayar sa a cikin aljihu ƙansa ya ɗago karaf suka haɗa ido da Abdulwahab da afiyaah ɗauke kai yayi yana cewa inshallah sai Ubangiji ya kawo sanadiyar rabuwar ki da abokina ya fadi haka a cikin zuciyar sa afili kuwa be nuna komai akan fuskar sa ba hannu ya bawa Abdulwahab suka gaisa yace '' ashe haka abu ya faru..?.''

wallahi kuwa ai wa'yannan yara sun nuna rashin mutunci kallo yadda sukai mata da fuska kallon fuskar afiyaah yayi ji yayi dariya tana neman kubbuce mai domin bakin ta yayi wani irin kato ya kumbura haka goshin ta ma duk halittar, ta tabi ta sauya dakyar ya iya saita ƙansa yace '' gaskiya basu kyau ta ba amma kema afiyaah ke dena tsokana Allah ma ya rufa asiri abin iya nan ya tsaya mu shiga daga ciki ko..?.''

taɓa rai tayi, tayi gaba da sauri Abdulwahab ya bita, domin baya so abin da zai saka be samu afiyaah ba.
girgiza kai kurum mukhtar yayi domin yasan halin Abdulwahab sarai ba mutumin kirki bane ,
bin bayan sa yayi suka shiga direct gurin D.P.O aka tura su, gaisawa yayi da su mukhtar sannan ya kalli AFIYAH yace '' me ya faru har suka fasa miki mota..da fuska?.''
Cikin kissa tace '' ina parking kawai naji ruwan dutsai ita wannan har cewa taka sai ta kashe ni..''
ta ƙara she maganar ta , tana nuna mardiyya.
da sauri mardiyya tace '' kiji tsoran Allah wallahi yallaɓai ita ta fara yi mana kuma ni bansan haka zata faru ba da ban yi ba tun a bakin kofar office din doctor ASIM take ci mana mutunci..''
D.o.p yace '' baku san hanyar zuwa gurin hukuma bane da zaku dauki mataki a hannun ku?.''
shiru, suka yi hankalin mardiyya a tashe yake , tsoran ta daya kar ace a gurin nan zasu kwana gobe suna da jarabawa.

Mukhtar ne yace '' yanzu dai ayi musu afuwa ke afiya kiyi hakuri komai ya huce su baki hakuri.''
wani kallo tayi mai ta dauke kai tace '' yallaɓai ni dai gaskiya abimin hakki na glass din motata ya fashe ni wallahi da ace iya glsss din motata ya tsaya da sauki kalli fuska ta yanzu dole sai na zauna nayi zaman jinya duk wani abu da nake yi ya tsaya ita zata dinga banu kudin da zan dinga cin abinci ?.''

d.p.o yace '' kiyi hakuri komai yana son masalaha kema baki san wata rana alfarmar da , za suyi miki ba kiyi hakuri ki fadi abin da kika kashe su biya ki , su gyara miki glass din motar ki.''
ya tsuna fuska tayi tace '' idan ma na faɗa iya biya za su yi kawai yallaɓai ku hukunta su , ko sharar office office ku basu da ta ajujuwan makaranta Saboda idan an biya kudi gaba za su ƙara idan kuwa jikin su ya faɗa musu ko cewa akai suyi wallahi ba za su yi ba..''
Mukhtar yace '' gaskiya ba za su yi wannan aikin ba ki fadi nawa ne na biya ?.''

D.o.p yace '' to ku zo ku hau kan kujerata sai ku yanke hukunci.''
matsar kwalla mardiyya tayi, malaman da suke yan iska ace su dinga tafiya suna share share a office din su.

AFIYAH tace '' kai hakuri yallaɓai ni dai ka duba fuskata ka tausaya min a yanke musu hukunci ni bana bukatar kudi nafi karfin abin da za su bani.

kallon mukhtar yayi da gaba ki ɗaya ransa yaka a ɓace yace '' kai me Zaka ce ?.''

Mukhtar yace '' ina nema musu sassauci kayi hakuri a basu sharar theater idan ya zama dole su yi, suyi shara ta rana daya shikkenan komai ya huce.''

yan rubuce rubuce yayi sannan yace '' ku ba ruwan ku da ita ko kallon banza wani a cikin kun ku yayi mata ke ki zo ki faɗa min sannan ku zan baku aiki ku share wannan theater ta new side ku share ta, tas.''
to suka ce nan suka saka hannu ya sallame su,
jan kunnen su mukhtar yayi sannan suka tafi hostel.
a bakin police station kuwa Abdulwahab cewa yayi '' ki bari zan gyara miki glass din yan zu hau mota ta , na kai ki gidan ku.''
AFIYAH da ranta duk yake a ɓace ba haka ta so ba tace '' a'a barshi yanzu zanyi waya a kawo min wata motar wannan bazan ƙara hawan ta ba.''
cikin rarrashi yace '' tsayawar da kikai anan be dace da ke ba kina hajiya big lady ki zo na kai ki gida ai mun zama ɗaya.''
ranta ne ya ƙara ɓace saboda a a police station kasa cewa komai yayu sannan yanzu zai zo yayi mata daɗin baki, iya uban me za tayi da wannan taga take taken sa , gwara ta taka mai burki tace '' da kata malam nace maka bana so ana dole ne ? a gaban ka komai ya faru amma sai ka rufe bakin ka kayi shiru ɓace min daga gani kar yanzu raina ya ɓaci nayi maka abin da banyi niya ba.''

Ran sane ya ɓace shi mace take fadawa haka macen da ya zamar da ita , tamkar rigar sakawar sa yan mata nawa ya buɗe aleda amma shi wata banza karuwa ke fada masa haka Allah ne kaɗai yasan irin mazan da take bi amma sai ya danne domin dole sai ya bakantawa asim rai, dole ya shiga inda asim yake shiga yace '' kiyi hakuri idan na bata miki rai dan Allah ki biyi Ni na kai ki gida..''

dankwalin kanta ta cire ta wullar a ƙasa tace '' kanka ake ji.''
kara wayar ta , tayi a kunne tana ɗagowa wata mota blue black hannu.
ƙarasa sowa inda take tayi da sauri ta buɗe motar ta shiga wanda ya kawo mata motar ta miƙa mai key din motar ta , ya amsa cikin ladabi.
aguje ya ta fita sosai take gudu tamkar wacce zata tashi sama , ranta gaba ki ɗaya a ɓace yake musamman ma da ta hau kan titi...
yau so tayi idan ta dawo, daga gurin asim zata huce club saboda akwai gagarimin party tsaki taja tana girgiza kai tare da dukan staring ɗin motar ta.
bata tsaya a ko ina ba sai a gaban tafkeken wani gida horn tayi mai gadi ya buɗe mata gate.

parking tayi, ta fito tana jan ƙaramin tsaki sosai tayi tafiya sannan ta ƙara so inda kofa take tana zuwa kusa da ita , ta buɗe shiga tayi wani irin hadaddan parlour ta shiga ba kowa a ciki.
wayar ta , ta ciro a cikin jaka ta shiga contact din ta ji tayi ta baya an rungume ta da sauri ta juyo tana cewa shegiya ashe kina nan , na zayi zatan kin fita ?.
turo dauri gaban goshi tayi tace '' ya za ayi na fita Alhaji yana nan.''
hnmmm kaji manya kece za ki iya zama batare da kin ci mace ba.
da sauri ta saka hannu a bakin afiyaah tana cewa kiyi a hankali yana nan.
me ya faru naga duk kin canza kardau wani ne yayi miki wannan dukan kinsan bariki ba tabbas.
hmmm mu zauna akwai labari.
afiyaah tace haka tana dafa kafaɗar shema'u.
Shema'u tace '' kinga mu shiga daga ciki bana so Alhaji yasan ina kawo mata cikin gidan nan kinsan fa besan me nake ba , maza zo mu shiga wancan dakin.''
Amina alhasan Muhammad opay 1k
814185374

Ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785374
free page ya kusan karewa.

*JAMI'A*

Ina hajjiyo da yan kwalisa to ku garzayo OUMYASMEEN COLLECTION domin samun kaya na kerewa Sa'a ki zama fitila wajen oga ba abin da bana siyarwa cikin fara shi me sauki

https://chat.whatsapp.com/DSd6g96hO2F41IG6k43rEl?mode=ems_copy_t

*Episode 6*

Kallon shema'u tayi tace '' ke ni ba zama na zo ba wallahi raina duk a ɓace yake.''
Shema'u tace '' Please mu shiga kar yazo ya ganki anan kinsan fa na faɗa miki gani yake gaba ki ɗaya na dena mu'amala da ku, tun da ya ja kunne na wai sai na rabu da yan iskan kawayena yan bariki.''

Afiyaah ranta ne ya ƙara ɓace tace '' akwai ɗan bariki da ya huce ke , ni wallahi kina ba ni ma mamaki nifa ba ayi namijin da zan zauna yana shinfiɗa min dokoki ba , shi ya saka ma aure baya gaba na me na nema na rasa ?.''
hmmm kawai shema'u tace ta buɗe wata kofa ta shiga afiyaah bata da wani zaɓi da ya huce itama ta bi bayan'ta.

me makon ta tarar da daki ƙatuwar baranda ta tarar an mata ado me kyau ga bishiyu sai rangaji suke.
sosai ya jinjina kudin Alhaji yahuza ashe haka yake da uwar dukiya, tsakanin sa da asim wa yafi wani kenan ? ai bata taɓa zaton a wannan ɗaular kawar tata , take ba

bin bayan ta , tayi suka shiga wata kofar glsss wani hadaddan parlour suka tarar afiyaah zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun parlour tana sauke ajiyar zuciya.
Shema'u zama tayi kusa da ita , tace '' kawata me ya faru?.''

kai shema'u ko drinks baki tare ni da shi ba kina tambaya ta me ya faru to budurwar asim ce ta , fasa min kai.
kama baki tayi da haɓa tace '' budurwar asim fa kika ce min?.''

Wallahi kawata budurwar sa , amma fa ba son'ta yake ba , kinsan waccan shegiyar uwar tasa , bata sona to ta matsa mai sai yayi aure, shi ne nace mai yayi auren contract da yarinyar nan da shekara uku ya sake ta , manufa ta yin haka kuwa bana tunanin ki shekara biyu wannan uwar tasa za tayi ciwon fa suga ne da ita rana ɗasai dai a wayi gari ta mutu kinga tana mutuwa ko arba'in ba zan bari a yi ba sai ya sake ta ya auri ni.

cikin mamaki shema'u tace '' to ke yanzu kin faɗa mai wannan maganar?.''
Chapter 11 · 0% Book details