← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 29

Sashe 6

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wannan shine tarihin soyayyar su shi da Madinah wanda ya tuna a wannan ‘yan dakikan da suke kallon debe tsammani shi da ita.
**** **** ****

Da tunanin sa ya zo nan, sai ya dauke kai daga kallon kudar da suke yi wa juna, ya juya da zummar cigaba da tafiya ya bar ta a wurin, ba tare da ya kara tankawa ba.
Madinah bata yi fushi ba, ta hakurkurtar da ranta da cewa fushin fari ba nata bane, Allah na nufin su da wani al’aamri maigirma da ya sake hada su (at appropriate time), ta sake biyo bayan sa jiki babu karsashi, yana saka kafa tana mayas da tata duk inda ya cire tasa, cewa tayi cikin muryar dake raurawa.
“Sarham, yaya bayan rabo?”
Cikin dakiya da tsare gida yace “bayan rabo kuma? Sai tarin alkhairi” “Kamar baka gane ni ba?” Madina ta fada kamar zata fashe da kuka wannan karon, idanun ta na kallon kasa, sun kasa rike hawayen yanzu, suna cigaba da tafiya zuwa dakin karatu, hawaye na tsirgo mata. Sarham yace.
“Madinah kenan, ni kuwa na gane ki, ko ba Madinah Attahiru diyar masu Bankin Musulunci na Duniya bace? Idan na gane ki sai me hakan zai kare ni da shi, ni Sarham dan yaku-bayi?”
Madinah tana hawaye tace “zaka iya fadin komai a kaina ba tare da na ga laifin ka ba Sarhm, laifi kan laifi na san na yi maka amma ina da DALILI na.
Abu daya nake so ka gane yanzu, Daddyna daka sani a da can, to bashi bane yanzu. Wannan sabon Attahiru SoronDinki ne, wanda duniya ta biyar dashi, yanzu ya gane cewa rayuwar kanta da dan adam kansa komai mukami da mulkin sa, da dukiyar da yake tinkaho duka ba a bakin komai suke ba.
To cut it short, Daddyna ya dade yana neman ka ido rufe domin ya nemi afuwar ka, ya kuma baka damar da ya dade yana hana ka”.
Murmushin da Dr. Sarham Shanono yayi irin wanda yafi kama da a kira,
“na dade da baiwa wannan tatsuniyar baya” ne.
A fili kuma yace “Madinah Soron Dinki, takamaimai me kike so da ni yanzu a takaice, da yasa kike min wannan binbinin haka?”
Ai jin haka Madinah ta tabbatar yanzu kam Sarham ya gama da babin ta, yau ita Sarham ke cewa tana masa binbini! Wannan ba Sarham din data sani a baya bane halinsa duk ya canza, wancan jovial ne mai saukin kai da dadin sha’ani, ko dai wani ne mai tsananin kama da shi da irin sautin sa ta gamu da shi saboda yadda ta saka shi a ranta???
Sai kawai Madinah ta durkushe anan inda take tsaye, cikin korran grass carpet (ciyayi) ta saki kuka mai cin rai.

A can zamanin baya Sarham ba abinda ke daga masa hankali irin damuwar Madinah Attahiru, amma wallahi yanzu bai ji ko gezau ba wai an tsikari kakkausa, ya yi kuka har fiye da wannan da take yi yau akan rashin Madinah, da kuma wulakancin da mahaifin ta yayi masa ranar da yace “ba zai taba baiwa dan almajirin gwamnati (dan malamin makaranta) ‘yar sa ba”.
Ita nata kukan kuwa a yanzu ai na jin dadi ne, abinda bai sani ba, kukan Madina yau ya kunshi abubuwa masu dimbin yawa, har da wadanda tunanin sa da tsinkayen sa bai bashi ba.
Bata taba daina son sa ba, a duka wadannan shekarun daidai da rana daya, ta yanke alaqar su ne domin ta samu damar yin biyayya ga mahaifin ta, wanda ba abinda bai yi mata a duniya ba, ya kuma fifita soyayyar ta akan ta ‘yan uwanta maza bakidaya kasancewar ita kenan masa diya mace, kuma auta a cikin ‘yan maza bakwai. Wannan shine dalilin nata.
Sarham bai tsaya Madinah ta gama kukan bay a cika bujensa da iska ya bar wurin, sai dagowa tayi bayan ta share hawaye ta neme shi a filin wajen ta rasa.
A lokacin ta cigaba da tuno rayuwarta ta baya tare da Sarham, abinda ya faru shekaru bakwai da suka gabata, ta tuno asalin ta, haduwar su, lokutan su tare a campus, da abubuwan da suka faru da ita bayan rabuwar tasu…….
**** ***** ****
Chapter 6 · 0% Book details