Sashe 12
Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kyar Surayyah ta motsa baki ta ce cikin rawar murya “I’m sorry Yaya Doctor!” Ta kara cewa “I’m so sorry” “Sorry for what?!” Ya tambaya (in exclamation). Sumayyah kanwarta wadda ta soma hawayen ganin yadda ransa ke hauhawa wajen baci tun ma kafin yaji laifin da Surayyah tayi masa, taga basu da mafita banda ta gaya masa gaskiya, sai tace. “Bhaiya, maganar gaskiya ko sau daya bata taba bani komai tace in kai musu ba, sai ranar da ka zo take gayamin ai kayan kwalliya take saye da kudin, ni ma kuma ban taba zuwa duba su ba, wallahi na manta hanyar gidan sam, lokunan (are complicated), don haka dukkan mu mun yi laifi Bhaiya, muna rokon ka in ka tashi hukuntamu, to kayi mana sassauci a hukuncin ba don halin mu ba, ka yi mana uzuri da ajizanci irin na kowanne dan adam”. Sarham ya kasa magana don takaici sai raba ido yake a kan su su biyu, amma kalaman ta na karshe sun yi tasiri sosai a cikin ran sa dake tafasa, ya ciza fatar bakin sa kadan, yana kallon su da lumsassun idanu duk sun zama unease, kada Surayyah ta ji labari, wadda ta kasa zama tana daga tsaye har lokacin amma kafafun ta rawa suke. Da kyar Sarham ya hadiyi miyau, yace cikin sanyin murya. “My only two and beloved Sisters ne suka ci amana ta haka?!” Sumayyah ta cigaba da hawaye tace “wallahi Bhaiya babu ruwa na, bata ma taba gaya min ba ni sai ranar da ka dawo. Ni nawa laifin na rashin zuwan maka ne kawai, da kuma rashin taya ka kula da abinda kake so a bayan idanun ka, wanda ko kadan baka cancanci hakan daga gare ni ba. Kamata yayi ace ko kare ka ajiye don kana son shi ya kamata in kula maka dashi in your absence balle mutane ‘yan adam. Na yi kuskure Bhaiya, amma na tuba, ka karbi hanzari da uzuri na, ajizanci ne na dan adam da mantuwa, na tuba Bhaiya bazan sake ba”. Sumayah ta durkusa a gabansa ta daga hannu cikin roko, hawaye na bilbila, Surayyah ta kasa kare kanta amma hakika yau ta ji kunya, ta kuma yi nadama a lokacin da bata da amfani, wato lokacin da ko ta bada sakon ba zai yi masa amfanin komai ba tuda ya riga da ya dawo, gashi ta san ta sirewa dan uwan nata yanzu, saboda rashin amana, koda bai fada ba bai kuma bai doketa ba. Mama ta shigo da sauri jin kukan Sumayyah, tana tambayar su “me ke faruwa ne haka a falon nan ake kuka har da kururuwa?” Sarham ya ce cikin kololuwar feeling of disappointment “Mama kin gan su, su duka sun ci amana ta!” Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini ranar da zan haifi Da maci amanar dan uwan sa, sun dai yi kuskure wanda ba wanda yake sama da aikata shi, ka yi hakuri Sarham ka yafe musu kaji! Duk da ban san girman laifin ba”. Sarham ya dubi Surayyah (feeling disappointed) ya ce “Surayyah idan abinda kika yi kyautatawa ne ga zumunci na da ke, na gode. Allah ya saka da alkhairi. Ke kuma Sumayyah baki yi min laifin komai ba, amma daga yau na san matsayina a wajen ki, na kuma ga ajin da kika ajiye ni, tunda bazaki zame min ‘yar uwar da a bayan raina zata kula da haula ta ko abinda na bari ba”. Sai ya sa kai ya fita, makwallaton sa har motsi yake don tsananin bacin rai, ba tare da ya tsaya yi wa Mama bayanin laifin da suka yi masa ba. Mama duk suka saka ta a duhu, ta rasa gane komai, sai da Sumayya ta share hawayenta ta gaya mata komai cikin muryar kuka. Mama ta kasa tuno mutanen da ake matsalar a kan su, ta san dai ire-iren jama’ar sa ne da baya rabo da kyautatawa, da irin jajibe-jajibensa, amma hakika ta harzuka da abinda Surayyah ta yiwa Yayanta, bata san ko su waye wadanda yake turowa kudin ba duk wata tun daga Jeddah ba, ba kuma tareda ta damu da ta sani ba, amma tunda har ya dauki tsahon shekaru uku yana turo musu kudi duk wata bait aba mantawa ba to masu muhimmanci ne a wajensa, kasancewar ta san halin sa akan son tamakawa mutane da son kyautatawa na kasa da shi da marassa lafiyansa, sai hakan bai zame mata wani sabon abu cikin halayen dan nata Sarham ba, Mama tace. “Da gaske wannan cin amana ne, kuma zai fi bakanta masa rai ne kasancewar mutane mafiya kusanci da shi ne suka yi masa”, ta dube su cikin fushi ta sake cewa “a duniyar nan in dan uwanka ciki daya bai rike maka amana ya rufa maka asiri ba, in bazaku kashe ku rufe kai da shi ba, ba tareda ko iyayen ku sun ji ba, waye zai yi maka? Sannnan da wa zaka yarda a duniya, kuma da wa zaka aminta? Kin yi kuskure Surayyah, ba dan uwa irin naku ake badawa kasa a idanu ba, saboda shi din dan uwa ne har dan uwa guda har da rabi, ko in ce Yayan da babu irin sa, ko don son da yake muku da kulawar sa da kyautayinsa gare ku”. Surayyah ta gama dukkan nadamar da mutum zai iya, a lokacin da yasan bai kyauta ba aka kuma ankarar dashi. Cikin kuka ta ce. “Mama don Allah ki bashi hakuri, na tuba na bi Allah na bi shi, zan biya shi duka kudin sa da zarar na fara aiki, dama ban kashe da niyyar bazan biya ba, kawai ya zo ba ‘notice’ dina ne, nayi niyyar in bata ta kai musu kafin lokacin zuwan sa, wallahi zan biya shi”, Mama ta wani harareta ta ce “ta baya ta raggo. Duk abinda zaki biya shi yanzu bazai karba ba, kuma bazai masa amfanin komai ba. Surayyah an yi bokon banza tunda shi ya koya miki son abin duniya, kayan kwalliyarbanza kayan kwalliyar hofi, saboda Allah da me iyayen ki suka rage ki banda son kyale-kyalen ki na banza da wofi da kika dorawa kan ki tun shigar ki jami’a, da son lallai sai kin hada kafada kin goga da kawaye da suka dauki karyar rayuwa suka dorawa kan su? Kullum ina nuna miki ‘reality’ akan barin sayen abubuwan nan masu tsada da suka fi karfin aljihun ki ko na iyayen ki, kina ganin kamar ni kaina ban waye ba, tunda bana sayen turare su ‘designer’ sai Humrah sai Oud, har ni zaki nunawa sanin ya kamata akan rayuwar duniya Surayyah? Yaushe aka haifeki har kikayi wayewar??” Mama tayi ta fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daman tana cike da halin Surayyah din kan irin tsarin rayuwar ta mai tsada, fadan da Sarham bai tsaya ya yi musu ba don bacin rai shi Mama tayi ta yi musu ta wanke Surayyah tas. Wankin babban bargo. Surayya dai sai hakuri take baiwa Mama ganin har tafi Sarham daukar zafi da al’amarin. Aka ce dan uwa rabin jiki, ganin yadda duk ta muzanta sai ta koma baiwa kanwar ta Sumayyah tausayi, Summy ta ji kamar a maida laifin ya koma kanta, ita a cigaba da yi mata fadan ita kadai, ta koma taya ta suka yi ta baiwa Mama hakuri da rokonta kan ta bashi hakuri in ya dawo, sunyi alkawarin bazasu sake yin kuskure makamancin wannan ba, Sumayyah dai ta ari laifin suka yafa shi tare da ‘yar uwar ta. **** **** ****