← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 29

Sashe 21

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hauwan ke faman yin nata, amma fa ita nata na farin ciki ne. Ganin yanayin wahala da rashin lafiya da ya same su ciki kuma a kauye ya karya zuciyar sa, wanda ba cikin sa ya tafi ya barsu ba. Cikin muryar kuka Hauwa ta ja sheshsheka ta ce “Likita sannu da zuwa”, tana mai yi ma saitin da muryarsa ke fitowa kallon ga ZULKIFLU YA DAWO. Sarham ya matso gaban ta har tana iya shako kamshin hamshakin turaren sa na ‘Oud Abyad’ ya ce “to ko ke fa Maijiddah! Amma kawai daga ganin mutane sai ki balle da bokitin hawaye? Ai sai su Malam Isa da Tafada su dauka baki yi maraba da zuwa na ba sam”. Tayi murmmushi, har kuncinta ya lotsa ciki sosai, wani abu da ke kara ma Hauwa’u kyau, yace “maza je ki kwaso kayan ku, Inna Tafada taimaka min ki dauko Inna don Allah a sa min ita a bayan mota, in yi maza in kaita asibiti, a kula min da ita da kyau”. A yau yana dakacen inama shi ba likitan ido bane, na zuciya ne! So that ya iya duba Innarsa da kansa”. Hawayen dadi ya sake kecewa Hauwa, don ita ai tayi-tayi Inna ta yarda ta zauna a asibitin Murtala a cigaba da dubata ta ki, tace in mutuwa ce ta isko ta, a barta ta mutu a cikin dakin ta yafi mata, ta fi so ta mutu a gida akan gadon asibiti, kada taje a kai gawarta mutuware a ajiye a firinji, a kuma jinkirta yi mata janaza. Kuma ita har gobe bata yarda da maganin asibiti ba, don bata ga ranar da ya yiwa idanun Kulu ba, aikin Kulu yasa ta kara nesanta kanta da asibiti, dama dole ce ta kaita a kan Hauwa dinma, shi yasa tunda ta fara ciwon nan suke dambarwa ita da Hauwa akan zuwa asibiti, daga bisani Hauwa ta dauko shatar mota tace mata zasu je asibitin Kuroda a bata magani kadai su dawo, da suka je asibitin, kallo daya likita yayi mata yace kwanciya zasu bata. Hauwa bata ankara ba sai ji tayi Inna ta tashi tsaye tace ta tashi su tafi, data tsaya yi mata magiya da gardama kan ta tsaya sai Inna ta kamo hanya abinta, ta kyale Hauwa a tebirin likita, dole Hauwa ta taso ta biyo bayan ta tana kira. Tausayi yasa ta dakata ta kama hannun ta, a lokacin suka taho gida. Hauwa bata daddara ba, washegari tayi ta rokon ta kan su je asibitin Murtala, ta tabbatar mata su bazasu kwantar da ita ba, da kyar da nacin kukan Hauwa Inna ta yarda suka je Murtala, nan suka hau layi har suka samu ganin likita, anan ne likita ya yiwa Hauwa bayanin dole Inna ta kwanta ayi mata aiki a zuciya, domin ta samu rami (hole) a zuciyarta. Ai jin haka Inna ta mike ta fice ta bar Hauwa da likita suna kiranta (again), Hauwa ta biyo bayan ta tana kuka da roko, sai Inna ta dakata da tafiya tace da Hauwa. “Idan kin manta haka aka ce min za’ayi miki aikin ido ki warke daga hakiya, amma kin warke din? To ni yanzu in aka yanka min zuciya kina da tabbacin zan mike? Ba tsoron mutuwa na ke ba domin kuwa a shekaru hamsin me nake jira banda neman hanyar dacewa da cikawa da Imani? Ke nake ji Hauwa-Kulu, in babu ni, rayuwar ki zata shiga wani hali na garari da walagigi har da da bara akan titi, don baki da mataimaki da mai yi miki jagora bata idanu kadai ba harma da rayuwar ki gabadaya, sai Allah da ya halicce ki”. Abinda Inna bata sani ba, ko babu ita Innar, ita HAUWA-KULU (modern makauniya ce), bata bukatar dan jagora don zuwa wani waje, kanta tsaye take zuwa ko’ina, iyakaci kai in ka fahimci bata gani kai ka kauce mata, wata irin brainlliant ce mai kaifin kwakwalwa da kaifin basira, gata da ji mai karfi irin na wadanda suka rasa idanun su da kuruciyar su Allah ya bata. Don dai UWA-UWA ce amfaninta yafi ga haka, wato ya wuce ta rayu don ta yi mata dan jagora, sai dai don ta zama GARKUWAR ta a rayuwa bakidaya kuma cikon farin-cikinta ta. Tun daga ranar bata kara yarda Hauwa ta ja ta asibiti ba, tayi ta kwanciya a gida suna cinye dan jarin nasu a sayen abinci kullum, tunda ba juyawa ake ba yanzu kashewa ake yi yasa kullum daurin kudin su sai kasa yake yi, kafin makwabcinta Malam Sani mai irin ra’ayin ta kan traditional medicine ya ce da gaskiyar ta, tazo ya kaita gidan mai magani inda zata samu magani na kowacce cuta ba tareda an tsaga kirjin ta ba. Aka fito da Inna daga cikin gidan ranga-ranga da daurin kayan su a bakko, aka sa a bayan motar Sarham, Tafada da Hauwa suka shiga, suka sa Innar a tsakiyar su, wadda bata san ma ko su waye a kan ta ba lokacin. Rabin jikin ta na kwance jikin Hauwa. Malam Isa na gidan gaba Sarham ya ja motar cikin nutsuwa da hanzari suka hau titin da zai maida su cikin birnin Kano. Suna tafe a hanya suka fahimci Inna ta farfado daga suman data yi, suka yi ta yi mata sannu da jiki. Malam Isa nata yiwa Inna fada da dacin rai, na yadda ta shiga duniya ta bar makwabtan ta masu kaunar ta, wai ace yanzu ta gwammace rayuwar sayar da abinci a tasha a kan zaman gidan sa, yace to yanzu me kika tsinto a tashar duk sana’ar taki ban ga kinyi arziki ba, ban ga kinyi kiba ba, na gan ki tsiya-tsiya rakace-rakace wutsiya a zage cikin ciwo. Rayuwa bata raggo bace. Haka azzaluman mutane ba’a kyale su su cigaba da aikata zalinci son ransu ga marassa karfi a doron kasa musamman mata da kananan yara kamar Kulu. Da kin zauna mun tashi tsaye mun hada karfi da karfe mun kwato miki hakkin ki, yadda makwabtanki suka fusata a lokacin da kin tsaya, in yafi karfin ki ai bai fi karfin shari’ah da Alkali ba, cewa fa mukayi ki tsaya zuwa wayewar gari mu shigar da kararsa maimakon mu dau Shari’ah a hannunmu. Kuma ni da kin zauna kin yi gaiba, na rufa miki asiri na killace ki a gidana karkashin inuwar aure in taya ki kula da ‘yar makauniyar ‘yar ki, amma ina! Ke ga ki kububuwa sarkin masu zuciyar duniya, kika dauki ‘ya ba ido kika bar BADALA!” Sarham ya rage gudun motar sa a dokar daji, a fusace yace “wallahi Malam Isa in baka yi mata shiru ba zan cillar da kai a dajin nan in ja mota ta, da me kake so ta ji? Da ciwon jikin ta ko da hayaniyar ka?” Daga haka aka samu Malam Isa yayi shiru, bai kara magana ba har suka isa asibitin Malam Aminu kano. Tun kafin su iso dama Sarham yayi waya da Dr. Babangida, wani babban likitan zuciya ne (cardiologist) abokin karatun sa a Jiddah da ya dawo yake aiki a nan AKTH, shi yasa aka karbi Inna cikin kulawa daga shigar su asibitin, aka yi imajensi da ita. Kuma da taimakon sanayyar sa da Dr. Babangida yasa ta samu attention din likitoci da yawa suka rufu akan ta, don binciken hakikanin abinda ke damunta. Sai da suka kwana suka wuni a A&E ana bata taimakon gaggawa kafin a basu daki a kwantar da Inna, amma da Sarham ya zo asibitin a washegari sai yace a maidata dakin ‘Amenity’ ya kuma biya komai aka maida Hauwa da Inna kebantaccen daki wato ‘Amenity’ a sashen mata. A kwana uku sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka yi wa Inna ya fito, da gaske tana da huda a zuciyar ta, wadda ke bukatar sai an yi mata aiki an cike ramin da zuciyar tayi. Madinah na can gidan kakannin ta tana jego, Sarham na jelen asibiti dasu Inna daga nasu gidan yake zuwa shi yasa bata san me yake ciki ba, sai dai duk sanda ta kira shi a waya zai ce mata yana asibitin Aminu Kano yana da ‘patient’ yana ‘busy’, ta kuma san shi sosai da Dr. Babangida shiyasa ta daga masa kafa, yau kwana uku bai zo Soron dinki ba balle ya ga Baby Hauwa da take kira (Waheedah) tun ranar sunanta. Kowa ya dauka saboda Haj. Kulu Sarham ya sakawa ‘yar sa suna Hauwa, shi kuwa zai iya rantsuwa ya saka sunan ne don ya dinga tunawa da Inna da Hauwa a lokacin da ya neme su ya rasa. Hatta a gida sun gane yana zirga zirga, kuma ba a wajen masu jegon ba, ko jiya ya saka Surayyah girki na hanta da koda da ‘vegetables’ da kunun gyada yace ta zuba masa madarar ruwa a ciki, Surayyah ta dauka shi zai ci, bayan ta gama ta gaya masa ta gama, sai yace ta shirya a basket ta kai masa mota, Mama ta bi Surayyah daki bayan fitar sa tana tambayarta ko wa Sarham zai kaiwa abinci? Surayya tace bata sani ba, yace dai yana da mara lafiya a asibiti ne. Mama tayi wani dan tunani sai ta ce “in kika bibiya bazai wuce mutanen sa na Badala ya gano ba. sune kadai zai dauka da muhimmanci irin haka ya kasa nutsuwa in suna cikin matsala”. Surayyah ta ce cikin mamaki “ba sun bar Kano ba? Ba sun bace masa ba tuntuni?” Mama tayi dariya tace “ko a ina suke in dai a fadin Najeriya ne na tabbatar miki sai Sarham ya nemo su, ki bar Sarham akan abinda yasa kan sa, ko yake kuma kauna da son taimakawa da zuciya daya”. Surayyah ta kwana abun yana bata mata rai, na yadda ta zage ta shirya masa abincin nan da kyau, don ita bata son zancen su ma, yadda aka sakata girkin wahalar wasu kauyawa wai su su Innar Hauwa, tarkacen BADALA, don haka washegari da ya saka ta girkin again tayi maza ta ce kanta na ciwo bazata iya ba, dole sai Nancy sabuwar mai aikin Mama ya saka tayi masa ‘potatoe porridge’ da yaji ganyen alayyahu. Da dafaffen kwai. Ita Hauwan ma da ake kaiwa garar abincin mai dan gina jiki, don a samu ta murmure ta
Chapter 21 · 0% Book details