Sashe 15
Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ya birkice da neman Inna da Hauwa, har iyayen sa suka fara damuwa da saka ayar tambaya, suka zaunar da shi suka ce ya gaya musu gaskiya, bayan tausayi da taimako, meye alakar sa da mutanen nan ne? Ta yaya zai yi sabon aure amma ya raba hankalin sa da nutsuwar sa, ai sai suma ya saka su a damuwa. Sarham ya ce babu wata alaqa tsakanin sa da su, sai kauna ta fisabilillahi da haduwar jini, yace shi kawai yana tunanin a wane hali suke ciki ne, yana tsoron fadawar su mugun hannu ko fadawa hannun kanin uban Hauwa wanda baya kaunarsu kuma azzalumi ne, sannan basu da kowa da zasu kira nau in ba shi din ba (Zakari). Mama tayi fuska ta ce daga yau bana son ka kara fita neman su tunda dai ba kananan yara bane, Allah shi yake kula da bayinSa marassa karfi da masu karfi, kafin ka shiga rayuwar su ai babu uban nasu, kuma hakan bai hana su rayuwa mai kyau da shaker numfashi ba. Saidai ban sani ba ko kana da wani dalilin a kasan ran ka a kansu bayan wannan?” Wai meyasa mutane suke kasa fahimtar sa ne akan Hauwa da Innarta? Zai iya rantuwa babu wani dalili a kasan ransa a kansu bayan wanda ya fada musu. Kwatakwata kenan babu alaqa ta mutunci da zumunci a tsakanin al’ummar Annabi sai mai kunshe da MANUFA? Haka mafa Sumayyah ta taba cewa wai….. abun babu ko dadin ji domin kuwa yadda yake kallon ta muharramar sa haka yake kallon HAUWA-KULU. Can tsakar kansa ya tsinkayi sautin Abba yana cewa “talakawa nawa ne a Nigeria da suke cikin halin kaka-nikayi? In ka ce duka sai ka tsayawa rayuwarsu ka hada kan ka da abinda ba zai taba yiwuwa ba, tunda dai kayi taimako iya yinka wanda dace ya kamata ka bar su a hannun Ubangijin da ya halicce su haka, ka maida hankali ga abinda ke gaban ka yanzu. Wato sabuwar rayuwar ka ta girma da yah au kanka”. **** **** ****