← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin yayyen nata, da yadda mahaifin ta ya raba su a baya, yanzu kuma su da kan su suka neme shi ba shi ya nemi Madinah ba ta dawo masa ba, har pretending din da yayi tayi mata don kada ya koma mata ya gaya musu, da kiran sa gidan su da Daddyn nata yayi, domin ya bashi hakuri da uzurin sa na hana shi auren Madinah. Amma abin mamaki duk da wannan labarin da Sarham ya bayar Mama taki saukowa ta amshi zancen Madinah da hannu bibbiyu, musamman da taji wai har aure an daurawa Madinah bata tare ba mijin ya rasu, sai ta kara ninka ‘opposition’ din ta da zancen, inda tace cikin mamaki, “Sarham! Kai kuma inda Allah yayi da kai kenan saboda soyayyah? Bazawara/widow zaka dauka kana saurayi wanda bai taba aure ba? Bazawara fa kaikuma saurayi? Ni ban yarda wai bata je gidan mijin ba, sun dai rufa ka ne don su sayo mata matsayin budurwa, shiyasa ko lefe aka ce ka bari, kai kuwa saboda Allah me Madinar nan ke da shi da sauran mata da kake gudu suna rububin ka basu dashi?” Abba yace “Maimuna har gobe baki san SO ba na ga alama, kyale rai da abunda ya afu ga so, aure kuma ai ba kaskanci bane daraja ne, haka mutuwar miji baya nufin darajarta ta ragu, ni ban ga laifi anan ba don yarinya ta taba aure, shin Manzon mu ba da bazawarar ya fara ba? Yarinyar nan ‘yar manyan mutane ce kuma ‘yar babban mutum, sama da abunda yafi haka zasu iya cewa kafin su bada auren ‘yar su, aka ce tuwon girma… miyar sa nama Maimuna, ko yanzun ba don ta rasa miji bane yasa suka bashi, a’ah, ya ci darajar soyayyah ne kawai Allah kuma ya tsaga cewa ita din rabon sa ce”. Mama tayi shiru amma ta ki gamsuwa, ta ce “ni kawai ko ‘yar shugaban kasa ce bai dame ni ba, tunda suka raina arzikin mu tun farko nima na raina mutuncin su, saboda basu yi amfani da ilmin su ba anan don wallahi ba yabon kai ba, Sarham dina ya wuce raini, tunda Allah ya bashi addini, nasaba, ilmi da basira to ya gama bashi duk wani arziki na duniya koda kuwa a kan jaki yake yawo”. Duk aka yi wa Mama dariya Abba yace “Maimunatu Dan farin? Kike wannan zakewar a kan sa babu fulatanci? Ina fulatancinki ya tafi ne?” Ta yi fuska sosai ta ci laya tace “ko rabin farko ne shi ba Dan fari ba, ina son abuna yadda suke so ‘yar su koma fiye, sun dauko sudin kwano sun bashi, ina dalili da gatan sa shima da komai?” Abba yana danne dariyarsa yace. “Barr. Maimunatu to yaya zaki yi? Tunda shi ya ji ya gani yana son leftover din nasa a haka?” Sarham dai bai ce komai ba kansa na kasa, kamar yace da kasar ta tsage ya shige, amma ya ji ciwon kalmar nan ta an bar masa sudin kwano, ta kara rura wutar kishin sa akan auren Madina da AVM Alkali. Duk ya daina dokin auren ma, Madinar ta kara bashi haushi, amma baya jin ruwa da iska zai fasa karbar auren Madinah ko da ta haihu goma da AVM wanda ke nufin so na hakika yake yiwa Madinah. Abba da Hajiya Kulu, suka yanke shawarar wadanda za’a tura Sorondinki daga waliyyan Sarham don gabatar da zancen aure don itama Haj. Kulu tayi na’am da zancen dari bisa dari don kuwa ta san Kakan Madinah farin sani marigayi Alkalin Alkalai wanda tace zuri’arsa ne kaf suka samar da Sorondinki. A daren Abba Prof. kwana yayi yana lallashin Mama cikin dabara da soyayya irin ta manya akan maganar auren Sarham, yace mata abu daya zata duba kawai; son da Sarham yake wa Madinah, in ta duba wannan to sai ta sakawa ranta salama. Domin shi ya lura son da Sarham yakewa Madinah mai yawa ne, tunda har ya iya kwashe shekarun nan babu aure saboda rashin ta, kuma jin ta auri wani kafun shi, bai say a ce ya fasa ba. Ita kuma Mama irin iyayen nan ne masu kishin ‘yayan su, wannan son da ake fadi yana wa Madina shi yafi komai bata mata rai, don a tsarin ta sam bata son Sarham ya auri macen da son da yake mata ya zarta wanda take masa, ko wadda zata zo ta canza masa behaviours da alaqarsa dasu. A ganin ta son da yakewa Madinah yayi yawa har ya zarta nata son, ba don haka ba ai da bata yarda ta auri wani kafin shi ba, tana tsoron kada Madinah tayi amfani da hakan ta bautar mata da shi, ko ta wahalar mata da shi tunda ta zame masa rayuwa dungurungum. Duk da ta san Sarham jarumi ne akan komai nasa ko a cikin maza, kuma tsayayyen namiji ne tun yana yaro akan ra’ayinsa, amma tana tsoron wannnan matsiyacin son da yake yi wa Madinah Attahiru. Haka Abba Prof. ya samu ya lallaba ‘yan kayan sa, don shikadai yasan abinda yake zuciyar Mama, ya nuna mata in bata cire kishin matar Sarham daga ranta ba zata zubar da girmanta, kuma zata sha wahala don matsayin kowaccen su daban a wajensa, ya roketa kada ta zama fitinannun iyayen mijin zamani masu tsanar surukansu babu gaira babu dalili kawai don yaransu na son su, tunda itama ba haka Hajiyar Gadonkaya tayi treating dinta ba duk da ta san son da Abban yayi matukar yi mata, da haka ya samu ya lallabata har dai ya samu lagonta ta amince aje akai kudin auren, ta kuma sakawa al’amarin albarka. Washegari waliyyan Sarham suka tafi SoronDinki. Suka dawo da albishir mai dadi na cewa Baffanta yace Juma’ar nan za’a je a daura auren a babban masallacin juma’ah na Kano, su sun shirya tuntuni, su suke jira dama. Suka kuma fadi irin karbar mutunci da saukar girma da aka yi musu, wannan ya kara sauko da zuciyar Mama. Iyayen Sarham sun gabatar da komai na auren har sadaki ga kanin Baban Madinah tun kafin juma’ar ta zo, kuma Baban Madina yana ta kara jaddadawa kanin shi ta waya ya gaya musu shi baya karbar lefe, sadaki da kudin aure kawai yake amsa. Wannan ma ya kara sanyayawa Mama. Juma’ah na zagayowa aka daura auren. **** **** **** Tun dawowar sa Najeriya Sarham bai samu nutsuwa ba ko ta kwabo, sai yau da aka daura auren sa da Dr. Madinah Attahiru bayan saukowa daga juma’ah, mahaifin ta da duka ‘yan uwanta maza hudu sun samu sun halarci dauren auren, Madinah ‘yar dangi ce gaba da baya kasancewar auren zumunci ne a tsakanin iyayen ta, sun kuwa nunawa Hajjah Ramlah zumuncin da karah, don kwansu da kwarkwatarsu zuri’ar Sorondinki sun yi dafifi a ‘main house’ din su, don halartar yinin bikin Madina a ranar da aka daura aure. Iyayen Madinah su ya kamata a kira masu Kano, ba kuma wai sarauta ce dasu ba domin iyayen ta da dangin ta na uwa dana uba wadanda duk abu guda suke, sun kame duk wasu madafun iko na Kano. Sai bayan daurin aure ne, da ya samu ya huta ya samu nutsuwa bayan mutane sun watse, a daren daurin auren ya samu ya zauna da Sumayyah yana tambayar ta yaya labarin su Hauwa da Inna? In ce ko tana zuwa tana gano masa su da baya nan kamar yadda ya bar mata sallahu? Kuma in ce ko duk wata tana kai musu sakon da yake aikowa ta hannun Surayyah?” Ya tsare ta da kaifafan idanun shi ganin yanda tun bai gama magana ba Sumayya ta shiga cikin rudani da damuwa, na farko dai itama ta mance da su Hauwa, bata kara tunanin zuwa kofar Na’isa ba tun bayan tafiyar sa, na biyu ga abunda Surayyah tayi, wanda ke nufin dukkan su sun zama masu laifi ga Bhaiya, sai dai a ce laifin Surry ya take nata wato, sawun giwa ne ya take na rakumi. To amma ta kwana da sanin halin Bhaiya baya son yayi maka tambaya wadda a wurinsa mai muhimmanci ce ka zuba masa na mujiya nan da nan zai harzuka, sai duk ta daburce, ta hau inda-inda da in-ina, tana son cewa ba ita bace Surayyah ce, tana kuma son kare Surayyar. Kawai sai jikin sa ya bashi babu gaskiya acikin al’amarin ta, ko wani abu mummuna ya faru dasu Inna a bayan tafiyar sa, gabansa yayi mummunan faduwa ya fiddo wayar sa ta tafi da gidan ka daga aljihun gaban farar shaddar shi Wagambari wadda ta sha maikon sabunta, Ango sosai, sai walainiya yake yi a cikin farar Excelcior din, yasa dan yatsan sa daya yana dannawa Surayyah kira, tana amsawa yace ta same shi a karamin falon Mama. Tun daga jin kiran sa itama Surayyah ta hau numfarfashi ta san ta gama barewa, a lokacin suna tare da wanda zata aura a harabar gidan su wato Engnr. Aliyu Barde, wanda dan abokin Baban su ne, iyayen su suka hada su, Aliyu ya fahimci hankalin ta ya rabu gida biyu tun bayan amsa wayar ta, yace “me ya faru ne a wayar?” Surayyah ta dauki excuse daga wajen Aliyu kan Yaya Doctor dinsu yana kiran ta a cikin gida, ko zai bata minti goma? Egnr. Yace ai tafiya ma zai yi don akwai inda zashi, don haka suyi sallama kawai, sai wajen jibi zai dawo. Don lokacin an saka musu lokacin aure. Bayan sun yi sallama ya tafi, Surayyah ta taka zuwa cikin gida tana tafe salalau-salalau kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Sarham har ya gaji da jiran shigowar ta ya mike zai biyo bayan ta yana huci sai gata tana shigowa. Tun kafin ta zauna ya jefo mata tata tambayar kamar yadda yayiwa Sumayyah game da sakon su Inna da yake turowa ta account din ta duk wata, yau shekara uku bai taba fashin turowa ba, wanda yace a dinga kaiwa mutanensa na kofar Na’isa. Surayyah tayi zuru-zuru ta yi wiki-wiki da ido tayi masa shiru, kiris ya rage ya mare ta, don baya son halin ko’in kula in yana maka maganar da a wurin sa mai muhimmanci ce, kayi shiru ka zuba masa ido kamar tsohon maye kana kallon sa. Da
Chapter 11 · 0% Book details