← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba jimawa da komawar ta makaranta aka yi jarrabawar kwalifayin, aka yi hutu, wanda in sun koma su Hauwa zasu shiga aji shidda na sakandire.
Sakamakon jarrabawar qualifayin din ta lokacin da ya fito, yafi na kowa a makarantar kyau, yafi na kowa daraja, komai nata daga ‘A’ sai ‘B’. A lokacin kam makerin budurci ya gama kera Hauwa Bilyaminu, da ka ganta kaga kyakkyawar bakanuwar budurwa, mai samun kulawar Uwa da tsaftar jiki da abinci mai gina jiki, yadda ya kamata.
Kafin su Hauwa su koma hutun da zata fara aji shidda suka bar sayar da abinci a tashar kuka, suka dawo sayarwa a tashar Kano-Line, ba don komai ba sai don yafi kusa da makarantar Hauwa kuma samarin tasha sun fara son matsawa Hauwa a can tashar Kukan, da cewa suna son ta har da masu neman ta da sakarci, duk da idon uwar ta kuwa.
Wannan ya tadawa Inna hankali ba kadan ba, ta ga dole su bar tashar kuka zuwa inda basu saba da kowa ba. In yaso ta hakura da ko me take samu a tashar don kare mutuncin Hauwa. Don da yawa suna amfani da sabo da mutuncin dake tsakanin su da Innar ne, su soko mata zancen suna son Hauwa, sabida kirkin Inna da yadda ta ke sakarwa kowanne kwastomanta fuska yasa take da jama’a, yawanci matafiya da masu shigowa Kano ta tashar tasu da direbobi dake cin abinci wajen ta. Ga ita Hauwar kam! Ai duk iya rashin kunyar mai zuwa cin abinci teburin su, bai ma isa ya tunkare ta da wata magana wadda ba ta sayen abinci ba, don babu fuska sam. Zata iya wuni bata yi koda murmushi ba. abinda Kawu Zakari yayi musu yayi mata illah a zuciya sosai ya rage mata walwala. “Hauwa-Kulun–Majadun” kenan.
Duk da cewa bayan sun dawo tashar Kano-line sun kama gida a unguwa uku shima mai daki biyu ne, amma sun fi ciniki sosai a tashar kuka, wani ko ba don Allah ba zai sayi abincin Inna a tashar kuka saboda daukar hankalin sa da makauniyar ‘yar nan tata tayi, wadda ke taya Innar ta aikin abincin da sayar da shi wa masu bukata da zarar ta dawo makaranta.
A wancan lokacin Hauwa ta gama isa aure har ta na neman wucewa don gab take da zana jarrabawar fita sakandire wato SSCE, ta samu damar da ‘yammata da yawa a zamanin basu samu ba, saboda da sun fara makarantar ake cire su ayi musu auren wuri, amma Inna bata bada fuskar da wani zai zo mata da zancen son Hauwa ba kwata-kwata, itama Hauwan ba fuska ko kadan. Don kullun Inna na gaya mata “da tun farko baki baiwa Jamilu fuskar zuwa inda kike da sunan neman aure ba, da har yanzu muna zaune gidan mu cikin sutturah, rufin asiri da kwanciyar hankali, da yanzu bamu zama masu sayar da abincin tasha ba”.
Sai Hauwa ta cuno baki gaba tace cikin kunkuni “to Inna Yaya jamilu ba dan uwana bane? Duk kin bi kin tsani Yaya Jamilu, kamar shine Baba Zakari, ina laifin sa? Halinsa daban na uban sa daban”.
Inna ta kama baki, ta bude shi ta mayar ta sake rufewa cikin al’ajabi, wai ta san soyayya, ta ce “hakane, dan uwan ki ne, na jini ma kuwa, amma wallahi ki sani ko shi ya saura da namiji a duniya, kema kika saura diya mace a duk fadin duniyar nan in dai ni SAFIYA ni na haife ki, kuma ina raye, to baza ku yi aure ba, ke ko ina gargarar mutuwa zan bar wasiyya ga duk wanda na samu cewa ba zuri’a ta babu ta Zakari”.
Hauwa aka kumburo baki sai ka ce zumbutu ta ce cikin wani sabon kunkunin “to ai ni dama ban sa aka ba, in dai maganar aure ne Inna, kawai na san ba’a raba hanta da jini, Yaya Jamilu dan uwana ne dana ke kauna tunda ba wani jini na da ya taba nuna min kauna bayan shi, kogobe na kara ganin sa In sha Allahu zan kula shi, zan tsugunna har kasa in gaida shi don bana manta alkhairin da yayi min, kuma bani da masoyi duk duniya bayan ke irin sa”.
Inna ta harzuka, yau akan Jamilu tana fade Hauwa na mayar mata? Tace “hantar taku sai in ba’a saka mata soson karfe da farin omo da sabulun dan jangabo ba, tuni in taji karta jinin zai rabu da ita koda zata kukkuje ta karce, wawuya kawai, mara kunyar wofi.
Ke na bi zumuncin naku da soyayyar taku da gudu na tattake su ba takalmi a kafata!”.
Hauwa sai ta kama dariya ta ce “tsakani da Allah Inna ban san ki da dorawa mutum laifin da ba nasa ba, duk da haka Inna Allah ya huci zuciyar ki, ni ba bakuwar zafi bace a kan Yaya Jamilu, ina ni ina wani aure alhalin ba ido?
Kawai ina son Yaya Jamilu a rai na, kasancewar duk cikin ‘ya’yan Baba Zakari wa ya taba nuna min zumunci da kauna ta fisabilillahi idan bashi ba? Kiyi tunani Inna, ki rage kin Yaya Jamilu, laifin Baban sa ne ya shafe shi, yasa kike ganin bakin sa. Shiyasa kome zai yi bazai burge ki ba, tunda Baba Zakari ya riga ya shafa masa, amma ko kadan bashi da laifi”.
Haushi ya ishi Inna, tayi mata shiru ta rabu da ita ta kaiwa banza ajiyarta, don ta dade da sanin in za’a kwana ana kushe Jamilu, to kuwa Hauwa bazata gaji da kwana a hanya tana kare shi ba.

Rayuwa ta mikawa Hauwa da Innar ta cikin rufin asirin Allah a tashar Kano-Line, inda suke gudanar da sana’ar su. Har gashi yau Hauwa sun fara zana jarrabawar WAEC wadda aka fi sani da SSCE a wannan watan da muke ciki.
Wadda da zarar sun kammala ta, Hauwa tayi sallama da makarantar kwalejin ilmi na musamman. Tunanin Hauwa kullum a yanzu shine, shin ko yaya rayuwa zata kasance mata bayan kammala sakandire?
Tunda dai Innarta ta ce bazata taba yi mata aure kamar kowacce mace ba wanda shi tafi bukata a wannan matakin? Ta sani ba don komai Inna take wannan kaffa-kaffan da ita ba, sai don kare mata martaba da mutuncin ta, har ma da tattalin kwanciyar hankalin ta, Inna tana bata kariya ne daga shiga matsalar gidan aure alhalin tana fama da wannan nakasar mai girma. Har ila yau, Inna tana guje mata shiga jami’a ne domin bata kariya daga fadawa ga soyayyar duk wani namiji da zata wahalar da ita a matsayin ta na karamar yarinya kuma mai raunin halitta na nakasar idanu, wadda har yau bata kai ga cika shekaru ashirin da haihuwa ba.
A wannan gabar da Inna ta san aure ne kadai ya ragewa Hauwa-Kulu, kuma ta fahimci tana ra’ayin yin sa da dan uwanta Jamilu ko bata furta ba, to bazata taba bari Hauwa ta kai kanta ga kowacce matsala ba.
Da dukkan karfin ta zata kare Hauwa-Kulun ta daga duk wata soyayyar da bazata yi mata amfani ba.
Inna tayi wa kanta alkawarin bazata bar Hauwa-Kulu taje jami’a ba, koda tana da ido kamar kowa, balle kuma BABU! Bazata lamunci shigar Hauwa jami’a bane don kada a gurbata mata tunani, ko kuma wani da yafi Jamilu iyawa ya hilace ta ya hure mata kunne, a karshe ya saka ta a matsalar da bazata iya fiddata ba.
Tana da yaqinin yadda Ubangiji Subhana ya nufe ta da yin ilmin sakandire ba tareda dabararta ba, ya kuma tsara mata yin rayuwa cikin nakasa ba tare da ta tagayyara ko ta tozarta a dalilin nakasar ba, (kamar yadda dan uwan mahaifinta ya so su wulakanta), sannan rashin mahaifinta tare da ita duka bai sa sun kasa numfashi da motsi cikin kudurar sa cikin duniya ba, ta tabbata shi din dai sarkin wannan kudura da iradar wato (Ubangiji Subhana) bai manta da it aba, shi zai cigaba da tsara mata sauran rayuwarta ta can gaba, kamar yadda ya tsara ta baya ta hanyar da bata taba tunani ko tsarawa kanta ba, tunda shi dai Ubangijin KOWA. In tace KOWA tana nufin KOWA, har da ita HAUWA-KULU!
Abin nufi anan, daga mai lafiya har mai nakasa duka nasa ne. shi ya halicci abunda yadda ya ga dama wato “Fa’alun lima Yureed ne”. Shi din, (Ubangijinmu), mai yawan hikima ne ga rayuwar duka bayinSa.
Bai kuma halicci wani a mai nakasa wani a mai cikar lafiya don baya son dayan ba, ko don ya kaskantar da shi cikin bil adama, ko don ya saka shi cikin bakin cikin rayuwa mara yankewa, kamar yadda ya dade da fada mata ne;
“Nakasa ba komai bace face jarrabawar Imani ga wasu daidaikun bayin Allah - (LIKITA SARHAM)”.

Idan haka ne kuwa zata tsaya tsayin daka wajen ganin cewa ta cinye wannan babbar jarrabawa da DR. SARHAM ya kwadaitar da ita muhimmancin cinyeta da TAUHIDI da IKHLASI (ta bakinsa), daga yau ta daina fito na fito da Innarta akan Yaya Jamilu, daga yau zata yi wa mahaifiyarta biyayya irin wadda wani da bai taba yi wa Uwarsa ba (koda ya san abun da take so din ba daidai bane), ita HAUWA_KULU zata yiwa Inna biyayya kan jiki kan karfi, akan duk abinda take so da ita da rayuwar ta, musamman hakura da rayuwar aure domin tserar da kwanciyar hankalin su.
Ta san Inna tana yi ne don amfanin ita Hauwan ba don nata amfanin ba.
Hauwa-Kulu ta cigaba da gayawa kanta daga yau ta cirewa ranta burin yin aure kamar kowacce mace mai lafiyar yinsa, ta barwa Allah ikonsa a kanta, ta daina yarda zuciyarta na kwadaita mata Yaya Jamilu, kai dama duk wani Da namiji bayan shi da zai biyo hanyarta, ta yarda da nakasarta babban gibi ce da zata hanata jin dadin rayuwa ta wani bangaren, ta kuma karbeta hannu bibbiyu, ta yarda nakasar ido bazata bata damar yin abinda ke kira “MARITAL LIFE” da “MOTHERHOOD” ba, wadanda sune ginshikin rayuwar kowacce diya mace, kuma su suka fi komai dadi da muhimmanci ga rayuwar kowanne dan adam.
Chapter 3 · 0% Book details