← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 29

Sashe 27

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta har ta shigo ta zauna akujerar dake fuskantar sa, suka gaisa, sai ya koma cikin kujera ya kishingida yayi shiru, har da dan juyawa ya kalli taga yaga ko Hauwa taji kunyar idonsa na abinda ya tarar tana yi (soyayya) tayi maza ta baro saurayin ta shigo gida ko a’ah? Amma ina! Ko keyarta bai gani ba, tana can suna sallama da Jamilu kamar bazasu rabu ba, Sarham ya mike dogayen kafafunsa a kasa. Bai iya kara cewa komai ba don al’ajabi da mamakin Hauwa. Can jimawa sai ga Hauwa ta shigo, tana tafe abunta kanta tsaye, babu ko lalube irin na makafi, tsabar ta gane hanyar dakinta, tasa kai zata wuce dakinta taci uban tuntube da kafafun Sarham, saura kadan ta kifa ta ci da baka. Ko sannu bai mata ba balle yayi ‘apologizing’. Cikin fushi tace. “Inna wa ya saka min kafa zai kayar da ni haka?” Inna ta yi mata shiru, kafin tace “daga ina kike?” tace “Yaya Jamilu ne ya kira ni soro”. Haba! Sai Inna ta balle da fada kamar ta rufe ta da duka, cewa take “da iznina kika fita zance gun Jamilu? Kece da zuwa zance Hauwa da wane idon zaki ga saurayin?” Saida Dr. Sarham yace “ya isa Inna, kinsan kinada matsalar zuciya, kada ki dinga bata ranki irin haka kan kananan abubuwa har ya tabo zuciyar ki”. Hauwa ta wuce dakin ta a sanyaye, bayan ta gaishe shi. Dr. Sarham yaki ko amsawa balle ya nuna ya san tana gaishe shi, har ta wuce tana mamakin me ta yi wa Dr. Sarham yau? Gashi dai yau bai kira sunanta da yake mararin kira na MAIJIDDAH cikin farin-ciki, yalwar fuska da far’ar nan tasa ba, bai kuma amsa gaisuwar ta da kulawa da (attention) kamar yadda ya saba ba. to me ta yiwa Likitan Inna? Ji yayi gabadaya yau ya kasa zama ya dade a gidan yadda ya saba, ya kuma kasa hira da Inna yadda suka saba, ita kadai take ta babatunta, daga karshe da Inna taga shirunsa yayi yawa sai ta dago ta dubeshi tace, “ko lafiya kake kuwa likita? Na ganka ba’a yadda na saba ganinka ba”. Sai kawai ya mike yana cewa “bari in karasa gida Inna, kaina ke min ciwo, yanata sarawa, idan na ji sauki zuwa gobe ko jibi in sha Allah zan shigo”. Inna tace “ni ai ban sani ba, gashi har nayi maka tuwon Acca kuwa, da miyar da kake so ta zogale” Sarham ya juya a lokacin yana saka takalman sa a bakin kofar falon, yace “ba komai Inna, some other time, zan ci”. Suka yi sallama dukkansu jiki babu kwari ya juya ya tafi. Ko sallama bai yiwa Hauwa ba. Yana tuki yana hada gumi kashirban, duk da sanyin AC din motar sa. Abun ya daure masa kai matuka. Ya kuma sakashi a damuwar da ya kasa sanin ma’anarta. Yana isa gida yaji ana murnar zuwan Sumayyah, wadda ta zo hutun karshen shekara da barkar haihuwar Waheedah. Kamar bai ga Sumayyah ba, bayan kuma har ido sun hada a falon, ya dauke kai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa bayan yace musu cikin jam’u “sannun ku da gida”. Mama ta bi shi da kallo, Sumayyah kuma ta ce. “Bhaiya lafiya kalau yake? Kaamr bai ganni ba Mama?” Mama ta ce “oho muku, kun fi kusa”. Surayyah ta ce “nafi tunanin wani ne ya bato masa rai daga waje, baki ga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ba?” Sumayyah sai ta mike ta bi bayan sa zuwa dakin nasa. Sallama tayi daga bakin kofa, sai da ya bata iznin shiga ta shiga dakin ta same shi zaune akan ‘study chair’ ya rafka uban tagumi, ta ce. “Bhaiya baka ganni bane ka wuce bamu ko gaisa ba?” Ya dago ya dubeta da jan ido, a lokacin taga idanuwansa sun kada, yace “a’ah Summy ce yau a gari? Saukar yaushe?” Tace tun dazu na sauka, ta gabana fa ka wuce, har ido mun hada, ka san mun yi hutu shine fa nace bari kawai in taho ganin Hauwa’u”. Ta zauna a kujerar ‘sofa’ kwaya daya dake dakin, ta ce “Bhaiya duk ka birkice, you are upset, anya lafiya kake kuwa? Na ganka ‘moody’ tunda ka shigo”. Yace “Sumayyah, bansan yadda zaki fassara abinda ya sani a damuwar ba idan na fada miki, ba wani abu bane serious I don’t know why I made it serious, abun ne ya bani mamaki, ya kuma bata min rai, wai Hauwar nan da kika sani ko ido bata da shi, amma ta iya tsayawa zance da saurayi a soro??? Ni ban taba ganin abinda ya bani mamaki ya rikitani irin wannan ganin dana yi ba”. Sumayyah tana sane tace “Hauwa wacce? Baby Hauwan mu?” Ya harareta, “ke bana son sakarcin banza. Hauwa ‘yar Inna mana, kanwata ta kofar Na’isa” Sumayyah ta wani ce “au ho! Ka ce min kawai Hauwar Inna, HAUWA-KULU ‘yar cikin BADALA!”. Sai ta hau tuntsira dariya tace “Bhaiya, yanzu ganin Hauwa da saurayi shine abinda ya birkita ka haka?” Sarham ya harareta yace “Sumayyah yaya ina miki magana ‘serious’ za kina dariyar rainin wayo, Hauwa fa, wadda ko ido bata da shi, ina zata kai wani namiji da sunan soyayya? Ganin ta nayi da wani cousin dinta suna zance fa, zance na saurayi da budurwa! Wai sunan sa Jamilu, dan kanin Babanta ne”. Ai kuwa Sumayyah ta kara tuntsirewa da dariya sai da tayi mai isarta, shi kuma ya shaka sosai, saida dariyar ta lafa mata ta ce. “Bhaiya makaho ba mutum bane? Ko kuwa makaho bai san SO da mai son sa ba? Don tana makauniya shikenan sai akace bazata yi aure ko soyayya ta ji dadin rayuwar ta kamar kowanne dan adam ba? Ko in bata saurari masu son ta ba kai din auren ta zaka yi? Yau nake ganin ikon Allah, yau ina ganin abinda ya gagari Kakata Kulu, kai ka dafe dahir har da ‘yar ka tubarkallah, shine ita zaka yi mata fatan ta tsufa a dakin uwar ta, alhalin kai ba son ta kake yi ba, wannan fa shi ake kira karfin hali barawo da sallama ko in ce, Bhaiya na, da tsabar son kai tsagwaro. Wani hali da ban san shi da shi ba. Ni wallahi gani nake ma babu wanda ya dace da ya aureta kamar dan uwan nata, tunda jinin su daya, ya san darajar ta, zai yi hakuri da nakasar ta, ya riketa da daraja a gidan aure, don kai kam Bhaiya, baka da alqiblah. Ayi magana cibi ya zama kari!”. Ta sake tuntsirewa da dariya ta ce “sai amara kirazan biki, mu ne manyan kawayen amarya Hauwa’u, a bikin ta da Yayanmu Jamilu”. Sumayyah har da dan gudu-gudunta ta bar dakin, tana cigaba da tillika dariyar shegantaka. Don ta san ta gama kunna shi in ta kara minti uku a gabansa zai iya losing control kai mata duka. Don tana ganin yadda yake girma idanunsa tunda ta soma shegantakarta. Maganganun ta dinnan, suka taru suka zamewa Dr. Sarham “a warm food for thought!” A tsayin wannan daren bakidayansa kona rabin away a kasa runtsawa. Sarham sai faman juyi yake a kan gadonsa, daga wannan gefen zuwa wancan, yana tauna maganganun Sumayyah a kwakwalwarsa, yana kuma fassarasu a zuciyarsa cikinma’auni na hankali da tunaninsa. Daren da yazo masa da tarin ‘alterations’ koko ‘revolutions’ wadanda a can baya bai taba hango yiwuwar makamantansu ba. Ko na minti daya ya kasa rintsawa. Idan ya tuna maganganun Sumayyah. A ganin sa Sumayyah maganganu ta gasa masa masu zafi ta cikin ruwan sanyi, koko yace jirwaye tayi masa mai kama da wanka, don dama tana kullace da shi akan abinda yayi mata, don kawai ta tambaye shi ko son Hauwa yake yi shekarun baya, bazata manta ba yayi mata wulakancin da bata zata ba, kiris ya rage ya doketa. A nata bangaren Sumayyah, ta dade tana kiwon mu’amalar sa da su Hauwa ta rasa alkiblarsa, musamman in ta tuna abinda yayi mata daga ta tambaye shi ko son Hauwa yake? Ta tuna a ranar dukanta ne kawai bai yi ba, shine abinda take nufi da “ayi magana cibi ya zama kari”. Da gasken gaske ya kasa barci a daren, sai faman tauna maganganun Sumayyah wadanda ya kira jirwaye mai kama da wanka. Washegari ya samu kansa da kasa zuwa gidan Inna, saboda har zuwa lokacin ransa a bace yake, haka a sauran kwanaki ukun da suka biyo baya ko hanyar kofar Na’isa bai kalla ba, yana like wajen su Waheedah, kamar ya maidasu ciki, don a can yake samun sanyin ran sa, daga zafafan maganganun Sumayyah da haushin Hauwa (a ganin sa bakaken maganganu ne Summy ta gasa masa son ran ta), da suka dade suna dafa shi kamar dafaffiyar masara, kuma ya kasa cewa Sumayyah komai a kai again bayan kuma ita kadai ce zai iya zancennan da ita. Madinah ta samu lokacin sa sosai a wannan satin, don yanzu kullum yana wuni tare da su baya zirga-zirgar gidansu Inna. Inna na talgen tuwo a yammacin yau da Sarham ya kwashe kwanaki bakwai bai zo gidan su ba, sai ya fado mata a rai, ta dubi Hauwa dake wankin sittirun ta a bakin famfo tace. “Kuluwa!” Hauwa ta tsuke baki ta kuma tsuke fuska bata amsa ba, ai ta san in ta ce mata Kuluwa bazata amsa ba, sai ta ce “ni kuwa kin lura da abinda na lura da shi?” Hauwa tace “me?” “Likita Sarhamu, yau kwana bakwai bai zo gidannan ba, tun ranar da ya zo yace min kansa na ciwo, yanzu haka jikin ne ya matsa masa tunda har kika ga yayi wannan dadewar bai zo ba”. Hauwa ta yi shiru bata ce komai ba, ta cigaba da wankin ta, ashe ba ita kadai ta lura da rashin zuwan nasa ba. Inna ta sake cewa. “kin ga da ace na san gidan su sai in je in duba shi”. A nan ne Hauwa ta bata amsa, “kai su Inna akwai wuce gona da iri”. “Ba wuce gona da iri bane Hauwa-Kulu, baki ji fadar bahaushe ba? Yace KA GAIDA MAI GAISHEKA KO DA BAZAI AMSA BA!” Wannnan magana ta karshe da Inna ta yi, ta yi ta ne a kunnen dan halak
Chapter 27 · 0% Book details