← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 29

Sashe 16

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE ARABIAN BRIDE M adinah na gidan kakannin ta bayan saukarsu a Kano, a daren ranar za’a kawo ta wajen Mama, an gyara dakin Sumayyah da kyau wato inda za’a sauke ta da ‘yan uwanta. Gidan ya dauki kamshin turaren wuta dan Maiduguri ko ta ina mai dadin kamshi, Mama da kawayen ta su Barr. Hannatu Mahdi da ’yan uwanta suka shirya karbar amarya da danginta. Har falon Mama aka shigar da Madinah-Munawwarah cikin lullubi, kafin a yi addu’a ta musamman ‘yan rakiyar amarya da ‘yan karbar amarya duk suka watse, gidan ya rage sai mutanen gidan kadai. Rana ta farko dasu Mama suka ga fuskar Madinan Sarham. So beautiful da ita, karshen gayu karshen class, Masha Allah. Mama ta ce a ranta dole kam Sarhamunta ya kamu ya tsunduma iya wuya, Madinah ko daga cikin lullubi kafin a ganta a zahiri an san matar manya ce kuma ‘yar manya ce. Tayi fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a mai alkbarka. Ya kade fitina, ya basu ikon sauke amanarta da aka damka musu. Yau Madinah ta samu kanta a gidan surukan ta wato iyayen Sarham suna ta haba-haba da ita. Sumayyah da Surayyah ma ba’a bar su a baya ba wajen kula da bakuwar tasu, Surayyah kuwa duk da ‘yar tsamar dake tsakanin ta da Sarham sai da ta kasa shiru, da ya shigo gaida Mama bayan ya dawo gidan da daddare sosai tace dashi. “Yaya Doctor, wallahi ka iya zabo mata, class iya class malam, kyau iya kyau, dubi mata kamar hurul- eeni, kamar ita tayi kanta don kyau da gayu. Wata mummunar harara Sarham ya zabga mata yace “ki fita idona in rufe, ki bar shiga harkata, na rantse Mama ki raba ni da Surayyah”. Sannan ya gaida Mama da gajiyar hidimar jama’a, wadda keta dariyar masifarsa, Mama tace “ban taba ji ko ganin ango yana masifa ba, duk wani ango far’a yake yi da farin ciki banda kai, tashi ka shiga dakin Sumayyah Madinah din tana can”, cikin jin nauyin Mama irin wanda bai taba ji ba a rayuwarsa yace, “Mama ki barta, sai da safe in Allah ya kaimu zamu gaisa in sha Allah, a barta ta huta, na san ta gaji, gata bata jure hayaniya”. Nan kuwa kunyar idon Mama ya hana shi zuwa yiwa Madinah barka da sauka cikin rayuwarsa. Sai da ya koma dakin sa yayi shirin kwanciya sannan ya kirata a waya, Madinah ta fito wanka kenan tana saka kayan barci zata kwanta kiran sa ya shigo mata, sai da ta ja aji, don taji haushin kiran data yi masa bai dag aba kuma bai biyo bayan kiran ba, kafin ta dauka da kyakkyawar sallama a bakin ta, maimakon ta ce tayi fushi, saboda bai zo inda take ba tun saukar ta a Kano, ko irin kananan korafin nan na amare da ke cikin lokacin da ake mararinsu, ina! Madinah nata salon daban ne, da wuya kaga bacin ranta akan abu, komai tana kokarin maida shi ba komai ba a rayuwarta (banda kishin Sarham), don ko shi Sarham zai rantse bai san me yake bata ran Madinah ba, sai ta karya murya cikin rangwadarta da zakin muryarta tace, “daga jin muryar ka mura kake, ina fatan angon Munawwarah yaci abincin dare?” Sarham yayi wata wawuyar ajiyar zuciya, tuni ya manta da kishin da yaci alwashin gasata akansa da zarar ta shigo gidansa, wato fushin aurenta da AVM Alkali, ya samu kansa da cewa “kayya! Anyway, kin zo lafiya Madinahtul-Munawwarah, ya gajiya ya aka ji da zafin garin mu?” Madinah tace “garin ku kai kadai? Ai ba’a canzawa tuwo suna. Zafi kuwa ai yana Saudi Arabia”, yace “kiyi min alfarma mu Arabian Bride, na san ke dinnan ma’abociyar tsinkaye, fahimta, da yi min uzuri ce, bazan iya shiga dakin Sumayyah inda kike ba kusa da dakin mahaifiyata ne, ba zan iya tsallake dakin Mama a gidannan in dinga zuwa inda kike ba, amma already nayi kokari nayi mana booking na komawa Jidda, don ni garin Kano ya fita kaina, zamu tashi rana ita yau in sha Allah muje mu ci duniyar mu da tsinke. Na yanke shawarar karbar aikin nan na Saudi-German”. Farin ciki mai yawa ya cika fuskar Madinah da zuciyarta, don dama tana cikin tunanin yadda zata iya rayuwa a garin Kano, ta shiga damuwa akan yadda zata iya rayuwa a Nigeria ma in general, tana dai daurewa ne albarkacin soyayya da yadda kowa nata ke lallashin ta, yayyenta kuma suke gaya mata aure babu inda baya kai mutum har bukka a jeji, amma hakika tafi son cigaba da rayuwa a Jeddah. A can aka haifeta acan ta rayu, acan ta girma. Abinda ta sani ta kuma yarda da shi kawai shine; ko a cikin ruga zata iya rayuwa in dai da Sarham Abbas ne, kuma in dai zasu kasance tare karkashin alfarmar aure da ni’imarsa itada shi har karshen rayuwar su. Sarham ya katse mata tunani, “kin amince ko?” Da sauri Madinah tace “haba-haba ai nima zan fi son hakan, da kunya kam mu kebe ko na minti biyu ne alhalin Mama da Abba suna cikin gidan, Allah ya kaimu lafiya, ni da ka kara mana wani satin ma a kan dayan ya zama munyi biyu tareda su kafin mu koma”. Yace “no, zamu tafi rana ita yau in sha Allah bana son zaman garin ne”. Ya tambayi Madinah ko me take yi yanzu? Ta ce ta yi wanka ne zata kwanta, ta gaji sosai, tace tun saukarsu a Kano bata huta ba. Sarham ya ce, “ai kuwa baki ga ta barci ba, kamar yadda nima ban ganshi ba. On this special day, ki tashi ki dauro alwallah ki yi sallah raka’a biyu nima zan yi yanzu, mu godewa Allah da ya cika mana burin mu da cikar alkawuran da muka yi wa juna yau shekaru goma! Kada ki manta a cikin sujjadar ki ta karshe ki roka mana ‘long life, prosperity, blessed children, unending love, and infinite peace. Madinah ina fatan ki zamo min ‘shelter’ kamar yadda birnin Madinah ya zamowa Annabin mu Shelter, refuge, security, safety and peace!”. Madinah ta lumshe idanunta cikin farin cikin da bazai misaltu ba, tace “kaima ina rokon ka roka min aljannah, don Hajjah Ramlah ta gaya min aljannah ta yanzu ta tashi daga dugadugan su ta dawo bisa dugadugan ka. Ka roka min ‘ya’ya masu yawa tare da kai kuma masu albarka, ka roka min Allah ya mallakamin zuciyar Sarham dina, nikadai raina bakidayan ta, don itace kadai ‘weakness’ dina a duniya (zuciyarsa)”. Finally, daga yau dai, sunansu ya tashi da ‘honorifics’ tunda ya koma Mr&Mrs. Dr. Shanono. Bayan tarihin fafutukar soyayyar shekaru goma!!! **** ***** **** A kwanaki bakwai din da Madinah tayi a gidansu Sarham, ta saba da kowa, kuma ta samu karbuwa ba laifi a wurin iyayen sa musamman Abba Prof. da yake ganin girman Kakan ta mai rasuwa Alkalin Alkalai, duk da ba wai sanayya ce a tsakanin su ba, amma yayi masa farin sani a matsayin daya daga cikin iyayen Kano. Ta fannin Mama kuma, ta zauna ne daga gefe tana laqantar Madinah a ma’auni na adalci da son sanin hakikanin halayen ta, inda a dan zaman su tare ta fahimci Madinah wayayyace, Madinah mai ilmi ce, bata da matsala sai ta rashin kawaici a kan Sarham, in bata gan shi ba sai ta ishi kannen sa da tambayar ina yake, wanda ke nuna zata yi kishi akan sa sosai, idan ya fita bazata nutsu ba sai ta ji shigowar sa gidan, tana da bala’in jan aji amma akan Sarham babu ajin ko kadan, don bata iya boye son da take masa a gaban iyayen sa da kannen sa. Gata da halaye na kowa tasa ta fishshe shi, wato halayen nasara, kai bazaka ce girman kasar larabawa bace, amma kuma duk da haka tana girmama su, musamman su iyayen sa, ta fahimci Madinah ta san abinda take yi yadda ya kamata, tunda duk rashin kawaicinta data fahimta, a duka kwanakin nan bakwai data yi tare dasu, bata tsallake su ta kebe da Sarham ba, ko ta bi shi inda dakinsa yake, ita da shi sai ko a waya, ko in ya shigo ya taddasu duka a falo, sai ya zauna ayi hirar tare da shi, amma baya sakewa musamman in Mama na wajen, tana kallon Madinah na kashe shi da murmushi. Shi da kan sa Sarham ya fahimci wani abu, wato tun bayan zuwan Madinah, mu’amalar sa da Sumayyah ta ja baya, Sumayyah ta daina shiga sha’anin sa sam, ko wuri ya shigo tana dariya sai ta daina, ta yi fuska. Ta daina kai masa abinci ko gyaran dakin sa wanda aikinta ne. A’ah, tun baya damuwa har ya fara tunanin laifin me yayi mata don wannan ba halin ta bane, me yasa ta daina ajiye masa abinci ko kiransa yazo ya ci, da gyara masa daki alhalin ta san ba wai Madinah ta tare bane, da zata cigaba da yin wadannan hidimomin da tazo ta tarar tana yi masa. Yau ya fita can karshen layin su yana wata irin romantic waya da Madinah, don hakurinsa kusan ya fara karewa da takunkumin da ya sanya musu, haka suke yi yanzu kullum da yamma in jama’ar gidan basa nan ko suna wasu sabgogin a kitchen, ko can dare in kowa ya kwanta, sai ga Sumayyah ta karyo kwana tana tafe cikin nutsuwa, ta zo har inda yake ta gifta shi bata ce masa ko sannu ba, har ta zarta shi kadan ya kashe wayar ya saka a aljihu, ya ce, “Sumayyah!”. Sumayyah ta dan dakata amma bata juyo ba, ta daure fuska sosai, ya ce “ko ba da Sumayyah nake magana bane?” Ta dawo ta tsaya a gaban sa tana tura baki gaba, ya ce “kin gama hada kayan naki?” Ta ce “hada kaya kuma? Ina zani?” yace “eh, Abba bai gaya miki da ke zamu tafi Jeddah ba, zaki zauna a gida na ki fara MBBS? Tukunnama wai me nayi miki kike gaba da ni haka? What’s wrong with you?” Sumayyah mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta soma hawaye na babu gaira babu dalili, tace “wallahi in dai a gidan ku zan zauna to na fasa karatun a can, ni
Chapter 16 · 0% Book details