← Book details Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Hauwa Kulu Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kulawa da darajjawa ne a gare shi. Ya Allah! Da me zata biya wannan bawan nasa banda addu’ar alkhairi mara yankewa gareshi, da iyayen da suka kawo shi duniya da zuri’ar sa??? Sukayi sallama ya tafi, ta koma gida tana labartawa Hauwa abinda ya faru a gidan Malam Isa da zauren su. Hauwa tafi Inna fusata, tace zata je ta tadda Talatu Maikosai ta gaya mata ba abinda zai kawo su gidan ta koda zasu koma kwana a kan kwalbati in sha Allahu. Inna ta hana ta tace “tura mata aniyarta mutuncin Malam Isan zaki duba, na gaya miki ashe dabbobina duka suna garken sa yana kiwata mini har yau”. Wannan ne ya dan sanyaya ran Hauwa ta daina jin haushin Malam Isa amma sosai ta shaka da Maikosai. **** ***** ***** RACE COURSE, KANO A wajen kallon Polo na Dawakai wato a filin sukuwa (Race Course) dake unguwar Nassarawa, Salele ya ga Jamil Zakari a matsayin wanda ya lashe kofin gasar dawakai (sukuwa) wanda akayi a ranar, dama dai Jamilu kwararren dan Polo ne, sun dade suna haduwa da Salele a wurare mabanbanta na tseren Dawakai, suna gaisawa, don ya san shi tun a jinyar da Hauwa tayi, sanda ya kadeta da mota. Yau da Jamil Zakari ya lashe kofi Salele ya shiga sahun samari masu kutsawa suna gaisawa da Jamil Zakari Dan Agundi, Salele yana cikin samari ‘yan kallo masu cike da fata da burin watarana su zama manyan ‘yan Polo kamar Jamil Zakari Dan Agundi. An fara watsewa kenan Jamilu ya shiga farar motar sa kirar (kia picanto) zai tafi sai ya hango Salele yana ‘waiving’ dinsa daga nesa wato yana ta dago masa hannu, har ya kunna motar ya dakata har Salele ya iso da gudu yana haki yana dariya. Jamilu ya fiddo gudar naira dari ya baiwa Salele, wadda a yanzu zata yi kimar kamar ace naira dubu daya. Salele don murna bai san lokacin da ya hau barin zance ba. “Yaushe zaka zo gidan su Innar Hauwa ne? Sun dawo bada jimawa ba, sun gine gidan su ya koma sabo dal, sun tare tuntuni, jiya ma Innar Hauwa ta shiga gun Innata sun gaisa har Innata ta zo gidan ta yiwa Hauwa kitso”. Jamilu yayi sakare! Yana sauraron Salele, kafin ya ji zuciyar sa ta harba, tsohon mikin son Hauwa-Kulu da yake kwana yake tashi da shi ya motsa kansa a kasan ransa, bai san sanda yace da Salele ya shigo gaban motarsa su je ba. Salele ya kame a gaban mota suka dauki hanyar Kofar Na’isa.
Chapter 25 · 0% Book details