Sashe 23
Hauwa Kulu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kissimawa ba, ina kissima yadda fuskar zata yi dai-dai da irin kyawawan kalaman ka ne, koyaushe kana magana wadda ta dace da muhallin ta, kana da tunani na ilmi (with abstract reasoning)”. Sarham wani irin kallon bakinta dake motsi a hankali yake yi, da murmushi yace ikon Allah. Ya akayi ni ban sani ba? Kamar wadanne iri ne kalamai na masu kunshe da abstract reasoning? Irin dai wadanda kake yawan yi cikin surutun ku kai da Inna, wani lokacin ina saurara, nafi zama mai sauraro a hirar mutane fiye da mai contributing, ta nan nake fahimtar yanayin zancen kowa, na fahimci maganganun naka duka a muhallin su kake yin su, kuma a takaice, amma cike da tarin maanoni da alfanu, sannan duk wani cukurkudadden alamari ka san ta yadda zaka bi ka warwareshi cikin hikima irin taka”. Sarham ya zura takalman sa, ya mike idonsa akan Hauwa, yana sakin dariyar da bai shirya zuwanta ba, ya lura yau in zasu kwana a haka, bazai gaji da sauraron dadadan furucin Maijidda gareshi ba, ya ce SAI WATARANA Maijidda sai watarana, ina rokon ki, duk runtsi kada ki bar zuwa makaranta, koda kin rasa dan jagora! Ina nufin against all odds, koda da rarrafe ne ki jure ki nemi ilmi, duk da nasan ba zai zamo abu mai sauki gareki ba, dama duk masu lalura irin taki, amma ki sani Allah ne gatan ki sai kuma shi (ilmin)”. Idan na rasa dan jagora da wanne idon zani makarantar? Misali, idan Salele ya daina kaini ko ya mutu?” Hauwa bata san sanda ta jefe shi da wannan tambayar ba, a lokacin har ya saka kai zai bar tsakar gidan su. Amma jin yadda muryarta ke rawa da karkarwa kamar kuka zai kwace mata yayin fadar hakan, a lokacin da take fadin hakan ma tuni hawaye ya ciko idonta, sai Sarham ya juyo yana kallon Hauwa da wani irin expression a idanunsa, cikin wata irin karaya da kewa, hasken farin wata ya haske masa fararen idanun ta suna jujjuyawa a cikin lalurar rashin gani. Ya kamata ya bata amsar wannan tambayar ta yadda zata dade tana tuna ta, wato tayi ta shawagi a kwakwalwarta, har ta zame mata tsani a rayuwa. Ta hanyar sakawa ran ki cewa zaki iya komai da mai lafiyar ido zai iya, hankali ke gani ido gululu ne, ki tuna kullum da karin maganar da Bahaushe ke cewa “ba nakasashshe sai kasashshe”. Bature kuma yace “theres ability in disability!”. Sannan kullum kisa a ranki “nakasa ba komai bace face wata kankanuwar jarrabawar imani ga wasu kebabbun bayin Allah na kwarai daga Azza wa Jallah”.