Sashe 21
Hauwa Kulu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya isa gidan ana kiran sallahr Isha, Inna na alwalah Hauwa na cin tuwo. Yayi sallama Inna ta amsa Kulu ko kamar yadda yayi tsammani a cikin cikinta ta amsa masa sannan bacin ran da yake zargin gani ya dan bayyana kansa a kan fuskar ta. Sai Sarham ya lallaba ya dauke kwanon tuwon daga gaban ta ba tare da yayi magana ba, ta shafa gabanta don kara kai loma sai taji wayam, babu kwanon, amma bai sani ba kamshin turaren sa da ya nashi hancinta (Oud Abyad) ya tabbatar mata shine a wurin ya dauke kwanon. Baya jan ta da wasa amma yau da yake sallama ya zo, shiyasa ya ke son ko yaya ta kula shi. Dan murmushi tayi, wani basakkwacen murmushi ta share shi, ta janye hannu ta koma gefe, ai kuma ta mike don wanko hannu, tana tafe kanta tsaye zuwa famfo kamar ba mara ido ba, ba tare da ta nemi Inna tayi mata jagora ba. sai data kai bakin famfon ta kunna sannan tace ka hutar ni dauke kwanon, dama na koshi ai. Mamaki yasa Sarham rufe baki yana dariya yace. Inna ashe idon mu ya bude! Inna tace fata nagari lamiri, me yasa aka ce muyi fatan alkhairi akan komai? Ai don bamu san tasirin bakunan mu ba, mai yuwuwa Allah ya biye bakin ka watarana Likita”. Sarham ya ce haka yake Inna, amma shi ya san da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, sai dai duk wani mumini yayi amanna da cewa ba abinda ya gagari Allah, suma likitocin lalube suke yi a cikin duhu. Sanin gaibu sai Allah. Ya russuna har kasa ya gaida Inna, ta kawo masa darduma ta shimfida, sai ya ce, “tunda sallah za kuyi, muyi jami gaba daya kawai, ban taba jan ku sallah ba Inna. Maijidda dauro alwallah. Daga inda take tsaye a jikin famfo tayi dan sakale! Bata ce toh ko aah ba, don jiya ta fara ganin jinin alada a rayuwar ta, itama bata sani ba, Inna ce ta gani a jikin zanin ta ta gaya mata, ta kuma taimaka mata wajen kunzugu, ta koya mata yadda zata dinga killace kanta da tsaftataccen tsumma, dankwalin sabuwar atamfarta mai tsafta ta dauko ta tsaga shi gida biyar ta koya mata amfani da shi, ta kuma gaya mata baa sallah da komai na ibada sai an samu tsarki, koda yake duk ta sani a makaranta tun kafin ta fara din Duk da cewa ta tsorata da Inna ta gaya mata ta fara alada, ta kuma tabbatar mata yanzu ta girma dole ta kula da kanta da tsare mutuncin ta daga wannan lokacin, da kuma koyon yadda zata ke muamala da maza daga yanzu. Inna ta zaunar da ita ta ja kunnen ta sosai, ta gaya mata yanzu da girman nan ya hau kan ta ko hannun ta namiji ya kama cikin shege ne zai shiga jikin ta kuma haramun ne. ta tsoratar da ita sosai akan maza ko yaya take dasu. Yinin jiya zungur laccar da Inna ta wuni tana yi mata kenan. Sarham ya gaji da jiran Kulu ta zo su tada sallah, don tunda ta shige daki ta ki fitowa ya dauka hijabi zata shiga ta dauko amma shiru kake ji. Sai Inna ce ta sadda kai ta ce, ja mu sallahr ka ji! Kuluwa girma ya zo!. Sarham cikin rashin fahimta ya tambayeta girma kamar yaya?. Duk surutun Inna da yadda ta ke sakewa da Sarham wannan karon kasa fada masa Hauwa ta fara alada tayi, ta hau inda-inda, har ya gaji ya tada sallah, amma daga karshe a matsayin sa na likita malamin kiwon lafiya sai ya dago su. Abu daya zai hana mace sallah uwarta ta bi bayan ta shine idan tana fashin sallah. Ikon Allah, har nawa Hauwa-Kulu take? Maiyuwuwa kuma irin jikin ta kenan. Irin su kuma sune masu haihuwar wurwuri. Koda yake kanwarsa Sumayyah ma haka ta fara da wuri, kuma shi ta fara gayawa tana kuka, don ta kasa gayawa Mama da Surayyah, tana ganin wani mugun abu ne ya faru da ita, ba zai manta ba shi ya fara saiwa Sumayya always pad ko Mama sai da Sumayya tayi wajen sau uku kafin ta sani. Bayan sun idar da sallah shi da Inna, kasa gaya mata tafiyar sa Saudi yayi, saboda sabo, da wata irin kewar su da tazo ta rufe shi, Inna kuwa tana ta hidimar hada masa tuwon masara miyar kuka da manshanu, ga yajin daddawa a gefe, ta kawo ta aje masa da ruwan randar ta mai sanyin dadi. Taga yayi shiru ya kasa cin abincin da doki kamar yadda ya saba, cikin kulawa Inna ta ce, likita ya dai? Jikin ko garin?” Ya nisa, kafin yayi kundumbala ya ce babu ko daya. Inna sallama na zo muku, zan bar kasar nan!. Ba Inna kadai ba hatta Kulu da ke daki fitowa tayi da sauri daga uwar dakin data je ta boye jin abinda Dr. Sarham yake cewa. Tafiya ta same ni zuwa kasa mai tsarki, zan tafi karo karatu na akalla shekaru uku, Inna ina fatan zaki cigaba da tayani kula da karatun Maijidda har ta kammala, alkawari ne na dauka tsakanina da Ubangiji sai na ga ta kammala sakandire hankali na zai kwanta, to amma ga yadda Allah ya tsara min. Ina fatan kafin in dawo Inna zaki tsaya akan karatun ta na sakandire har Allah ya cika min wannan burin nawa”. Inna gaba dayan jikin ta ya mutu. Bata san ta saba da Sarham ba sai yau da yake maganar barin kasar mu baki daya, bata san dimbin alkhairin sa mai yawa bane a gare su, sai yau da zai bar su. Kokari take ta mai da hawayen da suka kawo mata cafka, don kada ta kara karya masa guiwa da tata karayar, don hatta yadda yake maganar kadai zaka san ya fi ta shiga damuwa da kewa, ya karaya. Hauwa dai ba tace komai ba, amma a cikin ranta wani irin ‘dakace’ take yi, cewa take inamainama! Inama na ga fuskar sa yau, inama nayi masa kallon karshe yau kafin ya barmu, wanda zai sa kullum nake tuna fuskar sa, in yi ta masa addua!. Don duk tsayin lokacin nan da suka kasance da Sarham a cikin rayuwar su kusan koda yaushe cikin wannan fatan take, ba don komai Hauwa take son ganin fuskar Sarham a rayuwar ta ba, sai don ta yi quenching curiousity dinta a kan kamannin sa ta kuma yi matching din fuskar da kyawawan kalaman bakin sa na kullum a kan su, wadanda a kullu yaumin masu maana ne wadanda suke kara mata son ganin kamannin halittar sa, shi Sarham mutum ne mai fasahar zance na ilmi, da girmamawa ga mutane, ba tare da laakari da matsayi ko ajin rayuwar su ko nasa matsayin ba, kalaman Sarham har kullum masu tausasawa dan adam ne, a duk halin da yake ciki ya san kalaman da ya dace yayi masa, wato koyaushe kalaman sa na tafiya ne da irin yanayin da ya tarar da kai a ciki. Alal misali, in ya lura kana cikin farin ciki zai taya ka da zolaya da tsokana yakara maka farin ciki, haka in bakin ciki kake shima zai taya ka har a murya da zuciyarsa, daga yanayin kalaman sa kadai zaka tabbatar (he feels what you are feeling) kuma yana tayaka. Sarham ta kwana da sanin cewa shi din, wani kyautar Ubangiji ne koko tace (dauki) da Ubangiji ya kawo cikin rayuwar su, ya hada su da shi, a lokacin da suke tsananin bukatar tsayawar namiji a rayuwar su. Ubangiji ya nufe shida shigowa rayuwar su ne don ya zame musu fitila mai haske kuma sanyi daga kuncin da suka samu kan su rana daya na nakasar ta, wanda in ba hadin Allah ba, ba abinda zai sa ya shigo cikin rayuwar su ya tsaya kamar Yayanta na jini. Domin ta kowacce fuska babu ta inda rayuwar su ta zo daya. Yau da yake cewa zai tafi, har tsayin shekaru uku sai taji cewa lallai zasu yi rashin da baa mayarwa, zasu yi kewar da bata karewa, don shekara uku ba kwana uku bace, abu ce ta mai yawan rai. Inna ta cigaba da hana kanta kuka a gaban Sarham, tana gayawa kanta saboda su ba zai fasa gina rayuwar sa ba. Yo fisabilillah don su aka halicce shi? Daga taimako? Kuma dai duk wani abinda ya dace don kyautata rayuwar mutum Sarham ya gama yi musu shi, tunda yayi wa Hauwa sanadin cigaba da karatu bayan iftilain da ya same ta. Sun koyi abubuwa da dama daga gare shi, irin su magungunan da ya dace da taimakon farko na cikin gida (first aid), home hygiene, sanitation duk karshen wata, cin balance diet a gargajiyance da irin abincin da suke da shi, sun koyi abubuwa masu yawan gaske da suka shafi kiwon lafiya a bakin sa a dalilin zamansu tareda shi. Haka kuma ko yau bai yi shiru ba sai da ya ce da Inna ga kudi zai bar musu ta tabbata ta sayawa Hauwa auduga mai yawa a chemist, bai yarda da kunzugun tsumma ba, yace ita ba ido ba, don haka ba iya kula zata yi da kanta ba kada yaje ta dauki kwayoyin cuta. Kunya duk ta kama Inna. Kulu kuwa da ace a da ne Dr. Sarham ya fadi haka da tuni ta hau shan kunu da fushi da bacin rai na cewa an yi mata gorin ido, watakila harda su kuka, amma da yake yau itama zuciyarta ta tabu da zancen tafiyar tasa ba tace ko uffan ba, saima kunya da taji sosai itama kamar Innar. Inna har sai da ta kasa rike hawayen nata a wannan karon, da ya ajiye mata kudi masu dama a gabanta, tace. Dan nan shekara uku ba kwana uku ba. Allah yasa ka same ni a raye, rayuwar nan da bata da tabbas. Allah yasa muna da rabon sake ganawa, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi. Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ilmin da zaka je nema, ya kuma baka dukkanin abinda kake nema a cikin samunsa, ya huwwace maka saukin sa, ya kuma baka albarkar sa. Amin- amin Inna, nagode kwarai da gaske da wannan addua mai