Sashe 18
Hauwa Kulu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A cikin mota suna kan hanyar zuwa gadon kaya, Sumayyah ta kasa shiru, abubuwa da yawa sun tsaya mata a rai game da muamalar Sarham da gidan su Hauwa, babu tudu me ya kawo gangare? Ta saci kallon Bhaiya, wanda ke tukinsa hankalin sa a kwance, ta ce,
Bhaiya, ina da tambaya, if you permit, may I ask? Tsakani da Allah son Hauwa kake yi?
Wani irin wawan burki da Sarham ya ci da motar, saida dukkan su suka wuntsulo gaba, suka kusa ci da baka a gaban motar. Saura kadan ya kwadawa Sumayyah mari, domin ji yayi kamar ta yi sabo, amma ya daure ya rike hannun sa yana cewa ba zai taba dukan mace a rayuwar sa ba in sha Allah, balle Sumayyah, da yafi so duk gidan su, kowacce irin katobara zata yi masa kuwa, ba shiri Sarham yayi parking motar a gefen titi.
Cikin matsanancin mamaki da fushin da yake so ya danne yake kallon kanwarsa, yace da Sumayyah ke kuwa me ya kaiki wannan tunanin mai kama da sabo? Sumayya sakewa ta dake har ta kai da ki raina ni irin haka?
A duniya mutum bazai yi wata kyakkyawar alakar mutunci da zumunci da mutanen da ya san darajar su, suma suka san tasa ba, kuma yayi sanadin janyo musu lalurar da basu da yadda zasu yi da ita sabida raunin su, da rashin namiji tsayayye a cikin rayuwar su, mutum bazai yi tunanin taimaka musu da faranta musu domin Allah ba sai don wannan shirmen?
Sumayyah idon ta ya raina fata da ganin bacin ran Sarham karara, ta ce kayi hakuri Bhaiya, ba raini bane hasashe na ne dana kasa dannewa a rai na, na yi laakari ne da maganar Hausawa da suka ce in kaga kare yana sunsunar takalmi… dauka zai yi.”.
Da sauri Sarham yace amma kuwa Allah wadaran wannan bahaushen da a wajen sa babu kowacce alaqa ta mutunci da taimako a tsakanin alumma sai da manufa, babu kyautatawa mara galihu sai a dalilin wani shirmen banza wai SO!”. Yana fadi yana tada motar, da gaske a gareshi so shirme ne, don baiga ranar da so yayi masa ba.
Yana tukin yana maida numfashi, fuskar MADINAH ATTAHIRU na gilmawa a idanun sa. Itace silar bacin ran sa ba maganar Sumayyah ba, ita tayi fami ne akan gyambon da aka samu yayi healing ba tare da ta sani ba.
Sumayyah jikin ta har rawa yake ganin yadda jikinsa har tsuma yake, ta ce don Allah don Annabi kayi hakuri Bhaiya, ni tambaya kawai nayi bansan ranka zai baci haka ba, kayi hakuri bazan sake shiga abinda ba ruwa na ba.
Sai kawai ya fizgi motar ba tare da ya kara ce mata komai ba, amma ya fasa kaita gidan Hajiyar Gadon kaya, kofar gida ya maida ita wato can gidan su, New Site.
Tun bai gama tsayawa ba da motar yace, fice min daga mota malama, daga yau bazan kara fita da ke koina daya shafeni baba, uwar kaudi uwar tsugudidi, fadi baa tambaye ki ba.
Jikin ta nata bari ta bude kofar motar ta fita daga gaban motar, hawaye ya tsirgo mata, zata cigaba da bashi hakuri ya fizgi motar sa ya bar harabar gidan su.
Sumayya ta dade tsaye a wurin, tana nadamar shegen surutun ta, da bata iya gani tayi biris, daga karshe ta share hawayenta ta shiga gida.
Yinin ranar zungur, Sumayyah ta kasa sukuni idan ta tuna Bhaiya na fushi da ita, Aunty Surayya na tambayar ta me aka yi mata take kulubi da hade rai? Sai ta ce a fusace ina ruwanki dani? Ko ina shiga harkar ki? Mama tace ke ko! Ina laifin Yayan da ya damu da kai? Nifa rashin kunyar ki ce take hada ni da ke Sumayyah ta tashi fuuu! Tayi dakinta ta bar musu falon. Surayyah na fadin kyaleta Mama ta yi da yar halak.
Shikuma tunda ya sauketa asibitin Murtala ya koma. Ya shige ofishin sa ya kulle kan sa a ciki.
Maganar da Sumayyah tayi kuskuren furtawa ta tuna masa da shekaru biyar a baya, abinda ya dade da mantawa; ta tuna masa ‘first love affair din sa wato MADINAH ATTAHIRU (MADINAH SORON DINKI), yar ajinsu, wadda bai sha da dadi a hannun ta ba dama iyayen ta da sunan soyayya, shiyasa duk inda aka ambaci yana son mace, sai ran sa ya kai makura wajen baci.
Ya so Madinah kamar rai, irin son da ake kira (love at first sight) tun bai gama sanin ciwon kan sa ba, amma Baban ta ya wulakanta shi, don a cewar sa nawa yake a shekaru da matsayi? Sune samarinnan masu hurewa yaran mutane kunne su hana su karatu, bai isa auren diyar sa ba. Sannan Uban sa ma bai isa ba, tunda ba wani bane banda malamin makaranta, ina shi ina auren diyar sa?
A lokacin ko part three na karatun sa bai hada ba. Soyayya ta rufe musu ido, soyayya ce irin ta tashen balaga daga shi har Madinan, sun so juna shi da Madinah kamar daya bai iya rayuwa ba tareda dan uwansa ba, sun yi alkawarin aure da zarar sun kammala MBBS sabuda yadda suka zaku ga son mallakar juna, amma Baban ta sai ya canza mata makaranta ma, duk don ya raba su, ya nesanta Madinah daga gareshi kwatakwata, don yace ya fahimci zai hana yar sa karatun da ya kai ta ta yi a Jamiar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah ne kawai, shine dalilin da a karshe ma ya dauke yar sa ya maida ita Jamiar Yamboa dake kusa da Madinatul Munawwara, inda acan ne Madinah ta samu ta kammala nata karatun, shikuma ya kammala a King Abdul Aziz University ya dawo kasar sa ta haihuwa, daga lokkacin basu kara haduwa ba shi da Madina ko a hanya ko a waya ko a mafarki.
Baya ko son tuna wata kalma wai ita soyayya saboda abinda Baban Madinah yayi masa, shi ya san tsakani da Allah ya so Madinah ya kuma yi niyyar auren ta da zarar sun kammala karatun matakin farko na koyon likitanci, itama kuma sai ta baiwa mahaifin ta goyon baya dari bisa dari, lokacin da ya maidata Yamboa sai bata kara nemansa ba koda kuwa a email, ko a telephone, ko ta wasika da ake aikawa ta post office a lokacin.
**** ***** *****