Sashe 22
Hauwa Kulu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dadi daga bakinki, na ji dadin zama da ke Inna, zan kuma yi kewar ki ba dan kadan ba!. Sai da ya tashi tafiya yaga Hauwa ba tace masa komai ba, koda kuwa adduar fatar baki ce, ta sunkuyar da kai kawai. Wannan karon kam ya kufula da wannan mugun hali nata, ya ce Kuluwa!!!”. (Sunan da ya san ta tsana, kuma yana kular da ita), ta dago manyan idanun nan tayi harrr! Dasu a saitin da ta jiyo tashin muryar sa, ga mamakinsa hawaye ya gani ya kwanta dankam a cikin su, ya basu wata irin kala kamar na mai jin barcin da ke hamma, ya sake cewa, ko ba da Hauwa-Kulu-AKA-Kuluwa nake magana ba?. Hauwa ta tsuke baki, sannan ta sosa hanci cikin jin haushi, bata amsa ba, sai can data mula taga damar magana don kanta sannan tace, amma dai saboda Allah in mutum ya nuna baya son suna, bai kamata a dinga kiran sa da shi ba, har raina bana son suna KULUWA! an ce miki Kuluwar, Kulun Majadun, Hauwa-Kulu, Kululu, da wasu idanuwanki kamar na Kuliya (mage/mussa). Ke kam baki ji dadin halin ki ba, wallahi ba don Inna ta tabbatar min a gida ta haife ki ba, da na yi rantsuwa an canja mata ke a asibiti. Don Inna ba sumumu-kasau bace, bakin ta baya shiru don ya cutar da ita, ki fada kar ta kashe ki, mai yuwuwa kafin shekara ukun na mutu! Ko ke kin mutu! Ko dukkan mu mun mutu! Don haka fadi abinda ke ran ki yau da nazo yi muku sallama, ba tare da mun san ranar sake haduwa da juna ba. Hauwa zan iya rantsuwa kan ban taba jin kin yi min magana da ta wuce sentence biyu ba, a tsayin shekaru biyun da nayi da sanin ki. Ga wani ‘sadness’ da nake gani akan fuskarki a duk lokacin da kika ji sallamata a gidan ku. Me nayi miki haka? Meye dalili? Na rantse gaisuwa ma akan dole kike yi min ita. Kulu baki dauke ni dan uwa kamar yadda na dauke ki ba.. Hauwa-Kulu sai ta fara hawayen babu gaira babu dalili, ko da yake dama sun cika idon tuntuni suna so su zubo ne, tana fin karfin su. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ta ce dama kullace kake da ni haka duk tsayin lokacinnan ban sani ba?. Nake kullace da ke? Ko kike kullace da ni?. Inna bata san me yasa ta kasa sauraron takaddamar tasu ba, ko don cikin zafin rai kowanne yake furucinsa, sai ta tashi salin alin ta saka takalmanta ta dau buta da niyyar ta zagaya bayan gida, ba tare da tana jin fitsari ko kashi ba, kawai ta kasa jure ganin hawayen Hauwa shi kuma ta kasa jure ganin bacin ran sa karara yau, don bata taba ganin sa cikin bacin rai ba, shi Sarham ta fahimci kullum mai kirki ne, mai fara ne, mai walwala ne kuma mai farin-ciki da kowanne yanayi (jovial person). Kasancewar bai taba nuna bacin rai a kan share shin da halin koin kulan da Hauwa-Kulu ke nuna masa ba sai yau, wanda itama ta sha yi mata fada a kan bata kula shi, bata kyautata muamala da shi, bata masa fara kamar bata so yake zuwa gidan su, amma Hauwa sai ta ce, to Inna me kike so in dinga ce masa? Magana ba sai ta dauro ake yin ta ba? To ni ban da wata magana da shi banda gaisuwar da ta zame min dole, kuma ina gaida shi”. Rannan da Inna ta hau ta da fadan ya zo har ya fita ranar ko gaisuwar ma bata yi masa ba, Hauwa ta zaro manyan idanunta waje (ta manta da wa take magana) ta ce, Inna! Idan kin manta ni ban manta ba, daga gyaran ido ya karasa makanta ni, ni duk wannan kirkin nasa gare mu ta baya ta raggo, ido fa na rasa a hannun sa, Inna! Wani abu zai min ya biya ni?” A ranar Inna ta sha mamaki ta kuma tsorata, ta ce au, dama dalilin ki na kin girmama alamarin likita kenan?. Hauwa ta yi shiru, sai can ta kama hawaye. Tace Inna dalili na kenan, amma ba wai na rike shi a raina bane na san kaddara ta ce, amma kullum na tuna shi yasa idon ya karasa macewa saboda careless na aikin sa sai naji tsanar sa ta darsu min, tunda Inna ba abinda zai yi ya biya ni ido na, ba kuma abinda zai min da zan yi farin ciki da shi idan ba idanuna ne suka dawo min ba!”. Inna ta kai hannu zata mari Hauwa, ko me ta tuna? Malam Bilyaminu! Ya taba rokonta ko me Hauwa zata yi nasiha ta kasance tsakaninsu ba duka ko zagi ba, duka baya biyar da yaro yayi abinda kake so saidai ya kara kangarar da shi musamman mautum mai riko irin Hauwa-Kulu. Sai Inna ta rike hannun nata da daya hannun, ta hana shi isa ga fuskar Hauwa. Cikin tashin hankali tace mata na rasa me zan ce miki, Baban ki ya sha gaya min kina da kullata ban taba yarda ba sai yau, amma ina so ki sani Allah ne ya dora miki makanta ba Likita Sarhamu ba, su kawai masu taimakawa ne a samu lafiya amma suma basu hada sani da Allah ba, lalube suke cikin abinda suka karanta don su taimaki alumma kawai. Inaso ki sani Hauwa-Kulu, komai na rayuwar dan adam a rubuce yake a Lauhul Mahfuz, tun kafin halittar sa balle haihuwar sa. Ban so kika saka wannan mummunan tunanin a ranki ba Hauwa-Kulu, domin ya zama rashin yarda da kaddara, ya nuna baki dauki kaddararki da kyakyawar zuciya ba kenan, wanda yana cikin sharuddan imanin mumini. Yi maza ki ce “astagfirullah domin wani Likita duk kwarewarsa ko akasinta, bai isa yayi abinda Allah bai yi ba, kuma shi ba Allah bane da zai bayar da lafiya ko ya hana. Banda son zuciya irin naki, in ma tuhumar ne ni ya kamata ki tuhuma, ni da tun farko ban kai ki asibiti ba tun ciwon yana apolonsa, sai da idanun suka kusa tashi aiki. Haka Inna tayi ta mata waazi mai shiga jiki a lokacin, amma Hauwa-Kulu bata kara tankawa ba saboda miskilancin ta, don haka yanzun ma da Inna ta shige bayi ta bar su a nufin su gama fadan sannan ta dawo, Sarham ya ce wai ta fadi abinda ke ranta yau, kada ta bar shi a ranta ya kashe ta, sai taji kuka ya kwace mata ba kakkautawa a gaban sa. Sarham sai gashi jabar! Ya koma ya zauna dabas a kasa, akan rairayin tsakar gidan su Hauwa. Taja gefen hijabinta ta rufe fuska cikin kakabi da fushi da muryar kuka ta ce, babu komai a raina, sai fatan alkhairi ga kowa”. Sarham ya ce karya kike yi, kuma ni bana shiri da mai karya. Ko amon muryarki ya karyata ki, ya karyata abinda kika fada. Fatan Alkhairi ne a ranki game da kowa? Amma banda a kaina ni Sarham ko? Wa na kashe miki? Ko me nayi miki haka da zafi da kika kullace ni?. Hauwa ta rasa yadda zata yi da shi, don ba zata iya ce masa tana jin maqaqin sa a ranta ba, da cewa bai iya aiki bane ko kuma carelessness dinsa ga aikin sa ne yasa ta makance gabadaya. Sai ta samu bakin ta ya bige da cewa cikin rawar murya da rishin kuka. Ina dakace ne na cewa, inama ina gani! Inama in ga fuskar ka a zahiri in san kamannunka! Rashin idona yana hanani farin ciki da kowa da komai”. Mamaki ya kashe Sarham daga zaunen da yake na yadda nan da nan ta kirkiri karya don kaucewa tunanin ta na hakika, ya dube ta sosai cikin manayan idanun ta kamar tana ganin sa, zai so ace a lokacin da zai fadi abinda zai fada yanzu sun hada ido, yace cikin wata irin murya mai rauni. Maijidda you are accusing me for being the cause of your blindness, (Maijidda kina tuhumata da zamowa sanadin makancewar ki), hakane ko ba haka ne ba?!” Hauwa ta cira ido a firgice, zuwa inda take jin tashin sautin sa, ya daga gira yace Yes, ba wani son ganina da kike yi, karewa ma ba kya son gani na, you are just accusing me. Ni kuma na san bani na makanta ki ba ALLAH ne ya tsara miki wannan jarrabawa domin ya jarrabi imanin ki Maijidda. Nakaa ba komai bace face jarrabawar Ubangiji ga wasu kebabbun bayinsa. Unfortunately, kina neman faduwa jarrabawar ki Maijiddah, domin a zuciyar ki babu TAUHIDI babu IKHLASI. So ya rage naki kiyi maza ki gyara, kiyi istgfari, ki yi kokarin cin jarrabawar ki, ko ki bari shaidan ya ci nasara da galaba akan jarrabawar ki ya barki da biyu babu; ba ido ba imani. Don ni, da ke duka mun san yarda da kaddara yana cikin cikar imani. Hauwa ta dan tsorata da bayanin nan da Sarham yayi mata, amma dai ko ta gamsu da bayanin Sarham bazaka taba gane hakan akan Bakanuwar fuskar ta ba, mai iya boye abubuwa iri-iri da ki-fadi, tace, ta yaya zaka fadi abinda baka shiga zuciya ta ka gani ba? Saidai in dama kana tuhumar kanka ne”. Sarham yayi dan murmushinsa mai ban shaawa domin yanzu ya gama gane manufar ta, da abinda ke cikin ranta a kansa tuntuni da yake saka shi ganin sad expression akan fuskarta, yace. Nayi laakari da maganar hausawa ne da suka ce labarin zuciya ai fuska ake tambaya, kuma dai ‘Im older than you, and Im good at reading minds. Da babbar murya zan iya kiran kaina ‘behavioural analyst’, amma mu barshi a abinda kika fada din, watau kina son ganin fuskata ne, me kike kissimawa akan fuskar tawa? Idan kuma ni din mummuna ne fa Maijidda? Irin munin da in an gani sai an rufe ido don muninsa? Hauwa bata san sanda tayi murmushi ba, alhalin ga hawaye face-face a fuskarta, ta ce mummunan mutum ba mutum bane? Ai mummuna da kyan hali irin naka, sai yafi kyakkyawan gaske nagarta da shiga ran mutum, bayan haka ma a hakikanin gaskiya ni ba wannan nake