Sashe 13
Hauwa Kulu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Gambo, ta zame mata abokiyar zama suke zaune tare a gidan sa na Gadon Kaya wanda mallakin sa ne da ya gina da gumin sa. Lokaci-lokaci yana sabunta shi zuwa ginin zamani irin na wancan lokacin daidai da yawan iyalin sa. Har yanzu Hajiyar gadon kaya na can amma ta tsufa ainun, sun yi sun yi ta dawo ta zauna tare da su ta ki, don haka kusan koyaushe kafar su bata rabo da gidan Hajiya musamman Surayyah, saboda yadda Hajiya ta shagwaba ta, kuma tafi jan ta a jiki duk cikin su. Wannan ya samo asali ne daga sanda aka haife ta bada jimawa ba Mama tayi wani dogon rashin lafiya mai tsanani na lokaci mai tsaho wanda yasa dole aka dauke Surayyah a nono ba tare da ta isa yaye ba, Hajiya ce ta cigaba da rainon ta a dakin ta da madarar yara har ta yaye ta, sai ta cigaba da zama a wurin ta har bayan da Maman ta samu sauki, aka zo aka haifi auta Sumayyah, amma Hajiya ta rike Surayyah, bata kara bari ta dawo wajen Maman su ba, saidai ta zo da yawo har girma. Ita kuma Sumayya dalilin shakuwar su itada Sarham ya samo asali da cewa kusan Sarham shi yayi rainon ta, domin akwai rata ta kusan shekaru goma sha biyu a tsakanin su. In Mama na wajen aiki shi yake kula da Sumayya su tafi makarantar islamiyyar sa tare, har zuwa sanda itama ta isa shiga makaranta, malamai na hanawa azo da kananan yara amma Sarham ba ya jin Magana, gobe sai ya dawo tare da kanwar sa, in har ba za’a bar shi ya shiga aji da Sumayyah ba tofa zai koma bayan tagar ajin su ne shi da ita su make su yi ta leke, korar duniya malamai zasu yi masa ba zai tafi ba, har suka gaji suka kyale shi yake zuwa aji tare da ita, don Mama bata da lokacin kula da ita. Inda Mama ta zama akasin Prof. Kenan, shi kam yanada lokacin yaran sa no matter what, yana jan yaran uku a jiki, daga yamma zuwa lokacin barci idan ya dawo daga cikin makaranta suma suka dawo makarantar islamiyya zai kasance tare da su. Ita Mama zaka samu ko ta dawo aiki zata ce ta dawo da muhimmin (case) a hannunta zata yi nazari, tace su zauna a falo kada su dame ta. A haka Sarham da kannen sa biyu mata suka rayu tsakanin yan bokon iyayen su. Sai ya zama cewa a girman su ma Surayya ta fi shakuwa da Kakar su, itada Sarham basa ga maciji, sai fadan sako da sakuwa, yayin da Sumayyah kuma tafi shakuwa da shiri da shi fiyeda Mama.