← Book details Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 28

Chapter 06: When destiny came in disguise

Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 18 min read

Nanameera, YOTA/23.


Around 5:30pm ne, rana na kokarin shige wa cikin hazo, Iska tana kadawa da ƙanƙanin sanyi, tana ɗauke da ƙurar gawayi da tururin abinci daga kan tanderun masu talla. Orange Market ta cika sosai da jama'a kasancewar ranar Lahadi ne ko'ina kabi cike yake da hayaniya da motsin mutane

Shaguna sun cika har da ƙofofin su, 'yan kasuwa na ta waƙa da kiran sayarwa, "Fresh tomatoes! Dankalin turawa! Fruit ɗin sabo!" Murya na hadewa da kukan yara da tattausar dariyar mata yan talla masu soyayya. Fitilun titi na haskawa sannu a hankali, suna ba wa kasuwar wata kalar launin rawaya da ke rikita ido, Jama'a na yawo da buhuna a kafaɗa, wasu na cin abinci a bakin masu sayar da masa da soyayyen dankali.


Tsaki Zayyad ya yi ganin yanda traffic ya yi yawa a cikin kasuwar, kasancewar lokacin gefin magriba ne, kasuwar ta hargitse masu siye da siyarwa sai kai komo suke, Yayinda iska ta yawaita cikin kasuwar sakamakon kwantaccen hadarin daya ɓuya cikin gajimare. Kashe karatun motar Zayyad ya yi yana kallon Ahmad ya ce“Nifa duk sanda na shigo Mararaban nan ina jin wani irin yanayi, yanda kuke iya rayuwa a nan yafi bani mamaki fiye da Chemistry” Ahmad da ke kallon motocin da suke gabansa ya ce“Nima kuna bani mamaki yanda ku ke iya rayuwa ba tare da tunanin wasu ba, ai ita rayuwa kowa da irin tasa kuma duk inda Allah ya nufa dole nan ne inda zaka rayu” yanda ya yi maganar ya sanya Zayyad murmushi ya ce“To mene abun fusata kuma?”


“Wane ya ce maka haushi naji?, ai kana da right ɗin ka faɗi abin da yake ranka” harararsa Zayyad ya yi bai ce komai ba ya shiga danna wayarsa. Tamkar wanda aka ce ya juya haka ya kalli side ɗinsa daga cikin motar, Zaune take kan wani bencin tana ware ledar ruwan dake hannunta, daga gefenta wasu matane su biyu sai kuma namiji guda ɗaya. Da murmushi a fuskarta ta buɗe ƙatuwar coolern gabanta ta zaro ledar lemon tsamiya guda biyu ta saka cikin ledar data buɗe ta miƙawa matar gabanta. Amsa tayi tana murmushi ta ce“Allah ya yi albarka” murmushi Salma ta yi ta ce“Ameen Mama” daga haka ta bar wajen, ta juya ta sake karbar kuɗin ɗaya mutumin. Lemon zobo ta ɗauko ta miƙo masa sai dai kafin ya amsa ya suɓuce daga hannunta ya faɗi ƙasa nan take ledar ta fashe lemon ya tsiyaye a gefen wajen. Samun kansa ya yi da yin murmushi a fili ya ce“Allah shi ƙara” kallonsa Ahmad ya yi sai kuma ya ce“Kai dawa?” banza Zayyad ya yi masa ya cigaba da kallon yarinyar, Ahmad ma ya kalli wajen, Salma kamar zata yi kuka ta kalli mutumin ta ce“Yi haƙuri Baba” girgiza kai mutumin ya yi cikin sanyin murya ya ce“Bakomai yarinya” ta sake ɗauko wani zobon ta miƙa masa, a zuciyarta tana tunanin yanda zata yi da Umma idan taje gida. Ɗago kanta tayi cikin rashin sa'a suka haɗa idanu da ita, a fili kuma yanda zata ji ya ce“Da kin nemi sana'a mai ma'ana kin yi kin bar wannan sayar da lemon” Salma da ranta ke a ɓace ta kalleshi ta ce“Duk sana'ar da ba haramun bace ai bata zama mara amfani ba, ko an faɗa maka agogo ne kaɗai ke faɗa mana gaskiya?” ta ƙare maganar tana murguɗa masa baki. Tuntsirewa da dariya Ahmad ya yi ya ce“ka samu daidai da kai” haɗe rai Zayyad ya yi yana kallonta ta cikin motar ya ce“And who are u?” Salma ta ce“Ni ba kowa bace, kuma ba yar gidan kowa ba, amma nan gaba kasan irin maganar da zaka faɗawa mutum domin baka san halin wani ba” daga haka ta ɗauke kanta tana kallon wani wajen daban. Shiru Zayyad ya yi haka kawai ya samu kansa da kasa sake faɗar wata maganar, kawai ya juya yana danna wayarsa daidai nan suka samo hanyar shigewa. Suna barin wajen Ahmad ya kalleshi ya ce“Kaga abin da nake faɗa maka ko? Ba kowa zaka yi ma abu ya rabu da kai ba, kuma koda hakan na nufin kafi ƙarfinsa” tsaki Zayyad ya yi ya ce“Ni banida lokacin tsayawa ina magana da wannan yarinyar daga ganinta kasan tana rayuwane a cikin duhu, Bama tasan kanta ba”


“Oh really?.” Ahmad ya faɗa yana kallon Zayyad, banza ya yi masa, Ahmad ya sake faɗin


“But you have to know that ba kowane haske ke zuwa daga chandelier ba. Wani hasken na iya zuwa daga titin Orange market.”


Zayyad kallonsa kawai ya yi ta gefen ido, sai kuma ya kalli wajen daidai sanda iska ta kaɗa ya lumshe idanunsa. Murmushi Nayla tayi tana kallon Fatiha dake tsaye gaban mai sai da Alayyahu tana yanka mata ta ce“Nifa wani abun kwaɗayi nakeson siya” Fatiha ta yi dariya ta ce“Kamar me kenan?” juya idanu Nayla ta yi alamar bata sani ba. Ta kalli gefenta nan ta hango ana miƙawa wata mata sumammen zoɓo mai sanyi,


“I got it!”

Tafaɗa da ƙarfi tana dafa Fatiha, kallon inda take nunawa Fatiha tayi ta ce“Wai lemon can kike so?” gyaɗa mata kai Nayla ta yi, Fatiha ta ce“Ki bari idan mun je gida sai muyi, muje mu siya zoɓon” girgiza kai Nayla tayi ta nufi wajen mai siyarwar. Babu yanda Fatiha ta iya haka ta biyo bayanta. Salma take zaune tana ɗan kalle kalle ta amsa sallamar Nayla.


“How much?”


“Hundred Naira each” murmushi Nayla tayi dan ta burgeta ta ce“Okay bani guda biyar” to kawai Salma ta ce, sannan ta zaro baƙar leda tafara zuba zoɓon a ciki. Nayla ta ce“Oh ashe ba iya zoɓo bane”


“Eh akwai Tamarin ma”


“Haɗa min har da shi sai ki bada na 1k” Okay Salma ta ce sannan ta cigaba da zuba mata. Nayla ta kalli Fatiha dake tsaye kamar statue ta ce“Tyha bani 1k” zaro dubu ɗayan tayi a jakarta ta miƙa mata, Kallon kuɗin Nayla ta yi sai kuma ta ce“ƙara min wata” Fatiha ta sake bata ba tare da ta tambayi dalili ba. Salma nagama zubawa ta miƙawa Nayla, Amsa tayi tana murmushi ta ce“Thank you dear” daga haka ta miƙa mata duka 2k ɗin. Kallon kuɗin Salma ta yi sai kuma ta ce“Amma ba haka bane kuɗin ai, naga 2k kuma 1k ne kuɗina” Nayla na murmushi ta ce“Yeh i know, baki nayi” girgiza kai Salma ta yi ta miƙo mata tana cewa“A'a ki bar shi Nagode” murmushi Nayla ta yi ta riƙe hannun data miƙo mata ta ce“I insist”


“Kinga in zaki amsa ki amsa ana baki kuɗi kina wani baki so, as irin kinfi ƙarfin nan nashi” Fatiha tayi maganar tana kallon Salma fuskanta a haɗe. Jan hannunta Nayla ta yi tana cewa“Ayyah sister mene haka, isn't good fa” tsaki Fatiha tayi ta juya ta bar wajen, haka kawai taji Salman bata mata. Girgiza kai Nayla ta yi kamar zata yi kuka ta ce“I'm sorry on her behalf dear” daga haka ta juya ta bar wajen itama. Komawa Salma ta yi ta zauna ta sanya hannunta ta share hawayen daya zubo mata.


Sun fara tafiya Nayla ta kalli Fatiha ta ce“Abin da kika yi ba daidai bane Tyha, bakyau yiwa ɗan adam irin haka. Ke kina gani kinsan ƙaddarace ta sanyata a wannan rayuwar, kalleta mai kyau kuma ga ilimi bugu da ƙari daga ganinta tanada tarbiyya”


“And so what? Ke bakisan halin yan matan kasuwar nan bane shiyasa kike wani cewa haka, duk yan iska ne wlh. Dan kin ganta da kyau to Allah ne kaɗai yasan abin da take aikatawa, haka suke, iyayensu ke aikosu kasuwa da sunan suna talla, amma s zahiri da sana'ar ta kawosu ba, suna zuwa ne kawai dan su haɗu da zama, ayi abin da bai dace ba” Fatiha ta ƙarashe maganar tana yin tsaki. Shiru Nayla ta yi sai kuma ta ce“Yaya Zayyad wai haka?” shiru ya yi mata ba dan bai ji kiran da tayi masa ba, sai dan bashida interest akan hirar tasu. Nayla ta sake cewa“Yaya I'm talking to you fa, amma ka shareni” ba tare da ya juyo ba ya ce“Mene ne?” madadin ta bashi amsa sai ta mayar da idanunta kan Ahmad dake tuƙi ta ce“Yaya wai haka ne? Ni ban yarda da abin da Fatiha tafaɗa ba” murmushi Ahmad ya yi ya ce“Hakane Auta, but not all of them, wasu ba hakan bane, wasu ƙaddarace take kawosu kasuwar. Wata zaki ga mahaifinta ta rasa, wata kuma mahaifiya, wata kuma suna rayen amma basu da yanda zasu yi dasu, rayuwar Mararaba ba kamar ta Abuja bace, anan akwai ƙalubale dayawa. Wasu duhu ne ya cika rayuwarsu, kuma basu sami wanda zai nuna musu haske ba, basu samu wanda zai fitar dasu daga wannan ƙangin ba. Saboda haka babu yanda za'a yi ace duk macen dake sana'a cikin kasuwa ƴar iska ce” kamar zatayi kuka ta ce“Allah sarki, abun tausayi Yaya, nikam wannan duk inda take mutuniyar kirki ce, kuma bata rasa haske ba, daga ganinta ita kanta Hasken wani ce”. Murmushi Ahmad ya yi ya ce“Daɗina da auta kaifin tunani” tayi dariya bata ce komai ba har suka ƙarasa gida.


****Tafiya take a hankali tana tunane tunanen cikin ranta, duk rin horn ɗin da ake yi Salma bata ji ba, dan gabaɗaya zuciyarta bata wajen, Wani mutumi dake kusada ita ne ya yi mata magana yana cewa“Ku yaran nan meke damunku? Idan ya bigeki ai ubanki ya siya magani” sai a sannan ta juyo tana kallon motar ƙirar Accord mai launin baƙi. Parking mutumin ya yi ya fito daga motar yana nufo inda take tsaye, a sanyaye ya ce“Me kike tunani?” sunkuyar da kanta tayi cikin cool voice ɗinta ta ce“Dan Allah kayi haƙuri” murmushinsa mai kyau ya yi ya ce“Bakomai, Allah ya kiyaye. But ina zaki je?” ya yi maganar cike da kulawa.


“Mamana ta aikeni gidan ƙawarta” agogon hannunsa ya kalla, around 6:30pm ne ya ɗago ya kalleta ya ce“Okay, ina ne wajen? Can I help you?” Salma tayi saurin cewa “A'a nakusa zuwa ma ai, dana zagaya wannan layin ne” murmushi kawai ya yi ya ce“Alright sai kin dawo” murmushin itama tayi ta ce“Nagode” daga haka tabi ta gefensa ta shige. Da idanu ya bita yana murmushi sai kuma ya koma motarsa ya tada ya bar wajen. Salma na shan kwana ta tsaya tana dafe ƙirji, sosai mutumin ya bata tsoro a fili ta ce“Waya sani ma ko ɗan yankan kai ne” daga haka ta cigaba da tafiya dan tana hango gidan Aunty Maryam ɗin.


****Murmushi Mami tayi tana kallonta ta ce“Kenan ta burgeki daga ganinta?” jinjina kai Nayla ta yi ta ce“Mami ko ke kika ganta sai ta burgeki, she's cute kuma daga gani tayi karatu, can you imagine Mami har turanci ta iya?” Jinjina kai Mami tayi tana murmushi ta ce“Allah sarki, to Amma mene ya saka take talla a kasuwa?” watsa hannu Nayla tayi alamar bata sani ba. Fatiha dake kallonta tun ɗazu ta ce“Ke kina da matsala wlh, kinga Mami duk ta damu akan wata wadda bata sani ba” harararta Nayla ta yi ta ce“To ina ruwanki dani? Ni nace kiji tausayinta ne?”


“Allah ya tsareni da jin tausayin ƴar talla fitsararriyar banza”


“Fatiha!”


Mami ta kira sunanta a tsawa ce.


“Don't ever try it again”


A sanyaye ta ce“In sha Allah Mami” tashi Nayla ta yi ta ce“Ni bari na ɗauko lemona ma nasha, nasan yanzu ya sake yin sanyi” daga haka ta tashi ta shige kitchen. Cup guda biyu ta ɗauko kowanne ta zuba leda ɗaya na lemon wanda ya sake sanyi aciki sannan ta ɗauko ta fito. Mami ta samu zaune inda ta barta, ta miƙa mata daya tana cewa“Mami test it please” amsa Mami tayi tana dariya sanin halin Nayla. Without second thought kuma ta kai lemon bakinta. Lumshe idanu Mami tayi dan bata yi tunanin zai yi mata daɗi haka, sai da ta shanye tas sannan ta ajiye empty cup ɗin kan table tana cewa“Gaskiya Ya yi daɗi, na daɗe ban sha lemo mai daɗin wannan ba. A ina take a Orange market ɗin?” gyara zama Nayla ta yi bayan ta shanye nata itama ta ce“Kinji ko Mami? Ni dama daga ganinta nasan abunta zai yi daɗi wlh. A bakin titi take zaune kusada masu sai da abinci, kinga yanda ake layi kuma Mami?” Jinjina kai Mami ta yi ta ce“Allah sarki, aikuwa idan nashiga kasuwar zan biya na siya watarana” sosai Nayla taji daɗi jin yanda Mami ta yabeta. Ita kuwa Fatiha sai taɓe baki take duk da tanason tasha lemon ko dan taji abinda suke yiwa kwazozoton. Ana fara kiran sallar isha'i suka sakko daga saman, Mami ta kallesu sai kuma ta ce“Naga ka saka hula ina zaka je?” murmushi Zayyad ya yi ya ce“Mami dare nayi, tafiya zamu yi” haɗe rai Nayla tayi lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke. Taɓe baki Mami ta yi ta ce“Amma ai ka tsaya ku ci abinci ko? Ko kuma tafiya zaku yi da yunwa?” Zayyad ya ce“Mami ni dai wlh I'm full, Alhamdulillah”


“I see. Idan kai ka ƙoshi ita ai Nayla zata ci abinci” ta ƙare maganar tana kallon Nayla, gyaɗa mata kai tayi ta ce“Eh Mami ni yunwa nake ji, kuma na daɗe ban ci tuwo ba ni dai sai naci abinci” harararta Zayyad ya yi ta gefen ido. Mami ta ce“Saboda haka sai ka jirata ita taci abinci, kai kuma Allah ya ƙara ƙoshi” murmushi Ahmad ya yi ganin yanda Zayyad ya yi da fuska kamar zai saka ihu. Ya dafa shi yana faɗin “Baba let's go, mu koma daman ban gama da kai ba” wani kallo Zayyad ya watsawa Ahmad ɗin sannan ya juya ya koma saman. Mami ta bishi da harara.


“Mami ki ce ya barta ta kwana mana” Fatiha tayi maganar kamar zata yi kuka. Shiru Mami ta yi mata ta tashi ta shige kitchen dan ta duba girkin da take. Tasowa Fatiha tayi ta dawo gefen Nayla ta riƙe hannunta tana faɗin “Dan Allah ki kwana mana” murmushi Nayla ta yi ta ce“Yaya won't let me, ba zai barni ba nasani” tsaki Fatiha tayi ta ce“But sai kiyi pretending a zuwan baki da lafiya, kinga sai ya tafi ya bar ki”


“As if bakisan he's a medical doctor ba ko?” shiru Fatiha ta yi sai kuma ta ce“To ya zamu yi?” girgiza kai Nayla ta yi ta ce“Nima bansani ba, but wlh inason na kwana, banason komawa Abuja, nan yafi daɗi” Shiru Fatiha tayi tana tunanin hanyar da zasu bi Nayla ta kwana a Mararaba. Can ta tashi ta shige kitchen Nayla ta bita da idanu. Daidai nan aka fara knocking ƙofar parlon, tashi tayi ta buɗe dan Mami ta rufeta, shigowa ya yi yana sanye da wani yadi mara kauri, da gudu tafaɗa jikinsa tana faɗin


“Masoyiii”


Rungumeta Al-ameen ya yi yana dariya ya ce“Masoyiya ashe kin zo” gyaɗa masa kai tayi tana sakinsa ta ce“Muna nan da Yaya tun rana, but ban ganka ba ina kaje?” murmushi Al-ameen ya yi yana zama a kujera ya ce“Ina clinic wlh, Abubuwane suka yi yawa shiyasa” zama tayi kusa da shi tana faɗin“Then ka yadani ko Masoyi? Ba kira babu saƙo ko dai kayi sabuwar budurwa ne?” girgiza kansa ya yi ya ce“Duk mai son ganin rigima yazo wajen Autar Mommah, wane ya faɗa miki haka? Ke dai kika yada masoyinki bani ba, you left me” ya faɗa yana marairaice fuska, Tuntsirewa tayi da dariya tana cewa“Kaga fuskarka kamar wani Baby taɓ” lumshe idanunsa ya yi ya ce“I'm so tired wlh” Rau rau tayi da idanu ta ce“Ayyah Masoyi tashi kaje kayi wanka kazo kaci abinci Mami tagama” Tashi Al-ameen ya yi yana cewa“Ina Yaya Zayyad ɗin?”


“Suna sama da Yaya Ahmad” jinjina kai Al-ameen ya yi ya ce“To bari naje na shirya nazo mu sha hira” langwaɓar da kai tayi ta ce“Bayan tafiya zamu yi”


“Da daren nan? Why not ku bari sai gobe?”


“Yaya ba zai bari ba, ni nasani” shiru Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“Bari dai ina zuwa” daga haka ya haye upstairs.


Zaune suke kan dinning table ɗin kowa yana cin abincinsa banda Al-ameen wanda ya zubawa plate ɗin idanu, sau biyu Mami na kallonsa tana ganin yanda ya yi shiru kamar yana tunani, sanda ta ɗago idanunta ana ukun ne ta ajiye spoon ɗin hannunta tana faɗin


“Al-ameen”


Shiru bai amsa ba, alamar hankalinsa ma baya wajen, Nayla dake kusa da shi ce ta taɓa shi ta ce a hankali “Yaya, Mami na magana” sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta. Da mamaki ta ce“Lafiyarka? Me kake tunani?” numfasawa ya yi ya ɗauki spoon ɗin kan abincin ya fara kai tuwon semovitan da miyar agusi wadda taji nama bakinsa. Mami bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincinta. Ahmad ne ya kalli Zayyad wanda ke faman danna waya ya ce“Wai ba zaka ci abincin ba? Ko bakason tuwon?”


“Wai Ahmad meyasa kake yimin haka? Ina ruwanka dani?” ya faɗa yana harararsa, duka Ahmad ya kai masa yana cewa“Banza ni dan nayi maka abin arziki”


“But ai already tell you banason abun arzikin naka, kana wani yin abu kamar na Allah a gaban Mami. Mami can you imagine yanda Ahmad ke dakamin tsawa a Abuja, babu kalar zagin da baya yimin” Ya ƙare maganar yana kallon Mami. Murmushi tayi ta ce“To kayi hakuri, ni yanzu nace kaci abinci” Zayyad spoon kawai ya ɗauka ya yi bismillah sannan ya kai tuwon bakinsa, ya lumshe idanunsa jin yanda miyar tayi wani irin daɗi, daman Mami ba dai iya girki ba, that's why some years back yake zuwa takanas kawai dan ya ci abincinta. Basu gama cin abincin ba sai wajen 8:30pm Zayyad ya tashi ya haye sama da sauri, wanke bakinsa ya yi sannan ya fito yana kallon Ahmad dake tsaye a corridor


“Why not ku kwana Zayyad?”


“I will not” ya faɗa yana sauka kasa. Taɓe baki Ahmad ya yi sai kuma yabi bayansa. Zaune ya samu Nayla ta shirya sai tura baki tayi, Mami ta ce“Allah ya tsare hanya, make sure idan kun je gida ka kirani” Jinjina kai ya yi ya ce“In sha Allah Mami, mun gode Allah ya ƙara girma” Ameen ta ce sannan ta kama hannun Nayla wadda ta fara hawaye suka yi waje. Turus suka yi a veranda ganin yanda ruwan sama ke zuba kamar da bakin kwarya, wani murmushi Nayla da Fatiha suka saki, suna rike hannun juna. Mami ta ce“Ikon Allah, that's means sai dai ku bari sai gobe” daga haka takama hannun Nayla suka koma ciki as if abinda take jira kenan. Zayyad tsayawa ya yi a wajen kamar statue, yanzu ya za'a yi ya kwana anan? Ba zai iya kwana ba tare da ya sha giya ba. Yaya zai yi kenan?. Ya runtse idanunsa yana jin wani irin yanayi, ko menene ya sanya ya bari sukai magrib anan ma Ohho. Ahmad komawarsa ciki ya yi dan yasan halin Zayyad, a parlon ya samu Nayla sai dariya take bayan tayi wurgi da jakarta a ƙasa. Al-ameen da bai fita ba yana dariya ya ce“Ki bari ya shigo ya ganki kina dariya ya kwaɗeki” Sake fashewa tayi da wata dariyar tana faɗin “Kaga yanda yaya ya haɗe rai kuwa? Ai nikam naji daɗin ruwan nan, Yaya zo ka bani labari” ta ƙare maganar tana zama kan sofa. Zama shima Al-ameen ya yi yana kallonta ya ce“Labarin me zan baki Auta?” murmushi ta yi ta ce“Koma menene just kabani labari” gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce“Ɗazu gab da magrib ina ƙoƙarin dawowa gida na haɗu da wata yarinya. Ban san meyasa ba amma kawai naji tayi min, ke infact ma ni nasamu matar aure” gyara zama Nayla ta yi ta ɗora hannayenta duk biyu kan kumatunta tana kallonsa daga gani tana jin daɗin labarin. Jin ya yi shiru yasa ta ce“Yaya ka cigaba” murmushi ya yi ya ce“Tana da kyau kuma tanada hankali, ta burgeni sosai”


“Wannan wace mai sa'ar ce da har Al-ameen ɗin dana sani ya ce yana sonta, ko dai halin zaka gwada mata?” cewar Ahmad yana murmushi. Girgiza kai Al-ameen ya yi ya ce“No be joke Yaya, wlh da gaske ta shiga zuciyata, tunda muka rabu nake tunaninta”


“And what's her name, a ina kuma take?”


Girgiza kansa ya yi ya ce“Ban sani ba nima, a bakin titin Kabayi muka haɗu, tana tafiya ina faman horn bata ji ba” shiru Ahmad ya yi can kuma ya ce“Al-ameen kai ɗin dana sani ne kake cewa kaga yarinya a Kabayi, kai ɗin? Karka yaudari ƴar mutane” girgiza kansa ya yi ya ce“Ba zaku gane ba, wlh da gaske nake, babu wata yaudara a tattare dani” Fatiha dake zaune ta ce“Taɓ, kawai sai ka auri yar Kabayi kasa friends ɗina suna min dariya” Harara ya watsa mata kafin ya ce“To uwata, hanani tunda ke zaki zauna da ita, ƙawayenki ɗin banza” tashi tayi tana yin hanyar upstairs ta ce“Allah ba zaka aureta ba” da idanu suka bita Nayla ta ce“Barta Masoyi cigaba da bani labari” Al-ameen ya ce“Ai shikenan abin da ya faru fa” Nayla ta ce“To yanzu yaushe zamu je tare na ganta?” Dariya ya yi ya ce“Nima bansan inda zan sake ganinta ba, ban san gidans ba, bansan sunanta, kawai fuskarta nasani” da mamaki Nayla ta ce“To yanzu a ina zaka sake ganinta Yaya?” murmushi ya yi ya ce “Idan har ƙaddara tana nufin mu sake haɗuwa to nasan definitely zan sake ganinta sooner or later” tafi Nayla ta shige yi tana cewa“Yaya kaga yanda ka yi maganar with so much courage kamar a movies?” murmushi kawai ya yi ya ce“Da gaske?” Nayla na gyaɗa kai ta ce“Da gaske Yaya, in sha Allah zaka sake ganinta, ina a jikina ita ɗin taka ce” jan kumatunta ya yi ya ce“My Clever Auta”.


2:30am.


Kwance yake kan makeken royal bed ɗin, sai juyi yake, kwata-kwata bacci ya ƙi zuwar masa. Gajiya ya yi da kwanciyar ya tashi zaune, wayarsa ya janyo ya shiga WhatsApp kai tsaye kuma Aneeserh ya yiwa magana, ya tura mata da sallama, tana online sannan hakan yasa tayi masa reply da


“Bae, ba kayi bacci ba har yanzun?”


Text ya tura mata da Eh, ta sake cewa

“But why?🥺”


Murmushi Zayyad ya yi ya tura mata da text


“Nima bansani ba, kawai bana jin daɗi ne” Aneeserh dake kwance kan gadonta taga message ɗin nasa ya shigo. Tashi ta yi zaune ta sake masa text


“Kaje club ne?”


A'a ya tura mata ta sake cewa


“But you have to, meya hanaka zuwa?”

Zayyad bai bata amsa ba ya ajiye wayar kan gadon ya zura slippers ɗin dake bakin gadon ya buɗe ɗakin ya fito. Ko'ina tsit yake dan ko kukan karnuka ba'a ji, sauka ƙasa ya yi kai tsaye kuma ya shige kitchen dan ƙishirwa yake ji. Buɗe fridge ya yi ya zaro bottle ɗin ruwan, zai rufe yaga wani glass jug mai ɗauke da wani abu kamar tea. Daukowa ya yi sannan ya rufe fridge ɗin, ya yi jim yana kallon jug ɗin sai kuma ya ɗauko wani cup ya tsiyaya abinda ke ciki, a hankali kuma ya yi bismillah ya kai bakinsa. Lumshe idanunsa ya yi saboda sanyi da kuma tsamin tsamiyar daya ji, sai dai ya shanye tas sannan ya sauke kofin yana sakin ajiyar zuciya. Samun kansa ya yi da sake tsiyayar lemon a karo na biyu ya sake shanyewa, sai a sannan ya yi gyatsa ya mayar da jug ɗin inda yake sannan ya ɗauki ruwan ya fito. Yana dawowa ya ajiye ruwan kan bedside drawer ya koma ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukeshi.


# HASKEN CIKIN DUHU
08106608363,
Nanameera.

HASKEN CIKIN DUHU
Chapter 6 · 0% Book details