Chapter 25-26: Shadows of the past
Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 14 min read
Nanameera, YOTA/23.
Amrah ta dinga kallon Jiddah da mamaki, Ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Ba zan taɓa tona miki asiri ba Jiddah, Amma ki sani akwai ranar dana sani, Duk abin da ki ke ɓoyewa akwai ranar da zai fito kowa ya gani, Akwai ranar da zaki yi nadamar abubuwan da ki ka aikata.”
Daga haka ta fice daga ɗakin tana buga ƙofar da ƙarfi, Da idanu Jiddah ta bita har ta ɓacewa ganinta, Ta sulale ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka. Koda Amrah ta fita parlon Mummy ta samu zaune kan sofa tana danna wayarta, Tana ganinta ta ce
“Ba dai har zaki tafi ba Amrah?”
Dan murmushi ta yi ta ce“Eh Mummy magrib ya kusa tafiya zan yi, Kar Daddy ya nemeni”
Mummy ta jinjina kai sai kuma ta kalli bayanta ta ce“A'a ina Jiddahn? Ko har yanzu kukan take?”
Amrah ta girgiza kai ta ce“Ai tana sama Mummy, Mun yi sallama naga har yanzu bata saki jikinta bane”
“Allah sarki, Na rasa yanda zan yi da Jiddah da wannan damuwar, General ya ce min ana ta binciken yanda za'a samo shi, Amma ta ƙi kwantar da hankalinta”
Mummy ta ƙare maganar fuskarta cike da ɗumbin damuwa. Amrah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce“Nima ina ta faman rarrashinta Mummy, Kuma naga kamar ta fara haƙura. In sha Allah za'a gan shi”
Mummy ta ce“Allah yasa Amrah, Dan ina tsoron kar ciwonta ya sake tashi”
Amrah ta ɗan yi murmushi sannan ta ce“In sha Allah Mummy, Sai anjima”
“Okay, Ki gaisar da Mamanki kin ji”
“Zata ji in sha Allah”
Amrah ta yi maganar tana nufar hanyar fita daga parlon.
Tana ƙoƙarin buɗe motar ta Suhaila ta ƙaraso wajen, Ta kalleta tana murmushi ta ce
“Aunty Amrah har za ki tafi?”
Jinjina kai Amrah ta yi ta ce“Eh Suhaila, Dare zai yi”
Suhaila ta jinjina kai ta ce“Haka ne kuma, To ki gaida Yaya Tee”
Murmushi Amrah ta yi ta ce“ Iyye! Wato ko kunyata baki ji ba?”
Suhaila ta rufe fuskarta da fararen hannayenta tana murmushi ta ce“Kai Aunty Amrah, I'm just kidding fa”
Amrah ta gyaɗa kai tana mata wani kallo ta ce“Sannu to, Oyaa shiga gida ni my friend”
Suhaila ta tuntsire da dariya wanda ya ƙara fito da kyanta tana matuƙar kama da Jiddah amma ita fara ce saɓanin Jiddah data kasance baƙa, Amrah ta shige motarta tana cewa
“See you next time”
Bye bye Suhaila ta yi mata sannan ta nufi hanyar shiga gida tana tafe kamar zata faɗi saboda siranta.
****
Kaduna,
5 days later.
Maryam ta fito daga parlon tana kallon Salma dake zaune gefen wata bishiya tana wankin kaya, Ta ƙaraso wajen tana cewa
“Yanzu sai da ki ka yi wankin nan? Ba sai ki bari idan Abu ya dawo a haɗa a kai wanki ba?”
Salma dake matse wata rigar Zayyad ta ɗan yi murmushi ta ce“A'a Aunty ai gara na wanke kin ga babu abin da nake” Maryam ta girgiza kai ta ce“Da dai kin haƙura, Wai ina Zayyad ne naga ban ganshi ba?”
Salma ta ce“Aunty ya fita waje fa, Kin ga har yau ya ƙi kulani ko ɗazu da nayi masa magana banza ya yimin” Maryam ta yi murmushi ta ce“To ke ki rabu dashi mana, Maybe baya son kula kin ne”
Haɗe fuska Salma ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Amma Aunty baya kulani fa, Kuma babu abin da nayi masa ai”
“To gaya min meyasa ki ke jin ba daɗi? Kina son yayanki har haka Salma?”
Salma ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“Ni fa kawai na damu ne tun da ban yi masa komai ba ai, Kawai ya daina kulani”
Maryam ta ɗan yi murmushi ta ce“Anyway ki bari ya shigo sai nayi masa magana”
Sosai Salma taji daɗi ta ce“Yawwa Aunty. Ina zaki je ne?”
“Khalil zan ɗauko a school naga biyar ya shige, Kin san halinsa yanzu sai ya fara min kuka”
Murmushi Salma ta yi ta ce“Ai ko dai, Dana gama ai da sai na raka ki, Amma ki dawo lafiya”
“Allah yasa Salma” Daga haka ta nufi hanyar gate. Salma ta ci gaba da wankinta tana ɗan tunane-tunane, Duk da yanda take jin daɗin zamansu gidan Hashim. .
Tana shanya kaya ya buɗe gate ɗin ya shigo, Sanye yake da wasu English wears riga t-shirt sai wando na jeans kansa a gyara ba zaka taɓa cewa mahaukaci bane, Salma ta dinga kallonsa ganin ko inda take bai kalla ba ya buɗe ɗakinsa ya shige. Ji ta yi jikinta ya yi wani irin sanyi, Ta ƙarasa shanyar sannan ta ɗauke bokitan. Wanke hannunta ta yi a tap sannan ta nufi ɗakin daya shiga, Tura kofar ta yi ta hangeshi zaune gefen ƙaramin gadon ɗakin, Hannunsa rike da wani zare yana ta wasa dashi, A hankali ta ƙarasa gabanshi ta zauna gefen gadon tana kallonsa ta ce
“Yaya Yad”
Banza ya yi mata kamar ba dashi take ba, Ta sake kiran sunansa nan ma ya yi mata shiru, Ta sauko daga kan gadon ta tsuguna gabansa tana leƙan fuskarta ta ce“Yaya Zayyad ka yi hakuri kaji” Ko motsi Zayyad bai yi ba ballantana ta saka rai da yaji abin da ta ce, Hawaye ya fara kawowa Idanunta muryarta na rawa ta sake cewa
“To ka faɗa min me nayi maka? Ka yi haƙuri kaji ba zan sake ba ai nace, Ka yi haƙuri dan Allah”
Ci gaba ya yi da wasa da zarensa babu alamar zai kulata, Sai kawai ta fashe da kuka ta yi zaman dirshan a ƙasa, Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake ɗauke kansa. Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, Lokaci zuwa lokaci yake ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya sake mayarwa kan zarensa, Tafi minti goma tana kukan amma bai yi magana ba. Salma ta tashi ta nufi hanyar waje sai dai kafin taje bakin ƙofar ta yanke jiki ta fadi tana sakin wata razananniyar ƙara.
Da sauri ya kalli inda take ya hangeta zube kan tiles bata numfashi, Tashi ya yi ya ƙarasa wajen ya tsuguna yana kallonta.
“Keeee Mommah! Ke ki tashi mana, Ki tashi na ce miki”
Zayyad ya fadi maganar yana jijjigata, Shiru babu alamar Salma na jin abin da yake cewa dan ko motsi bata yi ba, Ya ɗagota gaba ɗaya yana kallonta ya ce
“Ki tashi mana, Ba kin ce zaki kai ni wajen Mommah ba, Ki tashi mu tafi nace”
Ya dinga faɗar maganar a mugun tsorace, Ganin da gaske Salma ba tashi zata yi ba kawai sai ya fashe da kuka, Ya zauna akan ƙafafunsa tana riƙe cikin hannayensa har sannan ya shiga kuka kamar ƙaramin yaro, Yafi 5mins yana kukan kafin ya ƙara ɗagowa ya dinga dukan fuskarta yana cewa
“Ba nace ki tashi ba, Ki tashi ke, Ki tashi mu tafi”
Tuntsirewa da dariya ya ji an yi, Salma ta buɗe idanunta tana kallonsa, Saurin sakinta ya yi ta tashi zaune tana sheƙa dariya kamar zararriya, Zayyad ya dinga kallonta da mamaki, Can kuma ya ce
“Ke Mahaukaciya ce ne?”
Yanda ya yi maganar ya sanyata sake fashewa da wata dariyar, Ta riƙe cikinta tana nuna shi da yatsa ta ce
“Hooooo nayi masa wayo, Gashi nan ka yi kuka kai ma”
Shi dai bin ta kawai yake da kallo dan har sannan bai gane in da zancen nata ya dosa ba. Ta ɗora hannayenta duk biyun bisa fuskarta tana kallonsa sosai ta ce
“Meyasa ka yi kuka? Ko kana tsoron Mommah ta mutu ta bar ka?”
Zayyad ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa, Hannunsa ta janyo tana murmushi ta ce
“Ai yanzu ka haƙura ko Yaya yad ɗina?”
Ya ƙura mata idanunsa masu kaifi, Sake waro nata manyan idanun ta yi ta kalleshi sai kuma ta ƙifta masa idanun ta ce“Mene ne? Me ka ke tunani, Ka faɗa min baka so na mutu?”
Tashi ya yi tsam daga zaunen da yake ya nufi hanyar waje, Cikin hanzari ita ma ta miƙe ta biyo bayansa tana cewa
“Yaya yad! Yaya Yad! Ka tsayani mana”
Turus ta yi ganinsa tsaye jikin shanyar da tayi yana faman kwashewa, Duk wadda ya ciro sai ya yi wurgi da ita a ƙasa, Da sauri ta ƙarasa yana ƙoƙarin yar da wata riga ta rike tana kallonsa ta ce“Mene ne haka? Ka bari”
Banza ya yi mata ya fizge rigar ya yi jifa da ita, Tafiya ta yi tana kwasar kayan da yake zubarwa tana kwashe wasu yana zubar da wasu, Gajiya ta yi ta zuba a bokiti ta ƙaraso inda yake a fusace ta ce
“Wannan wane irin abu ne wai? Kasan wahalar dana sha na wanke kayan ka ke zubar min, Ina ruwanka da kayana?”
Bai ko kalleta ba sai da ya watsar da duk kayan a ƙasa, Ta kalli kayan sai kuma ta sake kallonsa, A zafafe ta cafki kwalar rigarsa tana mitsi-mitsi da idanu na masifa ta ce
“Wallahi sai ka kwashe min kayana ai ni ba baiwarka ba ce, Tun da kai duk abin da aka yi maka ba zaka gani ba. Wallahi sai ka kwashe min kayana”
Kallona hannunta dake riƙe da rigarsa ya yi sai kuma ya kalleta, A fusace ya fizge hannun ya shaƙi wuyanta idanunsa suka sauya kala a take, Ya riƙe maƙoshinta kamar zai rabata da ranta.
Kasa numfashi Salma ta yi, Idanunta suka firfito waje, Hawaye ya dinga zubowa kan fuskarta, Sai da ta fara kasa motsi jikinta ya fara saki sannan ya yi jifa da ita tamkar kayan wanki, kanta ya daki karfen jikin balcony ta faɗi ƙasa Sumammiya. Juyawa ya yi ya fice daga gidan kamar zai tashi sama.
Bayan mintuna goma sha biyu Khalil ya buɗe ƙofar gate ɗin, Sanye yake da uniform ɗinsa na islamiyya da jakarsa goye a bayansa, Maryam ce ta shigo tana cewa
“Da ka ke saurin sai ka zo gida ba gashi...”
Maganar ta tsaya a maƙoshinta sakamakon Salma data hanga kwance a ƙasa, Khalil ya dinga kallonta da idanunsa, Da sauri ta ƙarasa gabanta tana cewa
“Salma lafiya? Me ki ke a nan?”
Jinin data gani kwance a ƙasa ya sanya taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa, Ta tsuguna tana kallonta hankali a tashe ta ce
“Salma! Salma! Salma!”
Maryam ta shiga kiran sunanta da ƙarfi, Ganin bata motsi ya sanya hankalinta ya ƙara tashi, Ta ɗago kanta tana cewa
“Salma tashi mana, Meya faru, Ke Salma!”
Tashi ta yi ta buɗe jakarta ta shiga kiran lambar Hashim, sai dai lambar gaba ɗaya bata shiga, Sau uku tana kira amma duk babu wanda ya shiga. Ta ajiye wayar ta fita da sauri, Mai Napep ta samu yana shirin barin layin,Ta ce ya zo ya taimaka mata zata kai wata asibiti. Da sauri ya kashe napep ɗin ya fito suka shigo gidan, Shi ya taimaka mata suka ɗauki Salma aka sakata cikin Napep ɗin suka nufi asibiti.
Wani private asibiti suka je, dan a nan insurance ɗinsu yake, Da farko ƙin karɓarta suka yi sai da ɗan sanda, Dakyar Maryam ta roƙesu sannan suka amsheta, Bayan sun yi mata dressing aka kai ta ɗaki suka saka mata ruwa.
Maryam zata yi gefenta tana kallonta, Khalil ma na zaune gefenta sai kallon Salma yake yana matsar kwalla, Maryam ta kalleshi ta ce
“Ka daina kuka ka ji, Zata samu sauƙi”
Cikin kuka ya ce
“Ammi Auntie Salma ta tashi, Tsolo ina ji ni”
Ya yi maganar cike da yarinta, Da hannu Maryam ta yi masa alama da ya zo, Ya taso ya dawo jikinta. Zaunar tayi kan cinyarta ta rungumeshi tana cewa
“Ai zata tashi, Baka ga doctor ya dubata ba kayi shiru kaji yaron kirki”
Gyaɗa mata kai kawai ya yi yana sauke numfashi ya yi lamo a jikinta.
Ana kiran sallar magriba kiran wayar Hashim ya shigo wayarta, Lokacin tana zaune gefen Salma wadda har sannan take bacci, Ɗaukan wayar ta yi daga ɗaya ɓangaren Hashim ya ce
“Na dawo gida ban ganku ba lafiya dai?”
Maryam ta sauke nunfashi sannan ta ce
“Abu Salma ce bata da lafiya muna asibiti”
“Subhanallahi, Wane asibiti?”
Maryam ta ce
“Muna Emar clinic”
Okay ya ce sannan ya kashe wayar, Maryam ta sauke wayar tana kallon Salma wadda take sauke numfashi dakyar, Tunanin abin da ya sameta take yi, Ko garin yaya ta fadi haka Allah masani. Mai da Idanunta kan Khalil ta yi wanda ya yi bacci a wajen har sannan uniform ne a jikinsa, Tashi ta yi ta shige toilet ɗin dakin ta ɗauro alwala, Ɗankwalinta ta shimfiɗa dan daman hijabi ne a jikinta ta gabatar da sallar, Tana idarwa wayarta ta fara ƙara, Ɗauka ta yi ganin Hashim ne, Bayan ta ɗaga ya tambayeta inda suke ta faɗa masa, Ba'a fi mintuna biyu ba ya shigo ɗakin.
Gaban gadon ya ƙarasa yana cewa
“Garin Ya ya haka ta faru?”
Maryam dake ɗaura ɗankwalinta ta ce“Wallahi nima ban sani ba, lafiya na fita na bar ta a gidan naje ɗauko Khalil a school kawai muna dawowa sai na ganta kwance a ƙasa kanta a fashe kuma babu kowa a gidan nayi ƙoƙarin kiranka wayarka kuma not reachable shi ne na fita na samu mai Napep na kawota asibiti, But I don't know what happened”
Hashim ya sauke nunfashi sai kuma ya ce
“Ina Zayyad?”
Maryam ta ce“Ban gashi ba, Bama ya gidan fa sanda muka fito, ko yanzu ka ganshi?” Girgiza kai Hashim ya yi ya ce“Babu kowa a gidan ko yanzu, kuma ban ma gan shi a Kofar gida ba”
Maryam ta yi shiru tana tunani can kuma ta ce“Allah yasa dai ba wani gurin ya yi ba to”
“Ameen”
Hashim ya faɗa, Doctor ne ya shigo ya kallesu ya ce“Ya mai jikin?”
“Da sauki Alhamdulillah”
Hashim ya bashi amsa, Sake dubata ya yi sannan ya kalli Hashim ya ce“Yawwa oga ka sameni a office” Okay Hashim ya ce sannan ya fita shi kuma ya bi bayansa.
Doctor ya kalli Hashim bayan ya zare glasses ɗin idanunsa ya ce
“Garin ya ya aka yi mata haka? An shaƙe wuyanta ya yi yawa wanda har ya kusa sanadiyar rasa ranta”
Da mamaki Hashim ya ce
“Shaƙe wuya kuma doctor? Ita Salman?”
Jinjina kai likitan ya yi ya ce“Eh, Sannan bayan haka ta fadi da kanta sosai, Saboda haka a dinga kula gaskiya. Ga wasu magunguna a siya mata su, Idan ta farka kuna iya tafiya gida”
Okay Hashim ya ce sannan ya amshi takardar, Ya ɗan duba sai kuma ya miƙawa likitin hannu suka gaisa sannan ya tashi ya fita.
Ɗakin ya koma ya samu Maryam zaune tana danna wayarta, Tana ganinsa ta ajiye wayar tana cewa “Ya ake ciki?”
“Wai shaƙeta aka yi, Amma wane zai shaƙeta?”
“Shaƙewa kuma? Salma ɗin?”
Hashim ya gyaɗa mata kai, Shiru Maryam ta yi can kuma ta ce”To ko dai faɗa suka yi da Zayyad? Amma ai naga kamar baya kulata”
Kafin Hashim ya yi magana Salma ta buɗe idanunta tana sauke numfashi a hankali, Khalil ya yi saurin cewa“Ammi kin ga ta tashi”
Daga Hashim har Maryam kallonta suka yi a tare kuma suka ce
“Kin farka?”
Salma ta gyaɗa musu kai tana sauke numfashi, Ƙarasawa Maryam ta yi ta zauna gefenta ta kama hannunta tana cewa
“Sannu Salma, Sannu”
Salma kasa cewa komai ta yi ta lumshe idanunta wasu hawaye suka shiga zubowa gefen fuskarta, Hashim ne ya ƙaraso wajen yana kallonta ya ce“Sannu Salma”
Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta gyaɗa masa kai.
****
Around 9pm suka shigo gidan, Kasancewar lokacin ana sanyi ya sanya unguwar shiru babu kowa. Babu kowa a compound ɗin amma an mayar da shanyar kayan, Hashim ya tsaya yana kallonsu ya ce”Ku shiga ciki bari na nemo Zayyad” Okay kawai Maryam ta ce sannan ta kama hannun Salma da Khalil suka shiga ciki, A parlon suka zauna Maryam ta kalli Salma ta ce”Tashi muje ki yi wanka sai ki ci abinci ki sha magani” Toh kawai Salma ta ce sannan ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin da take kwana. Sai da tayi wanka sannan ta fito tana sanya da wata doguwar riga da Maryam ta bata, Zaune ta samesu suna cin abinci. Ta ƙarasa tana tafiya a hankali, Hashim ne ya kalleta ya ce
“Salma sannu”
Ɗan murmushi ta yi duk yanda bata jin daɗin jikinta ta ce“Yawwa Yaya”
“Zo ki ci abinci”
Maryam ta faɗa tana jawo plate, Jollof rice ce wadda taji kayan haɗi sai kamshi take ta zuba mata, A gefe ɗaya Salma ta zauna ta dinga cin abincin a hankali, Ko rabi bata ci ba ta ajiye, Maryam ta kalleta ta ce
“A'a lafiya dai naga kin ajiye?”
Kamar zata yi kuka ta ce“Na ƙoshi Auntie”
Girgiza kai ta yi ta ce“A'a dai Salma, Da kin cinye”
“Wallahi Aunty na ƙoshi sosai”
Magungunan ta miƙo mata ta ce“Ohya sha maganin sai ki je ki kwanta”
To kawai ta ce sannan ta amsa ta buɗe, Ruwa ta miƙo mata ta ɓalli maganin ta sha ta kora da ruwa. Ganin ta ajiye ledar ya sanya Maryam ta ce”To ki je ki kwanta ki huta”
Tom kawai Salma ta ce duk da yanda take son ta ga Zayyad amma ta miƙe
“Salma”
Taji muryar Hashim ya kirata, Juyowa ta yi tana kallonsa ta ce“Na'am Yaya”
“Ina son magana da ke”
Tom ta ce sannan ta dawo ta zauna, Maryam ta kalleshi ta ce
“Amma ai da ka bari sai da safe ko Abu”
Girgiza kansa ya yi ya ce“Yanzu nakeson maganar ai” Shiru Maryam ta yi dan bata saba jayayya dashi ba, Salma ta koma ta zauna ta yi shiru, Hashim ya dinga kallonta kafin ya gyara zamansa ya maida hankalinsa sosai ya ce
“Salma zan tambaye ki abu ina son ki faɗa min gaskiya”
Toh ta ce kanta a ƙasa, Ya numfasa sannan ya ce
“Su waye ku Salma? Wane Zayyad a wajenki? Me yasa ake nemanku a Abuja?”
# HCD
# Yaya Yad
# Salma
# Nanameera
08106608363.
*HASKEN CIKIN DUHU*