← Book details Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 28

Chapter 19-20: "Stay with me"

Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 17 min read

Nanameera, YOTA/023.


Mutumin ya ja dogon numfashi ya sauke kafin ya ci gaba da fad'in “Nasan kina da haƙuri to ki ƙara, Kina da tausayi to ki ƙara, Akwai abubuwan da zasu faru wanda baza su miki daɗi ba amma dole ne ki yi haƙuri sannan kuma ki jure kowace irin wahala, Tabbas lokaci zai zo komai zai shige kamar ba'a taɓa yin sa ba!”


Ɓat mutumin ya ɓacewa ganinta, Juyi ta shiga yi daga kwancen da take, A firgice ta tashi zaune tana dafe ƙirjinta wanda yake bugawa da ƙarfi, Kallon wajen ta dinga yi tana tunanin abin da mutumin ya ce mata. Daman ba gaske bane mafarki ta yi? Salma ta tambayi kanta, Ganin babu kowa a wajen ya sanya ta sake gazgata hakan, A hankali ta juya Idanunta kan Zayyad. Bacci yake har sannan ya cure jikinsa waje guda da alama sanyi yake ji, Mayafin kanta ta ware ta tashi ta ƙarasa inda yake kwancen ta tsuguna ta rufa masa mayafin. Ajiyar zuciya ya saki yana mai gyara kwanciyarsa ya ci gaba da baccinsa hankali kwance, Numfasawa Salma ta yi sannan ta tashi ta koma in da take ta zauna tana ci gaba da tunane tunane.


****Zaune ya sameta ta zuba uban tagumi, Ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido ba tare da ya ce komai ba. Ganin irin kallon da yake mata ya sanya Salma kallonsa itama a sanyaye ta ce


“Mene ne Yaya yad?”


Langwaɓar da kansa ya yi bai magana ba, Ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta ta ce“Ka zauna a nan naje na siyo mana abinci”


Miƙewa ya yi yana karkaɗe ƙasar jikinsa, Ta kalleshi sai kuma ta ce


“Ka zauna yanzu zan dawo fa”


Maƙale kafaɗa ya yi still looking at her, Salma ta sauke nunfashi sai kuma ta yi gaba shima ya bi bayanta. Duk inda suka shige sai an kallesu dan lokacin safiya ce yara sai tafiya makaranta suke, Ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya tana tunano sanda ita ma take zuwa makarantar, A duniyar Salma idan da abin da tafi ƙauna to karatu ne, Burin rayuwarta taga tana zuwa makaranta ta tara ilimi mai yawa, Sai dai rayuwa kowa da ƙaddararsa ita rashin karatun shi ne ƙaddararta. Ihun da taji ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, Da sauri ta ƙarasa wajen ganin Zayyad ana kokawa dashi da wasu yara.


Sosai jama'a suka fara taruwa ya riƙe kwalar rigar mutumin ya ƙi saki, Ta cikin mutane ta kutsa ta shiga inda suke, Kallonsa ta yi ta ce


“Mene ne haka Yaya Yad sake shi mana”


Ko kallonta Zayyad bai yi ba sai ma sake riƙe shi da ya yi, Salma ta kalli tarin jama'ar dake wajen ta matsa kusa da shi sosai ta ce

“Ka sake shi ko na tafi na bar ka ba zaka sake ganina ba”


Kallonta ya yi da idanunsa wanda suka yi wani irin jaa, Ta jinjina masa kai alamar tabbatar da abin da ta faɗa. Hankaɗa mutumin ya yi ya faɗi ƙasa a wajen, Ya juyo yana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, Ja da baya kowa ya yi aka dara masa hanyar ya yi shigewarsa hannunsa duk biyun bisa ƙugunsa kamar mace. Girgiza kai Salma ta yi sannan tabi bayansa, Sai da suka ɗan yi nisa sannan ta kalleshi ta ce


“Idan kana shaƙe wuyan mutane zan daina tafiya ko ina da kai, Ba'a shaƙe wuyan mutum ko kana son ka yi kisa ne?”


Cak ya tsaya da tafiyar da yake ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“Ni abokin wasansu ne to?”


Sosai ta yi mamakin furucin nasa ta ce


“Me suka yi maka to faɗa min”


Harararta Zayyad ya yi ya miƙi hanya ba tare da ya amsa maganarta ba, Ta girgiza kanta sannan tabi bayansa. Orange market suka je, Ta tsaya gaban masu suyar masa tana kallonsa ta ce


“Na siya maka waina?”


Girgiza mata kai ya yi ta ce“To me zaka ci?”


Ledar biscuit ɗin hannunsa ya nuna mata, Ta amshi ledar ta juyata sannan ta ce“To zan siya maka” Daga haka ta ƙarasa wajen masu suyar wainar, Sai da ta siya masu wainar sannan ta dawo inda yake tana kallonsa ta ce“Tsaya a nan naje na siyo maka biscuit ɗin a shagon can” Ta ƙare maganar tana nuna masa shagon dake gefen hannun hagunta. Daga haka ta yi gaba, Biyota taga ya yi ta tsaya ta ce“Ba zaka jiranin ba?” Gyaɗa mata kai ya yi ta ce“Tom muje”.


Tunda ta shiga shagon yake kallonta, Salma da bata lura dashi ba ta miƙawa mai kantin kuɗi ta faɗa masa abin da zai bata, Kamar daga sama taji an ce


“Salma!”


Da mamaki ta juyo dan ganin wanda ke kiran sunanta, Sakar baki ta yi tana kallonsa shi kuma ya yi mata murmushi.


A nutse ya ce


“Rufe bakin mana”


Kunya ce ta rufeta ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, Dariya mara sauti Al-ameen ya yi kafin ya ce“Ina ki ka tafi na daina ganinki? Naje gidanku aka ce wai kun tashi meya faru Salma?” Numfashi ta sauke kafin ta ce“Abbana ne ya rasu shiyasa, Ni yanzu ma banida gida ai” Da mamaki ya ce“Kamarya baki da gida, A ina ki ke kwana kenan?” Ɗan murmushin yaƙe ta yi ta ce“A waje, Ina dai neman inda zan zauna ne”


Shiru Al-ameen ya yi yana nazarin kalamanta, Da gaske babu wasa ko ƙarya a ciki, Sai dai mamaki ya ishe shi daman yarinya mai shekaru irin nata zata iya wannan rayuwar?


“Sai anjima”


Maganar Salma ta dawo dashi daga tunanin da yake. Girgiza kansa ya yi a sanyaye ya ce


“Why not ki zo gidanmu Salma, Mami na da kirki zata riƙe ki kamar ya”


Wani irin abu taji ya tokare mata a ƙirji, Zuwanta gidansu Zayyad ya faɗo mata a rai. Hawaye yaga tana yi ya girgiza kansa a ruɗe ya ce“A'a Salma yi haƙuri idan hakan ya ɓata miki rai, Idan baki so ba sai kin zo gidanmu ba”


Goge hawayenta ta yi cikin shassheƙar kuka ta ce“Nagode sosai da niyyar taimakona amma ba zan iya zuwa gidan kowa ba, So nake na samu inda zan dinga aiki ana biyana na samu na kama mana gida”


Al-ameen ya ce“Au bake kaɗai ba ce?”


Saurin kallonsa ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“Ni kaɗai ce mana”


Jinjina kansa ya yi ya ce“Shikenan yanzu kamar nawa ki ke ganin zai isheki ki kama gidan?”


Kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta ce“Nima ai ban sani ba fa”


Ɗan murmushi Al-ameen ya yi ganin yanda ta yi da fuska ya ce“Alright, Zaki jirani a nan yanzu na dawo?” Numfasawa ta yi sai kuma ta gyaɗa masa kai. Murmushi ya yi ya nuna mata bencin dake wajen ya ce“Oyah sit I'll be back right” Jin jina kanta kawai ta yi ya juya ya bar kantin.


****Tana nan zaune har bayan mintuna talatin kafin Al-ameen ya yi parking motarsa ya fito, Ƙarasowa ya yi yana murmushi ya ce“Sorry na bar ki kina jira” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Har na gaji kuma

Jakar hannunsa ya miƙa mata ya ce“Nasan zai iya isarki ki kama gida har na shekara biyu, sauran kuma sai ki siya abinci, Iya ka abin da nake da shi kenan Salma, Duk mun zuba kuɗin a company”


Bata san sanda ta fara hawaye ba, Ta girgiza kanta cikin shassheƙar kuka ta ce“Har abada ba zan manta da abin da ka min ba Yaya Al-ameen, Idan na samu dama zan saka maka in sha Allahu, Allah ya biya ka” Lumshe idanunsa ya yi ya ce“Ameen Salma”


Ya miƙa mata wani kwali yana murmushi ya ce“Ki rike wannan wayar a hannunki na dinga kiranki”


Amsar kwalin wayar ta yi ta shiga jujjuya shi sai kuma ta ce“Tom in sha Allah Yaya” Murmushi ya yi ya ce“Tom Allah ya sake haɗa fuskokinmu”


Gyaɗa masa kai ta yi still smiling ta ce“Ameen ya rabbi”


Daga haka ta tashi daga zaune da take ta ɗauki ledojinta ta yi gaba tana tafe tana waiwayensa. Sai da ya ga ta nufi hanyar Kabayi sannan ya sauke ajiyar zuciya ya koma in da ya yi parking motarsa ya shiga.


Tafiya kawai take tana dube-dube a hanya ko Allah zai haɗata da Zayyad, Sai dai iya dubanta bata gansa ba har ta ƙarasa inda suke zaune kwana biyun nan.


Zaune ta sameshi ya kifa fuskarsa a tsakanin cinyoyinsa, Da sauri ta ƙarasa gabansa ta dire ledojin hannunta da jakar kudin tana murmushi ta ce


“Yaya yad ɗago kaga, Na samar mana kuɗi zamu je mu siya gida”


Banza ya yi mata bai ɗago kansa ba ta sake masa magana, A fusace ya ɗago ya hankaɗeta daga kusa da shi, Da mamaki Salma ke kallonsa ganin yanda idanunsa suka yi wani irin ja jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, Jiki a sanyaye ta sake nufo shi muryarta na rawa ta ce


“Yaya Yad, Mene ne haka?”


Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa. Ta sake matsawa daf dashi kamar zata yi kuka ta ce“Meyasa ka ke fushi dani to?” Ɗauke kai Zayyad ya yi yana kallon gefe, Salma ta yi shiru sai kuma ta janyo kansa gaba ɗaya ta ce“Yaya Yad ɗinaa, Ka yi haƙuri kaji, Na siyo maka biscuit ɗin fa” Kallonta ya yi sai kuma ya sake ɗauke kansa yana magana ƙasa ƙasa, Girgiza kai Salma ta yi ta janyo ledar da tazo da ita ta buɗe. Biscuit ɗin ta ɗauko ta miƙa masa tana murmushi, Kallon ledar ya yi sai kuma ya kalleta, Ta gyaɗa masa kai tana murmushi, Ya sanya hannunsa ya karɓi biscuit ɗin sannan ya ce


“Da kin siyo mana ki ka bar mu a tsaye, Shi wannan likitan da kike magana dashi ai na sanshi”


Sai a sannan ta gane dalilin fushin nasa, Ta yi murmushi ta ce“A ina ka san shi?” Farke ledar biscuit ɗin ya yi ya ɗauki ɗaya ya kai baki sannan ya ce“Na taɓa masa allura” Salma ta girgiza kanta dan ta gane zancen soki burutsu yake ta ce“Tom shikenan kaci biscuit ɗin zan je na dawo” Gyaɗa mata kai ya yi ta tashi ta ɗauki jakar da Al-ameen ya a bata ta bar wajen, Ta yi nisa sosai ta ji ya ƙwala mata kira ya ce


“Kar ki daɗe ki bar mu”


Murmushi ta yi ta ɗaga masa hannu sannan ta juya ta ci gaba da tafiya, Shi kuma ya mayar da hankalinsa kan abin da yake.


Yawo Salma ta dinga yi cikin Kabayi, Har wajejen ƙarfe 12pm tana tafiya daga nan taje nan, Daga ƙarshe kawai ta yanke shawarar zuwa gidan Hajiya Turai ƙawar Ummarta.


Da sallama ta shiga gidan, Babu kowa tsakar gidan sai tarin datti da kayan wanki dan daman Hajiya Turai gwanar ƙazanta ce, Sai da ta yi sallama sau biyu kafin ta ɗaga labule ta fito, Da mamaki take kallonta kafin ta ce


“Wa nake gani kamar Salma?”


Murmushi Salma ta yi ta ƙaraso ciki ta tsuguna ta gaisheta, Cikin fara'a ta amsa tana cewa


“Daman kina nan Salama?”


Jinjina kai Salma ta yi ta ce“Eh, Umma ina nan, Daman zuwa nayi na tambayeki”


Hajiya Turai ta ce“To Salama shigo ciki” Daga haka ta nufi cikin ɗakin, Tsaf ɗakin yake saɓanin tsakar gidan, Salma ta zauna gefen kujera ita kuma Hajiyan ta shiga cikin kitchen, pure water mai sanyi ta ɗauko ta kawo mata sannan ta zauna tana cewa


“Ina jin ki Salama”


Numfasawa Salma ta yi kafin ta ce


“Umma daman ina son ki haɗani da waɗanda zan samu gida a wajensu na haya ina son na kama na dinga zama a ciki tunda Ummana ta tafi ta bar ni”


Shiru Hajiya Turai ta yi na wasu sakwanni kafin ta ce“Ke kaɗai zaki zauna Salama?”


Salma ta gyada mata kai a hankali, Numfashi ta sauke kafin ta ce“Kuma a garin nan?”


Nan ma Salma ta gyada kai, Girgiza kai Hajiya Turai ta yi ta ce“A'a garin nan ba zai miki ba ki zauna ke kaɗai a gida Salma, Kin san dai yanayin tarbiyyar nan, Ni a ganina ki bar garin nan kamar zai fi miki”


Shiru Salma ta yi tana tunani, Ita dai Hajiya Turai ta tsaya tana kallonta can ta ce“To Umma idan na bar garin nan ina zance?” Gyara zama Hajiya Turai ta yi ta ce“Yawwa ƴar gari, Akwai wani gidan haya dana sani zaki iya zuwa can ki zauna. Ɗaki ɗaya ya isheki”


Salma ta kalleta kafin ta ce“A wane gari ne Umma?”


Hajiya Turai ta ce“Cikin Kaduna ne”


Salma ta kalleta ta ce“Umma bai yi nisa ba, Ban san kowa ba a can”


Murmushi Hajiya Turai ta yi ta ce“Shi ne zaki rayu ba tare da wata matsala ba Salma, A nan kowa ya sanki, Zama ke kaɗai a gidan haya zai sanya idanun mutane ya koma kan ki, Amma idan ki ka bar gari babu wanda ya sanki”


Salma ta yi shiru tana tunani, Tabbas abin da Hajiya Turai ta faɗa mata shi ne zai fi dacewa da ita. Bayan wasu mintuna ta ce“Tom Umma na yarda zan ɗauki shawararki” Jinjina kai ta yi ta ce“Yawwa Salamatu, Yanzu ki yi wanka dan naga kamar da datti jikinki sai na baki kayan Fati ki saka” Godiya Salma ta yi, Ta tashi ta shiga ɗaki.


****
Abacha road, Mararaba.


Taɓe baki Mami ta yi hannunta riƙe da glass cup mai ɗauke da smooth ta kalli Fatiha ta ce“Haka aka ce miki?” Cikin shassheƙar kuka Fatiha ta ce“Wallahi haka ne Mami, Ni daman tun da naga yarinyar nan naji bata kwanta min ba. Babu yanda ban yi da Nayla ba amma ta kafe ai mutuniyar kirki ce. Ni ban san ma in da Yaya Zayyad ya samota ba!”. Mami ta ce“To kin san gidansu ne a nan ɗin?” Girgiza kai Fatiha ta yi ta ce“Ni ban sani ba Mami, Sai dai ko ita Nayla”. Ahmad ne ya ce“Ni fa nagane yarinyar, Ranar da muka je Orange market ita ce ta masa rashin kunya, But I don't know what comes over his mind da har suka sake haɗuwa ba har ma ya kai ta gidansu”


“Ba sonta yake ba?”

Al-ameen ya yi maganar yana saukowa daga stairs, Kallonsa Mami ta yi sai kuma ta ce“Haka ya ce maka? Zayyad ne zai ce yana son yarinya yar middle class kamarta”


Numfasawa Ahmad ya yi ya ce


“That's what I'm thinking too Mami, Zayyad fa baya ƙaunar yarinya mara aji, Duk yaran da zaki ga yana dating dasu ya'yan manya ne kamarsa, I'm just confused wallahi”


Fatiha ce ta yi saurin cewa“Wallahi ni fa yaya ina ganin da gaske aikota aka yi ta haukata shi, Tun da ba zai rasa maƙiya ba”


Mami ce ta ce“Ni ku bar wannan maganar dan Allah, Ɗazu mun yi waya da Khadijah ta ce an baza securities za'a gan shi soon, Har hoton yarinyar an baza”


Al-ameen ne ya kalli Fatiha ya ce“Kina da pic ɗin yarinyar, Ni ban santa ba”


Ya ƙare maganar yana zama kan kujera, Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta janyo wayarta akan table ta shiga gallery, WhatsApp pictures ta shiga ta yi scrolling kafin ta zo kan hoton wanda yake ita da Nayla ne. Miƙa masa ta yi tana cewa


“Give it a look Ya Al-ameen”


Amsar wayar ya yi, A firgice ya tashi tsaye yana sake kallon hoton


“Salma!”


Maganar ta kufce masa, Kallonsa duk suka yi, Ahmad ya ce“Lafiya?”


Kasa basu amsa ya yi sai sake kallon hoton yake as if his life defend on it, Fatiha ce ta ce“Ka ganta ko yaya, wallahi ta yi kama da yan leƙen asiri daman”


Shi dai Al-ameen bai ce komai ba, Ya sake taɓa daya hoton wanda take ita kaɗai ta yi murmushi, Girgiza kansa kawai ya shiga yi, Ahmad ya taɓa shi ya ce


“Kai me ya dameka? Ka santa ne?”


Gyaɗa masa kai ya shiga yi, Ahmad ya gyara zamansa yana kallonsa sosai ya ce“A ina? Wace ce ita?”


Ajiye wayar Al-ameen ya yi ya ce


“Yaya Na santa fa, Ita ce yarinyar da nake ce muku ina sonta, Sunanta Salma.”


Da mamaki Ahmad ya ce

“Ita ce wadda ka ce kaje gidansu baka sameta ba?”


Ya jinjina kansa, Mami ta ce“To yanzu ina zamu sameta, Tare suka fita da Zayyad so definitely ita tasan inda yake”


A ruɗe Al-ameen ya ce“Nifa i didn't understand wallahi, Yaya ko ɗazu fa na ganta” Miƙewa tsaye Ahmad ya yi yana kallonsa ya ce“A ina? Yaushe? Zaka gane inda ka ganta?”


Kafin yayi magana Mami ta ce“Ahmad ku je tare, Bari na kira Khadijah na sanar da ita” Shi dai Al-ameen kallonsu kawai yake, Mami ta yi dialing numbern Mommah, Kira biyu ta amsa tana zaune gefen gado kusa da General wanda ke kwance hannunsa maƙale da drip a sanyaye ta ce“Mami ina yini” Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce


“Khadijah yarinyar da ake magana a kai Al-ameen ya ce ya ganta ɗazu, Ki sanar da General a turo jami'an tsaro sai a samu a duba duk cikin Mararaban” Kafin Mommah ta yi magana General ya tashi zaune dan wayar a handsfree take. Duk yanda jikinsa yake hakan bai hana shi magana ba, Ya ce


“A ina ya ganta? Kar ku ɗauki wani mataki yanzu zan turo jami'ai” Daga haka ya tashi fizge drip ɗin hannunsa ya yi sannan ya yi waje, Da idanu Mommah ta bi shi, Mami ta katse kiranta.


Mai da Idanunta kan Ahmad ta yi ta ce“Ku je tare dashi Ahmad” Okay ya ce sannan ya kama hannun Al-ameen wanda ya zama kamar statue suka nufi hanyar waje.


****

Hajiya Turai ta rakota har soro tana cewa“Duk yanda ake ciki idan kin je ki sanar dani Salma” Gyaɗa mata kai Salma ta yi ta ce“Tom Umma in sha Allah zan kira ki, Sai an jima” Suka sake sallama sannan ta fito daga gidan, Gaba ɗaya hankalinta ya yi kan Zayyad dan haka ta dinga sauri har ta fito titi. Motocin sojoji ta dinga gani suna shigewa convey ya cika ko ina na unguwar, Yara sai kallo suke, Haka kawai taji jikinta bai yarda da motocin ba hakan yasa ta ƙara sauri dan taje ta isa ga Zayyad.


Koda ta dawo wajen zaune ta sameshi da wasu yara suna ta faman wasa sai dariya yake, Asalin kyansa ya sake bayyana. Ƙarasawa ta yi tana murmushi, Yana ganinta ya tashi yana dariya ya ce


“Naga kin sauya fata”


Ya ƙare maganar yana kallon hijabin dake jikinta, Murmushi kawai ta yi ta ce“Wanka nayi, Kazo mu tafi kai ma sai kayi”


Girgiza kansa yayi ya ce


“Ni banaso ba zan yi ba”


Langwaɓar da kanta ta yi ta ce“Haba kai kuwa, Baka son kayi kyau kai ma ka sauya fata irin nawa?”


Shiru ya yi ta sake cewa“Shikenan tawo mu tafi tun da baka so” Sai a sannan ya saki murmushi sannan ya ƙaraso, Hannunta ta miƙa masa ya riƙe sannan suka fara tafiya. Hira ya dinga yi mata duk da bata gane inda zancen nasa ya dosa a haka har suka ƙaraso bakin titi. Wani gidan wanka ta gani ta kalleshi ta ce


“Kana son ka ci gaba da bina?”


Gyada mata kai ya yi kamar ƙaramin yaro, Ta ce“To mu shiga nan ka yi wanka kaji Yaya Yad ɗina” maƙale kafada ya yi, Ta saki hannunsa ta ce“To ka yi tafiyarka kar ka sake bina” Daga haka ta juya ta ci gaba da tafiya. Bin ta ya yi da idanu sai kuma ya tsaya, Sai da tayi nisa sannan ta waigo ta hangeshi tsaye in da ta bar shi, Numfasawa ta yi sai kuma ta ci gaba da tafiya. Bayan two minutes ta sake juyowa sai dai bata ganshi ba, Da mamaki ta dinga kallon inda take hangensa da, Kawai ta dawo wajen, Dube dube ta shiga yi amma bata ganshi ba, Nan da nan hawaye suka fara sauka kan fuskarta. Ta dinga kiran sunansa tana kuka kamar itama na neman zarewa. Kamar daga sama taji dariyarsa, Ta juyo ta kalleshi, Dariya sosai yake ya riƙe ƙugu, Ba zaka taɓa ɗauka mahaukaci bane, Da gudu ta ƙaraso gabansa kawai ta rungumeshi tana sakin kuka.


Shi dai Zayyad tsayawa ya yi yana kallonta, Bayan wasu sakwanni ta ɗago kanta har sannan da hawaye a fuskarta cikin kuka ta ce“Yaya Yad ka bani tsoro, Kar ka sake yimin irin haka dan Allah” Kamar daga sama ta ji ya ce


“Ba tafiya zaki yi ki bar ni ba Mommah?”


Girgiza kanta ta yi ta ce“Wasa fa nake maka, Ba zan taɓa tafiya na bar ka ba”


“Alƙawari?”


Zayyad ya faɗa a nutse yana miƙo mata tafin hannunsa. Gyaɗa kanta ta yi tana hawaye ta ɗora nata hannun ta ce“Eh nayi maka alƙawari ba zan taɓa barinka ba Yaya Yad, Zan zauna da Kai a duk yanda ka ke” Ya saki dariya yana tafa hannu, Itama murmushin ta yi sannan suka ci gaba da tafiya, Napep ta tsayar musu ta ce tasha zai kai su, Sannan suka shiga, Basu yi nisa ba suka iske tarin motoci da babura duk a cunkushe, Sojoji sai yawo suke a tsakanin kowa ce mota ana cajesu, Salma ta kalli Zayyad wanda ke kallon tit yana dariya abin sa, Ta sunkuyar da kanta tana hawaye dan tasan shikenan yanzu za'a rabata dashi, Ta sake kallonsa taga ya ƙura mata ido, Ta sakar masa murmushi hawaye na biyo kan fuskarta.


# HCD
# Light within the darkness
# Yaya Yad
# Salma
# Nanameera
08106608363.

*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 18 · 0% Book details