← Book details Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 28

Chapter 33-34: A twist of fate

Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 16 min read

Nanameera, YOTA/023.


Malam ya juyo yana kallonta, kuka take sosai kamar zata shiɗe, ya girgiza kansa cikin natsuwar data gama ratsa shi ya ce“ba zan yarda da wannan amincewar taki ba, domin yanda ki ke kuka ya nuna ba so ki ke ba, kina ganin kamar an miki dole ne. Ni kuma ba zan taɓa yi miki dole ba Ummulsalma, saboda haka ki yi tafiyarki shi ma zan mayar dashi ga iyayensa”


Durƙushewa ta yi a ƙasa cikin shessheƙar kuka ta ce“dan Allah Malam kada ka rabani dashi, ba ina kuka bane saboda na amince, ina kuka ne saboda tunanin abin da zai je ya dawo. Malam idan auri Yaya Zayyad a yanzu ba tare da yardarsa ba, duk ranar daya dawo cikin hayyacinsa zai iya cewa bai yarda ba. To ya zan yi Malam?”


Numfasawa Malam ya yi yana kallonta cike da tausayawa, ya ɗan yi jim kafin ya ce“idan har kina ganin akwai damuwa to kawai a haƙura, ki yi tafiyarki ko kuma ki bini na mayar daku gidansu”


Ɗago kanta ta yi da sauri ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a malam ba zan iya komawa gidansu ba, kasheni zasu yi. Na yarda zan auri Yaya Zayyad kuma zan zauna dashi a kowane irin yanayi”


Malam ya dinga kallonta yana nazarin kalamanta kafin ya furzar da iska daga bakinsa“shikenan ki shiga ciki zuwa gobe da safe sai a ɗaura auren ku tafi”


Tashi ta yi daga durƙushen da take ta ce“malam ba za'a iya ɗaurawa yanzu ba mu tafi? Bana son na sake kwana a garin nan” malam ya yi shiru can kuma ya ce“to tunda haka ne shiga ciki ina zuwa” to kawai ta ce sannan ta nufi ƙofar gidan, har ta shiga soron ya kira sunanta, ta juyo bayan ta amsa ya ce


“kar ki ce musu wani abu akan su Maryam, kawai ki yi shiru” toh kawai ta ce sannan ta shige cikin gidan. Ya kalli Zayyad da ke tsaye kamar statue yace“mu je ka rakani" langwaɓar da kai ya yi sannan ya yi gaba Malam yana biye dashi.


Koda ta shiga gidan kowa na ɗakinsa saboda ɗan sanyin da ake, ta nufi ɗakin Ummar Maryam, sai da tayi sallama sannan ta ɗaga labulen. Umma dake zaune gefen kujera ta ce


“a'a Salma ke ce da magribar nan?”


Sai da zauna sannan ta ce“Eh Umma, nazo wajen Malam amsar wa Yaya Zayyad rubutu shi ne na shigo”


“Malam ɗin baya nan kenan?”


Girgiza mata kai ta yi ta ce“A'a na ganshi cewa ya yi na ɗan jira shi zai je ya dawo”


Umma ta jinjina kanta ta ce“Eh to sai ki jira shi” Daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin. Ba'a fi minti biyu ba ta dawo hannunta riƙe da plate ta ajiye gaban Salma ta koma ta zauna. Shinkafa da wake ce wadda taji salad da yaji a gefe, Salma ta yi murmushi ta ce“Umma ai na ƙoshi fa” wani kallo ta yi mata tana taɓe baki ta ce“naga kin rage min ko kaɗan ne sai ranki ya ɓaci” langwaɓar da kai Salma ta yi ganin yanda Umma ta haɗe rai ya sanya ta ɗauki spoon ɗin kan abincin ta yi bismillah ta fara ci.


****

Jiddah tsayawa ta yi da folding mayafin da take tana kallon Suhaila, ganin irin kallon da take mata ya sanya Suhaila ta ce“baki yarda bane wai?” babu yabo babu fallasa Jiddah ta ce“na yarda mana” Suhaila ta yi murmushi sannan ta ce“Auntie Jidda kenan, ni nasan baki yarda ba wallahi” taɓe baki Jiddah ta yi ta buɗe press ta ajiye mayafin sannan ta ce“ni kin isheni da magana, ki fita please”


Turo baki Suhaila ta yi ta ce“kai Auntie, Mummy ce fa ta ce nazo na kira ki”


“but I'm doing something ai, ki ce ina zuwa”


Suhaila ta ɗan kwaɓe fuska sai kuma ta ce“to ni na tafi, kuma ba zan sake dawowa ba ma” daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin. Jiddah ta sauke numfashi ta ci gaba da folding kayan nata har ta gama sannan ta zauna gefen gadon, dafe saitin zuciyarta ta yi jin yanda take mata wani irin zafi, ta tashi ta nufi hanyar toilet tana tafiya a hankali. Jikin sink taje ta zubawa mirror idanu, hannunta ta kai ta taɓa ƙashin da ya yi mata sarƙa a wuya, hawaye ya fara zuba akan fuskarta


“Ba zan bar shi ba, I'll definitely take my revenge”


Jiddah ta yi maganar cikin shessheƙar kuka. Amai ne ya tawo mata ta sunkuya da niyyar ta yi sai dai madadin ta ga aman sai taga jini na fitowa daga bakinta, ta dinga aman jinin har da guda-guda. Sai da ya daina fitowa sannan ta kunna tap ta wanke bakinta, idanunta ya yi wani irin fari ta ɗago kanta hawaye na ci gaba da bin fuskarta.


“Jiddah! Jiddah! Jiddah”


Muryar Mummy ta daki kunnuwanta, da kyar ta sauke numfashi sannan ta wanke fuskarta ta nufi hanyar fita daga toilet ɗin, tana buɗe ƙofar Mummy ta dinga kallonta kafin ta ce


“lafiyar ki klao?”

She just nodded her head dan bata jin zata iya magana, ta nemi kan sofa ta zauna tana sauke numfashi. Mummy ta ƙaraso gabanta ta dafata a sanyaye ta ce“Jiddah! Jiddah!”


In a very cool voice ta ce“na'am Mummy”


”tell what wrong with you? Kar ki ce zaki min karya ko kuma ki ɓoyemin abin da ke damunki, I'm ur mother, baki da wadda zaki faɗawa matsalarki sama dani Jiddah. Saboda haka just tell me the truth”


Yanda Mummy ta yi maganar ya sanya jikinta ya yi sanyi, ta ɗago runannun idanunta ta kalleta amma ba ta ce komai ba. Mummy ta zauna gefenta ta janye hannayenta duk biyun ta rike cikin nata ta ce“Jiddah kin san na damu dake ko? Kin san bana son abin da zai taɓa ki ko? But why ba zaki bar ni na huta ba? Ina lura da ke tun lokacin da aka ce Zayyad ya ɓata baki sake samun kwanciyar hankali ba. Jiddah yau idan ciwonki ya tashi sai nafi kowa shiga tashin hankali kin san da haka? Kina jin mahaifinki ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu kuma zasu samo shi, amma kin ƙi yarda, kin ƙi kwantar da hankalinki. Me yasa Jiddah!? Baki son ganina cikin kwanciyar hankali ne?”


Madadin ta amsa duk maganganun Mummy sai kawai ta faɗa jikinta tana fashewa da wani raunataccen kuka, rungumeta Mummy ta yi tana jin yanda take kuka kamar ranta zai fita, above 5mins kafin ta fara sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kukan ta ce


“Ki yi haƙuri Mummya, hankalina ya kasa kwnaciya ne, dan Allah ki tayani da addu'a ji nake zuciyata kamar zata fashe, ƙirjina nauyi yake min Mummy, idanuna...” ta kasa ci gaba da maganar saboda sabon kukan daya tawo mata.


Mummy ta dinga kallonta jiki a sanyaye, sai kuma ta girgiza kanta muryarta kamar mai shirin fashewa da kuka ta ce“shikenan Jiddah tun da ba zaki iya faɗa min damuwarki ba zan taya ki da addu'a, Allah ya yaye miki abin da yake damunki, ya bar ki da alherin rayuwa a duk yanda yake. Amma ki sani idan har ki ka cutar da kan ki ba zan taɓa yafewa kaina ba, kuma ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba”


Daga haka ta janyeta daga jikinta ta tashi ta fice daga ɗakin, Jiddah ta dinga kallon Mummy kamar ta je ta sameta ta sanar da ita duk abin da yake damunta, sai dai hakan ba abu bane wanda zai taɓa yiwuwa ba!. Ba zata taɓa iya faɗawa Mummy wannan damuwar ba sai dai ta bar ta cikin ranta har ta yi ajalinta. Ta sulale ƙasan tiles tana sake rushewa da wani sabon kukan...


Mummy na fita ta tsaya a corridor tana goge hawayen daya zubo kan farar fuskarta,


“Hafsa!”

Taji muryar General Kabeer ya kirata, muryarta na rawa ta ce“Na...na'am..”


Takowa ya yi har in da take ya dinga kallonta da mabayyanin mamaki kafin can ya ce“lafiya? Kukan me ki ke yi?”


“Dan girman Allah general ku sake tsaurara bincike akan neman Zayyad, dan Allah ku dawo dashi ko na samu hankalin ƴata ya kwanta, idan har wani abun ya sameta ba zan iya rayuwa ba...” ta ƙare maganar kuka na kwace mata, General Kabeer ya dinga kallonta sai kuma ya ce“ku mata meyasa mentality ɗinku iri daya ne? Kema zaman kukan ki ke saboda tana yi kenan, kun san irin neman da muke masa? Kun san abubuwan da muka jingine kawai saboda bincike akan inda ya shiga? Tun da har aka ce za'a dawo dashi ba shikenan ba, Please Hafsa ki daina biyewa magana ta yara, in sha Allah nan bada jimawa ba Zayyad zai dawo kuma za'a fita dashi domin samar masa da lafiya, so you don't need to be worry dan Allah, idan kuma kinason depression ya kama ki ne to”


General ya ratsa ta gefenta ya nufi downstairs, da idanu kawai Mummy ta bishi sai kuma ta yi hanyar nata dakin har sannan kuma bata daina kukan ba.


****
Mami ta girgiza kanta ta ce“ba haka ya kamata ayi ba, wannan abun da general yake ba shi ne daidai ba, akan me zai je ya ɗauko mata da ɗanta da mijinta saboda an ce an ga su Zayyad a gidan? Idan kuma ƙarya ake fa? Koma a ce gaske ne tunda shi bai gansu a gidan ba ai babu hujjar da zai sa a kamasu”


Mommah ta sauke numfashi ta ce“to me zan ce Mami? Bai ma bani listening ear ba, kin san dai halin general ba'a sauya masa ra'ayi ko nayi magana baya ɗaukanta mai amfani” Mami ta yi tsaki ta ce“zama da Idris ko ƙaddara! Yanzu mene ne abin yi?”


Mommah ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“Ni da cewa nayi ko muje gidan Malam Barau a ɗan taya da addu'a Mami ko a samu a ganshi” Mami ta ɗan yi murmushi ta ce“idan har addu'a ce to kawai mu yi anan ni bana son harkar malaman nan” toh kawai Mommah ta ce parlon ya ɗauki shiru kowa da abin da yake sakawa cikin zuciyarsa. Mommy ce ta buɗe ƙofar ta shigo tana sanye da wani ubansu lace mai azabar kyau ɗinkin boubou ta ɗaura ɗankwalin lace ɗin ta yafa mayafi sai tashin ƙamshi take daka ganta ka ga matar manya. Har ta zauna akan sofa babu wanda ya ce wani abu ta yi murmushi tana kallon Mami ta ce“Afuwan hajiya sanda ki ka shigo ina wanka” sai a sannan Mami ta kalleta ta ce“Ai babu komai, Mun sameku lafiya?” Mommy ta ce“Lafiya Alhamdulillah ya yaran?”


“Suna nan klao”

Mami ta faɗa sai kuma ta yi shiru, jinjina kai Mommy ta yi ta maida idanunta kan Mommah wadda ta rame sosai kamar ba ita ba ta ce“daman zamu je gurin waɗanda aka kamo ne daga Kaduna, shi ne nace ko kema zaki je?”


Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“a'a ba zan je ba, bana son haɗuwa da kowa wallahi”


Mommy ta yi shiru can kuma ta ce“Da dai kin daure mun je, kin ga ko wata tambayar ce kya yi musu” Mommah ta sake girgiza kanta ta ce“a'a fa kawai ku je, wallahi bana son ganin kowa, ko magana wahala take min”


Mommy ta numfasa sai kuma ta ce“tom shikenan, Allah ya shige mana gaba sai mun dawo”

“Amin, Allah ya tsare”

Amin ta ce sannan ta nufi ƙofa, Sai da ta fita sannan Mami ta kalli Mommah ta ce“why ba zaki bi su ba?”


“Mami bana son ganinsu, bana son ina tunawa da wasu abubuwan, babu wanda yanzu nake fatan nagani sama da Zayyad”


Mami ta ce“Idan har kina son ganin Zayyad to tabbas zaki so ganin waɗanda suka gan shi, ko babu komai zaki tambayesu halin da yake ciki”


Kallonta kawai Mommah ta yi amma bata ce komai.


****
Kaduna, Unguwar rigasa.


Ana idar da sallar isha'i aka ɗauren Salma da Zayyad akan sadaki naira dubu hamsin wanda Malam ya biya, koda suka dawo gidan tana zaune kan ladduma bayan ta idar da sallar isha, Malam ya sanya aka kirata tsakar gida, fitowa ta yi ta tsuguna muryata a sanyaye ta ce“Baba gani”


Kallonta ya yi sai kuma ya ce“Alhamdulilahi, an ɗaura aurenki da Muhammad yanzun nan, ga kuma sadakin ki” ya miƙa mata kuɗin hannunsa. Hannunta na rawa ta amsa sai kuma ta sunkuyar da kanta, Malam ya sake cewa


“Ku bari da safe sai ku tafi”


Salma ta ɗago ta kalleshi, bata son musu dashi haka kuma bata jin zata iya kwana a cikin gidansa dan a kowane lokaci ana iya zuwa nemansu. Ta girgiza kanta muryarta na rawa ta ce“dan Allah Malam ka bari mu tafi yanzu, wallahi bana son sake kwana anan”


Ganin yanda ta damu sosai ya sanya ya jinjina kansa ya ce“shikenan Ummulsalma, zan bari ku tafi amma bana so ku yi nesa damu sosai, yanda idan wani abun ya faru zan sani” Salma ta ce“Tom Baba, ina Yaya Zayyad ɗin?”


“Yana waje, ki tashi ki je ki mata sallama sai ki zo ku tafi”

Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta koma ɗakin Umma, Sallama ta yi mata da niyyar cewa gobe da safe zata dawo Umma ta ce“tom sai kin dawo ɗin, ki gaishesu” tom ta ce sannan ta juya ta fita tana jin wani iri. Bata samu malam a tsakar gidan ba dan haka kawai ta fice ƙofar gidan. Tsaye ta same shi da Zayyad yana yi masa duk da ba ganewa yake ba. Yana ganin ta fito ya juya ya kalleta ya ce“yanzu daga nan ina zaku je?” girgiza kanta ta yi ta ce“nima ban sani ba Baba, tunani nake”


Malam ya ce“to idan haka ne zan haɗa ku da wani wanda ya san wajen gari sosai sai ya kama muku haya a can ku zauna” Salma ta ce“Tom Baba an gode Allah ya saka da Alkhairi”


Ameen kawai ya ce sannan ya zaro wayarsa ya danna kira, bayan sun gama waya da mutumin ya ce masa gashi nan zuwa ya koma ya zauna yana kallonta ya ce“zauna kema”


Gefe ɗaya ta samu ta zauna, ya yi gyaran murya ya ce“Ina son na tunatar da ke wasu abubuwane, Ummulsalma ki sani yanzu ke matar aure ce, matar auren kuma ga wanda bai san inda hankalinsa yake ba. Na aura miki shi ne saboda addini ya yarda idan har wanda zai yi auren ya ga ya yarda zai iya zama da ɗayan a haka, kamar yanda ki ka yarda zaki zauna dashi da haukansa. Dole ki gane akwai banbanci da wadda take auren mai hankali da kuma wadda take auren wanda bashi da hankali, duk da ina masa fatan samun lafiya nan kusa dan abubuwansa sun fara raguwa, amma ki sani dole sai kin yi haƙuri, dole sai kin jure, dole sai kin ɗauke kan ki akan abubuwa dayawa wanda zai aikata. Sannan duk da bashi da hankali wajibi ne a gareki ki yi masa biyayya kamar yanda addini ya bada umarnin mace tabi mijinta, nasan kina da halin kirki sannan kuma kina da sauƙin kai amma ki ƙara, ki zama macen kwarai ga mijinki, sannan har abada kada ki taba cewa zaki yi masa gori wannan shi ne babban abin da yake lalata zamantakewar aure, ki ɗauka duk abin da kika yi masa dolenki ne kuma haƙƙinsa ne da yake kan ki, Da haka nake miki fatan samun albarka a rayuwar aurenku, Allah ya fitar da ku daga matsalar da ku ka shiga, ya bashi lafiya”


Cikin shassheƙar kuka Salma ta ce“Amin Malam, Mun gode sosai, Allah ya biya ka da gidan aljanna, in sha Allah ba zan taɓa yin abin da zai zama cutarwa a gare shi, zan zauna dashi komai tsanani kamar yanda na yi alƙawari”


Ya jin jina kansa cikin jin daɗi ya ce“Allah yasa Ummusalma”


Amin kawai ta ce sannan ta yi shiru tana tunani cikin ranta, Suna na zaune har wajen 8:30na dare sannan mutumin ya zo, bayan Malam ya yi masa bayani ya ce to su zo su tafi, Sallama suka sake yi da Malam ya rakosu har bakin titi sannan suka tsaida Napep tana ɗaga masa hannu, shima ya ɗaga mata hannun yana yi mata Allah ya tsare mai Napep ɗin ya ja motar, Zayyad ya dinga leƙen Malam fuskarsa a kwaɓe kamar zai fashe da kuka.


****
Maitama, Abuja.


“Wato mahaukaciya ma ka ɗaukeni ina maka magana ka yimin banza ko Farouk? Saboda kaga ina rabuwa da kai ya sanya ka ke min kallon wadda ban san me nake ba ko? Dan kaga na sakko da kaina ko?” Nimrah ta jera masa tambayoyin tana sakkowa daga stairs ɗin, Faruk ya tsaya cak yana kallonta amma bai ce komai ba ta sake cewa “Shikenan ka je kayi aurenka, ba dai aure bane kaje kayi amma na rantse maka da Allah sai dai ka sakeni yanzu kuma ba sai an jima ba. Wallahi sai dai ka sakeni Farouk! Ka sakeni na ce maka!”


Ta ƙare maganar tana shaƙar kwalar rigarsa, Ban da kallonta babu abin da Faruk yake, dan shi gaba ɗaya lamarinta ma tausayi yake bashi. Ya janye hannunta daga jikinsa ya ce“bari mana Nimra, wane irin abu ne wannan?ke ba zaki taɓa barina na samu peace of mind ba kenan, kin dinga takurawa rayuwata kenan”


“Takura, ai to bari kaji baka ga komai ba cikin abin da zan yi maka muddin ka ce sai kayi auren nan Faruk, wallahi ba zan bar ka ka samu kwanciyar hankali ba koda da na second ɗaya ne!”


Girgiza kansa kawai ya yi sannan ya juya ya nufi hanyar main parlon, da gudu ta biyoshi ta riƙe masa riga cikin kuka ta ce“Dan girman Allah Faruk kar ka sake auren nan, ba gashi muna zaman lafiyarmu ba? Ba na daina duk abin da nake ba? Ka yi haƙuri ka bar maganar auren nan dan Allah”


Sosai ta tashi tausayi ya kamo hannunta muryata a sanyaye kuma cikin nutsuwa ya cw“Nimra nima ba wai ina son dole-dole sai na ƙara aure bane, wallahi idan da a ce ta ni ne kin isheni daga nan har lahira, amma wannan auren umarnin Mama ne, kuma ba zan iya tsallake umarninta ba. Dan Allah ki tayani yin wannan aikin kin ji, kar ki sare min gwiwa, farin cikinki shi ne nawa Nimra!”


Zare hannunta ta yi daga cikin nasa, ta girgiza kanta tana hawaye sai kawai ta koma sama da gudu tana kuka, da idanu kawai ya bita, ya sauke numfashi sannan ya juya ya fita.


****
Tun da suka shiga gurin Mommy ke faman kai kawo har sai da aka ce su shiga su gansu, babban ɗaki ne mai ɗauke da sofa guda uku sai carpet da curtains. Maryam ta dinga kallon Mommah ganin yanda take kama da Zayyad sosai, ƙarasawa suka yi suka zauna kan sofa sojoji na tsaye a kansu.


Mommy ce ta kallesu cike da masifa ta ce“Ku yanzu baku ji kunya ba? Aje har garinku a tawo daku saboda kun bawa masu laifi matsuguni, ban da ma rashin sanin abin da ya kamata ya za'a yi ku ga mace da mahaukaci sannan ku bar su a gidanku? Wannan sai dai idan daman can daku a haka haɗa baki aka haukata shi, bari General ɗin ya zo!”


Tun da ta fara magana Mami ke kallonta amma bata ce uffan ba, Maryam kuwa kuka kawai take dan tasan shikenan ɗauresu za'a yi daga taimako, sai dai can ƙasan ranta tana fatan kada su Zayyad su shiga wani hali. Tashi Mommy ta yi tana kallon su Mommah ta ce“Ba zan iya ci gaba da zama cikin ɗakin nan ba, wallahi zuciyata zata iya tarwatsewa!”


Daga haka juya ta fice kamar zata tashi sama, Mommah ta bita kallo sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. Tashi ta yi ta ƙarasa har gaban Maryam, ta zauna ta kamo hannunta cikin wata irin murya mai matuƙar rauni ta ce


“Na san ke uwa ce, ko ba uwa ba ce ke mace ce, nasan kin san zafin rashin ɗa, na san kin san abin da mahaifiya ke ji a lokacin data rasa ɗanta. Bana iya bacci, bana iya cin abinci, bani da kwanciyar hankali, a koda yaushe tunanin halin da ɗana yake nake, zuciyata ta gagara samun sukuni. Da nace ba zan zo ba, amma Yayata ta yi insisting ɗina akan nazo. Tun da na ganki naji na samu gwarin gwuiwa, naji tamkar naga Zayyad, domin na san ba zaki faɗa min abin da ba shi ne ba. Dan Allah dan Annabi ki faɗa min ina Zayyad ya ke? Ina zan samu ɗana? Ki faɗa min dan Allah...”


Maryam ta dinga kallon Mommah tana jin wani irin tausayinta, hawaye na zubowa akan fuskarta ta ce“


# HCD
# Salma
# Zayyad
# Nanameera
08106608363.*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 25 · 0% Book details