← Book details Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 28

Chapter 39-40:

Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 25 min read

Book 1 End


Nanameera, YOTA/023.


Unguwar Rimi, Kaduna state.
Saturday, 8:30am

Hasken sun rays ɗin daya shigo ɗakin shi ne ya sanya ya buɗe idanunsa dan direct hasken kan fuskarsa ya sauka, ya tashi zaune yana mitsitsika idanunsa.


“Morning love”


Ɗago idanunsa ya yi ya kalleta, wata kyakkyawar mace ce tsaye tana sanye da sleeping dress doguwar riga mai sulɓi wadda ta tsaya dai-dai gwuiwarta, baƙaƙen ƙafafunta suka fito sosai sai glowing suke. Tana da siririyar fuska da manyan idanu kamar zasu fito, bakinta mai ɗan fadi ya yi daidai da fuskarta. Ta sakar masa murmushi wanda ya bayyanar da wushiryar da ke tsakanin haƙoranta na gaba, hannunsa ya miƙa ya kamo nata ya jawota gefensa, zama ta yi tana murmushi ta ce“Yau ka yi bacci dayawa fa” jan kumatunta ya yi ya ce“but why u didn't woke me up?” langwaɓar da kanta tayi ta ce“Ayyah gani nayi kamar ka gaji shiyasa na barka ka huta tun da yau Saturday” taɓe bakinsa ya yi ya janye duvet ɗin da ke jikinsa ya zura ƙafafunsa kan floor yana cewa“amma ai zan fita” tashi ta yi tana kallonsa ta ce“tom ka shirya nima daman ina so naje na gaida Hajiya”


“Not today”

Ta ji ya furta sannan ya shige toilet, kallon ƙofar ta dinga yi sai kuma ta girgiza kanta ta juya ta bar ɗakin.


Tana tsaye jikin dining tana jera warmers ya ƙaraso wajen, da sauri ya amshi wani jug daga hannunta yana murmushi ya ce”let me help you ko Beb”


Turo baki ta yi cike da shagwaɓa ta ce“ai kana gani duk nagama ayyukana baka ce zaka tayani ba sai yanzun?”


Dungure mata kai ya yi yana cewa“ke kin fiye rigima ai daman”


Dafe gashinta ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kai Noorie daga wasa?” kujera ya ja ya zauna sannan ya ce“madam ni yanzu nake ji, serve me please” plate ta ɗauko ta buɗe warmer, fried irish potato ne wanda ya yi jar suya ta zuba masa sannan ta buɗe ɗayan ta saka masa wainar kwai, ta tura masa gabansa sannan ta shiga haɗa masa tea. Ganin yanda take masa hira ya sanya ya ce“Kar ki ci ka min sugar”


Da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce“Ni kuma ka ke tunawa Noorie?” Girgiza kansa ya yi ganin yanda ta haɗe rai ya ce“i'm sorry Madam”


Tura baki kawai ta yi ta miƙo masa mug, sannan ta ja kujerar da ke gefensa ta zauna. Da kansa ya jawo mug ɗin ya raba musu shayin sannan ya miƙa mata. Karɓa ta yi tana murmushi ta ce“Good samaritan!” harararta ya yi ya ce“i'm i ur mate?”


“Ayyah dan nace maka yaron kirki?”


“Iyyeh! Ni ne yaron naki?”


Ta marairaice fuska ta ce“to Babba, babban mutum, mijina abin alfaharina, Noorie na abin ƙaunata, Zakina mai tare min faɗa”


Kyakkyawan murmushi Aliyu ya yi ya girgiza kansa yana juya cokalin cikin tea ɗin ya ce“Zakiyyana, Thank you baby”


Lumshe idanunta ta yi ta ce“Ni zan gode maka Noorie” ta faɗa tana ɗora hannunta akan nasa, matse hannun ya yi sannan ya ci gaba da shan tea ɗinsa.


****
Ƙarfe 11:00 na safe ta tura ƙofar ɗakin, zaune ta sameshi kan sofa yana danna system ɗin gabansa. Ta ƙarasa ta zauna gefensa cikin cool voice ɗinta ta ce“wai baka shirya ba? Ni fa sauri nake doctor” kwaikwayon irin maganarta ya yi ya ce“yanzu zan shirya Madam” tuntsirewa ta yi da dariya ta ce“ni ka daina tsokanata” sai da ya rufe system ɗin ya miƙe sannan ya ce“nima ki daina min rigima. Ki je ki jirani nan da 1pm sai mu fita in sha Allah”


Kallonsa ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kawai zan yi gaba sai ka tawo, ni sauri nake naje gurin Hajiya”


Babu yabo babu fallasa ya kalleta ya ce“to ba zaki tafin ba sai kin jirani”


Daga haka ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, tura baki ta yi sannan ta juya ta bar ɗakin.


Turo kofar dakin ya yi ya tsaya yana kallonta ya ce“Taso mu tafi” banza ta yi masa, ya ɗan yi murmushi sannan ya taka har gabanta, kan drawer ya zauna ya leƙa fuskarta. Ganin babu alamun dariya ya sanya ya ce“ko nayi tafiyata ne?” idan gadon da take kai ya amsa ta tabbas ita ma ta amsa maganarsa. Ya tashi yana murmushi ya kama hannunta ya ce“sorry i kept you waiting gani nayi fitar mu da wurin bashi da wani amfani shi ne na ɗan tsaya na ƙarasa wasu abubuwa but sorry”


Ɗago idanunta wanda suka yi jajur ta yi ta kalleshi muryarta na rawa ta ce“ka... kawai baka son naje gurin Hajiya ne shiyasa, tun ɗazu na lura da abin da ka ke nufi, akan me zaka hanani zuwa wajenta? Ko kai kaɗai ta haifa ban da ni”


Aliyu ya dinga kallonta amma bai ce komai ba, ta tashi ta gyara zaman mayafinta wanda da ta sake shi sannan ta ɗauki wayarta gefen madubi ta nufi hanyar waje ba tare da ta sake bi ta kansa ba. Numfasawa ya yi sai kuma ya juya ya bi bayanta, Har suka yi nisa bata ce komai ba ta juyar da kanta ma sai kallon hanya take, gyaran murya ya yi idanunsa zube kan titi shi ma ya ce“Nifa ba wai bana son ki je wajen Hajiya ba ne, kar ki fassara ni. Kawai ɓacin rai ne bana so”


Ta gefen ido ta kalleshi amma bata ce komai ba. Hannunta ya kamo ya riƙe yana matsawa a hankali ya ce“shikenan I'm sorry dear” ɗago idanunta ta yi ta kalleshi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“ni ba haushi naji ba”


Yana sauka daga flyover ya ce“oh really?”


Ɗauke kanta ta yi bata bashi amsa ba shima kuma bai sake mata magana ba har suka ƙarasa GRA ɗin.


Babban compound ne mai ɗauke da part guda uku, kowanne part daidai yake dana ɗan uwansa, ya yi parking motarsa a tsakiyar compound ɗin sannan ya kalleta, girgiza kansa ya yi ganin yanda ta yi shiru kamar mai tunanin wani abu. Ya ɗan yi murmushi ya ce“don't be afraid, okay?” jinjina masa kai ta yi sannan ta buɗe motar ta sauka. Bayan ya rufe motar ya dawo side ɗinta ya naɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce“ina zamu fara shiga?” kallonsa ta yi sai kuma ta ce“sai ma ka tambaya, wajen Hajiya mana” ya ce“okay let's go” daga haka ya kama hannunta, ita dai Zakiyya kallonsa ta dinga yi amma ta kasa ce masa komai.


Sallama ya yi sannan suka shiga parlon, da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce“laaa yaya sannu da zuwa” murmushi ya yi ya ce“auta ina Hajiya?”


“tana sama bari na kirata”


Okay ya ce ta juya ta gudu ta yi upstairs, kallon Zakiyya ya yi ya ce“zauna mana” to ta ce sannan ta zauna kan 2 seater ya zauna a gefenta. After 5mins sai gata ta dawo ta zauna tana ci gaba da danna wayarta,


“Maama ina take?”


Ɗago kanta ta yi ta kalleshi ta ce“Yaya gata nan ta ce min tana zuwa” ko rufe baki bata yi ba suka jiyo ƙarar taku,da sauri ya mayar da idanunsa ga benen. Wata mata ce ta shiga sakkowa fara tas da ita daka ganta ka ga Aliyu ko ba'a faɗa maka ba kasan ita ce mahaifiyarsa, tana da jiki amma ba can ba. Zakiyya ta sunkuyar da kanta tana jan fingers ɗinta, kallonsu ta dinga yi sai kuma ta nemi kujera ta zauna, Aliyu ya ce“Barka da rana Hajiya” Babu yabo babu fallasa ta ce“Ya kuke?” Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya ce“Alhamdulilah”


Zakiyya ta ɗago kanta muryarta na rawa ta ce“ina...ina yini Hajiya?” kallonta ta yi ta ce”lafiya kalao, kina lafiya?”


“Alhamdulilah Hajiya”


Hajiya ba ta sake cewa komai ba ta miƙe tana kallonsa ta ce“toh ku gaida gida” daga haka ta shige ta koma sama abin ta. Sosai jikin Aliyu ya yi sanyin duk da daman yasan hakan zata iya faruwa, ya juya ya kalli Zakiyya yaga tana goge hawaye daga idanunta. Kasa magana ya yi sai kawai ya miƙe, kallon Maama ya yi yaga ta taɓe baki. Ya tashi muryarsa a dake kamar babu komai ya ce“tashi muje wajen Inna” miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta yi waje, yabi bayanta. Tsaki Maama ta yi a fili ta ce“ƙaryar banza”


****
Kallonta ya yi ganin yanda taja ta tsaya, ya ce“muje mana” muryarta na rawa ta ce“a...a'a doctor kaje zan jiraka anan” haɗe ransa ya yi ya ce“innar ce ba zaki gaisar ba? Okay ya yi kyau” daga haka ya nufi cikin parlon, sauke numfashi ta yi sannan tabu bayansa jiki a sanyaye.


Koda ta shiga parlon tsaye ta sameshi Inna har ta fara bashi labari sai murmushi yake. Durƙusawa ta yi a hankali ta ce“Inna ina yini?”


“lafiya”

Cewar inna tana mayar da idanunta kansa, Aliyu ya kalleta ganin yanda ta yi sak sai kuma ya kalli Inna ya ce“mene haka kuma?”


A fusace ta ce“ban sani ba, tambayata ma kake? To ubanka ne, saboda ka mayar damu yan iska gantalallu ya sanya har wani kawo mana ita gida ka ke, wato kowa ma ya gani baka ji abin da aka ce maka ba. To kaje ka ci gaba kuma bari uban naka ya dawo wallahi sai an yita ta ƙare, ba zamu ci gaba da saka maka idanu kana abin da ka ke so ba, zama da juya ko masifa, duk sai ka tsofe a haka babu ya'ya to wallahi baka isa ba, dole sai ka yi aure”


Wani irin kallon ya dinga yi mata sai kuma ya ce“to daman ana dole ne Inna? Bana son auren dan girman Allah ki daina min irin haka, ba ma sai na sake zuwa inda ki ke ba”


“Kar ka zo kada Allah yasa ka zo, ai daman ta shanyeka ita da iyayenta matsiyata. To bari kaji wallahi mun fi ƙarfinka, kuma ba zaka ci gaba da zama a haka da juya ba, shekara 6 ko ɓari ta kasa yi, to wallahi baka isa ba! Kaji ma na gaya maka”


Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce“ wai mene ne matsalar ku Inna? Ba dai matata ba ce? To ni babu wani auran da zan sake!”


Cikin kunfar baki ta ce“to yimin rashin kunya! Na ce zageni saboda juyat matarka da bata da amfani! Ka zageni na ce!”


Ƙarar rufe ƙofar da suka ji ya hana shi magana, da sauri ya bi bayanta, can ya hangota tana tafe tana sauri, yabi bayanta da sauri ya sha gabanta. Fuskarta a rufe da mayafin abayar jikinta sai kuka take kamar ranta zai fita, hannunta ya kama ta fizge tana girgiza kanta, saurin riƙeta yayi kawai ya rungumeta ta sake fashewa da wani raunataccen kukan, dafa bayanta ya yi yana jin yanda hawayenta ke zuba kan ƙirjinsa, ya sauke numfashi ba tare da ya ce komai ba. After 2mins ya ja hannunta suka ƙarasa wajen motarsa ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan ya zagaya ya shiga shima ya yiwa motar key suka bar gidan.


Sun yi nisa sosai ya sami gefe ɗaya ya yi parking jin yanda take kuka kamar ranta zai fita, kallonta ya dinga yi yama kasa ce mata komai, can dai ya yi ƙarfin halin cewa


“Zakiyya, ki yi hakuri dan Allah, kar ki damu da abin da Inna ta ce, dan Allah ki yi haƙuri”


Cikin shassheƙar kuka ta ce“ka kai ni gida” ya yi shiru sai kuma ya ce“a'a gida zamu tafi, gobe na kai ki”


Cikin kuka ta ce“dan Allah... Dan Allah Aliyu idan ba so ka ke zuciyata ta buga ba ka kai ni gidanmu”

Ganin tana kukan kamar zata shiɗe ya sanya ya ce“okay” ya juya ya ci gaba da driving ɗin.


****
Salma ta dinga kallonsa amma bata ce komai ba, ɗan haɗe ransa ya yi ya ce“wannan kallon fa na mene?” saurin rufe fuskarta ta yi da hannunta tana dariya, ya girgiza kansa sai kuma ya ci gaba da yankan salak ɗin da yake, tashi ta yi ta shiga kitchen bata daɗe ba ta dawo hannunta riƙe da plate wanda ta zuba shinkafa da wake, gabansa ta zo ta ajiye ganin ko rabin yankan bai yi ba ta karɓa tana cewa“ni Yaya bani baka iya ba” taɓe baki ya yi ya ce“zaki sake cewa na taya ki” murmushi kawai tayi sannan ta ƙarasa yankan salak ɗin ta tashi ta koma kitchen, wankewa ta yi sannan ta dawo dashi ta zuba kan abincin ta tura masa gabansa. Kallon plate ɗin ya dinga yi sai kuma ya ce“ke ba zaki ci ba?”


Girgiza kanta ta yi ta ce“a'a ba zan ci ba ni, sai su Aunty Maryam sun zo, ta ce min suna hanya”


Taɓe bakinsa ya yi sannan ya ce“okay” daga haka ya gyara zamansa ya yi bismillah ya fara cin abincin.


Kan kujera ta koma ta zauna ta ɗora hannunta kan kumatunta ta zuba masa idanu, Yau sati biyu kenan bayan samun sauƙinsa. Suna zaune lafiya dashi yanda yake kula da ita abun har mamaki yake bata, he's always behind her happiness, koda wasa bai so yaga ɓacin ranta, bayan kwana biyu suke zuwa gidan Malam yana sake bashi rubutu, kuma su Maryam sun dawo dan zuwansu gidan biyu. Yau ma sun ce zasu zo saboda za'a yi maganar sauya gidansu da kuma tafiyarta makaranta, Salma ta sake lumshe idanunta tana sake godewa Allah daya bata Zayyad a matsayin miji, duk da yarintarta amma ta fuskanci abubuwa dayawa akansa, bashi da yawan surutu amma yana da kulawa fiye da ƙima, sannan kuma yana da halin kirki amma idan ya so. Ɗago kansa ya yi yaga yanda take kallonsa kamar ta samu tv, ajiye spoon ɗin ya yi ya ce“Idan ki ka cinyeni sai ki daina kallona” sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, tasowa ya yi ya dawo kusa da ita, hannunta ya riƙe cikin nasa in a very cool voice ya ce“faɗa min meyasa ki ke yawan kallona?”


Salma ta kalleshi hawaye na kawowa idanunta ta ce“kawai ina son ganinka ne Yaya Zayyad, idan ina kallonka sai naji tamkar ina da komai a rayuwa. Idan kana kusa dani kewar iyaye da yan uwa tana ragar min sosai. Bana son ka yi nisa dani tsoro nake ji Yaya” ta ƙare maganar hawaye na biyo fuskarta, Zayyad ya dinga kallonta kafin ya numfasa ya ce“ki daina shirme Salma, kin ga yanzu kin girma har aure ki kayi, sannan kuma makaranta za ki fara zuwa be wise man, ko kin fasa zama likitan?”


Murmushinta mai kyau ta yi ta ce“ina so mana Yaya, ina son na zama likita saboda na taimaki mutane, ba zan bari wani ya mutu ba in dai ina da halin taimaka masa, sannan idan zan yiwa mutum aiki zan yi masa koda a ce bai kawo kuɗin ba, sai daga baya ya biya”


Zayyad ya jinjina kansa ya ce“saboda me to?”


“sabo...saboda... Saboda da a ce an yiwa Abbana aiki kafin mu kawo kuɗi da yanzu bai mutu ya bar ni ba, da yanzu ban zama marainiya ba, da yanzu ina zaune tare dashi, da ban rasa kowa ba...”


Hawaye ya dinga zubowa kan farar fuskarsa, sosai jikinsa ya yi sanyi, ya sanya hannunsa ya goge mata hawayen sannan ya ce“ba haka bane, ita mutuwa lokaci ce, idan har kuma ya yi to babu makawa sai mutum ya tafi, koda a ce kun kawo kuɗin, ko da a ce an yi masa aikin sai ya mutu domin iya lokacin da zai yi a duniya kenan, dan haka ki daina irin wannan tunanin kin ji”


Gyaɗa masa kai ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce“Yaya Zayyad!”


“Ummulsalma!”


Ta kalleshi sai kuma ta yi shiru, ɗago haɓarta ya yi ya ce“talk mana” girgiza kanta ta yi tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce“babu komai fa, i just want to talk to you”


“Go ahead”


Girgiza kanta ta yi kafin ta ce komai ta ji ana buga ƙofa. Tashi ta yi da sauri ta fita ya bita da idanu.


Rungume Maryam ta yi tana dariya ta ce“oyoyo Auntie Maryam” dariya ita ma ta yi ta ce“to ɓallani Salma” sakinta ta yi tana dariya, ta ɗauki Khalil ta ce“Aboki i dey missed you amma kwana zaka yi?” Girgiza mata kai ya yi ya ce“ni ba zan kwana ba” harararsa ta yi ta ce“sai ka kwanan” daga haka ta nufi cikin ɗakin Maryam na biye da ita. Da sallama ta shiga ya miƙe yana kallonsu ya ce“sannunku da zuwa” Maryam ta zauna tana cewa“Yawwa yaya Zayyad, ina yini?”


“Lafiya kalao ya gida? Ina Hashim?”


Ya jera mata tambayoyin, Maryam ta ce“Alhamdulilah, Ya fita amma idan zamu tafi zai zo” Zayyad ya jinjina kansa sannan ya tashi ya shige ɗaki, Salma ta ajiye musu ruwan data ɗauko tana cewa“Auntie zamu je gidan malam ɗin?” harararta ta yi ta ce“ba zan je ba ɗin” murmushi ta yi ta ce“haba my sweet Auntie, shinkafa da wake fa nayi miki” da sauri ta ce“haba?” Salma ta ce“wallahi har da salak da yaji mai daɗi na daka” Murmushi Maryam ta yi ta ce“to zuba min mana, zamu je to” tuntsirewa da dariya Salma ta yi ta ce“Hajiya Aunty Maryam” daga haka ta nufi kitchen Maryam ta girgiza kanta tana dariya.


Koda ya shiga ɗakin waje ya nema ya zauna ya yi shiru yana tunani, time to time Mommah take faɗo masa a rai, ya gama shiri next week zai je Abuja ya ganota idan da hali sai ya tafi har Salman, ya numfasa sai kuma ya kwanta kan katifa ya lumshe idanunsa.


****
Jiddah ta sake ƙasa da muryarta ta ce“yanzu ina yaron yake?” daga ɗaya ɓangaren aka ce“yana can mana, bashi da lafiya ne shi ne yasa suka kirani fa, idan zaki samu dama ki fito gidanmu yanzun” Jiddah ta sauke numfashi ta ce“Meema bana son wani abu ya sameshi, Meema ina son ɗana, kin sani ai” daga ɗaya ɓangaren Meema ta ce“that's why yasa na ce ki zo Jiddah, ina son ki ganshi domin shima yaron yayo missing ɗin ki, sai kin ganshi abun tausayi” Jiddah ta ce“shikenan wait for me zan tambayi Mummy na ce zan zo gidanku sai muje” Okay Meema ta ce sannan ta kashe wayar.


“Jidda!”

A firgice ta juyo ganin Mummy ya sanya jikinta ya yi sanyin, cikin rawar murya ta ce“Mumm... Mummy na'am” hawaye taga tana yi, ta ƙaraso wajen da sauri ta riƙeta tana cewa“subhanallahi! Innalil lahi, Mummy meya faru?” silalewa ta yi ta faɗi a ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka, Jiddah hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, ta durƙusa ta riƙeta tana kuka ita ma ta ce“Dan girman Allah Mummy ki daina kuka, ki faɗa min me aka yi miki, dan Allah ki daina kuka”


Muryarta na rawa ta ce“Jiddah! Jiddah! Jiddah!” cikin tashin hankali ta ce“Mummy ki yi haƙuri dan Allah”


“Jiddah ɗa? Jiddah ina ki ka samu ɗa? Jiddah ban gane ina ki ka dosa ba, kimin bayani kafin zuciyata ta buga dan Allah”


Tashi Jiddah ta yi ta fara takawa a hankali, jikin window ɗin ɗakin ta tsaya tana hango can ƙasan gidan, cikin shessheƙar kuka ta ce“Ki yi haƙuri Mummy, na kasa, ban san da wane ido zan kalleku bane, ba zan iya ba, Mummy mema zan ce muku? Ba laifina bane!”


Mummy data zo gabanta ta dafata cikin kuka ta ce“Kenan da gaske ne abin da naji? Jiddah kina da ɗa? Yaushe haka ta faru ni mahaifiyarki ban sani ba? Yaushe Jiddah!”


Juyowa ta yi ta kalleta da runannun idanunta ta ce“A lokacin da nayi nesa daku Mummy, A lokacin dana zamana banida mai faɗa min daidai da rashin daidai, a lokacin da ku ke tunanin kun tura ni domin samun ilimi. Mummy shi ne dalilin komai! Shi ne dalilin kamuwa da ciwon zuciyata! Shi ne dalilin rugujewar farin cikina! Mummy da gaske na samu ciki kuma na haihu sannan na ɓoye ɗan gudun ku gane...” ta kasa ci gabawa saboda kukan da yaci ƙarfinta, ta zube ƙasa gaban Mummy tana rera kuka.


Kallonta kawai ta dinga yi tana jin ƙafafunta kamar ba'a jikinta suke ba, ta buɗe bakinta dakyar ta ce


“Jiddah! Wanene ya yi miki haka? Wanene sanadin wannan cikin! Ki sanar dani dan Allah”


Muryarta na rawa ta ce“Shi ne Mummy...shi ne wallahi, Shiyasa na tsaneshi! Shi ne Mummy...”


“Shi wane? Shi wane”


Cikin wata iriyar muryar mai nuna zallar ƙiyayya ta ce“Zayyad ne! Zayyad ne Mummy, Shi ne...”


Da wani irin tashin hankali Mummy ta kalleta, hannunta bisa ƙirjinta ta ce“Ji... Jiddah me ki ka ce? Jiddah...”


Wani irin ihu Jiddah ta saka ganin Mummy zube a ƙasa a sume, ta dinga jijjigata tana kuka ta ce”Dan Allah Mummy ki tashi, Mummy ki buɗe idanunki, nashiga ukuna Mummy, wallahi ba zan bar shi ba, daman zan ɗauka mataki amma ki tashi! Dan Allah ki buɗe idanunki...”


Jiddah ta dinga kukan cikin fitar hankali.


****
Maryam ta dinga kallonta tana murmushi, kwaɓe fuska ta yi ta ajiye liner ɗin ta ce“Auntie meyasa ki ke min dariya?” Maryam ta girgiza kanta ta ce“a'a ni babu dariyar da nayi miki ci gaba da kwalliyarki” Salma ta kalleta sai kuma ta ci gaba da lining ɗin da take tana kallon ɗan ƙaramin madubin da yake hannunta ta ce“kuma ai nayi kyau, Yaya Zayyad nake yiwa kwalliya, Malam ya ce na dinga faranta masa rai” Maryam ta jinjina kanta still smiling ta ce“Ai ko kin kyauta, ki dinga yi masa” murmushi ta yi ta ce“To auntie nayi kyau?” Maryam ta kalleta tun daga ƙasa, wata Egyptian Abaya ce a jikinta baby pink, ta saka veil ɗin rigar a kanta ta sake shi kawai madadin rolling, fuskarta fresh babu kwalliya sai liner data saka a idanunta da kuma zagayen bakinta, she looks quite and elegant, Maryam ta ce“irin wannan kyau haka Amaryar Zayyad” rufe fuskarta ta yi tana murmushi a shagwaɓe ta ce“auntie Maryam ban so”


“muje ni”

Ta buɗe bakinta zata yi magana taji ana knocking ƙofar gidan, Salma ta ce“ko wane kuma?”

“Je ki buɗe mana sai kiga”

Okay kawai ta ce sannan ta fito parlon ta wuce wajen, tana buɗe ƙofar ta ce“au Yaya kai ne...” sai kuma ragowar maganar ta maƙale saboda waɗanda idanunta ya gani, ta yi saurin barin jikin ƙofar tana girgiza kanta, Shigowa Mommah ta yi sai kuma General. Ya dinga kallon gidan kafin ya mayar da idanunsa kan Salma, sunkuyar da kanta ta yi tana hawaye ya shiga takawa cikin isa har inda take.


“Daddy!”

Muryar Zayyad ta daki dodon kunnensa, ɗago kansa ya yi ya kalleshi da sauri ya ƙaraso ya rungume shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya General ya sauke ya ɗago shi ya matse kafaɗunsa yana murmushi mai tafe da hawaye ya ce“son! Zayyad kai ne, kana lafiya?” ya shiga tattaba jikinsa a ruɗe, murmushi kawai Zayyad ya yi sai kuma ya sake rungumeshi muryarsa a dakushe ya ce“Daddy!”


Yanda ya yi maganar cikin wani irin raunin zuciya ya sanya Daddy fashewa da kuka ya ce“ka yafeni, I fell, I fell Zayyad!” Ɗagowa ya yi ya kalleshi ya ce“stop saying that Daddy” daga haka ya juya yana kallon Mommah wadda ke tsaye tana kallonsa kamar statue.


Da gudu ya tafi ya faɗa jikinta, Mommah ta ƙamkameshi sai kawai ya fashe da kuka, rauninsa gaba ɗaya ya bayyana a jikin wadda kewa kallon mahaifiya. Ita kanta kukan take, kowa ya dinga kallonsu a wajen cike da tausayawa. After some minutes ta ɗago shi tana taɓa shi ta ce“Zayyad! Zayyad! Da gaske kai ne? Meke damunka, zo mu tafi gida, muje Zayyad”


Murmushi ya yi ya sanya hannunsa ya share mata hawayen ya ce“babu komai Mommah I'm feeling better now” girgiza kanta ta shiga yi tana kuka ta ce“ka zo mu tafi, kazo mu tafi dan Allah” ta dinga jan shi. Hannunsa ya sanya ya riƙe nata ya ce“Mommah wait! yanzu zamu tafi” ci gaba ta yi da jansa tana cewa“jirgin mu yana can yana jiranmu muje kaji” Ya kalleta amma bai motsa ba, juyowa ta yi taga ya Girgiza mata kai, sakin hannunsa ta yi ta ce“Ba zaka bini ba ne? Ba zaka tafi ba Zayyad? Ina som muje gida, ka zo mu tafi dan Allah, ko baka sona yanzun?”


“Mommah!”

Ya kira sunanta hawaye na kawo idanunsa, juyawa ya yi ya kalli Salma wadda ke tsaye ta zuba musu idanu hawaye sai zuba yake akan fuskarta kamar an buɗe famfo. Da hannu ya yi mata alama da ta zo, ta ƙaraso tana tafe kamar zata faɗi. Kallonta Mommah ta yi amma bata ce komai ba, ya kamo hannunta ya yi shiru yana kallon fafaren yatsunta, jan numfashi ya yi ya sauke sai kuma ya ce“Salma zan...”


“Yaya Mommah tana son ta ganka, zan jira ka kaje ka dawo, zan zauna wajen Aunty Maryam, nasan ai ba zaka daɗe ba ko? Zan fara zuwa makarantar ma kaga...”


“Salmaaaa!....”

Ya kira sunanta yana matse yatsunta, hawayene suka sake zubowa fuskarta ta ce“na'am Yaya, ba zan yi kuka ba fa, ai zaka dawo ko?”


“Zayyad!”

Mommah ta kira sunansa, kallonta kawai ya yi sai kuma ya mayar da kansa wajen Salman ya numfasa amma bai ce komai ba, ta dinga kallonsa ganin yanda ya yi shiru ya sanya ta ce“ko tare zamu tafi? Ni bana son naje gidanku Yaya”


“Son jirgi na jiranmu kaji”


Cewar Daddy ganin yanda ya yi shiru bai ce komai ba. Gyaɗa masa kai kawai yayi sannan ya motsa bakinsa muryarsa a raunace ya ce


“Salma nasan kin bani kulawa, kin soni, kin taimakeni da kuɗinki, da lokacinki, da lafiyarki, kin zauna dani a halin da ba kowace mace ce zata iya zama da namiji ba. Kin bani kulawa tamkar daman can kin saba dani, duk da yarintar ki bai saka kin Gaza ba, na so na zauna da ke, naso na saka miki da Alkhairin da ki ka min, naso na baki kulawa irin wadda ki ka ban, sai dai...”


“Sai dai me Yaya? Babu komai fa, ai kai mijina ne, kuma kaima ka taimakeni a lokacin da nake buƙata, dan haka duk abin da nayi maka tamkar dole ne a wajena, bana son ka gode min, ai muna tare zan ci gaba da faranta maka har ƙarshen rayuwata. Yaya Zayyad ka san me? Ina sonka! Ina sonka Yaya! Tun ranar dana fara ganinka naji na kamu da sonka, ban san taya ba amma tabbas kai ɗin na daban ne, ashe ƙaddara zata haɗa mu, ashe zan zama matarka. Ina jin nafi kowace mace Sa'a a duniya dana sameka, Yaya ina sonka wallahi ina sonka!”


Zayyad ya kasa magana sai girgiza mata kai yake a hankali, Maryam dake kallonsu ta share hawayenta tana jin jikinta ya yi wani irin sanyi, Salma ta bata tausayi sosai, Zayyad ya sauke numfashi a karo na barkatai kafin ya ce


“Nagode miki Salma, Thank you for everything, your time, your care, your love, I'll never forget you in the rest of my life, those memories zan ci gaba da ajiye su, zan ci gaba da tunaki har abada. Zaki ci gaba da zuwa makaranta, zaki zama likita kuma ki taimaki masu neman taimako, zan tabbatar da wannan burin naki ya cika”


Salma dinga kallonsa ta kasa gane abin da yake nufi, ta kasa gane in da zancensa ya dosa, Ita dai tasan idan ya tafi zai dawo, ba zai barta ba tana da wannan tabbacin. Abin da ya sanya a tafin hannunta shi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, ta kalli hannunta, wata well folded paper ce, ta ɗago ta kalleshi sai kawai taga ya Girgiza mata kai ya sannan ya ce


“Zan tafi Salma, ban so haka ba amma babu yanda zan yi, zan koma ga iyayena da kuma yan uwana, I'm sorry to say na sake ki saki ɗaya, I'm sorry Salma, zaki ci gaba da zama wajensu Maryam, ki yi karatu kin ji, one day I'll be back to you, but as for now zamu rabu. Naso na aureki sai dai ina da matar da aka zaɓa min kuma ita zan aura nan bada jimawa ba, thank you, ba zan taɓa manta abubuwan da ki ka min ba, zan kuma dinga miki addu'a a kullum. Sannan ina son na faɗa miki idan kin samu miji ki yi aurenki Salma, kuma ki zauna lafiya da mijinki, ki so shi kamar yanda nake da tabbacin zai so ki, domin kin cancanta a soki, I'm sorry kin ji. Allah ya haɗa kowa da Alkhairin rayuwarsa, good bye Salma, sai anjima!”


Ya saki hannunta ya juya ya bi bayan Mommah, kallonsa ta dinga yi tana jin kamar yana tafiya ne zuciyarta da nutsuwarta, can kuma ta fasa wata irin ƙara, tabi bayansu, Maryam ta biyota da gudu. Tsaye ta ganta gabansa ta rike rigarsa tana wani irin kuka mai raunata zuciyar duk wani mai sauraro, da sauri Maryam ta ƙaraso wajen ta riƙeta tana janyeta daga jikinsa, sai dai irin riƙon da ta yi masa ya sanya ta kasa janyeta, cikin gunjin kuka ta ce


“A'a Yaya! A'a! Kar ka tafi ka bar ni dan girman Allah, ka ji tausayina, wallahi ba zan taɓa ɓata maka rai ba, zan yi duk abin da ka ke so, dan Allah kada ka sakeni! Ka da ka yi nesa dani, Idan ka tafi ka bar ni mutuwa zan yi Yaya! Wallahi mutuwa zan yi...”


Wani soja ya zo ya janye hannunta da ƙarfi, Maryam ta rungumeta itama tana kuka kamar ranta zai fita, Zayyad ya kalleta sai kuma ya shige mota kawai, Salma ta saki wani ihun tana ƙoƙarin bin su, amma Maryam ta riƙeta tsam tana girgiza mata kai. Cikin kuka da fitar hayyaci ta ce“Auntie tafiya zasu yi fa, da gaske tafiya zai yi ya bar ni, Auntie ki cikani na bi shi dan Allah, ina son Yaya Zayyad, Auntie ki barni! Ki bar ni Auntie! Ki daina riƙeni...”


Maryam ta kasa cikata, haka tana ji tana gani motocinsu suka dinga tafiya daga layin ɗaya bayan ɗaya, Salma ta dinga jin kamar ƙarshen rayuwarta ne zai zo, ta fara ganin wani irin hazo cikin idanunta kafin daga bisani jikinta ya yi wani irin sanyi, ta fadi ƙasa Sumammiya.


****
Kallonta ya dinga yi sai kuma ya ce“me ki ke nufi Zakiyya?” tana kallonsa ta ce“i mean ba zan dawo ba Aliyu! Ba zan ci gaba da zama da kai ba! Ni ba zan taɓa samar maka da ɗa ba, kuma iyayenka da danginka ba zasu taɓa sona ba! Zan zauna wajen Auntyna, kaje kawai! Ka nemi wata Aliyu. Ka yi aurenka dan Allah ka auri wadda zata haifar maka ɗa, idan ta haifi mace ka saka mata sunana...” ta juya ta shige cikin gidan da gudu.


“Zakiyya! Zakiyya! Zakiyya..”

Ya yi kamar zai bita sai kuma ya tsaya, ya sauke numfashi sai kuma ya juya ya koma mota, da niyyar da dare sai ya dawo ya lallaɓata.


Wayarsa ce ta dinga ringing ganin sunan da yake kan screen ɗin ya sanya ya ɗauka, daga ɗaya ɓangaren aka ce “Wai kana ina ne?” Aliyu ya ce“ina unguwar rigasa I'm coming” Mujaheed ya ce“okay, but wait meya sameka naji muryarka haka?” Aliyu ya ce“idan na ƙaraso kaji” okay kawai ya ce sannan ya yi cutting kiran.


Salma ta shiga buɗe idanunta tana ƙarewa ɗakin kallo, tashi zaune ta yi ta dinga kallon gidan sai kuma ta miƙe tsaye tana cewa “A'a Yaya Zayyad! Ba zaku tafi ku bar ni ba wallahi! Sai na biku!”


Maryam da ke cikin kitchen taji kamar muryar mutum ta ce“Salma” Salma ta kalli hanyar kitchen ɗin sai kuma ta girgiza kanta da gudu kuma ta fice daga parlon, buɗe ƙofar gidan ta yi ta ɗebi gudu ta nufi hanyar titi. Koda Maryam ta fito ta dinga kallon parlon ganin babu Salman data bari kwance, ta shiga duk ɗakunan amma bata ganta ba, tsakar gida ta fito sai dai ganin ƙofar gidan a buɗe ya sanya taji jikinta ya yi sanyi, ta koma da sauri ta ɗauko wayarta ta shiga kiran lambar Hashim.


Koda Salma ta zo titi motoci sun cika dan yammaci ne, bata ko kallon gabanta ta nufi tsakiyar titin da niyyar tsallakawa, Cikin rashin sa'a wata mota ta yi sama da ita sannan ta faɗo ƙasa kanta ya bugu da kwalta nan take jini ya fara zuba, cikin tashin hankali ya yi parking ya fito, mutane duk aka taru ana kallonta jininta sai malala yake akan titin, wani ne ya ɗago fuskarta, Aliyu ya ɗan ja da baya sai suka ya ce“innalil lahi wa ina ilayhi raji'un! What i did!?”


Wanda ya ɗagotan ne ya tattaɓata sai kuma ya ce“wannan ai ta mutu, ta mutu wallahi!”


*Alhamdulillah anan na kawo karshen book 1, sai mun haɗu a book 2 wanda yake na kuɗi ne akan ₦700 kacal, via 7041901078 Hauwa lawan Adamu Opay, evidence via 08106608363 Nanameera*

# HCD
# Betrayel
# Nanameera
08106608363
Chapter 28 · 0% Book details