Chapter 11: Between Grief and Promises
Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 15 min read
Nanameera, YOTA/023.
Kyakkyawan murmushi ya sakar mata yana sauke glasses ɗin idanunsa, ganin irin kallon da take masa ya sanya ya girgiza kansa still smiling ya ce “Rufe bakin mana” kunya ce ta rufeta, ta sanya hannayenta duk biyun ta ɓoye fuskarta. Girgiza kai Zayyad ya yi yana murmushi shima ya ce“Kin gane ni?” langwaɓar da kanta ta yi a sanyaye ta ce “Yaya Yad ya zan manta ka?” Zayyad ya gyara tsaiwarsa yana cewa“Sai ki mantani mana, wait idan baki mantani ba ina ki ka sanni?” wani kyakkyawan murmushi ne ya kwace mata, ta Jinjina kanta ba tare da ta ce komai ba. Shiru wajen ya ɗauka iskar damuna mai ɗauke da danshi tana kaɗawa a hankali. Furzar da numfashi ya yi kafin ya sake kallonta ya ce
“Ya jikin Abba?”
Shiru Salma ta yi lokaci ɗaya hawaye suka kawo kurmin idonta, da mamaki Zayyad ke Kallonta, a nutse ya ce
“Lafiya dai?”
Kasa bashi amsa ta yi, sai kawai ta fashe da kuka, ƙarasowa gabanta ya yi ya zuba mata idanu, a hankali ya sanya hannunsa yana janye hijabin data rufe fuskarta dashi, sake rufe fuskar ta yi tana ci gaba da kukanta. Ya yi tsaye wajen yana kallonta, ganin ta ƙi yin shiru ya sanya ya ce
“Ina miki magana kina ji na?”
Bata basa amsa ba, dan ko ɗago fuskar bata yi ba, ya girgiza kansa ya ce“shikenan tun da ba za ki faɗa min ba sai an jima” daga haka ya juya yana komawa in da motarsa take.
“A'a Alhaji ina za ka je? Dawo mana, me ta ƙo faɗa maka?”
Zayyad wanda yake tsaye riƙe da handle ɗin mota ya juyo dan ganin wanda yake magana. Umma ce tsaye kusa da Salma ta lulluɓe jikinta da mayafi sai rarraba idanu take, tun daga sama har ƙasa Zayyad ya kalleta, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin bai ce komai ba ya sanya Umma sake cewa
“Salman ce sai addu'a, tun da baban nan nata ya mutu shikenan bana gane kanta, ko abinci ma ba tsayawa take ta ci ba, to babu mai daɗi”
Da mamaki Zayyad ke Kallonta, Sai kuma ya kalli Salma wadda har sannan ke kuka, ya gyara tsaiwarsa kafin ya ce“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, yaushe ya rasu?” Umma ta sake langwaɓewa kamar abar tausayi muryarta har rawa take ta ce“Wallahi yau a kayi kwana uku, To da yake baban nata ba wasu dangine dashi a nan kusa ba ya sanya baka ga jama'a ba, Yanzu ni ce uwarta ni ce ubanta”
Shiru Zayyad ya yi for some seconds can kuma ya ce“Allah ubangiji ya jiƙansa ya sa ya huta, ya kyautata namu zuwan” a sanyaye Umma ta ce
“Ameen”
Shiru wajen ya ɗauka Umma sai bin sa take da kallo, Zayyad ya juya ya koma motarsa, Umma ta dinga leƙensa tana son ganin abin da yake yi. Dawowa ya yi hannunsa riƙe da wrappers na 1k guda uku ya miƙawa Umma yana cewa “Gashi a yi sadaƙa”
Jikin Umma Rahmatu na rawa ta amshi kuɗin tana cewa “To...To Allah ya ƙara buɗi... Allah ya biya buƙata” Zayyad bai ce komai ba, ta kalli Salma ta ce can ƙasa
“Sai kin shigo”
Daga haka ta shige gida da sauri. Takaici da baƙin ciki ya sanya Salma sake fashewa da wani sabon kukan, Shiru Zayyad ya yi ya kamo hannunta a hankali, saurin fizgewa ta yi ta janye hijabin fuskarta, idanunta caɓa-caɓa da hawaye ta ce
“Ni...Ni karka sake taɓani”
Jin jina kansa ya yi ya ce
“Ni magana zan miki, meyasa Abba ya mutu?”
Salma na kuka ta ce“Sanda na dawo sai na tarar an kawo gawarsa, Abba bai jirani na dawo ba ya mutu ya barni, Ni na daina kulashi”
Sosai ta bashi dariya amma ya dake, A nutse ya ce“Bayan ya mutum za ki ce kin daina kula shi? Addu'a za ki dinga masa kin ji” gyaɗa kanta ta yi tana share hawayenta. Agogon hannunsa ya kalla ya ce“Koma gida to, sai na sake zuwa” sake gyaɗa masa kai ta yi ta juya ta shige gidan. Numfasawa Zayyad ya yi kafin ya juya ya shige motarsa ya bar ƙofar gidan.
Salma na shiga ta tarar da Umma zaune kan tabarma sai lissafa kuɗaɗe take, har ta rufe jin taku da taga Salma ce kuma sai ta buɗe, ƙarasowa Salma ta yi ta zauna gefenta. Hannu Umma ta miƙo mata, Salma ta kalleta da mamaki dan bata gane me take nufi ba
“Ina abin da ya baki?”
Baki buɗe Salma ke kallonta, a ɗan tsawace Umma ta ce“Ko baki ji ina magana ne? Ina kuɗaɗen daya baki?” A sanyaye ta ce“Umma ni babu abin da ya bani fa” waro idanu Umma ta yi ta ce“Ni za ki yiwa ƙarya? Na tabbata ya baki kuɗaɗe kema kamar yanda ya bani” Salma na hawaye ta ce“Ni wallahi bai bani ko biyar ba, Ni ba kuɗinsa nake so ba” riƙe baki Umma ta yi ta ce
“Eh lallai! To shi me yake so idan ba kyan ki ba? Ke bana son tsirfa fa! So nake na aurar dake, Kuma dole ki ci kuɗin samari”
Tura baki Salma ta yi ta tashi ta shige ɗaki da sauri, da idanu Umma ta bi ta sai kuma ta yi tsaki tana cewa“Shashasha wadda bata san inda yake mata ciwo ba, har irin wannan attarijin ya zo wajenki ki ce wai ba kuɗinsa ki ke so ba? Ni dama bari ya yi na gama takaba ya aureni” Ta ci gaba da ƙirga kuɗaɗenta. Koda ta shiga ɗaki kwanciyarta ta yi kan tabarma tana kuka ita kaɗai, ba'a fi mintuna goma ba Umma ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce “Zan fita, Ki zo ki ci gaba da girkin nan” Da mamaki Salma ta ɗago ta kalleta, a sanyaye ta ce“Umma wadda take tabaka ai bata fita”
“To uwata hanani fita! Na ce hanani” ta ƙare maganar tana zabga mata uwar harara. Shiru Salma ta yi dan bata da abin sake cewa, Umma ta juya ta bar ɗakin.
****
A hankali ya buɗe ƙofar parlon yana murmushi ya ce“Shigo Mama” Shigowa ta yi tana sanye da wata atampa glitter, ɗinkin riga da zani, Ta yafa veil wanda ya hau da atamfar, hannunta riƙe da jaka. Zama ta yi kan ɗaya daga cikin royal sofa ɗin dake zagaye da parlon. Farooq na murmushi ya ce“Bari na kirata” daga haka ya nufi hanyar upstairs. Koda ya shiga ɗakin zaune ya hangeta tsakiyar gado idanunta zube kan system ɗin gabanta tana murmushi abin ta, Da mamaki yake kallonta ya ƙarasa gaban gadon a zaune gefenta a hankali ya ce
“Love”
Ɗago idanunta ta yi ta kalleshi, murmushi ya sakar mata kafin ya ce“Guess what?” langwaɓar da kai ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Just tell me” Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“Mama na downstairs” shiru Nimra ta yi can kuma ta ce
“Shine baka faɗa min ba?”
Farooq ya ce“Yanzu ai gashi na faɗa miki” Rufe system ɗin gabanta ta yi ta sauka kan gadon, toilet ta shige dan riga da wando ne jikinta. Bata ɗauki lokaci ba ta fito, wata atampa ɗinkin riga da skirt, ta ɗaure kanta ta ɗan yi simple kwalliya a fuskarta kafin ta baro ɗakin. Koda ta sakko downstairs Mama kawai ta samu zaune kan sofa tana danna waya, ƙarasowa ta yi ta zauna kujerar dake facing ɗinta a nutse ta ce“Ina yini Mama?” murmushi Mama ta yi ta ce“Lafiya klao Nimra ya gida?” “Alhamdulilah” Nimra ta ce sannan ta tashi, kitchen ta nufa ta haɗo drinks a tray ta kira wata maid ta ɗauko mata, a gaban Mama aka ajiye tray ɗin, tana ɗan murmushi ta ce“Mama ki sha ruwa, Me za'a dafa miki?” Girgiza kai Mama ta yi tana murmushi ta ce“A'a ba sai kin wahalar da kan ki ba, Ai baki san zan zo ba, Ba sai kin yi girki ba” Murmushi kawai Nimra ta yi ba ta ce komai ba ta koma kitchen ɗin. Ƙarar door bell ne ya fito da ita daga kitchen ɗin, duk a tunaninta Farooq ne ya dawo. Turus ta yi bayan ta buɗe ƙofar tana kallonta da mamaki, Tsaki Deejah ta yi ta ce“Dalla matsa min hanya ni” wani irin Ihu Nimra ta saka ta rungumeta tana dariya ta ce“Welcome Bestie” Tureta Deejah ta yi ta ce“Ba wani Bestie, abin da kin manta dani? Yaushe rabon da ki zo in da nake? Ke kin yi aure ko?” langwaɓar da kai Nimra ta yi ta kama hannunta suka shiga ciki tana cewa “Ya Uk ɗin?” “Alhamdulillah, Ai kin yi missing yarinya” Dariya Nimra ta yi, Daidai sanda suka zo parlon. Kallo ɗaya Deejah ta yiwa Mama dake zaune kan kujera ta ɗauke kanta, Hannunta Nimra ta ja tana mata alama data gaisheta. Harararta Deejah ta yi kafin ta kalli inda Mama take daga tsaye ta ce
“Good afternoon Ma”
Murmushi Mama ta yi ta ce“How are you yarinya?”
“Alhamdulilah”
Deejah ta faɗa, Mama ta Jinjina kanta bata sake cewa komai ba. Deejah ta kalli Nimra ta ce“Ni zan shiga ciki sai kin shigo” daga haka ta yi hanyar upstairs, Mama ta bita da idanu. Taɓe baki Nimra ta yi sanin halin Ƙawartata ta koma kitchen dan ƙarasa abin da take.
Asokoro, Abuja.
Zaune suke cikin katon parlon, Mami na kallon Mommah dake mata bayani tana jin jina kai, Mommah ta ci gaba da fad'in
“To kinji abin da ya faru Adda, na rasa yanda zan yi da Zayyad, kwata-kwata General baya son laifinsa, ban isa na ce ya yi ba daidai ba sai ya nuna ɓacin ransa. Zayyad duk ya sake lalacewa, sai sanda ya ga dama fa yake shigowa yanzu” Numfasawa Mami ta yi ta ce
“Idan haka ne zan yi magana da General kuwa, ya daina lalata masa tarbiyya da sunan tausayi da soyayya, Abubuwan Zayyad sun yi yawa, Ahmad ya ce min har giya yake sha, wace irin rayuwa ce wannan?” Mommah ta girgiza kai kafin ta ce “Wallahi Adda idan kin ga yanda nake fama sai kin tausayamun, Zayyad baya so gaskiya, tunda ya dawo daga Uk komai na sa ya lalace, ya je ya yi rayuwa da mutanen banza, Babu irin club ɗin da bai sani ba. Allah ne kaɗai ya san irin abubuwan da yake yi ma a ɓoye” Dafata Mami ta yi ta ce“Ki ci gaba da haƙuri Khadijah, Karki manta Zayyad amana ne a wajenmu, Allah ya rufa asiri ma da kece ki ke auren Idris. Ke ce matsayin Mahaifiyarsa, Kece ki ka shayar da shi, ke yake wa kallon uwa. Saboda haka ki dage masa da addu'a da naiman taimako kuma ci gaba da masa faɗa koda a ce baya so, watarana sai Allah yasa ya ji” Goge hawayen daya zubo mata ta yi tana sauke numfashi ta ce“Haka ne Adda, Kodan Yaya dole nayi iya ka kokarina, domin ta kula damu, Ta bamu tarbiyya, Haƙƙine a kaina na kula da rayuwarsa, Allah ya shiryesa” Ameen kawai Mami ta ce parlon ya ɗauki shiru koda da abin da yake tunani.
“Khadija ku kula da rayuwarku, ki zauna lafiya da mijinki, na saka kin auri Idris ne saboda mu sake samun kusanci. Idris ƙanin mijina ne uwa ɗaya uba ɗaya, duk wani halin kirki da Khalid yake da shima yana da shi, Duk da ya fi Khalid zafin zuciya amma nasan yana da halaye na gari, Ki yi hakuri, Ki zauna lafiya da mijinki, Dan Allah Khadijah”
Mommah ta sake share hawaye tunawa da maganar da Marigayiya Jidderh ta faɗa mata lokacin data auri General. Kallonta Mami ta yi ganin tana sharar kwalla ta ce “Haba Khadijah, kuka ai ba magani bane, Addu'a za ki dinga mata” ɗora kanta ta yi kafaɗar Mami tana sake fashewa da kuka ta ce “Dole nayi kuka Mami, Yaya ta tafi ta barmu, Ta tafi ta bar Zayyad a lokacin da yafi buƙatarta fiye da komai, Wallahi tausayi yake bani Yaya, Yana cikin wani hali, yana cikin duhu wanda Allah ne kawai zai kawo masa hasken rayuwa. Ina ma Yaya tana nan” Rufe mata baki Mami ta yi tana girgiza kanta ta ce“Ki daina cewa haka, Allah ya san da hakan ya ɗauke ranta. In sha Allah komai zai zama tarihi, Duk yanda duhu zai mamaye waje wata rana sai haske ya bayyana, ina ji a jikina Zayyad zai samo HASKEN CIKIN DUHUnsa nan ba da jimawa ba”
Mommah ta jin jina kai ta ce“I hope so”
****
Jinjina kai kawai Zayyad yake yana saurarenta amma gaba ɗaya ta ishesa, hannunta ta kamo kamar zata yi kuka ta ce“Yaya I'm talking fa” ɗago lulu eyes ɗinsa ya yi ya zuba mata kamar zai fasa ihu ya ce“Dan girman Allah Nayla ki rabu dani, I'm tired wallahi” turo baki ta yi ta janye system ɗin gabansa tana cewa.
“Kwana nawa bana nan amma ko missing ɗina baka yi, Kuma na zo ina maka magana shi ne ka ke ce min haka?”
Girgiza kansa ya yi ya mike daga kan gadon yana cewa“An jima ma yi magana, tashi ki tafi” kallonsa ta yi sai kuma ta ajiye system ɗin ta miƙe ta fice daga ɗakin tana buga ƙofa da ƙarfi. Da idanu ya bita sai kuma ya taɓe baki ya nufi toilet abin sa. Ana kiran sallar la'asar ya fito sanye da wata dakkakiyar shadda milk colour, sai ƙamshi turaren Clive Christian No. 1 yake, kai tsaye parlon Mommah ya nufa, Babu kowa a parlon don haka ya shige bedroom ɗin kai tsaye. Zaune ya same su da Mami suna hira, Ya tsaya daga bakin ƙofar yana kallonsu bai ce komai ba.
“Ina kuma zaka je Zayyad?”
Lumshe idanunsa ya yi kafin ya ce
“Zan ɗan fita ne, but ba zan daɗe ba. Mami ku jirani please”
Harararsa Mami ta yi ta ce“Naƙi na jira kan, Ahmad na zuwa zamu tafi, idan mun yi dare kai zaka mayar damu Zayyad?” gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce“Wallahi zan kai ki har Abacha road” Ta taɓe baki kafin ta ce“To ka yi sauri dai” Jinjina kansa ya yi sannan ya juya ya bar dakin. A corridor suka ci karo da Khalil wanda shigowarsa gidan kenan, Ya kalleshi ya ce “Yaya unguwa zaka je?” Zayyad na nufar downstairs ya ce“Uhm” Khalil ya bi shi da idanu ya ce“A dawo Lafiya”
“Allah yasa”.
Cikin Maitama gidan yake, ƙaton gida mai ɗauke da securities da sojoji, gidan Babban soja kamar General Kabeer. A compound ɗin gidan ya yi parking dan already an san da zuwansa. Ya yi jim a motar kafin ya ɗauki wayarsa ya yi dialing wata number. Ringing ɗaya aka ɗauka a nutse ya ce
“I'm outside”
Cikin cool voice ɗinta ta ce“Ka shigo ciki tom” okay kawai ya ce sannan ya kashe motar ya fito. Cike da nutsuwa da tagama tsarata take tafiya har ta ƙaraso tsakiyar parlon. A sanyaye ta ce“Ina yini” Sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta. Kyakkyawar budurwa ce wadda ba zata shige 22-23yrs ba, baƙa ce doguwa mai siririyar fuska, da ka ganta kaga baƙar shuwa. Zama ta yi kujerar dake facing wadda yake kai a nutse ta ce
“Fatan ka zo lafiya?”
Zayyad ya ce “Alhamdulilah ya ki ke?” lumshe idanunta ta yi ta ce“Ina nan klao, Ya su Mommah?” Sosai ya yi mamaki jin ta ambaci sunan Mommah sai bai nuna ba ya ce ”Tana nan klao” Ta sake cewa“To idan ka koma ka gaida min dasu” shiru parlon ya ɗauka can kuma ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin
“Dad ya ce na zo na gan ki daman”
Ɗan sunkuyar da kanta ta yi ta ce “Eh Nima haka Daddyna ya ce min, And kuma na ganka ka kwanta min, ban sani ba ko nima nayi maka?” ɗan murmushi Zayyad ya yi ya ce “In sha Allah” Ta yi murmushi bata ce komai ba. Ganin lokaci na tafiya ya sanya ya miƙe tsaye, tashi itama ta yi tana kallonsa ta ce “Naga ka tashi?” Zayyad ya ce
“Mum na jirana ne, Zan dawo in sha Allah” Murmushi ta yi ta ce“Tom Allah ya dawo da kai lafiya” Zayyad ya ce Ameen Sannan ya nufi Kofar fita daga parlon.
“Jidda, Ba dai har ya tafi ba?”
Juyowa ta yi tana kallon wadda ke magana kafin ta ce “Eh Mummy, Wai ana jiransa ne” Shiru ta yi can kuma ta ce“Tom sai ku yi waya ai” murmushi Jidda ta yi ta ce“Eh Mum, Kuma wallahi yanda na gashi a hoto ma sai naga yafi haka kyau a zahiri” riƙe haɓa Mummy ta yi ta ce“Ikon Allah, To sai ki faɗawa General ɗin idan ya dawo, a yi abin da ya kamata nan da 1 month a ɗaura aure” da gudu ta tafi ta rungume Mummy tana murmushi ta ce“Shiyasa nake son ki mummyna”.
Kabayi, Mararaba.
Gyara zama Hajiya Jinjin ta yi tana kallon Umma ta ce“To yanzu ya ki ka yi?” Umma dake zaune gefen kujera ta ce“Sai na kwatanta masa gidana, Kin ga kuwa a mota zundumemiya” shewa Jinjin ta yi ta ce“Kin yi kyan kai ta gurina, Ai dama ba'a wasa da irinsu” Umma ta ce“Ai yanzu dana gama wannan takabar sai Aure” tuntsirewa da dariya Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Au ke yanzu sai ki yi aure? Taɓ!” Da mamaki Umma ke kallonta sai kuma ta ce“To Hajiya tun da na samu wanda ya ce yana sona me zan yi idan ba aure ba?” Da hannu ta yi mata alama da ta kawo kunnenta, Umma ta miƙa mata ta faɗa mata wata magana. Shiru Umma ta yi jiki a sanyaye ta ce
“Ni kuma Hajiya da girmana?” tsaki ta yi ta ce“To har yaushe ki ka yi girman da zaki ce haka? Mu ma duk harkokin da muke kenan, kafin tsufa ya cimmaka ka yi abubuwa dayawa” Jinjina kai Umma ta yi ta ce“Kuma fa haka ne, na yarda da maganganunki, Haka ma za'a yi. To yanzu maganar ita kuma Salama fa?” Hajiya Jinjin ta yi dariya kafin ta ce
“Dana faɗa miki ai baki yarda ba, To bari ki ji kin ga yanda aka fara sallamar nan da ita gara ki bar ta, idan ba haka ba Wallahi kina nan zata dauko abun kunya” Jinjina kai Umma ta yi ta ce“Nima na fuskanci haka wallahi, Yanzu dai bari na koma, idan Allah ya kawo wannan mutumin na je na masa magana idan yana so” girgiza kai Jinjin ta yi ta ce“A'a ai ba'a shiga dawa dan ƙarya, Yanzu dai ki tashi mu je gidan naki, akwai abin da zan aikata” Zumbur Umma ta mike tana cewa“Mu je to, A yi ta ta ƙare wallahi!”.
# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera
08106608363.
https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t
*HASKEN CIKIN DUHU*