Chapter 23-24: Fury's price
Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 15 min read
Nanameera, YOTA/023.
I would like to take this opportunity to thank my beloved ones💞, book lovers, and all my followers wherever they are. I am truly grateful and appreciative. May Allah keep us together always, Nanameera heart you 💕❤️.
Mutumin ya kalleta ganin yanda take kuka yasa ya ce“Haƙuri zaki yi, Haka mutane suke, Kawai ya yi amfani da yardar ki ne ya cuceki” Cikin kuka ta ce“Wallahi koda wasa ban yi tunanin zai cuceni ba, Mutumin kirki ne sosai” Auwal ya ce“Ai fa haka suke, A fuska kamar na Allah amma idan kaga irin cutar da zasu yiwa mutum sai abun ya baka mamaki”.
Mai gidan ya girgiza kai sannan ya maida idanunsa kan Salma ya ce“Yanzu ki tashi ki daina wannan kukan, Ni zan taimakeki”
Ta ɗago kumburarrun Idanunta ta kalleshi sai kuma ta ce“A'a ni bana so, Banason kowa ya taimakeni wallahi”
Sosai ta bashi dariya ya girgiza kansa ya ce“Kina tsoron kada nima na cuceki, Ba zan cutar dake ba, Sunana Hashim a nan nake aure ina da mata ɗaya da ɗa ɗaya, Bari na kirata a waya ta dawo sai ku shiga gidan”
Ya faɗa yana zaro wayarsa daga aljihu, Salma kallonsa kawai take. Duk wannan abun da ake Zayyad na tsaye gefe yana zaro idanu, Ya kalli wannan sai ya mayar da kallonsa ga wani, After 5mins mutumin ya sauke wayar yana kallonta ya ce“Na kirata yanzu za ki ganta ta dawo” Salma na share hawayen fuskarta ta ce
“An gode Allah ya saka da Alkhairi”
Ameen kawai ya ce sannan ya nemi benci ya zauna.
Suna nan zaune har bayan mintuna ashirin matar ta sauka daga Napep, Fara ce mai kyau babu laifi hannunta riƙe da wani ƙaramin yaro wanda ba zai shige 4yrs ba, Ta karaso kantin tana kallonsu, Hashim na ganinta ya miƙe yana murmushi ya ce
“Har mun gaji da jira”
Langwaɓar da kai ta yi ta ce“Afuwan dan Allah Abu, Wallahi ban samu mai Napep da wuri bane, Ina baƙin?”
Ta ƙare maganar tana kallonsa, Da hannu ya nuna mata Salma dake zaune a ƙasa ta yi wujiga-wujiga da ita, Ta ƙura mata idanu tana kallonta har sai da Hashim ya ce
“Maryam lafiya dai?”
Girgiza kanta ta yi a hankali, Ta saki ɗan murmushi ta ce“Sannunki da zuwa” A sanyaye Salma ta gaisheta, Matar ta kalli Zayyad wanda ke tsaye kamar an dasa shi ta ce“Sannu Yallaɓai” Idan bango ya yi magana to tabbas Zayyad ma ya amsawa Maryam, Ta kalli mijinta wanda tun ɗazu ya lura Zayyad ɗin nada matsala, A sanyaye ta ce
“Muje to”
Okay kawai Hashim ya ce sannan ya kalli Salma ya ce“Taso Ummusalma”
Miƙewa ta yi suka yi gaba ta kalli Zayyad wanda bai motsa ba ta ce“Muje mana”
Ko inda take bai kalla ba, Ta girgiza kai kamar zata yi kuka ta ce“Kaga dai na gaji, Ka zo mu tafi nace” Nan ma shiru ya sake mata, Ta yi tsaki ta fice daga kantin ba tare da ta sake bi ta kansa ba. Auwal ne ya kalle shi ya ce“Ka bisu mana”
“Kai dallah rufe mana baki ko mun kula ka?”
Kamar daga sama Zayyad ɗin ya yi maganar, Da mamaki Auwal ke kalonsa dan bai yi tunanin mahaukaci bane, Ya ce“Allah ya baka haƙuri”
Wata uwar harara Zayyad ya zabga masa, ya taɓe baki wanda yake ɗabi'arsa sannan ya fice daga kantin.
Babban compound ne mai ɗauke da yan shuke-shuke na zamani, Ko ina a tsaftace ko ba'a faɗa maka ba kasan matar gidan tana da tsaf sosai, Hashim ne ya kalli Salma ganin ita kaɗai ya ce
“A'a ina dan uwan naki?”
Salma ta ce“Yana waje ya ƙi shigowa ni kuma nagaji ba sai ya yi ta yi ba”
Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Hashim bai ce komai ba ya buɗe gate ɗin ya fita, Ita kuma Salman tabi bayan Maryam dake kiran sunanta.
Zaune ya sameshi kan wani dakali ya tara duwatsu a gabansa yana jifa dasu ɗaya bayan ɗaya yana dariya, Hashim ya ƙarasa gabansa ya ce
“Baka gaji ba duk da haka? Ka tashi kaje kayi wanka ka ci abinci mana”
Zayyad ya ɗago dara-daran idanunsa ya yi wa Hashim wani kallon sheƙeke sai kuma ya ci gaba da jefa dutsen da yake, Da mamaki Hashim ke kallonsa yana tunanin ko dai baya jin magana ne, dan haka da ƙarfi ya ce
“Bawan Allah ka tashi muje”
Wata irin tsawa Zayyad ya daka masa yana cewa
“Kai wane irin mahaukaci ne, Baka ga muna aiki bane zaka shigo mana kai tsaye, Ya'yan talakawa kawai!”
Hashim kasa rufe bakinsa ya yi, Ya dinga kallon Zayyad kamar ya samu tv, Kodai yana da matsala? Amma how? Wannan babban mutumin a ce yana da matsala, Ganin abun na son fin ƙarfinsa ya sanya ya koma cikin gidan domin ya tambayi Salma.
Babu kowa a Parlon sai tashin ƙamshi da yake, Ɗan ƙaramin yaron na zaune kan kujera one seater idanunsa zube kan tv yana kallon wani cartoon da ake haskawa a MBC 3, A nutse ya ce
“Khalil”
Juyowa yaron ya yi ya kalleshi sai kuma ya ce“Na'am Abu”
“Ina Amminka?”
Cikin siririyar murya irin ta yara ya ce“She's inside the kitchen Abu”
Jinjina kai kawai Hashim y yi sannan ya nufi kitchen ɗin, Tsaye ya sameta gaban cooker tana juya stew, Ya girgiza kansa sannan ya ce
“Maryama sarkin ƙoƙari har yaushe ki ka fara haɗa abincin?”
Juyowa ta yi ta kalleshi kafin ta yi ɗan murmushi ta ce“And who told you yanzu nafara haɗa abincin? Already fa ina da stew na, Kawai ina warming ne” Jinjina kansa ya yi ya ce“I see” ta kalleshi kawai ta yi murmushi, Shiru ya ɗan yi can kuma ya ce“Ina Salma take? Ɗan uwan nan nata yaƙi shigowa fa, Yana zatunka wanda ban gane kansu ba”
Maryam da ke ɗauko food flask daga kwali ta ce“Tana ɗaki maybe ma wanka take, Meya hana shi shigowa? Naga babba ne sosai”
Hashim ya ƙaraso ya janyo mata flask ɗin ganin tsayinta ba zai kai ba sannan ya ce“Eh babba ne, Daga gani ma zai girmeni, But yanda yake magana abun ya bani mamaki”
Sai da ta amshi flask ɗin sannan ta ce“Okay bari na kirata, Ko baya son shigowa gidan mutane ne, Sai ya zauna a daƙinka na balcony ai”
Hashim ya ce“Okay je ki kirata please, Eh idan baya son mutane ba” To kawai ta ce sannan ta rage gas ɗin ta juya ta fice daga kitchen ɗin. A Parlon ta samu Khalil har sannan yana kallo, Ta girgiza kanta kawai ta shige ɗaki.
Tsaye ta samu Salma tana ƙoƙarin mai da hijabinta bayan ta fito daga wankan, Maryam ta yi murmushi ta ce“Haba dai ba sai ki kirani na baki kaya ba Salma?”
Salma sunkuyar da kanta kawai ta yi, Maryam ta juya ta fita daga ɗakin ita kuma ta bita da kallo. Bata jima ba ta dawo hannunta riƙe da wata Abaya black colour, Ta miƙawa Salma tana cewa
“Ki saka wannan sai ki fito, Kin ga ɗan uwanki ya ƙi shigowa Abu ya ce yaji yana wasu zantuka”
Amsa ta yi sannan ta ce“Tom Aunty, Bari na zo na tawo dashi”
Okay Maryam ta ce sannan ta sake fita daga dakin, Salma ta ware Abayar mai stones a jiki ta sanya. Mayafin Abayar wanda yake babba ta yafa, Nan da nan ta dawo hayayyacinta duk da ta rame sosai amma har yanzu kyawunta bai gushe ba. Ta fito parlon tana tafiya a sanyaye, Zaune ta sami Maryam da Khalil yana ta mata surutu.
Tana ganin Salma ta sauke shi daga jikinta tana cewa
“Yawwa Salma, Je ki ki tawo dashi”
Toh kawai ta ce sannan ta nufi hanyar fita daga parlon. Dube-dube ta shiga yi tana neman in da yake, Can ta hangeshi zaune a ƙasa yana ɗiban ƙasar yana zubawa cikin rigarsa, Da sauri ta ƙarasa tana kallonsa ta ce
“Mene haka ka ke yi?”
Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce“Nurse tayani kwashe maganin nan, Na tawo a hanya ya zube”
Takaici ne ya isheta, Ta tsuguna ta tankaɗe hannunsa ƙasar ta zube, Ta zazzage ta cikin rigarsa tana masa wani mugun kallo ta ce
“Wai kai ba zaka yi hankali ba? Kana ganin kowa yana kallonka, Ka daina wannan shirman, Da an yi magana ka ce daga asibiti ka ke, Asibiti zaka je, Magani zaka bawa mutum, Wane zai amsa, Ka tashi mu tafi ni”
Tun da ta fara maganar yake kallonta kamar idanunsa zasu faɗo, Sai da ta yi shiru sannan ya sauke nunfashi kawai taga ya fashe da kuka. Rikicewa ta yi ta riƙe hannunsa ta ce
“Mene ne? Ka yi shiru ni ce ba zan sake maka faɗa ba”
Ci gaba ya yi da kukansa kamar ƙaramin yaro, Salma gaba ɗaya ta ruɗe, Ta sanya hannayenta duk biyun tana share masa hawayen ta ce
“Ba na ce ka yi shiru ba, Kayi haƙuri ba zan sake ba”
Babu yanda ba tayi da Zayyad ba amma ya ƙi yin shiru, Ta nemi waje ta zauna a ƙasan ta zuba masa idanu tana kallonsa, Tuni hawaye suka wanke mata fuska itama. Suna nan zaune har bayan mintuna goma, Hashim ya ƙaraso wajen yana kallonsu da mamaki
“Salma lafiya? Meya faru ku ke kuka?”
Hashim ya yi tambayar yana kallonsu. Cikin shassheƙar kuka ta ce
“Yaƙi yin shiru Yaya, Ka ce masa ya daina kuka ba zan sake masa faɗa ba wallahi”
Hashim da bai gane kan zancen ba ya ce“wane? Shi mene ne ya sanya shi yake kuka?”
“Saboda nayi masa faɗa shi ne yake kuka, Kuma na bashi haƙuri ya ƙi yin shiru, Ka ce ya tashi mu tafi”
Hashim ya kalli Zayyad a sanyaye ya ce“Taso mu tafi gida” Zayyad ya miƙe tsaye jikinsa duk ƙasa ya ƙarasa gaban Hashim yana ci gaba da kukansa, Shi dai Hashim kallonsu yake kamar soko ya riƙe hannun Zayyad suka fara tafiya. Ganin haka ya sanya ita ma ta taso ta biyo bayansu.
A compound ɗin gidan suka tsaya ya kalleshi ya ce“Mene ne yasa ka ke kuka? Ai ƙaddara ta riga fata, Ka yi haƙuri dan Allah”
Shi dai Zayyad kukansa kawai yake bai ma san me Hashim ɗin ke cewa ba. Maryam ta fito tana kallonsu ta ce“Lafiya dai? Salma meya faru?”
Tana goge hawayen fuskarta ta ce“Babu komai Auntie, Dan Allah a ina zan kai shi ya yi wanka ya shirya?”
Hashim ya ce“Kawai je ki ciki zan kai shi da kaina”
Salma ta ce“To Yaya, Amma ko ka yi masa magana ba lallai ya amsa ba, Bashi da lafiya ne”
Sai a sannan Hashim ya ɗan fahimta ya jinjina kansa kana ya ce“Tom shikenan shiga ciki, Kema ki daina kukan”
Ta ce to sannan ta shiga ciki Maryam na biye da ita..
****
Zaune take kan carpet ta zuba tagumi tana kallon abincin gabanta, Maryam ce ta fito daga ɗaki ta dinga kallonta da mamaki ta ce
“Salma meya hanaki cin abincin?”
Shiru taji ko amsawa bata yi ba, Babu ma alamun tana jin abin da take cewa. Ta tsuguna a gabanta ta dafata ta ce
“Salma!”
A ɗan firgice ta kalleta sai kuma ta ce“Na'am Auntie”
“Lafiya tunanin me ki ke yi?”
Maryam ta tambayeta, Girgiza kanta ta yi ta ce“Babu komai Auntie”
Maryam ta kafeta da idanu, Ganin haka ya sanya Salma sunkuyar da kanta, Ta ce“Tell me what's going on dear? Ke dawa? Me ki ke tunani?”
Fashewa ta yi da kuka, Ta sanya gefen mayafinta tana rufe fuskarta, Maryam ta dinga kallonta sai kuma ta ce“Ba zaki sanar mini ba ya sanya ki ke kuka? I'm i not ur sister?”
Salma ta girgiza mata kai tana shassheƙar kuka ta ce“Aunty Yaya Zayyad bai ci abinci ba, Kuma kuka yake har yanzu, Naje wajensa ya ƙi kulani”
Maryam ta yi shiru can kuma ta ce“Shi ne yasa ki ke kuka? To ai Abu zai bashi abinci, Baki ga yana wajensa ba tun ɗazu na kai masa abinci nasan yanzu ma ya ci, Don haka kema ki cinye naki”
Gyaɗa mata kai kawai Salma ta yi amma bata daina kukan ba, Maryam ta tashi tsaye ta fice daga Parlon. Tsaye ta samu Hashim ya yi shiru kamar mai tunani, Ta ƙarasa kusa da shi, Ta ce
“Abu lafiya? Me ka ke tunani?”
Kallonta ya yi sai kuma ya numfasa ya ce
“You know what Maryam, Wannan mutumin bashi da hankali fa, Jikina duk ya yi sanyi Maryam, Look at him babba mutum matashi mai shekaru kamar nasa, Ke daga ganinsa kin san ba'a wahala yake ba. Da akwai hutu sosai a tare dashi, Duk inda yake ɗan manya ne”
Maryam ta girgiza kanta cike da damuwa ta ce“Tun sanda ku ka shigo nayi noticing haka, Allah ne kaɗai yasan abin da ya sameshi, But I think zan tambayi Salma zuwa dare ta faɗa min abin da ya same shi, Bai yi kama da dan uwanta ba”
“To ko mijinta ne?”
Hashim ya faɗa, Maryam ta girgiza kanta ta ce“Bana tunanin haka gaskiya, saboda kai da ka ganta kasan yarince ƙarama, Bana jin ta yi shekaru ashirin wannan. Dole akwai abin da ya fito dasu daga gida”
Hashim ya jinjina kansa kafin ya ce“Haka ne, But a ganina bai dace ki tambayeta ba, If she wish zata faɗa miki da kanta”
Maryam ta yi shiru na wasu sakwanni kafin ta ce“Shikenan duk yanda ka ce sai a yi hakan, Yanzu zaka fita ne?”
Girgiza kansa ya yi ya ce“A'a gaskiya, Kawai zan haƙura sai gobe, Kin san ma next week zan shige Abuja”
Maryam ta haɗe rai kamar ba ita ba ta ce“Yanzu dan Allah har yaushe ka dawo daga Abujan da ka ke shirin komawa? Baka son zama a gida koda yaushe sai ka dinga tafiya kana barina”
Dariya ya yi ya ce“Rigima dai irin taki Maryam, Ke zama ki ke a gidan? I thought kina zuwa school kullum, Beside ma kin san Abujan nan aiki nake zuwa da nima ba zan je ba, Amma kullum ki dinga korafi”
Turo baki ta yi ta ce“Ni dai wallahi ka bari ba yanzu ba”
“Wai cewa nayi gobe zan tafi ko jibi?”
Ya faɗa yana kallonta, Ɗauke kanta ta yi ta ce“Koma yaushe ne bana so ka dinga nesa dani, Gaba ɗaya sai na dinga ji na a cikin duhu wallahi”
Ya jinjina kansa kafin ya ce
“Uhm, Sai ki nemo Haske ai”
Hannunsa ta kama cike da so da ƙauna ta ce“And then u're my light, Kai ne HASKEN CIKIN DUHUN nawa ai”
Hashim ya lumshe idanunsa yana jin so da ƙaunar matar tasa na ƙaruwa cikin ransa, Ya ja kumatunta ya ce“Me too Maryama, Kece Haske a cikin duhuna, Tun ranar da Malam ya aura min ke abubuwa dayawa suka sauya a rayuwata, Inason ki, Ina sonki sosai”
Maryam ta rasa abin cewa kawai ta rungumeshi tana dariya.
****
Asokoro, Abuja.
Da sallama ta shigo ɗakin hannunta riƙe da tray na abinci, Zaune yake kan gadon ya jingina da jikin bango idanunsa a lumshe. Mommy ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a kan table sannan ta zauna gefen gadon tana kallonsa a sanyaye ta ce
“Yallabai”
General ya buɗe idanunsa wanda suka yi jajur dasu, Mommy ta dinga kallonsa cike da tausayawa kafin ta ce
“Ya kamata ka rage damun kan ka, Kana ganin yanda bp ɗinka yake ta hawa, Kada ka jawo mana wata masifar bayan wadda muke ciki dan Allah”
General ya yi mata wani kallo, Ya gyara zamansa sosai kafin ya ce
“Hajara ki ka ce na bar tada hankalina? Na kwantar da hankalina? Zayyad baya gida over a week shi ne hankalina zai kwanta. Yaron nan Amana ne a wajena ke kin sani shi ne baya nan Ban san halin da yake ba ki ke cewa na daina damuwa. To Hajara ta ina zan daina damuwa? Ta ina hankalina zai kwanta? How?”
Mommy ta girgiza kanta ta ce
“Ba fa nace kar ka nuna damuwarka bane, But you have to calm down, At least ka daina wannan zaman kana tunani, Kasan yanayin lafiyarka fa Yallaɓai, Duk abin da ake saboda kai ne, Yanzu idan wani abun ya sameka ai mune a cikin tashin hankali, Kaga saboda haka ya kamata ka sassautawa kanka, In sha Allah Zayyad yana hannu nagari”
Numfasawa General ya yi ya ce“Hajarah dan Allah tashi ki fita”
Mommy ta kalleshi sai kuma ta ce“Yanzu saboda nayi maganar...”
”I said get out!”
Ya faɗa a ɗan tsawace, Tashi tayi jiki a sanyaye ta fice daga dakin.
Parlon Mommah ta shiga dan yanzu ba zaman main parlon take ba, Zaune ta sameta kan sofa ta yi shiru da alama tunani take dan tun bayan ɓatan Zayyad bata da abin yi sai shi. Mommy ta karasa ta zauna kujerar dake kusa da ita ta ce
“Khadijah”
Mommah ta kalleta dan bata san sanda ta shigo ba ta ce“Na'am, Ashe kece”
Mommy ta ce“Kema kina nan kina tunanin kenan”
Numfasawa kawai Mommah ta yi cike da damuwa ta ce“Wallahi bana iya bacci Mommy, Damuwa tayi min yawa, Kullum da Zayyad nake kwana dashi nake tashi, Idan wani abun ya samu rayuwarsa ba zan yafewa kaina ba, Jidda ba zata taɓa jin daɗi ba”
Hawaye Mommy ta fara yi tana kuka ta ce“Kowa ya damu sosai, Allah sarki Jiddah, Mace mai halin kirki, Wallahi hankalina a tashe yake, Allah ya dawo da ɗan nan gida Lafiya, Allah ya sanya yana hannu nagari, Duk wanda ya yi masa wannan mugun abun Allah ga ganshi kuma ka san shi ka hukuntashi, Allah ka nuna mana shi mu ganshi”
Mommah ta girgiza kanta itama tana hawayen ta ce
“Ai shi Allah ba azzalumin bawansa bane, Duk wanda ya aikata wannan abun ya san kansa, Kuma Allah ba zai bar shi ba, Ko nan kusa ko nesa sai Allah ya yi hukunci domin baya barin zalunci”
Mommy ta ce“Wannan haka yake, Wannan yarinyar ita da Allah, Ko su wane suka sakata aikin Allah masani”
Mommah ta ce“Akwai Allah ai”.
****
Tun da tafara magana Jiddah ke kallonta taba taɓe baki, Tana yin shiru ta gyara zamanta daga kwancen da take ta ce“Kin gama?”
Amrah ta kalleta ta ce“What do you mean by nagama?”
A hasale Jidda ta ce“Duk abin da ki ka ɗauka haka nake nufi Amrah, zantukanki basu da wani amfani a gareni” Amrah ta girgiza kanta ta ce“Jiddah ki ji tsoron Allah, Ki sani duk wanda ki ka cutar Allah ba zai bar ki ba, Koda ace babu wnada ya gani ai kin san Allah baya bacci, Kuma yana sane dake!”
“And who told you bansan me nake ba? Ko kin fini sanin Allah ne Amrah? Ko kin san abin da nasani ne, Ina ruwanki dani ma”
Amrah ta ce“Ki yi duk abin da ki ke ganin zaki yi Jiddah, But you have to know akwai ranar danasani, Mene ribarki idan kin cutar da ɗan Adam, Cutarwa mafi muni, Kin san girman abin da ki ka aikata kuwa?”
Sauka daga gadon ta yi ta riƙe ƙugunta tana yi mata wani banzan kallo ta ce
“Let me tell you something Amrah, Idan kin ga dama ki fita daga nan ki je ki sanarwa da kowa, Ni na haukata Zayyad! Ni Jiddah ni ce na haukatashi kuma wallahi ko yanzu ya dawo daidai sai na sake haukatashi! Zayyad ba, Ba zai taɓa samun jin daɗin rayuwa ba sai dai idan bana numfashi wallahi!”
# HCD
# Zayyad
# Salma
# Jiddah
# Nanameera
08106608363.
*HASKEN CIKIN DUHU*