Chapter 17-18: "Where Did You Leave My Heart?"
Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 16 min read
Nanameera, YOTA/023.
Danshin ruwan da taji akan fuskarta shi ne ya farkar da ita, Ta shiga buɗe lumsassun idanunta a hankali tana ƙarewa wajen kallo.
“Sannu yarinya, Sannu”
Salma ta kalli wanda ke maganar tana ƙoƙarin tashi zaune, Wani ɗan dattijon mutum ne hannunsa riƙe da ledar pure water, Ganin bata ce komai ba ya sanya ya sake cewa
“Daga ina ki ke? Ina iyayenki?”
Kalle kalle ta shiga yi sai kuma ta miƙe tsaye cikin tashin hankali ta kalli mutumin ta ce
“Dan Allah Baba ƙarfe nawa yanzu?”
Tashi ya yi daga durƙushen da yake ya zaro keypad daga aljihunsa ya ɗan danna sai kuma ya ce
“Yamma ta yi sosai, Ƙarfe 5:46pm”
Dafe kanta tayi saitin inda ya fashe, Ta runtse idonta saboda yanda take jin zafi.
“Ya kamata ki je asibiti yarinya Allah ya tsare gaba”
Mutumin ya faɗa yana ƙoƙarin barin wajen, Da sauri tabi bayansa tana faɗin
“Babba dan Allah baka ga wani mutum anan ba? Wani fari kamar mahaukaci”
Girgiza mata kai ya yi ya ce“A'a yarinya ban ganshi ba”
Shiru Salma ta yi tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, Ina ya tafi?. Juyawa ta yi ta koma in da take kwance, Ɗankwalinta ta ɗauka ta yafa sannan ta bar wajen. Yawo sosai Salma ta dinga yi cikin gangaren Kabayi amma bata samu Zayyad ba, Wanda ya gashi ma bata gani ba.
Ana kiraye-kirayen sallar magriba ta samu wani dakali ta zauna, Fashewa ta yi da kuka baƙin ciki, Gaba ɗaya bata san yanda zata yi ba, Ga yunwa ga ƙishirwa, Ga Zayyad ya ɓata bata ganshi ba. Ta ina zata fara?
“Laa Salma!”
A ɗan firgice ta ɗago kanta, Da mamaki suke kallon juna kafin Khadijah ta yi murmushi ta ce
“Daman kina nan? Me yasa bana ganinki?”
Tashi tsaye Salma ta yi tana kallon Khadijah amma bata ce komai ba.
“Na ganki haka ko baki da lafiya ne?”
Khadijah ta sake tambayarta, Kuka Salma ta fara yi ba tare da ta ce komai ba. Kamo hannunta Khadijah ta yi tana girgiza kanta ta ce
“Yi haƙuri Salma, Nima ban ji daɗin abin da ya faru ba, Na so a ce Ummana ta bar ki kin ci gaba da zama a gidanmu”
Salma goge hawayenta ta shiga yi tana jan numfashi ta ce
“Babu komai Khadijah, Ai kona zauna a gidanku dole wata rana zan bar shi, Kaddarata kenan, Tun da Abbana ya riga da ya mutu shikenan ai”
Sosai jikin Khadijah ya yi sanyi, Taɓa jikin Salman ta yi ta ji zafi, Ta janye hannunta ta ce
“Kin ci abinci?”
Girgiza mata kai Salma ta yi, Ta buɗe hand bag ɗin hannunta ta ɗebo kuɗaɗe, Dubu ashirin ta kirga sannan ta miƙawa Salma. Amsa ta yi tana kallonta, Khadijah ta ce
“Ki dinga cin abinci kin ji”
Girgiza kai Salma ta yi ta zari dubu ɗaya daga cikin kuɗin ta miƙawa Khadijah sauran tana cewa
“A'a wannan ma ya isheni ai”
Harararta Khadijah ta yi ta ce
“Nasan da hakan kuma na baki ai, Ki riƙe a wajenki zai miki amfani”
Shiru Salma ta yi tana kallon kuɗin can kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ce
“Nagode sosai, Allah ya biya ki”
Khadijah ta yi murmushi ta ce“Ameen Salma, Bari naje kar na rasa abin hawa”
Toh kawai Salma ta ce, Khadijah ta juya ta bar gurin. Jujjuya kuɗin Salma ta dinga yi tana tunanin yanda zata yi da su. Zayyad ne ya ƙara faɗo mata a rai, Ta gyara riƙon kuɗin sannan ta bar wajen tana tafe da sauri.
Kai tsaye Orange market ta nufa, Ta dinga yawo cikin kasuwar amma Allah bai haɗata da Zayyad ba, Gajiya ta yi ga yunwa data isheta, Idanunta har rufewa suke saboda tsabar azaba. Dubawa ta yi ta ga duk masu abincin kasuwar sun tashi, Haka ta bar kasuwar tana tafe kamar zata faɗi. A bakin titi ta sami wani mai gashi Gurasa, Ta ƙarasa gabansa ta siya ta ɗari biyar, Wani kanti a gefe ta shiga ta amso ruwa pure water sannan ta ci gaba da tafiya.
***Ban da kuka babu abin da take har ta dawo inda suka zauna ɗazu da Zayyad saboda wajen kamar yafi mata tsaro, Inuwar mutum ta hanga zaune kan yashi ya tankwashe ƙafafunsa, Da gudu ta ƙarasa duk da yanda take jin jikinta. Turus ta yi a kansa tana kallonsa, Wasa yake da tarin ƙasa da yashin wajen, Idan ya haɗa sai ya wargaza yana yi yana yan maganganu.
Sakin ledar hannunta ta yi ta durƙusa gabansa tana kallonsa, Ɗago kansa shima ya yi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi, Fuskarsa tass da ita kamar bashi ba, Duk yanda take jin tsoronsa haka ta dake ta ce
“Ina ka tafi? Me yasa zaka yi tafiyarka?”
Shiru ya yi mata Sai dai bai ɗauke Idanunsa daga kanta ba, Zaman dirshan Salma ta yi akan yashin sai kawai ta fashe da wani irin kuka. Bin ta da kallo ya dinga yi ganin yanda take kukan kamar ranta zai fita, Tashi ya yi ya ɗauko ledar bayansa ya miƙo mata, Ɗago kanta ta yi ta kalli ledar sai kuma ta kalleshi, Karɓar ledar ta yi ta cillar da ita gefe sannan ta ci gaba da kukanta. Kwaɓe fuska Zayyad ya yi sai kuma ya ɗora kansa akan cinyarta ya fara kukan shima. Tsit Salma ta yi ta ɗago kanta tana kallonsa, Kuka sosai yake yi tana jin zubar hawayensa kan cinyarta, Ji ta yi jikinta ya yi sanyi ta ɗago kansa a hankali ta ce
“Ka daina kuka ya isa”
Gyada mata kai ya dinga yi kamar ƙaramin yaro, Ta sanya hannunta ta goge masa hawayen sannan ta ce
“Shikenan nima nayi shiru kai ma ka daina kuka Yaya Yad, Amma nan gaba kar ka sake tafiya wani wajen ka barni”
Bai bata amsa ba, Sai kawai ya tashi, Ta bishi da idanu tana kallon abin da zai yi. Ledar data yar ya ɗauko sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, Da kansa ya buɗe ledar, Shinkafa da miya ce a ciki har da salad, Ta kalleshi da mamaki ta ce
“Ina ka samo abinci? Wane ya baka?”
Bai bata amsa ba, Ya ɗauko ledar pure water dake bayansa ya fasa, Hannunta ya kama ya fara wanke mata kamar yanda ta yi masa ɗazu. Ta dinga kallonsa tana murmushi mai haɗe da hawaye, Sai da ya gama tsaf sannan ya tura mata ledar gabanta.
Gefen hannunta ta sanya ta share hawayenta sannan ta yi murmushi ta sanya hannunta cikin ledar, Ɗiban abincin ta yi ta kai baki bayan ta yi bismillah, Ya dinga kallonta tana cin abincin har ta gama. Murmushi ya yi sannan ya jawo wata ledar ya shiga buɗewa yana cewa
“Yanzu sai na baki magani ki sha, Ki kwanta”
Ya yi maganar yana jin jina kansa, Buɗe ledar ya yi taga duk tarkacen ledojin pure water, ledar biscuits, ledar chocolate har da robar lemo. Salma bata san sanda ta fara hawaye ba tana shassheƙar kuka a hankali, Ɗago kansa ya yi ya kalleta yana ɗaura wani zaren tabarma jikin robar lemon ya ce
“Ki bar kuka yanzu zan baki magani”
Wani irin tausayinsa ta ji ya rufeta, Ta janye ledar daga gabansa, Kafin ta yi magana ya ce
“Ina zaki kai min magungunan, Daga asibiti fa nake”
Shar hawaye suka sake zubowa kan fuskarta, Cikin shassheƙar kuka ta ce
“Ajiye maka zan yi”
Zai sake magana ta fito da ledar Gurasar data siya. Murmushi ya yi yana kallonta ya ce
“Mommah Abinci ki ka siyo min?”
Gyaɗa masa kai ta yi still crying ta ce
“Eh, Kaci, Sai ka bani maganin”
Jinjina kansa ya yi sannan ya amshi ledar daga hannunta, Buɗewa ya yi ya leka sai kuma ya ture yana haɗe fuska, Ta kalli ledar sai kuma ta kalleshi ta ce
“Mene ne? Ko baka so”
Tura baki ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce
“Ni ba irin wannan ba, Mene wannan?”
Ɗan murmushi ta yi ta ce
“Gurasa sunanta, Yana da daɗi fa, Ni na siya maka ko baka son abincin hannuna?”
Ta ƙare maganar da damuwa akan fuskarta. Kallonta kawai Zayyad ya yi sai kuma ya sake karɓar ledar ya ɗora kan cinyarsa ya sanya hannunsa ya ɗauko slice na gurasar ya kai bakinsa. Lumshe idanunsa ya yi yana murmushi ya ɗauko wata ya sake kai wa baki, Salma kallonsa kawai take tana murmushi mai ɗauke da hawaye.
Sai da ya kusa cinyewa sannan ya kalleta, Harararta ya yi sai kuma ya ce
“Ke mene ne ki ke kallona ko kin sanni ne?”
Girgiza kanta kawai ta yi tana murmushi ta ce
“Ni ban sanka ba”
Ya gyaɗa kansa ya ce
“Yawwa to dai, Ni bana son kallo.”
Salma dai bata ce komai ba sai kallonsa take, Tas ya cinye gusarar ya miƙo mata ledar yana cewa“Amshi nan ki je ki ɓoye” juya ledar ta yi sai kuma ta ce“Ledar zan ajiye kuma?”
A fusace ya ce “Ko ba zaki ajiye bane? Ni abokin wasanki ne?”
Shiru Salma ta masa, Ya tashi tsaye ya shiga zagaye a filin sai kuma ya dawo, Shaƙe mata wuya ya yi ta baya, Ta sanya hannunta duk biyun tana dukan nasa hannun. Cikin kakkausar murya yake cewa
“Ni abokin wasanki ne ina miki magana zaki min banza, Kin ga ina miki wasa? Ko mahaukaci ki ka ɗaukeni!”
Dakyar Salma ke numfashi, Ta ci gaba da dukan hannunsa, Ƙin cikata ya yi ya sake takure hannunta a wuyanta, Idanunta suka fara firfitowa.
Kamar daga sama taji wani mufini na magana, Ya ƙaraso wajen ganin yanda Zayyad yake durƙushe, Taɓa shi ya yi ai kuwa ya saki Salma ya shaƙe nasa wuyan. Dafe wuyanta ta yi tana sauke wani wahalallen numfashi, Sai dai ganin yanda Zayyad yana ƙoƙarin raba mutumin da numfashinsa ya sanya ta tashi tsaye, Ihu ta saki ta ƙarasa gabansu. Rirriƙeni Zayyad ta yi tana kuka ta ce
“Dan girman Allah Yaya Zayyad ka bari, Ka dawo cikin hankalinka mana, Ka rabu dashi”
Hannu ɗaya ya saka ya hankaɗata ta fadi ƙasa sannan ya mai da hankalinsa kan mutumin yana sake matse hannunsa.
Duk yanda ta bugu a ƙasa hakan bai hanata sake yunƙurawa ta tashi ba, Ta sake nufarsu ganin yanda idanun mutumin suka yi, Dukan Zayyad ta shiga yi tana bashi hakuri amma sam ya ƙi saurarenta, Ta yi baya ta zubawa sarautar Allah ido, Can kuma ta sake nufarshi da sauri. Dagewa ta yi ta sakar masa ciwo a gefen ciki zafi da kiɗimar daya shiga ya sanya ya saki wuyan mutumin ya dafe gefen cikinsa. Tafiya mutumin ya yi ya fadi ƙasa ya riƙe wuyansa yana sakin numfashi dakyar, Da gudu ta ƙarasa wajensa tana kallonsa ta ce
“Sannu Baba, Tashi ka gudu kar ya sake biyo ka”
Muryarsa bata fita ya ce
“Mahaukaci ne daman?”
Gyada masa kai kawai ta yi tana hawaye. Ya girgiza kansa ya ce “Meyasa ba zaki kai shi asibiti ba, Ina iyayensa?”
A sanyaye ta ce“Zan kai shi Baba, Ka tashi ka tafi kar ya sake dawowa kaga babu mai cetonmu”
Dakyar mutumin ya tashi ya bar wajen yana tafe jiki babu kwari, Salma ta maida idanunta kan Zayyad wanda ke tsaye har sannan yana kallon gefen cikinsa. A mugun tsorace take dashi dan ba ƙaramar shaƙa tasha ba, Gani ta yi ya maido idanunsa inda take, Gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Tashi tsaye ta yi tana kallonsa a firgice ganin ya fara tawowa, Da gudu ta juya ta bar wajen, Yana ganin haka shima ya bita da gudun.
Zagaye suka dinga yi cikin filin, Har da shiga gonar mutane, Cikin rashin sa'a ta daki wani dutse ta bige ƙafa, Durƙushewa ta yi a wajen ta runtse Idanunta. Kallon ɗan yatsan ta yi taga yana jini ta matse da hannunta tana jin wata irin azaba. Dariyar data ji ya sanya ta juyo tana kallonsa, Zaune ta gansi yana tuntsira dariya yana girgiza kansa. Ɗauke kanta tayi daga kallonsa ta tashi ta fara tafiya a hankali, Sai kawai taga shima ya tashin ya sake biyota. Ihu ta saka ta kwashi gudu ta take ƙafar duk da azabar da take mata. Suka ci gaba da zagaye cikin filin, Gajiya ta yi ta tsaya, Cak shima taga ya tsaya yana nunata yana dariya.
Kuka ta fara yi tana kallonsa ta ce
“Kaga Yaya Yad ka rabu dani, Ni ka daina bina wallahi, Bana so”
Tuntsirewa ya yi da dariya har da tafa hannu. Ta goge hawayenta sai kuma ta juya ta bar gurin, Ganin shima ya ci gaba da tawowa ya sanya ta sake ɗiba da gudu. Zayyad kuwa tsayawa ya yi yana dariya yana girgiza kansa, Can kuma ya juya ya koma inda suke zaune.
****
Asokoro, Abuja.
Turo kofar dakin ta yi a hankali, Zaune ta hangeta gefen gado ta zuba uban tagumi, Ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso ciki. A gefenta ta zauna tana kallonta ta ce
“Khadijah”
Ɗago kumburarrun Idanunta ta yi ta kalli Mami, Kawai ta rungumeta tana fashewa da kuka. Ita kanta Mami dauriya kawai take hawaye suka shiga bin fuskarta, Sun ɗauki lokaci a haka kafin ta janye jikinta daga nata tana kallonta ta ce
“Ya isa haka, Ki yi shiru, In sha Allah za'a gan shi”
Cikin shassheƙar kuka Mommah ta ce
“Yaushe Mami? a ina za'a ga Zayyad? Mami ya haukace fa, Ta haukata shi daga taimako”
Mami ta ce
“Karki damu in dai an ganshi ai da sauki, General ya saka a baza hotunansa a Abuja, Ai duk inda yake ba zai shige nan ba. Zayyad ba zai ɓata ba in sha Allah”
Jinjina kai Mommah ta yi ta ɗauke kanta tana kallon gefe ta ce
“Wallahi Mami nayi nadama, Nayi dana sanin yarda da yarinyar nan, Babu kama wallahi”
Numfasawa Mami ta yi ta ce“Duk da haka kema kina da laifi, Akan me zaku bari ya bar gidan nan da sunan ya haukace? Korarsa fa kuka yi. Koda Zayyad ya haukace at least ya kamata a ce an bar shi a gidan nan an duba lafiyarsa, Akan me za'a koreshi daga gidan ubansa?”
Cike da damuwa ta ce “Mami ai dole sai ya bar gidan a sannan, Haka aka ce in dai har ya fadi wanda ya masa asiri to sai dai ya bar gidan, Shiyasa”
Tsaki Mami ta yi ta ce“Ai shikenan sai ku yarda da wannan maganar”
Mommah zata yi magana aka buɗe ɗakin aka shigo, Kallonsu ya yi sai kuma ya ce
“Mami dare nayi”
Kallon agogon hannunta ta yi sai kuma ta ce “Tom Ahmad gani nan” Okay ya ce sannan ya kalli Mommah wadda ke hawaye, Bai sake cewa komai ba ya juya ya fice daga ɗakin. Numfasawa ta yi sannan ta sake maida idanunta kan Mommah ta ce
“Ni zan tafi dare nayi, Duk yanda ake ciki sai mu yi waya, Amma a tabbata an samo Zayyad”
Toh kawai Mommah ta iya cewa, Mami ta tashi ta fita daga ɗakin dan Mommah ba fita zata yi ba drip ne a hannunta. A corridor ta sami Ahmad ya yi shiru daga gani wani abun yake tunani,
“Ahmad”
Mami ta kira sunansa. Ɗago kansa ya yi ya kalleta da idanunsa wanda ruwa yake a kwance ya ce “Na'am Mami”
A sanyaye ta ce ”Muje”
Okay ya ce sannan ya fara sauka daga stairs ɗin, Har ta nufi stairs ɗin sai kuma ta juya ta buɗe ɗakin ta shiga. Babu kowa a parlon hakan yasa ta shige bedroom ɗin kai tsaye. Zaune ta hangeta tsakiyar gadon ta cure jikinta waje ɗaya sai shassheƙar kuka take. Numfasawa Mami ta yi sannan ta ƙarasa ta zauna gefen gadon still looking at her ta ce
“Auta”
Ɗago fuskarta wadda ta yi caɓa caɓa da hawaye ta yi ta kalli Mami, Girgiza kai Mami ta yi ta ce
“Ki daina kukan nan mana Nayla”
Kamar Mami ta turata haka ta sake rushewa da wani sabon kukan. Mami ta riko hannunta cikin sanyin murya ta ce “Kuka ba zai magani ba Nayla, addu'a zaki dinga yiwa Yayanki In sha Allah za'a gan shi”
Cikin shassheƙar kuka ta ce
“Mami Yaya Zayyad fa ya haukace, Mami yayana ya haukace, Kuma wallahi ba Salma ce ta haukata shi ba sharri aka yi mata. Duk su Mommy sun ƙi yarda dani, Salma bazata aikata haka ba”
Goge mata hawayen Mami ta yi ta ce“Ko ita ce ko bata ita ba ce Allah zai bayyana Nayla, Allah zai kawo hasken da zai warware komai, Gaskiya bata taɓa ɓuya saboda haka bana son kina wannan kukan ki tashi ki yi wanka ki ci abinci kin ji”
Jinjina kanta kawai ta yi amma ba dan tana jin zata iya tashin ba. Mami ta sauka daga kan gadon ta ce
“Be a good girl kin ji Nayla, In sha Allah idan na dawo zan tafi dake”
To kawai Nayla ta iya cewa tana goge hawayenta. Mami ta juya ta bar ɗakin.
Sun ɗan yi nisa Ahmad ya kalleta ya ce
“Any news Mami?”
Girgiza kanta ta yi tana kallon titi ta ce“Ko kaɗan Ahmad, Ban gane in da suka dosa ba gaba daya, I'm bit confused yanda general zai bar Zayyad ya fita a gidansa. Wannan ba daidai bane!”
Furzar da iska Ahmad ya yi yana ci gaba da kallon titi ya ce“I think so Mami, Duk da ban san yarinya ba amma ina jin kamar ba zata yi haka ba, Yanda suke faɗa fa sa'ar Nayla ce, Tayaya mai shekaru irin na Nayla zata yi tunanin haukata mutum kamar Zayyad, And idan ma ta haukatashin wace riba take da? Dama cewa aka yi tana son aurensa sai nace”
Mami ta girgiza kanta ta ce“Bar sharrin duniya Ahmad, Za'a iya haɗa baki da ita koda ba ita ce take da desire na haukatashin ba. Wannan ba zamu yanke hukunci kai tsaye ba, Amma duk abin da ya faru bai dace General ya bar shi ya fita a gida ba tunda har ya san bashi da hankali, Amma in sha Allah za'a ganshi cause sun saka matakan tsaro sosai”
Ahmad ya ce“Allah ya sa hakan, Amma Abin yana bani mamaki Mami, Wai Zayyad ya haukace, How?”
Numfasawa Mami ta yi ta ce“Kaddararsa kenan, Allah ya bashi ikon cinyeta ya dawo dashi gida lafiya”.
Ahmad ya ce Ameen sannan ya maida hankalinsa kan tuƙin da yake.
****
Tafiya take kamar mara gaskiya tana leƙen inda yake, Har sannan yana zaune kan yashin yana wasa dashi. Ta ƙaraso tana kallonsa hannunta riƙe da takalmanta, Zama ta yi can nesa dashi tana kallonsa. Ya ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya tuntsire da dariya, Gyara zamanta ta yi tana gani ko tashi zai yi sai taga ya yi kwanciyarsa nan ƙasa yana ci gaba da dariya. Ita dai Salma kallonsa kawai take, Ta yi shiru tana tunanin yanda zata yi, Ba zata ci gaba da zama dashi a haka ba, Kuma bata san inda zata kai shi ba. Babban abin da ya dameta daya kasance basu da wajen kwana, Ga yanayi na damuna. Tana wannan tunanin ta ga ya tashi daga kwancen da ya yi, Ya dawo inda take ya zauna yana bin ta da wani irin kallo, A ɗan tsorace ta ce
“Mene ne...?”
Langwaɓar da kansa ya yi ya ce“Nurse Mommah ce acan gurin zata tafi dani kar ki bar ta”
Ji tayi gabanta ya faɗi ta kalli inda yake nuna matan amma bata ga komai ba, Sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta yi sai kuma ta ce
“Babu kowa fa, Ka kwanta dare ya yi”
Maƙale kafada ya yi ya ce“To kema ki kwanta ni ba bacci zan yi ba”
Murmushi ta yi ta ce“To zan kwanta kai ma ka kwanta” gyaɗa mata kai ya yi ta gyara ɗankwalinta ta kwanta kan yashin duk da sanyin da wajen ya ɗauka. Lumshe idanunta ta yi don daman mugun bacci take ji nan da nan kuma ya ɗauketa, Ƙura mata idanu Zayyad ya yi yana kallonta can kuma shima ya kwanta ya rufe idanunsa.
Can cikin bacci taji kamar ana taɓa fuskarta, Ta buɗe Idanunta a hankali, Inuwar mutane ta kalla, Ta tashi zaune tana ja da baya, Kallon mutumin dake tsaye a kanta ta yi, Ya saki murmushi haƙoran suka bayyana duk da duhun da wajen yake da cikin kakkausar murya ya ce
“Ummulsalma kenan, Ba zaki iya gujewa ƙaddararki ba, Dole ki ci gaba da zama da wannan mahaukacin domin ke ce hasken rayuwarsa, Ke ce wadda za ki fito dashi daga cikin duhun da yake, Baki isa ki sauya wannan al'amarin ba, Saboda haka ki shirya kalubale kala kala anan gaba, Ba'a fara komai ba Salma, Baki fara ganin komai ba cikin abubuwan da zasu faru nan gaba daga ƙarshe kuma zaki yi farin ciki, Zaki ji dadi sai dai wani abu zai zo da zai yanke wannan jin daɗin...!”
# HCD
# Light within the darkness
# Yaya Yad
# Salma
# Nanameera
08106608363
For more information contact me.
*HASKEN CIKIN DUHU*