Chapter 14: Rescued by Fate
Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 13 min read
Nanameera, YOTA/23.
Hajiya Jinjin ta ƙare maganar tana zabga mata wata uwar harara, Ba Salma kaɗai ba har Khadijah sai da ta kalli mahaifiyarta, Koda wasa bata yi tunanin Umma Rahmatu tafiyarta ta yi ta bar Salma ba, Duk zatonta taje ta dawo ne kamar yanda ta faɗa. Salma kasa cewa komai ta yi, Sai bin ta take da kallo, Hajiya Jinjin ta ja hannun Khadijah suka shige ɗaki. Sai a sannan Salma ta fashe da wani irin raunataccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Yanzu ina zata je? Wa zata kalla taji daɗi? Da wa zata yi rayuwa? Babu dangi babu ƙawaye babu wanda tasani a rayuwarta, Ina zata nufa??. Ta durƙushe a tsakar gidan ba tare da ta damu da jiƙewarsa ba tana ci gaba da kuka. Ta ɗauki mintuna a wajen kafin Khadijah ta fito daga ɗakin sanye da mayafi ta ci uwar kwalliya, Ta ƙaraso gabanta kamar ta shigeta sai kuma ta ce
“Da kin zo mun tafi tare Salma, Tun da babu in da zaki je yanzu”
Ɗago kanta Salma ta yi ta kalli Khadijah sai kuma ta girgiza kanta bakinta na rawa ta ce“Ni ba zan je ba”
“Kin gwammaci ki dinga yawo a gari Salma?”
Khadijah ta tambayeta. Kafin ta bata amsa Hajiya Jinjin ta fito daga ɗaki tana kallonsu ta ce“Ke shige ki tafi abin da ke gabanki dare nayi, Ke kuma ki tashi ki bar gidan nan tun da ba za'a yi abun arziki dake ba wallahi ba zan iya ciyar dake ba, Ƴata ma bata zauna ina ciyar da ita ba ballantana ke da babu abin da ya haɗani dake!” Ta ƙare maganar idanunta kan Salma. Girgiza kai Khadijah ta yi duk sai ta ji bata ji daɗi ba, A sanyaye ta ce“Umma ki bari mana, Zata tashi” Harararta Hajiya Jinjin tayi ta ce“Kin shige kin bar gidan nan ko sai ranki ya ɓaci kema” Tura baki Khadijah ta yi ta fice daga gidan tana waiwayen Salma. Sake daka mata tsawa Jinjin tayi Salma ta tashi jikinta na rawa ta yi hanyar ɗakin da suke.
“Akwai abin da ki ka ajiye a nan ne da ki ke nema?”
Cikin shassheƙar kuka ta ce“Abuna zan ɗauka” Daga haka ta shige ɗakin, Bata fi minti biyu ba ta fito har sannan kuka take tayi waje jiki a sanyaye, Hajiya Jinjin ta bita da harara sai kuma ta yi tsaki ta ce“Gayyar tsiya!”
Yayyafi ake har sannan, gabaɗaya babu mutane a bakin titin Kabayin kasancewar dare ya fara yi kowa ya kama gabansa, Cikin wannan yanayi take tafiya a hankali jikinta na wata irin rawar sanyi, Tafiya kawai take ba tare da ta san inda ta nufa ba, Batasan kowa ba, Bata san ko ina ba, Babu wani wanda zata ce wannan danginta ne balle taje gidansu. Gajiya ta yi da tafiyar ta nemi dakalin wani gida ta zauna tana mai da numfashi, Zuwa sannan ko kukan ta gagara yi sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai.
Abacha road, Mararaba.
Leƙo kansa ya yi yana kallonsa ya ce“Yanzu ka kwana ka ke ganin asara? Ba gobe sai mu tafi tare ba” Zayyad dake danna wayarsa ya ce“Look ba zan iya kwana ba, Yanzu fa ba wani dare ne ya yi ba, And kuma nayi wa Anisa alƙawarin zamu haɗu” Da mamaki Ahmad ya ce“Anisa kuma? Meya haɗaka da Anisa Zayyad?” Ɗago kansa ya yi ya kalleshi bai ce komai ba. Ahmad ya girgiza kansa kafin ya ce“But kasan abin da kake ba dai dai bane right? Bayan an saka ranar aurenka da wata matar amma ka ci gaba da kula wata, Kuma kasan ba aurenta zaka yi ba” Tsaki Zayyad ya yi sannan ya ce“Zaka fara ko? To ba wani abun zan je yi wajenta ba zan faɗa mata gaskiya ne, Sai ka kwantar da hankalinka” Murmushi Ahmad ya yi dan ba ƙaramin daɗi ya ji ba ya ce“Ai dole hankalina ya tashi, Shikenan ka je amma dan Allah daga bata haƙurin kar ka sake wani abu” Kallon sheƙeke Zayyad ya masa kafin ya ce“Wani abu like how?” Girgiza kai Ahmad ya yi yace“Calm down, Ka gaida Mommah da Nayla” A can maƙoshi Zayyad ya ce“I'll” Ahmad ya janye kansa daga motar yana ɗaga masa hannu, Zayyad ya yi reverse ya bar ƙofar gidan. Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke sai kuma ya girgiza kansa, Ya juya ya shige cikin gida.
Yana kan titin Orange market wani irin ruwa ya kece, Yanda ruwan yake zuba da matuƙar yawa ya sanya ba zai iya ci gaba da tafiya ba, Ya nemi gefe ɗaya ya yi parking yana ɗan tsaki a hankali. Idan da abin da Zayyad ya tsana a rayuwarsa bai shige zubar ruwan sama ba, Gaba ɗaya ya ji baya jin daɗin zaman motar. Kwalin cigarette ya ɗauko ya kunna da lighter ya fara zuƙa yana furzar da hayaƙin a hankali, Yana nan zaune sai da ya shanye tsinke uku kafin ya haƙura ya jingina da jikin motar yana jin yanda ruwan yake zuba kamar da bakin ƙwarya. Kamar wanda aka tsikara haka ya buɗe idanunsa, Haka kawai ya ji ta faɗo masa a rai, Kallon agogon hannunsa ya yi yaga karfe 8 har da 12 na dare, Ya sauke ajiyar zuciya sai kuma ya kunna motar ya ci gaba da tafiya, Yana zuwa bakin titin Kabayi ya tsaya yana kallon hanyar, Ko ina a jagwalgwale yake ya ɗan yi tsaki kafin ya danna motar cikin layin, A ƙofar gidansu ya yi parking ya yi shiru yana kallon gidan kafin ya sakko daga motar, Zuwa sannan kuma ƙarfin ruwan ya ragu sai yayyafi a hankali. Tsayawa ya yi yana tunanin yaron da zai samu ya kira masa ita sai ga wani mutumi ya tawo daga hanyar masallaci hannunsa riƙe da carbi. Da mamaki Zayyad ya kalleshi dan iya saninsa babu namiji a gidan, Mutumin ya tsaya shima yana mamakin ganinsa a ƙofar gidansa. Ƙarasowa ya yi suka gaisa kafin Zayyad ya ce“Sannu Malam" Mutumin ya yi murmushi ya ce“Yawwa Alhaji, Lafiya dai?” Zayyad ya ce“Salma nake kira yarinyar nan gidan?” Ya faɗa yana nuna kofar gidan, Shiru mutumin ya yi sai kuma ya ce“Allah sarki, Ai ko sun tashi, Dan yanzu ni ne a gidan na siya a hannun wata mata”. Sosai Zayyad ya yi mamaki amma ya ce“Allah sarki, Ko kasan in da suka koma?" Girgiza kai ya yi ya ce“A'a wallahi ban sani ba, Dan ban ma taɓa ganinsu ba” Jinjina kai Zayyad ya yi ya sake bashi hannu suka gaisa ya ce“Tom Nagode sai an jima” Murmushi mutumin ya yi ya ce“Nima haka, A sauka lafiya” Zayyad ya juya ya shige motarsa yana mamakin al'amarin.
Har ya fito titi tunanin maganar da mutumin ya faɗa masa yake, To ina suka koma? Me yasa bata sanar dashi ba? Taɓe bakinsa ya yi tunawar ba wata alaƙa ba ce tsakaninsu ballantana har ta sanar dashi abin da suke ciki. Saurin taka burki ya yi, Ya tsaya yana kallon ikon Allah, fitilun motar ya kunna ya dallaresu da idanu, Hannayensu suka saka suka shiga rufe fuskarsu. Maza ne su uku sai mace guda ɗaya, Tsaki Zayyad ya yi a fili ya ce“Nonsense” Daga haka ya kunna motarsa yana ƙoƙarin barin wajen ya ji ihun yarinyar, Har zai shige sai kuma ya tsaya. A hankali ya fito daga motar yana kallon in da suke, Gaba ɗaya sun yi rumfa sun saka yarinyar a tsakiya sai ihu take, Ya ƙarasa gabansu ya jawo rigar ɗaya daga cikinsu. Juyowa suka yi duka, Da alama ma duk a buge suke, Yarinyar na ganin haka ta ɗago fuskarta. Da wani irin mamaki Zayyad ke Kallonta, Ita kuwa ko lura da waye ma bata yi ba, Ta rufe fuskarta tana ci gaba da kuka har sannan, Hannunta ɗaya ya riƙe ganin tana ƙoƙarin guduwa. Ta sake fashewa da kuka tana ƙoƙarin kwace hannun nata, Ji tayi an janyeta gaba ɗaya ya riƙeta sosai har sannan idanunsa na kansu. Tsaki mutumin ya yi ya kawo hannunsa yana shirin kwaceta, Murɗe masa hannu Zayyad ya yi ya saki wani razanannen ihu yana yarfe hannu, Ji ka ke ƙas wanda ke alamta cewa ya ƙarya masa hannun, Saurin ja da baya sauran suka yi, Ya hankaɗashi yana masa wani irin shegen kallo. Durƙushewa ya yi a wajen yana birgima ya riƙe hannun da ɗayan hannun, Salma data gama tsorata ta sake ƙamkameshi tana sakin wani irin kuka, Jan hannunta ya yi ya koma in da ya yi parking motarsa ya buɗe front seat ya sakata sannan ya zagaya ya shiga motar shima, Bai ko kalli in da take ba ya ja motar ya ci gaba da tafiya. Sai da suka shigo garin Abuja around 9:20pm sannan ya samu gefen titi ya yi parking jin yanda take kuka a hankali. Furzar da iska ya yi daga bakinsa jin yanda take neman damunsa ya ce“Ko kimin shiru ko kuma ki saukar min a mota” A matuƙar razane ta ɗago kanta tana kallonsa, Ya kalleta fuskarta ta yi caɓa caɓa da hawaye da majina, Girgiza kanta ta shiga yi ƙoƙarin yin magana take amma kukan da take ya hanata. A nutse ya ce“Yau kuma mene ya haɗa ki da maza?” Shiru ta yi masa tana ci gaba da kukanta, Sosai ransa ya ɓaci dan ya tsani ya yiwa mutum magana ya ƙi bashi amsa. Ya sanya hannunsa ya jawota har suna iya jin nunfashi juna murya a dake ya ce“Baki ji me nace miki bane?” Madadin ta bashi amsa sai kuma ta faɗa jikinsa ta fashe da wani sabon kukan, Shiru Zayyad ya yi jin yanda ta zagaye hannayenta a jikinsa gabaɗaya ta ɓata masa gaban riga da majina da hawaye. Shiru Zayyad ya yi yana kallonta, Ta ɗauki lokaci mai tsawo tana kukan kafin ta fara sauke ajiyar zuciya a hankali, Sai a sannan ya shafa kanta ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“Ya isa haka, Yi shiru kin ji” Yanda ya yi maganar ya sanyata sake fashewa da wani sabon kukan, Ta rufe fuskarta a ƙirjinsa. Murmushi ya yi ya ce“Oh dan na baki haƙuri shi ne ki ka ci gaba?” Ta yi shiru bata ce masa komai ba. Ganin ta yi shiru ya sanya ya leƙa fuskarta ya ce“To sakeni mana” Kunya ce ta rufeta, Ta yi saurin ɗaga shi ta koma gefe tana sunkuyar da kanta. Girgiza kai kawai Zayyad ya yi ya gyara zamansa yana kallonta ya ce“Now tell me what happened? Me ki ke yi a waje da daddare? Meya samu gidanku?” Saurin kallonsa ta yi hawaye na sake zubowa kan fuskarta
“Kar na sake tambayarki”
Turo baki ta yi, Cikin shassheƙar kuka ta ce“Ummana ce ta tafi ta barni, Ta siyar da gidan, Yanzu banida kowa kuma ban san inda zan je ba. Shi ne na fito titi na haɗu da waɗanda mutanen suka ce zasu samar mini gidan da zan dinga yin aikatau sai na dinga kwana acan, Kuma shi ne suke...” Kuka ya sake kwace mata. Shiru Zayyad ya yi ya zuba mata idanu, Can kuma ya ce“A saboda ke yarinta da wawta ya miki yawa ya sanya ki ka yarda da wasu maza za su samar miki aiki a cikin dare?, Stupid!” Ya ƙare maganar yana harararta. Ɗan kallonsa ta yi sai kuma ta ɗauke kanta tana kuka ta ce“To ya zan yi ni? A ina zan zauna? Dole na yarda dasu” Jinjina kansa ya yi ya ce“Eh kam dole ki yarda dasu, To sannunki, Kin yi ƙokari” Ya yi siririn tsaki sannan ya tada motar suka ci gaba da tafiya.
A cikin compound ɗin gidan ya yi parking bayan an buɗe masa ƙaton gate ɗin gidan, Ita dai Salma sai bin ko ina take da kallo as if her life defend on it. Sauka ya yi daga motar ya zagayo inda take ya buɗe yana kallonta ya ce“Idan kin gama kallon sai ki sakko” Sosai ta ji kunya sai kai ta tura baki ta sakko daga motar, Mayar da ƙofar ya yi ya rufe sannan ya nufi hanyar entrance na gidan, Duk in da taga Zayyad ya yi ita ma nan take yi. Kai tsaye ɗakin Nayla ya shiga, Zaune ya sameta tsakiyar gado tana sanye a wasu riga da wando marasa nauyi kanta sanye da hular Chantilly tana danna system ɗin gabanta. Tana ganinsa ta rufe system ɗin tana murmushi ta ce“Yaya ka dawo?” Zama ya yi gefenta ya ce“Ƴar ƙanwata na dawo, Ya school?” Sakar baki Nayla ta yi tana kallonsa jin yanda yake mata magana kamar ba shi ba. Ta yi murmushi ta ce“Alhamdulilah Yaya, Daman ina da Assignment ɗan Allah zaka yimin?” Jinjina kansa ya yi ya ce“Bring it out” Sauka ta yi daga kan gadon tana murmushi ta nufi dresser ɗinta, Handout ɗin ta ɗauko da kuma plain sheet ɗin ta kawo masa, Karɓa ya yi ya ce“Shikenan zan yi miki zuwa da safe” Dariya ta yi ta ce“Shiyasa nake sonka Yayana Thank you”
“Have a seat, let's talk”
Ya faɗa yana nuna mata gefensa, Zama ta yi ta ɗora hannayenta kan cheeks ɗinta ta ce“Ina ji" Numfasawa ya yi kafin ya ce“Daman na kawo sabuwar baƙuwa ne, Zata dinga aiki a gidan nan, abin da nakeso dake da safe ki je apartment ɗin Maids ki ce musu su ce su suka zo da ita, Su zo wajen Mommah su kawota, But for now Inason ta kwana tare da ke” Waro idanunta ta yi sai kuma ta ce“Yaya ni zan kwana da maid ɗin kuma? Na kai ta dai ɗakinsu Habiba ta kwana” Girgiza kansa ya yi ya ce“Nan nakeson ta kwana” Tura baki Nayla ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Shikenan tana ina?” Da hannu ya nuna mata parlon sannan ya tashi ya ce“Mu je ki ganta” Tashi ta yi tabi bayansa suka fita daga ɗakin. Tsaye suka sami Salma ta juya musu baya hannunta rufe kan fuskarta da alama wani sabon kukan take.
“Keee!”
Zayyad ya kirata daga inda yake tsaye, Juyowa ta yi ta sauke hannunta tana kallonsa hawaye na bin fuskarta..
“Salma!”
Nayla ta kira sunanta da mamaki, Zura mata idanu Salma ta yi can kuma ta gano inda ta taɓa ganinta, Da mamaki Zayyad ke kallon Nayla kafin ya ce“Then u know her?” Gyaɗa masa kai Nayla ta yi ta ce“Na santa Yaya, Na santa a Mararaba, Ita ce wadda nake baka labari fa, Ina ka santa Yaya? A ina ka samota?” Nayla ta jera masa tambayoyin, Ɗan tsaki ya yi ya ce“Zaki nutsu ko kuma za ki ci gaba da tambayar?” Shiru ta yi tana kallonsa ya kalli Salma ya ce“Mahaifinta ne ya rasu, So tana buƙatar taimako shiyasa na kawota nan gidan. But tun da ma kin santa shikenan komai ya zo da sauƙi, Ku zauna tare zuwa da safe sai ki je ki yi introducing ɗinta gurin Mommah” Nayla da jikinta ya yi sanyi ta ce“Tom yaya in sha Allah” Jan kumatunta ya yi ya ce“Good gal, Sai da safe” Daga haka ya juya ya bar parlon, Salma ta bi shi da kallo. Kamo hannunta Nayla ta yi tana cewa“Zo mu shiga ciki Salma”. Koda suka shiga ɗakin ta nuna mata gefen gado tana cewa“Zauna kin ji” Zama Salma ta yi Nayla ta zauna gefenta fuskarta a kwaɓe kamar zata yi kuka ta ce“Allah sarki, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Salma. Ki yi haƙuri kin ji” Ta ƙare maganar tana dafata. Duk yanda Salma ta so ɓoye hawayenta kasawa ta yi, In dai an yi maganar Abbanta to sai ta zubar da hawaye, tana goge hawayenta ta ce“Ameen Ya Allah, Nagode sosai” Ɗan murmushi Nayla ta yi ta ce“Ki bar min godiya, Na dinga bada labarin ki. Amma yanzu tashi ki yi wanka ki sauya kaya” Bata jira cewarta ba ta shige toilet.
Salma na toilet ta ji ana knocking ƙofar, Saurin wanke fuskarta ta yi ta fito sanye da towel ta nufi kofar duk a tunaninta Nayla ce, Dan taje kawo mata abinci. Turus ta yi ganin wanda yake tsaye, Ta kalleshi taga kallonta yake, Saurin kallon jikinta ta yi sai kuma ta saki wani irin ihu, Saurin yar da ledar hannunsa ya yi ya rufe mata baki, Ƙoƙarin kwace bakinta ta shiga yi yaƙi sakinta ya ƙarasa shiga ɗakin ya rufe ƙofar. Sai a sannan ya saketa yana mata wani kallo ya ce“Baki da hankali ne?” Durƙushewa ta yi wajen ta fashe da kuka kamar wanda aka mata wani abun. Tsaki ya yi sannan ya jawo kanta yana kallonta ya ce“Wani abun nayi miki?” Cikin shassheƙar kuka Salma ta ce
“To ai babu kyau ganin tsirarar mutum!”.
*Second to the last free page, HASKEN CIKIN DUHU isn't free it's ₦700 via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, evidence via 08106608363, Ki biya ki karanta cikin salama❤️*
# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera
08106608363.
*HASKEN CIKIN DUHU💋💋*