← Book details Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 28

Chapter 10: The Cost of Being Alone

Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 14 min read

Nanameera, YOTA/023.

Ranar Alhamis aka yi sadaƙar ukun Malam Habu, babu mutane a gidan kasancewar ba dangi ne dashi ba a Kabayi yasa a ka yi addu'ar a masallaci. Ɗage labulan ɗakin ta yi tana kallonta, zaune take ta jingina da jikin bango wanda yake cement ne kawai ba tare da an yi paint ba, idanunta a lumshe yayinda hawaye yake gangarowa gefen idanun, shiru Umma ta yi ta zuba mata idanu tana kallonta. Sallamar da aka yi ya sanya Salma buɗe idanunta, Umma ta sauke labulen tana amsa sallamar, Hajiya Jinjin ta ƙaraso tsakar gidan wanda yake a ɗan jiƙe kasancewar an yi ruwa da safe, Umma ta kalleta tana cewa


“Au Hajiya kece da yammar nan?”


Numfasawa ta yi ta ce“Wallahi Rahmatu, ya ƙarin haƙuri?”


Umma ta ce


“Alhamdulillahi, shigo ciki mana”


To ta ce sannan ta ƙaraso ɗakin, tana shigowa Salma ta gyara zamanta tana kallonta ta ce a sanyaye


“Ina yini”


Sai da ta zauna sannan ta ce


“Lafiya klao Salama, ya ƙarin haƙuri”


Salma ta ce


“Alhamdulillah”


Shiru ɗakin ya ɗauka, ganin kamar suna son yin wata magana ya sanya Salma ta tashi tana kallon Ummarta ta ce


“Bari naje ɗakin Abba”


To kawai Umma ta ce, ta juya ta fice daga ɗakin tana tafe a sanyaye. Sai da ta fita sannan Hajiya Jinjin ta kalli Umma Rahmatu ta ce


“Yanzu ya za'a yi ne?”


Numfasawa Umma ta yi kafin ta ce


“Nima shine ban sani ba Jinjin, kuɗaɗen bansan me zan yi dasu ba? Ko gwala-gwalai zan siya na ɓoye?”


Ɗan murmushi Hajiya Jinjin ta yi ta ce


“Ke daɗina dake rashin basira, idan ki ka siya gwal sai ki ci gaba da zama a haka? Ita ma Salmar a haka zata zauna?”


Umma ta ce


“To me zan yi mata dan Allah? Ko bar ta zan yi da waɗannan maƙudan kudaɗen?”


Dafata Jinjin ta yi ta ce


“Ai ba haka za ki yi ba, fito da kuɗin nan zaki yi a kasafta su, ita ma yarinya ki bata nata, kema ki ɗauki kasonki”


Girgiza kai Umma ta yi ta ce

“Na bawa Salma kuɗi? Haba Hajiya, ba zan iya ba wallahi. Ai ita bar ta kawai ta ci gaba da sana'ar zoɓonta, wannan kuma idan Allah ya kawo mata mijin aure ma yi buƙata tun da dai yanzu babu ran Malam”


Wani irin kallo Hajiya Jinjin ta yi mata, ta jin jina kanta tana cewa “Eh lallai baki san rayuwa ba Rahmatu, baki san mutuwar miji ba” Tagumi Umma ta yi ta ce“Ni da mijina ya mutu ai kuwa nasan mutuwar miji, kin san ko tsohon mijina fa naji mutuwarsa” Gyara zama Jinjin ta yi tana kallonta sosai ta ce


“Kin ga ki fuskanci abin da yake gabanki, wannan kuɗin ki fito dashi, ki bawa Salma rabi”


Zumbur Umma ta miƙe tsaye tana kallon Hajiya Jinjin ta ce


“Ai ko wannan ba abu bane mai yiwuwa, akan me zan bata wannan dukiyar? Ko ubanta bai taɓa ganin kuɗi mai yawan wannan ba, ballantana ita” ta ƙare maganar tana sauke numfashi. Tsaki Jinjin ta yi ta ce “Ke daɗina dake bakya cin ribar zance, ki zauna ki ji abin da zan ce miki”


“Ai maganar taki ce naji bata zama ba ce, wannan zance kamar babu kai” Umma ta faɗa tana ƙoƙarin zama. Sai da ta zauna Hajiya Jinjin ta dafata ta ce


“Kin san me yasa na ce ki bawa Salma wannan kuɗin?”


Umma ta girgiza kai tana gwalalo idanu. Gyaɗa kai Hajiya ta yi ta ci gaba da fad'in


“Saboda Salma ita ce jarin ki yanzu, tun da har ta iya samo waɗannan maƙudan kudaɗen to abar ki tattalata ce, dole ki fito da kuɗi ki kashe mata, ki siya mata kaya na gani na faɗa, ki siya mata mayuka masu tsada, a siyo kayan mata a bata tasha. Ni kuma nasan inda za'a dinga kai ta, wallahi sai kin yi mamakin arzikin da zaku samu, dan irin su Salama maza ke so, yarinya ƙarama kuma mai abun arziki”


Tun da ta fara magana Umma ke kallonta kamar zararriya, duk da bata wani damu da Salma ba amma ba zata iya yiwa rayuwar yarinyar haka ba. Ganin ta yi shiru ya sanya Hajiya cewa


“Naga kin yi shiru?”


Nannauyan numfashi Umma ta sauke kafin ta ce


“Gaskiya wannan maganar ta ki ba mai yiwuwa ba ce ba Hajiya, Salma fa? Ba zan iya ba gaskiya” Ta ƙare maganar tana girgiza kanta. Baki buɗe Hajiya ke kallonta kafin ta yi shewa tana faɗin


“Eh lallai Rahmatu, sannunki! To wallahi za ki yi babban danasani, tunda har tafara gane tabi namiji ya bata kuɗi to wallahi ba zata zauna ba. Idan ma baki ɗorata a hanya da kan ki ba, to kina zaune zata dinga ficewa abinta, ke wata rana ma wallahi idan ta tafi ba zaki sake ganinta ba. Kin ga kin yi asara, Gara ma kin san inda take idan ta samo ku dinga rabawa”


Shiru Umma ta yi ta tafi tunanin maganar Hajiya Jinjin, Above 5mins kafin ta sake girgiza kanta tana cewa


“Gaskiya ba zan iya ba Hajiya, ba zan iya ba! Salama ba zata taɓa tafiya yawon duniya ba, kuma wannan ma ai kyauta aka bata”


“Kina da tabbacin kyautar aka bata? Wane ya faɗa miki zata samu wanda zai bata kuɗi kyauta a Abuja? Kuma a otel? Ke bama haka ba, kwana fa ta yi acan, nan aka yi an ganta a bakin titin Kabayi wani ya direta a zundumemiyar mota, har tana ɗaga masa hannu”


Hajiya Jinjin ta ƙare maganar tana kallon Umma da kyau. Shiru Umma ta sake yi, can kuma ta ce “Duk da haka, koma ta aikata nasan saboda Babanta ne, yanzu ba zata sake ba” Tashi Hajiya Jinjin ta yi tana cewa


“To ai shikenan, Ni bari na shige, Allah ya rufa asiri” Ita ma Ummar miƙewa ta yi tana cewa


“Tom ki gaida gida, duk yanda ake ciki zan leƙo ki in sha Allah” riƙe haɓa ta yi tana cewa


“Ke kuma da ki ke takaba?” taɓe baki Umma ta yi ta ce


“Dan ina takaba idan fita ta kamani ba zan yi ba?”


Girgiza kai Hajiya Jinjin ta yi suna fitowa daga ɗakin. Salma dake share tsakar gidan ta tsaya tana riƙe da tsintsiyar.


“Hajiya Salama ƴar Abuja”


Sunkuyar da kai Salma ta yi tana sake danasanin bin mutumin da tayi, ganin yanda ta yi ya sanya Hajiya cewa


“Ke bafa wani abun na ce ba, ba ki yi laifi ba karki damu”


Salma da tuni hawaye suka kawo idanunta ta share da hannunta tana gyaɗa kai. Umma kallonta kawai ta yi bata ce komai ba, Hajiya ta yi hanyar soro tana cewa


“Allah ya bamu Alkhairi”


“Ameen ki gaida gida” cewar Umma.


Ganin ta fita ya sanya Umma kallon Salma ta ce


“Ki ajiye tsintsiyar nan ki koma ciki, ban da gulma ina abun sharar yake a nan?” Daga haka ta ɗauki buta ta yi hanyar banɗaki, da idanu Salma ta bita sai kuma ta dire tsintsiyar ta shige ɗakinta, tana zuwa ta kwanta kan tsohuwar tabarmar dake shinfiɗe a ɗakin, ta fara kuka a hankali, har sannan zuciyarta ta kasa yadda Abbanta ya rasu, gani take kamar zai dawo idan magriba ta yi, sai dai yau gashi har an kwana uku babu shi babu dalilinsa, ya tafi kamar yanda Amminta ta tafi ta barta, sun tafi sun bar ta cikin duhu wanda Allah ne kawai zai iya kawo mata HASKE domin ta gane in da rayuwarta ta dosa..


Abacha road, Mararaba.

5:45pm.

Da gudu ta shigo parlon tana dariya, Mami dake zaune kan sofa tana danna system ta ɗaga ido ta kalleta, girgiza kanta ta yi ta ce


“Ke da wa kuma?”


Kafin Nayla ta ce komai ya buɗe ƙofar parlon, da gudu ta faɗa gefen Mami tana cewa


“Mami kin gansa ko, Save my Mami”


Ƙarasowa ya yi yana shirin jan hannunta Mami ta zabga masa wata uwar harara, ya yi baya yana sosa ƙeyarsa.


“Me ta yi maka Al-ameen?”


Kwafa ya yi kafin ya ce


“Wai Mami yarinyar nan muna tafe ta kusa sakawa muyi hatsari, wallahi sai ranta ya ɓaci” ɗagowa ta yi daga jikin Mami ta ce


“Mami wai dan na ce masa akuya kar ya kaɗeta shine sai ya dake ni”


Kallonsa Mami ta yi ta ce


“Saboda kai shashasha ne ya sanya zaka buge rai kuma an maka magana shine zaka daketa? To zo ka daketa!” Ta ƙare maganar a ɗan fusace. Girgiza kai Al-ameen ya yi bai sake cewa komai ba ya yi hanyar upstairs, sai da ya kusa kai wa ƙarshe ya juyo yana kallonsu ya ce


“Yaya Ahmad bai dawo ba Mami?”


“Ga ganshi ne to?” Ta bashi amsa, murmushi kawai ya yi ya juya bai sake tankawa ba. Tashi Nayla ta yi tana ɗaukan ledar da ta shigo da ita ta ce


“Bari na ƙarasa haɗa kayana, sai yaushe Fatiha zata dawo ne Mami?” agogon ɗakin ta kalla kafin ta ce


“Tana hanya, maybe ma ta tsaya shegen surutu ne”


Murmushi Nayla ta yi ta ce

“Ai gobe tare zamu tafi Abuja” Mami ta kalleta tana murmushi ta ce


“Inji wa?”


“In jini man”


Girgiza kai kawai Mami ta yi tana murmushi, Nayla ta haye sama tana tafe tana waƙar kizz denial ta Terminator. Bayan sallar isha'i suna zaune a daki, Nayla na ƙarasa linke kayanta tana zurawa cikin ƙaramar trolley ɗin Fatiha wadda aka bata, Mami ta buɗe ɗakin ta shigo, kallonsu ta yi ganin yanda suke hira abin su. Ta zauna gefen gadon ta ce


“Gashi kuma zaki tafi bamu samu an je Orange market ɗin ba”


Langwaɓar da kai Nayla ta yi ta ce a shagwaɓe


“Ayya, shikenan ai, dan Allah Mami idan kin je ki ce ina gaisheta”


“Wa kenan?”


Cewar Fatiha, kallonta Nayla ta yi ta ce


“Salma mana, Mami sai kin ganta wallahi zata burgeki, tana da kirki, ga hankali kuma kyakkyawa da ita” murmushi Mami ta yi ta ce


“Kuma ita take siyar da lemon?”


Gyaɗa kai Nayla ta yi ta ce


“Me sef I'm so surprised Mami, kin ganta kuwa, maybe dai wani abun ya faru”


“Allah sarki, shiyasa duk yana yin daka tsinci kanka ake cewa ka godewa Allah. Ta bani tausayi duk da ban ganta ba”


“Mami wallahi ba wata abar tausayi ba ce ba fa, kawai Nayla ce ta iyayinta, irin fa yaran kasuwar nan ne masu buɗewar ido” Fatiha ta yi maganar tana hararar Nayla. Mami ta ce


“Kin santa ne da zaki bada shaida a kanta?”


Girgiza kai Fatiha ta yi Mami ta ce


“To kar na sake jin irin wannan rashin hankali, sai ka ce baki je islamiyya ba?” shiru Fatiha ta yi gudun faɗan Mami. Nayla kuwa ta sake cewa


“Yawwa kar ki manta Mami sunanta Salma”


Tashi Mami ta yi ta ce“Tom ba zan manta ba in sha Allah, ku kwanta da wuri, da safe zamu shige kar mu yi rana” Okay Nayla ta ce suka mata sai da safe sannan ta juya ta fita.


“Banza kawai”


Fatiha ta faɗa tana harararta, murmushi Nayla ta yi ta ce“Naji ɗin, Ni wallahi da ace zata yarda da Yaya Zayyad ya aureta”


“Amma ban tabbatar da baki da hankali ba sai yau Nayla, wannan yar ƙananun mutanen zai aura? Mutun mai class kamar Yaya Zayyad? You are kidding right?” Girgiza kai Nayla ta yi ta ce


“No be joke fa, seriously nake magana wallahi, tana da hankali”


Tashi Fatiha ta yi ta ce


“Tsayawa magana dake bashi da wani amfani wallahi”


Daga haka ta fice daga dakin tana buga ƙofar. Murmushi kawai Nayla ta yi dan ita ba komai ne yake ɓata mata rai ba, kuma babu ruwanta da abin da mutum zai ce ta dauki niyyar faɗawa Yaya Zayyad wannan maganar koda zai daketa.


Wuse 2, Abuja.


A hankali ta turo ƙofar ɗakin, da sauri ta wurgar da wayar hannunta ta tashi zaune tana gyara duvet ɗin jikinta. Wata kyakkyawar mata ce wadda ba zata shige 47yrs ba, kana ganinta kaga riƙaƙƙiyar yar boko, ƙarasowa dakin ta yi ta kunna haske tana murmushi ta ce


“You haven't sleep Aneeserh?”


Marairaice fuska Aneeserh ta yi tana kallon matar wadda take matuƙar kama da ita ta ce

“I will Mom”


Zama ta yi gefen gadon tana kallon ta ta ce


“Akwai wani abun ne?”


Girgiza kai Aneeserh ta yi, matar ta tashi still looking at her ta ce

“Ki kwanta sai da safe”


Daga haka ta nufi ƙofa, tana shirin fita ta ji ta ce


“Mom sai yaushe Dad zai dawo ne?”

Sakar handle ɗin ƙofar ta yi tana kallonta ta ce


“Maybe next week, baku yi magana dashi ba ne?”

Girgiza kai Aneeserh ta yi ta ce


“Last two days muka yi magana dashi, but I didn't ask him” Mom ta ce

“Then u should call him tomorrow” jin jina kai ta yi ta ce


“okay ma, good night”


Murmushi Mom ta yi ta ce

“Good night baby” har ta juya sai kuma ta ce


“Au zan manta, ba lallai bane gobe ki tashi ki sameni, i have alot to do at office z and kuma zan je transport wajen Uncle” Gyaɗa kai Aneeserh ta yi ta ce


“Okay Mom, I'll take care of my sef don't worry”


“Sure Baby?”

Aneeserh ta gyada mata kai tana murmushi, okay Mom ta ce sannan ta juya ta bar ɗakin. Ajiyar zuciya Aneeserh ta sauke sannan ta koma ta kwanta ta janyo wayarta, Khairiyya dake kan video call ta kalleta ta ce


“Ni kin ga nagaji da wannan, kawai ki zo transcorp mana”

Girgiza kai Aneeserh ta yi ta ce

“Mom gobe zata je can ɗin, ba zani ba gaskiya” tsaki Khairiyya ta yi ta ce


“Idan aka yi sallar Asuba ba sai ki komo gida ba, ni muna nan ni da su Feedy”

Shiru Aneeserh ta yi can kuma ta ce

“I'll not, bacci zan yi yau” harararta ta yi ta ce


“Bacci za ki yi ko kuma kin shirya wayar dare da Zayyad?” taɓe baki Aneeserh ta yi ta ce


“Ke baki sani ba, kwana biyu ma bamu yi shiri sosai ba, ko kulani baya yi” waro idanu Khairi ta yi ta ce


“For what reason kenan?”


Daga kafaɗarta ta yi ta ce

“I don't know, kawai yana banza dani ne, kin san wani lokacin girman kansa ya yi masa yawa”


Murmushi ta yi ta ce

“Da yake kula ki ma kenan, wai yaushe zaku yi auren?” numfasawa Aneeserh ta yi ta ce


“Idan Dad ya dawo zamu yi maganar sai a ke gidansu”


“And who told u daga gidansu budurwa ake zuwa?”


Murmushi Aneeserh ta yi ta ce

“Silly me, anyway I go talk to Zayyad tomorrow”


“Better”

Khairiyya ta faɗa kafin tayi cutting kiran.


Washegari ko da ta tashi bata tarar da Mom ba, shiryawa ta yi cikin wasu riga da wando ta yi rolling jersey veil akanta, ta ɗauki school bag nata ta yi waje. Tana cikin driving taga kiransa, ta samu gefe ɗaya ta yi parking kafin tayi answering call ɗin, daga ɗaya bangaren Dad ya ce


“Daughter”


Shagwaɓe fuska ta yi kamar tana gabansa ta ce


“Dad i dey missed you alot, come back please”

Murmushi ya yi daga nasa bangaren ya ce


“My poor neeserh, in sha Allah on Monday zan sauka a 9ja”


Waro idanunta ta yi tana murmushi ta ce

“Dad are u serious?”


Dad dake kan layi har sannan ya ce

“Yeh, just wait for me my baby girl”


Aneeserh da murna ta isheta ta ce

“Okay Dad am, I'll, sai ka dawo”


Murmushi ya yi ya ce

“Akwai wani abu ne?”

Aneeserh ta langwaɓar da kanta kafin ta ce

“Dad i dey broke those days wallahi”


Daga ɗaya bangaren Dad ya ce


“But why u didn't tell me neeserh? Saboda wa nake neman kuɗin? Karki sake irin haka?” murmushi ta yi ta ce

“Okay First love, I'll not”


“Zan saka miki 1m a keystone naki, ya isheki?”


Aneeserh ta yi dariya ta ce

“My one and only Dad, thank you”


Murmushi ya yi jin dariyarta ya ce

“Haka nakeson jin ki koda yaushe kina farin ciki kin ji”


Aneeserh ta ce


“Idan ina da kai Dad ai ba zan taɓa kuka ba, driving nake zani school I'll call u later” Dad ya ce


“Okay love, bye”

Daga haka ya yi cutting kiran. Kallon screen ɗin wayar tayi tana sake yiwa Allah godiya daya bata Dad a matsayin mahaifi, he's always behind her happiness, ajiye wayar ta yi sannan ta ci gaba da driving ɗinta.


Kabayi, Mararaba.

Zaune take kan kujera a tsakar gida tana tsince wake, Umma na zaune kan tabarma tana yanka sallad wani yaro ya yi sallama ya shigo, yana wasa da tsolon rake ya ce


“Wai Salma ta zo”

Kallonsa Umma ta yi sai kuma ta ce

“Kace tana zuwa”

Salma dake sunkuye ta ɗago ta kalli Umma kafin ta yi magana Ummar ta ce

“Tashi ki je ki ga wane”

Kasa motsi Salma ta yi, ta tafi tunanin wanda ke nemanta.


“Baki ji bane Salama?”


A sanyaye ta tashi ta shige ɗakinta, wani hijabi maroon colour ta ɗauko ta saka, ta fito ta zura takalmanta ta nufi hanyar waje


“Sauran ki wulaƙanta mutum”

Salma ta juyo ta kalleta sai kuma ta juya ta ci gaba da tafiya.


Tsaye yake jikin motarsa, yana sanye da wata dakkakiyar shadda royal blue, idanunsa maƙale da shades glasses, da matukar mamaki Salma ke kallonsa yayinda shi kuma yake sakar mata murmushi.


“Kai ne?”


# HCD
# Nanameera
08106608363.


*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 10 · 0% Book details