← Book details Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 28

Chapter 37-38: Her heart's last anchor

Hasken Cikin Duhu Book 1Complete Hausa Novel · about 16 min read

Nanameera, YOTA/023
Arewabooks @Nanameera08


Malam ya dinga kallonts da mamaki sai kuma ya jinjina kansa ya ce“shikenan tun da haka ki ka zaɓa, ba zan raba ki dashi ba, Allah ya baku zaman lafiya, zan tafi, ta Yi gobe ki ganni idan Allah ya yarda” tashi Salma ta yi tana goge hawayenta ta ce“tom malam, Nagode Allah ya saka da Alkhairi ya ƙara girma” Amin kawai ya ce sannan ya nufi hanyar ƙofa yana ɗan jan carbin hannunsa. Salma ta bi shi da idanu har sannan hawaye bai bar zuba kan fuskarta ba. Sai da taga ya tafi sannan ta je ta rufe ƙofar ta koma cikin ɗakin, kwance ta same shi ya yi ruf da ciki, ta ƙarasa ta zauna gefen katifar muryarta na rawa ta ce


“ka yi haƙuri Yaya Zayyad, in sha Allah zaka je ka ga Mommah nan kusa amma kawai ina tsoron a rabani da kai ne, bana son su ɗauke ka”


Shiru ya yi mata duk da yana jin abin da take cewa, ta sunkuyar da kanta tana shessheƙar kuka ta ce“ni bana son na zauna ni kaɗai, bani da kowa yanzun sai kai idan suka tafi da kai shikenan ba zan sake ganinka ba. Kuma babu wanda na sani, sai dai na dinga rayuwata ni kaɗai, tsoro nake ji Yaya Zayyad”


Ta ɗago ta sake kallon bayansa, ganin ba magana zai yi ba ya sanya ta tashi ta fice daga ɗakin ta koma nata ta zauna tana ci gaba da kukanta, sosai taji kewar Abbanta, taji kamar yau ne ya mutu ya bar ta, taji ina ma Umma Rahmatu bata siyar da gidansu ba su koma ta zauna, da a ce bata siyar da gidan ta ƙarasa tarwatsa ragowar rayuwarta ba da har yanzu suna zaune tare da daɗi ba daɗi, da Zayyad ba zai shigo rayuwarta ba, ballantana har a yi mata sharri mafi muni a rayuwa, da bata fara jin tana sonsa ba. Sai dai duk wadannan abubuwan ba laifinta bane, kaddarace ta zo mata a haka, kuma ta yi alƙawarin duk runtsi duk wahala zata zauna tare da Yaya Zayyad koda a ce shi baya sonta, zata zauna dashi kodan taimakon da ya yi mata, ba zata taɓa gazawa ba. Amma shi zai sota?? Salma ta tambayi kanta, sai kawai ta sake fashewa da wani sabon kukan ta kwanta kan simintin ɗakin ta ci gaba da rera kukanta.


Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya turo ƙofar dakin ya shigo, zaune ya sameta kan ladduma tana sanye da hijabi da alama sallah ta idar. Ta dinga kallonsa har ya zauna ɗan nesa da ita, muryarta na rawa ta ce“Ko zaka ci abinci Yaya?” kamar ba zai magana ba sai kuma ya gyaɗa mata kai a hankali. Ajiye carbin hannunta ta yi ta tashi tana shirin fita daga ɗakin taji ya ce“Ni waina nakeso” juyowa ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce“wainar masa?” ya sake gyaɗa mata kamar dangin ƙadangaru, dawowa ta yi ta buɗe jakar da kayanta ke ciki, naira dubu daya ta ɗauka a kuɗin da malam ya bata ta juya tana kallonsa ta ce“tom bari naje na siyo maka” daga haka ta nufi ƙofa dan tasan ba amsawa zai yi ba.


Koda ta je bakin titin kalle-kalle ta dinga yi ganin yau gurin kamar an sauya shi babu jama'a kodan sanyin da ake ne ya sanya dan ko unguwar ma babu tarin jama'a kamar da. Ƙarasawa ta yi bakinta ɗauke da sallama ta miƙawa yaron matar kudi, ba'a fi 2mins ba aka miƙo mata ledar wainar ta amsa sannan ta juya, tana fara shiga layin nasu taji horn ɗin mota, ganin yana shirin bigeta ya sanya ta ja ta tsaya, parking y yi a wajen ya fito yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce“afuwan na ɗan takura miki ko?” Salma ta kalleshi amma bata ce komai ba, Ya girgiza kansa ya ce“na ganki ne a wajen mai waina shi ne nace bari na zo mu gaisa Salma Candy”


Da sauri ta kalleshi a ɗan tsorace ta ce“a ina ka san sunana?”


“Salma kenan, sanin sunanki ba abu bane mai wahala, anan unguwar na san sunanki" Salma ta dinga kallonsa ba dan ta yarda da abin da ya ce ba dan ita ta san kaf unguwar nan babu wanda ya santa tun da babu gidan wanda take shiga, haka zalika kuma babu wanda ya san ana kiranta da Candy, suna tun na makaranta. Jin ta yi shiru ya sanya ya ce“kar na takura miki, idan babu damuwa ina son ki bani lambar wayarki sai mu yi magana, ko ki min izini na ƙarasa gidanku idan ya so sai mu yi magana”


Wani irin kallon ka zama mahaukaci ta yi masa sannan ta taɓe baki cike da tsiwa ta ce“Su wadanda suka faɗa maka sunan nawa basu ce maka ni matar aure ba ce? To kar ka sake tsayar dani akan hanya, ni matar aure ce yanzu haka mijina yana gida shi ne ma ya aikeni”


Aliyu ya ɗan yi murmushi sai kuma ya ce“yara ma sun iya ƙaryar cewa suna da aure? Ke Salma ke ce mai aure? To ai ko duk jikina kunnene ba zan taɓa yarda ba, kin ɗauka auren abun wasa ne? Shi mijin naki ne zai zauna a gida sannan ke ya aike ki da daddare, to idan har haka ne auren bashi da amfani yin sa, ballantana ma baki da wani aure amma nan ba da jimawa ba zaki yi shi in sha Allah”


Harararsa Salma ta yi ta ce“Ba sai ka aure nin ba mu gani”


Daga haka ta juya ta ci gaba da tafiyarta, ganin ya biyota ya sanya ta dinga wani irin sauri har sai da ta yi tuntube ta faɗi, ledar ta fadi gefe guda. Da sauri ya ƙaraso wajen yana kallonta ya ce“subhanallahi sannu kin ji, tashi”


“Ba za'a tashi ɗin ba, ina ruwanka dani mugu kawai!”


Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, tsayawa ya yi yana kallonta sai kawai ya yi murmushi dan ba ƙaramin burgeshi ta yi ba, ta tashi ta ɗauke ledarta ta ci gaba da tafiya. Bin bayantan ya ci gaba da yi har sai da yaga taje ƙofar gidan, ta zaro key ta sakawa ƙofar. Shiru ya yi yana tunani, To ko dai da gaske matar auren ce? Girgiza kansa ya yi a fili ya ce


“No impossible, ko da a ce haka ne ba zan bar ki ba, sai na mallakeki a matsayin mata Salma, ke ce irin matar dana daɗe ina nema, tabbas sai na mallakeki, ko da hakan na nufin zan sha wahala ba zan haƙura da ke ba!”


Aliyu ya ƙare maganar idanunsa zube akanta har ta ƙarasa buɗe ƙofar gidan ta shiga ta kuma rufo ƙofar.


Rufe gidan ta yi gaba ɗaya sannan ta nufi cikin dakin, zaune ta sami Zayyad a parlon ya yi jigum yana tunanin daya saba, ta ajiye ledar ta tsuguna tana ƙoƙarin kwancewa ta ce“Yaya ga wainar” kallonta kawai ya yi sai kuma ya zamo ya sakko ƙasa, ta tura masa robar gabansa sannan ta tashi ta shige kitchen, pure water ta ɗauko masa ta dawo ta ajiye masa gefe ta nemi can gefen kujera ta zauna. Zayyad ya dinga taunar wainar kamar magani bai fi rabi ya ci ba ya tashi ya ɗauka robar ya dire a gabanta sannan ya nufi hanyar ɗakinsa. Salma ta dinga kallon robar sai kuma ta juya ta ga babu shi babu alamunsa, sai kawai ta ɗauka dan daman bata ci abincin dare ba ta hau cin wainar, bayan ta gama ta maida robar kitchen ta wanke hannunta sannan ta dawo parlon, neman guri ta yi ta zauna can kuma ta tashi ta shiga ɗakinta ta kwanta.


**** Kwaɓe fuska ya yi sannan ya ce“Mommah sai yanzu ki ka zo ki tafi dani?” gyaɗa masa kai ta yi kana ta ce“Eh Zayyad ka yi haƙuri da tafiyar da nayi na bar ka kaji, ba zan sake ba” ya marairaice fuska ya ce“To ni ai bana so na biki”


“Baka son ka dinga ganina Zayyad?”

Ya girgiza kansa ya ce“Ina so mana, to ai ke ce ki ka tafi dani, kuma ki ka bar ni” murmushi ta sake yi sannan ta ce“tom ka yi hakuri ba zan sake barin ka ba, tawo mu tafi” ta miƙo masa tafin hannunta. Kallonta ya yi ta ɗaga masa gira sai kawai ya ɗora nasa hannun, Sai dai tamkar walƙiya haka ya nemeta ya rasa s firgice kuma ya farka


“Mommah! Mommah!”

Ya dinga kallon dakin da mamaki, tashi tsaye ya yi sai kuma ya nufi ƙofa, zaune ya hangeta ta ɗora kanta jikin kujera tana bacci, ya ƙarasa muryarsa na rawa ya ce“Salma! Salma!”


Cikin magagin bacci ta buɗe idanunta, ta ɗago kanta ta kalleshi da idanunta da basu gama buɗewa ba ta ce“Yaya mene ne?”


“Gida zan je, ina son naje gida Salma, wajen Mommah zan je, ina son naje na ganta, ina son ganin Daddy, ki zo mu tafi gida kin ji”


Bata san sanda ta miƙe tsaye ba tana kallonsa ta ce“Yaya meya faru? Kasan me ka ke faɗa kuwa?” Jinjina mata kai ya yi sannan ya ce“Nasani mana, ni ba mahaukaci bane, I'm Zayyad B. Musa, na gane wane ni fa, ki zo mu tafi gida”


Matsawa ta yi daga kusa da shi tana girgiza kanta ta ce“A'a wallahi ba zan yarda ba, ba kai bane, kai Yaya yad ɗina ne, ba kai ne wancan Zayyad ɗin ba, ba zan yarda da kai ba”


Kallonta Zayyad ya dinga yi da mamaki, ganin yanda ta ruɗe ya sanya ya ce“Ke baki gane ni bane? Ni ne fa Zayyad, ina son naje gida”


Fashewa ta yi da kuka tana ci gaba da kallonsa ita ma ta ce“a'a ban gane ka ba, ba kuma zan taɓa ganeka ba, sai safiya ta yi na kira malam sannan” daga haka ta shige ɗakinta da gudu ta rufo ƙofa, daman tsautsayi ne ya sanya ta sake fitowa. Ƙarasowa ya yi ya dinga buga ƙofar yana kiran sunanta amma sam taƙi buɗe masa, gudun kada ya ɓalla ƙofar ya sanya ya koma ya zauna kan kujera yana tunanin abubuwa dayawa, wane irin mugun mafarki ne wannan ya yi?? Ya girgiza kansa sai kuma ya tashi ya koma ɗakin da yake, banɗaki ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito nan parlon ya fara gabatar da sallar nafila.


Gari na fara wayewa ya tashi ya koma jikin ƙofar ya ɗan buga a hankali ya ce“Salma! Salma ki buɗe ƙofar kin ji”

Salma ta sake takure jikinta a ƙarshen ɗakin tana shessheƙar kuka a hankali, ya fi 5mins yana kiran sunanta amma bata amsa ba, sai kawai ya bar wajen ya koma yana shirin zama a kujera pillow ya fado ƙasa, ɗaukoshi ya yi yana shirin mayarwa yaga wani bunch of keys ya kai hannunsa ya ɗauka, da sauri ya juya ya koma jikin ƙofar ya zura key guda ɗaya cikin Sa'a kuwa yana murɗawa kofar ta bude, Zabura ta yi ganin ya shigo ta tashi tsaye tana girgiza kanta ta ce“kak...ka bari...ka bari ba kai bane, ni ba kai nake so ba! Sai naje na faɗawa Malam”


Daga haka ta tawo da sauri tana shirin ficewa ta gefensa, hannu ɗaya ya sanya ya jawota, ganin tana ƙoƙarin zamewa ya sanya ya riƙeta tsam a ƙirjinsa, ƙoƙarin kwacewa ta shiga yi amma sam ta saka samun damar haka sai kawai ta fashe da wani raunataccen kuka ta yi luf a ƙirjinsa, shiru ya yi yana sauraren yanda take kuka kamar ranta zai fita, ya dinga patting bayanta a hankali har sai da yaga ta fara yin shiru, ɗago fuskarta ya yi yana kallonta ya ce“Ya isa haka, tare zamu je wajen Malam ɗin”


Salma janye jikinta ta yi daga nasa ta fice daga dakin da sauri, ganin haka ya sanya Zayyad yabi bayanta shima..


A tsakar gida ya sameta ta tsaya sai kuka take, tsayawar shima ya yi ɗan nesa da ita, ya zuba mata idanu hannayensa harɗea ƙirjinsa. Ganin ba shiru zata yi ba ya sanya ya koma cikin gidan ya rabu da ita, Around 9am ya fito sanye cikin wasu English wears onion colour ya ɗora rigar sanyi a kai dan ba ƙaramin sanyi aka tashi dashi ba. Tsaye ya sameta har sannan sai rawar sanyi take, Muryarsa a nutse ya ce “ki zo ki yi wanka sai muje gidan Malam ɗin” juyowa ta yi ta kalleshi da fuskarta wadda tayi kaca-kaca da hawaye sai kuma ta ce“Ni ba wanka zan yi”


Shiru y yi yana kallonta kafin ya numfasa ya ce“shikenan muje” daga haka ya ƙaraso wajen ya sanya key ya fara unlocking ƙofar gidan, takalmanta kawai ta zura sannan tabi bayansa dan har ya fita daga gidan, ya mayar da ƙofar gidan ya rufe sannan kalleta ganin yanda ta tsaya ya ce“muje mana” Gaba ta yi yana bin ta a baya har suka je bakin titi, da kansa ya tsayar da mai Napep ɗin ya ce ta faɗa masa unguwar dan bai sani ba, suka yi ciniki dashi sannan suka shiga. Har suka je gidan babu wanda ya ce da wani uffan a tsakaninsu, Da kanta ta shiga har cikin gidan bayan ta yi sallama Umma ta samu tsaye tana kwashe kaya ta gaisheta sannan ta ce“Baba baya nan?” Umma ta ce“a'a yana nan kin san yau ana sanyi ne, to yana cikin ɗakin soro” Tom kawai Salma ta ce sannan ta juya jiki a sanyaye ta nufi soron, bakinta ɗauke da sallama ta shiga ɗakin. Malam na zaune kan carpet yana jan carbi, yana ganinta ya gyara zamansa da mamaki ya ce“Ummulsalma ke ce da safiyar nan?”


“Eh Baba, Da Yaya Zayyad muka zo”

Salma ta yi maganar a sanyaye, ɗan leƙa bayanta Malam ya yi sannan ya ce“ina yake?”


“Yana waje bari na kira shi”

Tom kawai Malam ya ce ta tashi ta fita, after 1min suna dawo tare, tun da ya shigo malam ke kallonsa ya nemi gefe ɗaya ya zauna cikin kamilallyar muryarsa ya ce“Malam ina kwana?”


Malam ya kalleshi sai kuma ya kalli Salma, Ta gyaɗa masa kai muryata na rawa kamar mai shirin fashewa da wani sabon kukan ta ce“Malam ba Yaya Zayyad ɗina bane, bashi bane, ya sauya malam. So yake ya tafi ya barni malam, baya sona!”girgiza kai Malam ya yi ya ce“Ya isa haka tashi ki je gida” bata sake cewa komai ba ta tashi ta fice daga ɗakin, Zayyad ya bita da kallo sai kuma ya ɗauke idanunsa.


Malam ya ɗan yi shiru na wasu sakwanni kafin ya ce“Zayyad!”

“Na'am Baba”

Malam ya jinjina kansa ya ce“Alhamdulilahi, Allah alhakamu, Allah ya ƙara maka lafiya” Zayyad ya kalleshi ya ce“Amin malam, amma dan Allah meya faru? Nayi wani mafarki mai ban tsoro, a cikin mafarkin na sanka kuma dana tashi sai naga duk abin da yake cikin mafarkin akwai shi a zahiri, da gaske ba'a Abuja nake ba, ina son naje naga Mommah”


Malam ya Girgiza kansa sannan ya ce“Allah sarki, wato Zayyad duk abin da ka gani cikin mafarkinka ba haka bane, a zahiri ya kasance babu wani ruɗani”

Ya dinga kallon Malam kamar idanunsa zasu fito kafin ya ce“da gaske ne nayi hauka malam? Duk abubuwan da suka faru gaskiya ne kenan?” jinjina masa kai Malam ya yi ya ce“wannan haka yake, amma yanzu tun da ka dawo hayyacinka to Alhamdulillahi daman shi ne abin da muke fata kuma ya tabbata, sai ka dage da addu'a domin duk wannan sharrin shaidanu ne, ba dan ma kana da riƙon addini ba da Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru”


Hawaye ne suka shiga sintiri kan fuskarsa, bakinsa na rawa ya ce“D...da gaske na bar iyayena malam?” gyaɗa masa kai kawai ya yi, Zayyad ya ce“ina son naje gida, ina son na tafi malam, tafiya zan yi, Ina son naga Mommah da Daddyn, na san hankalinsu ya yi matuƙar tashi, tafiya zan yi Malam”


Malam ya yi shiru can kuma ya ce“Tabbas kana da bukatar ka tafi Zayyad, domin iyaye daɗi garesu, kodan a sako su Maryama ma zan so ace ka koma a gida, amma ita Salma ina tsoron zuwanta can saboda kada su cutar da ita”


Zayyad ya ce“Salma, ai ba da ita zan tafi ba Malam, kawai tafiya zan yi ni kaɗai, ku zauna da ita idan ya so duk abin da kama sai na dinga aikowa dashi daman Daddy ba son zamanta yake acan ba”


Da mamaki Malam yake kallonsa sai kuma yace“A'a Zayyad, matarka ce ita, saboda haka duk in da zaka je ka tafi tare da ita, kuma ka kareta kamar yanda ta kare ka, ka kula da ita kamar yanda ta kula da kai, ko da a ce iyayenka sun nemi su ɓata mata kai ne zaka nuna musu muhimmancinta a gareka, idan har suna son ka to ba zasu ƙi ta ba”


Shima Zayyad kallon mamaki ya dinga yiwa Malam kafin ya ce“ai ba matata ba ce Malam, kawai dai na ganta a hanya ne tana neman taimako na taimaketa shi ne na kai ta gidanmu har haka ta faru, babu aure tsakanina da ita, ni an saka min ranar Aure da ƴar abokin Daddyna”


Malam ya Girgiza kansa ya ce“Ashsha mantawa nayi ban faɗa maka ba, domin ta zauna tare da kai bata son wani abun ya sameka ta yarda ta aureka a haka ni ne wanda na biya sadakin”


“Aure kuma? Da Salma ɗin? Wannan yarinyar Malam?”


Jinjina masa kai Malam ya yi, Zayyad ya girgiza kansa ya ce“a'a malam, Salma ta yi yarinta da aure, ba zan iya aurenta ba”


“Amma ita ta aureka Zayyad kuma dole ka zauna da ita”


Malam ya yi maganar in a serious tone. Sunkuyar da kai Zayyad ya yi dan yana ganin girman Malam sosai, Malam ya ce“Ko da wasa ka da ka taɓa cewa zaka rabu da yarinyar nan, domin ita ɗin ƙaddararka ce, tana sonka duk da yarintar ta, kar ka ce zaka watsa mata ƙasa a ido dan girman Allah Muhammad”


Shiru Zayyad ya yi duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi ya ɗago kansa yana kallon Malam ya ce“In sha Allah ba zan barta ba. Amma ina ga ta zauna anan idan naje sai na dawo na ɗauketa”


Malam ya ce“wannan ma ba wani abun bane, amma koda zaka tafi to ba wannan satin ba Zayyad, inason ka zauna da ita ka fahimceta. Sannan ka sanar da ita da kanka cewa zaka dawo ka ɗauketa, domin tun jiya da na fahimci samun sauƙinka nace zaka koma gida take kuka, kada ka tafi yanzu ka bar ta”


Shiru ya yi yana nazarin kalaman Malam can kuma ya sauke numfashi ya ce“tom in sha Allah duk yanda ka ce hakan za'a yi Malam”


Murmushin jin dadi ya yi ya ce“Yawwa Allah ya yi maka albarka, Amin” Da Amin shima ya amsa sannan Malam ya sake cewa“Muje ciki ka gaida matan gidan” Toh ya ce sannan ya miƙe ya fito daga dakin malam na biye dashi suka shiga cikin gidan. Farin ciki ba kaɗan ba Umma tayi da samun lafiyarsa, bayan sun gama gaisawa suka koma ɗaki aka kawo musu abin karin kumallo, Salma kuwa zama tayi kamar mara lafiya sai kwnaciya ko abinci ta ƙi ci..


****
Abuja.

Mommah ta yi murmushi tana kallon Maryam ta ce“Dan Allah da zarar kun sauka ki kirani” Maryam ta gyaɗa kanta tana cewa “Tom Mommah, in sha Allah muna sauka zaki ji waya” jin jina kanta ta yi sannan ta kalli Hashim dake riƙe da Khalil ta ce“A sauka lafiya to” Murmushi ya yi sannan ya ce“Mun gode sosai Allah ya saka da Alkhairi ya ƙara girma” Mommah ta ce Amin tana kallon Khalil ta ce masa“Ko zaka zauna anan?” girgiza kansa ya yi ya ce“gida zan tafi” Mommah ta ce“ai shikenan na daina baka sweet” ɗan murmushi yaron ya yi sannan ya ce“ai nasan zaki bani saboda kina da kirki sosai” duka suka yi dariya, Suna nan tsaye har aka fara sanarwa cewa jirgi zai tashi, Maryam ta kalleta ta ce“Tom Mommah sai Allah ya sake haɗamu”


“Kar ki manta Maryama”


“Har abada mommah”


Daga haka suka juya suka nufi cikin jirgin tana ɗaga musu hannu, sai da ta daina hangosu sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta koma in da suka yi parking motoci sojoji na biye da ita, basu bar cikin airport ɗin ba har sai jirginsu Maryam ya tashi i zuwa Kaduna, Mommah ta sauke numfashi tana yi musu addu'ar samun nasara, kafin drivern ta ya ja motar suka bar cikin airport ɗin gaba ɗaya.

_Sauran kaɗan fa book 1 ya ƙare, make ur payment mana ,7041901078 Hauwa Adamu lawan opay evidence via 08106608363 Nanameera_

# HCD
# Salma
# Zayyad
# Nanameera
08106608363

*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 26 · 0% Book details