Sashe 4
Harijin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Hibba tabisa dawani irin kallon mamaki da bacin rai, yana tafiya security sa daya saka black suit biye dashi abaya, Allah baitaba hadata da straight forward dan iska irin mutumin nan ba, gashi yasha babban riga da hula kaman na Allah, wlh tsabagen bacin rai saitaji she just wanna go home daman it’s almost time for her shift to end 1PM hakan yasa tabude kofa tafito manager na kallonta tahaderai tamau direct tawuce changing room dinsu tacire kayan tadaura abayanta baki akai tai rolling gyalenta tadauki handbag dinta tafito ko sallama batama kowa ba kawai ta wuce ta tafi sauran ma’aikatan na tabe baki har bakin titi taxi along tahau kusan guda biyu har zuwa village na Jahi nan gidansu yake da kafa take dandarawa cikin anguwansu har takai gidansu wanda yake gidan haya, flat flat ne tawuce flat nasu, kafin takarasa aka bude kofan wani yaro ne dayadan tasa yafito kana ganinsa bazai wuce 8yrs ba, baida jiki at all kaman tsinke siririn gaske, yana sanye da yadi riga da wando ajikinsa sai bakar sweater da bakar safa akafansa, da hulan sanyi akansa dan sanyi na damunsa, yace “Mommy oyoyo, Mommy oyoyo, Mommy oyoyo, Mommy tadawooo” duk yanda ranta yake abace saitaji ya mance gabaki daya ganinsa, hannu ta budemai tana murmushi harta baiyi wata wata ba yazo yana gudu kaman iska zai kwashesa ya rungumeta itama tai hugging nasa tsamtsam ajikinta tace “Hibban din Mommy oyoyooo” dasauri yasaketa yakai hannunsa zai zare jakanta daga kafada da murna yace “me kika kawomin Mommy”? Duk taje aiki takan kawomai dan snacks haka ko nama ko kaza wanda tadan samu idan an rage, yau ranta yabaci duk batai hakan ba, dasauri takama hannunsa tace “bari na huta anjima kadan sai mu fita mu saya ko, kasha maganin rana”? Dasauri yana sake karban handbag nata yace “Umma tace yakare” bugawa kirjinta yayi sosai bana wasaba tama kasa magana ta tsaya sai Hibban ne yaja hannunta yace “let’s go Momy” ijiyan zuciya ta sauke tabisa har gaban flat nasu ta zaro kafafunta daga sneakers tai sallama tashiga falon while Hibban ya duka dan daukan takalminta ya bubbuga yashiga dasu ciki dan gidan nan ana satan takalmi, the only takalmi da ake bari waje is slippers, bubbuge takalmin yayi saiga kati mai kyau yafado tare da kasa daga kasan takalmin, dasauri Hibban yasa hannu yadauki card din yasa hannunsa ya kakkabe ya goge kasan saiya taso rike da takalmin da katin da hanbbag yabude dakin yashigo yana maida kofan yarufe yace “Mommy is this for you?” Bakowa a dan madaidaicin falon dayake dauke da kujeru ga yar TV da Gotv sai dakuna guda biyu sai kitchen da bayi daya, dasauri yace “Mommy” bude kitchen akayi aka fito wata yar budurwace dabazata wuce 16yrs ba tana kama da Hibba, duktai zufa tace “dalla chan wai bazaka yima mutane shiru ba kahanani jin abinda akeyi a Guddan din Zeeworld” hararanta Hibban yayi sosai dan ko kadan basa shiri yace “baza’ayi ba” da gangan yadaga murya dayafi nada ma yace “Mommyyyyyy” aiko cikeda harzuka yarinyar ta taho wajen batai wata wata ba ta kwadesa da mari tace “kai mara kunya ko” dafe kumatunsa yayi sai kuka dasauri Hibba dake bayi tabude kofa tafito, yana ganin Mamansa yakara sautin kuka yace “Mommy kinga Anty Salma ta dakeni ko” Hibba ta kalli Salma tace “mesa zaki maresa Salma? Kome yamiki bazaki gayamin ba bakiga bayida lafiya ba” cikeda tsiwa Salma tace “yasan baida lafiya bazai natsu ba, ya isheni ni da gidan ubana, yaje gidansu yayi haukan nan mana yaga idan damai dauka su tattakasa, suda ko biscuit dinsu babu acikinsa” “me kikace Salma?” Duk sukaji muryan wata dattijuwa na magana takaraso wajen tanama Salma wani kallo cikin matukar bacinrai Umma tace “me kikace Salma?” Cikin fushi da bacinrai dakuma rashin kunya Salma tace “duk kunbi kun bata yaro sabida sikila ne shi yanama mutane rashin kunya laifi nane, ni wlh duk sun isheni da dare yahana mutane bacci da rashin lafiya da rana kuma rashin kunya wawa kawai….” Hannu Umma takai zata kaimata duka tace “kaniyanki Salma” dasauri Hibba tarike hannun Umma tace “Umma dan Allah karki tabata kiyakuri, shima ai Hibban din ba kanwan lasa bane, akanme zai dinga ihu? Bakasan inda nake bane ko ba agabanka na shigo gidan ba? Wuce muje” sai kawai takama hannun Hibban suka wuce dayan dakin dake gefen na Umma, Umma ta kalli Salma tace “kinji kunya Auta yanzu yayanki Hibba kikema rashin kunya?” Cikeda tsiwa tace “kaman ya Umma ni da ita nayi ko da danta mara kunyan yaro” wani girgiza kai Umma tayi tace “ahhh yayi kyau, kodan abinda take miki bazaki dagama danta kafa ba, Salma ce makarantan ki ita tabiya miki jarabawan WAEC har dinkin Candy saida tamiki, indomie nan dakike dafawa ba ita tasaya ba iyye Salma kikema Hibban haka wayafi karfin ciwo aduniyan nan” cikin kwakwalan yarinta tace “nidai nagaji da Hibban kuma bazan fasa fadaba ku maidasa gidansu babansa mana ha’a kawai an hanani kallo ba” cikeda takaici Umma tace “wannan Gotv yakare wlh bazan bari tayi wani ba Shegiya ja’ira kwadayayya” Umma tai maganan tajuya tai wajen TV ta kashe.
Idan tace abinda yafaru bai mata zafi ba tai karya but bata taba nunama Hibban she’s sad, sabida yanzu yayi wayau sosai, to yaron da yanzu tsayinsa yakai wajajen kirjinta ai yayi wayau, babban katifa ce lomba one adakin akasa agyare tun na aurenta ne anan take kwana da Hibban dakuma Salma, Hibban ya ijiye jakanta da canvas nata yazo yazauna kusada ita yana bata card din yace “Mommy I saw this on your shoe” kallo daya tama card din tagane wanda mutumin nan yabata ne dasauri ta karba ta jefar chan kasa ahankali tace “mesa bakajin magana Hibban mesa kakema Anty Salma rashin kunya bakasan tana matsayin Mamanka bane” make kafada yayi yace “you are my only Mommy Anty Salma muguw….” Wani kallo tamai hakan yasa yagadiye maganan yace “she’s always beating me Mommmm” jawosa jikinta Hibba tayi ta shafa fuskansa tace “don’t be rude to anyone again okay” gyadamata kai yayi yace “Mommy I want to eat indomie inje incema Anty Salma kince ta zubamin”?
Dasauri tace “no bari tagama zan dafa mana ga caprisone chan dauko kasha” dasauri yace “da biscuit?” Gyadamai kai tayi wani jumping yayi cikeda jin dadi tabisa da kallo kafin tadauki magungunan sa tana budewa duka sun kare, maganinsa gabaki daya idan ta tashi saya is about 118k cus yanada phenomena kap kudinda take dashi yanzu bazasu kai 20k bama a account nata