← Book details Gidan Kwarata Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Gidan Kwarata Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

Kirjin Ammie ne ya buga,nan ta kalli Aliyoun hadi da shafa sumar kanshi tana cewa"Ayya Aliyou kaga yanxu Asibiti xan tafi,kayi xaman gida,idan na dawo xan biya gidan Su Inna na duba Hafsat din kaji?

Kaman baxai yarda ba,sai kuma yace mata tom Ammie,adawo lfy".

Yowa aamien Haidar dina,sai na dawo?.

Tana fadin haka ta fice daga falon shi kuma yana Nufar Dakin baccin shi don ya watsa ruwa ya samu yy bacci,amma sam ya kasa rintsawa,burin shi kawai ya gano Hafsatu hankakin shi xaifi kwanciya".

Shityawa yy tsaf yana Shigar sa ta manyan kaya,Yana saka wata lallausar yadi milk da akayi masa Dinkin zamani,sosai ta amshi jikin shi".

Nan ya fara shirin isa Farfajiyar gidan,hadi da kirar Drivern su don ya kaisa gidan su Hafsatu.

Itakam Ammie da fitan ta hamdalah tayi,kana ta Kwana kan moton ta xuwa gidan Inna,don yau ake taron bikin Hafsatu da Maccido".

Wanda bayan komawan sa rugar su ya tada balli,aifah abinni da masu son Hafsatu shi baxai hakuri tayi ta boko ta dawo tace bata son shi ba,gwamma ayi masu aure kawai.

Hakan ko yasa Iyayen su Amince da mgnar Maccido yanda aka tsaida mgnar Auren Hafsatu da maccido a sati hudu kacal.

Tun ranar da Aka hana Hafsatu fita tafara jin babu dadi,sai a yanxu ta fahimci tabbas ta saba da Aliyou duk da bata son shu,amma ta dauke shi anatsayin kani kuma dan uwan ta".

Tuno da halin da zai shiga na rashin ta,yasata duk tabi ta fada,abinci na bata iya ci na kirki".
*************************
Bayan Driver ya ajiye shi ne ya fito,yana bin mutanen dake Kofar gidan,Kowa fuska cike da annuri,shelan Wani maroki yaji yana cewa"Ayau an daura Auren maccido da Hafsatu...allah yakawo xuria na gari....Nan duban jama'a suka amshe da Amin".

Wani Abune ya soki xuciyar Haidar,meyakejin yana fada wannan mutumin?

Wata Hafastun?

Badai nasa ba?

Ji yy anriko hannin sa,waigowar da xaiyi Omar ya gani,fusjar sa a yamutse bb annuri,yyn dakara waigawa can wurin mutanen da xaiyi ya hango Maccido da wasu kaya masu sheki,shigen yi shirun ka maraya,yanata washe baki da mutane".

Bakin Haidar na rawa yace da Omar,Wai da gaske Hafsatu tayi Aure? hafsa ta tafi tabarni?

Tayi Aure Omar?

Shiru Omar yy yana jiyo tausayin Haidar na ratsa jijiyoyin jikin shi".

Wanda su Inna da Amie kai harda Amaryar Hafsa lbrn xuwan Haidar tuni ta Iso masu,hakan yasaka Hafsat kasa sukuni,sai data taho har soron gidan,tana hango Omar da Aliyoun da batasan me suke cewa va,amma dagani kasan yana cikin tashin hankali ne".

Su Inna ma da Ammie hakan ta faru suna gyefe suna addoan Allah yasa Haidar ya dangana,Amma kuma mene?

Cewan Da Omar yy masa Aliyou kayarda da Kaddarar ka,dama tuncan Allah ya kaddara Hafsaru ba matar ka bace,da gaske ne Hafsatu tayi Aure...ai bai karaki fadi ba,Aliyou yy baya,don duhu
yake gani can yafara jiyo mgnar Ammie dana inna sama
sai kuma Yajiyo difff.....

Da gudu Hafsatu tayi cikin gida tana wani irin kuka kaman ranta zai fice,yyn da Hauwa duk dakiya irin nata saida itama tasa nata kukan.

Aliyou kam bai farfado ba sai a garin Abj.

Don can Ammie ta nufa dashi sbd rudewar da tayi,ta rasa yin komai,da daya tilo....Asalin gidan su Wato nan gidan Danlarabawa ta dawo dashi suka bar garin Kaduna,wanda koda ya cinci kanshi a gidan,haka ya abuce shi dai kawai Hafsa,yakoma kamar xatattace...Ammie kuka Shi Kuka,Surayya ma da tun dawowan su taxo itama kuka take,tana bin Wannan Hafsatun da Allah ya isan ta,tun da ta cutar mata da Cousin din ta'.

Ganin Abun na Aliyou sam yaki natsuwa ne yasa..Daddy cewa a taho dashi Uk su zauna tare,don a lokacin Daddy yaje karo couse a kasar America,nan Ammie ta tafi dashi....Wanda acan Alhmdllh Yadan saki ranshi,amma kullum yana aikin Tunanin Rayuwar shi da Hafsatu,dakuma tunanin ko tana wqni hali ayamxu?

Anan ne ya hadu da Jalil don tare da Dad din shi yake.....dayake Jalil Architecture ne,kullum yana aikin Wahalar Haidar,dob baida aiiki sai kwatanta masa yanda Hafsatu take ya yi ta xana ta,in yagama yy ta kallon hoton nata....

Itakam Hafsatu wannan kukan da tayi na ganin halin Da haidar ya shiga,ya kular da Maccido..wanda tun daga nan xaman lfy tayi kaura tsakanin su..kullum fada da hantara,bb dadi dai xaman nasu,tayi kuka ta share,hadi da kai kukan ta ga mahalicci....Kamin wani lokaci ta jeme ta lalace sbd wahalar da bata saba,kullum tana aikin daji da Nemo karmami ga xuwa kasuwq sayar da nono,a haka rayuwa tayi ta gungurawa da ita".
*************************
Aliyou kam bai dawo nigeria ba,sai da ya kammala secondary din shi,wwanda da saukar shi kasar ya nufo Asibitin Ammie don Yasan baxai tadda ta a gida ba".

Tun da ya isa Labour word don tanan ne xai hau stairs din da xai sada shi da Office din Ammie yake jiyo sautin muryar ta ta karatun Alqur'ani...suunan tana halin Unconcious ne amma bb abun da bakin ta ke furtawa sai kalmar Allah".

Inna kam sai kaiwa da komowa take,don Hafsatun da cikin ta yakai haihuwa dawowa tayi,don ta haihu a gaban ta".

Dik dauriya irin na Inna sai da tayi ta sharce hawaye".

Inna?

Ya kira sunan ta cike da mmkin ganin ta awurin".

Saurin juyowa tayi jin muryar da baxasu taba mantawa dashi a rayuwar su ba".

Haidar?

Takira sunan cike da mmki?

Inna ina Farin ciki na?

Ina Hafsa?

Cikin zubar da kwallah inna tayi masa nuni da dakin da take a kwance tana nukuda".

Likitoci da nurses duk suna a kanta ciki kam hards Ammien Haidar".

Daga masu xuvar da hawayen tausaya mata sai masu sharce gumi".

Ganin Haidar a dakin haihuwan yasanya Cike da
Tsoro Ammie tace"Haidar meya kawoka nan?

Bai bata amsa ba,illah takawa da yy har xuwa gaban gadon Da hafatu take idon ta a rufe,sai harshen ta dake fitar da karatun Alqurani cikin Suratul maryam".

Cak tajah ta tsaya,kana a hankali tafara ware idon ta,wanda vata sauke su akan kowa ba,sai akan kwayar idon sa,da fuskar shi da baxata taba mantawa dashi ba har abada".

Haidar?

Takira sunan sa cikin wqta irin wahalalliyar murya".

Saurin karasawa gavan ta yy yana riko hannun ta da tadago tana mikamasa....Hawayen kuncin sa na sauka saman taffan ta".

Aliyou kayi hakuri ina mai baka hkri,akan vun danayi maka,Ka sa aranka ni ba matar ka bace dama...amma ga yata ko dana nan,na baima ka halak malak ..zan tafi xan koma ga Mahalicci na,ka rike mun su tamkar dan daka haifa da jinin ka....Ka tarbiyartar mun dasu ta fanin Addinin musulumci...na baka Danako yata kar ka bari susha wahalar dana sha arayuwa....Ka.....harshen ta ne ya datse,kamin ta hau kakari tana fitar da wani irin aman bakin jini,sai kuma jikin ta ya saki....daga cijgan da takeyi".

Hafsa...yakira sunan ta da Karfin gaske da saida ya dawo da hnklin inna dake waje".

Allhu Akbar,allah me girma annabi mai dunbin daraja,nan take Allah ya amshi Rayuwar Hafsa...Maganan likitocin da Ammie yaji tana cewa"a maxa ayi nata Operation don ceto dan dake cikin ta".

Rasa me xaiyi yayi,kuka kome ne?

Kawai sao jyawayy yana fita daga dakin,kwallah na bin kuncin sa,kaman yanxu ne suka fara rayuwa yakeji......moto ya shiga driver na jan sa hadi da nufar gidan Dan larabawa dashi".

Anyi nasarar fiddo da diya mace,wanda Faroq da inna awannan rana ya xama masu ranar da baxasu taba mantawa dashi ba,a rayuwa".

A ranar mutan Rugar suka taho,kuma anan aka shirya Hafsatu aka kaita gidan ta na gsky".

Bayan kwana bakwai da rasuwarta ne aka maida sunan Diyarta da Hafsa,wanda Mutan rugar suke kirar ta da Hasile".

A hannun inna Aka bar Hasile,wanda Aliyou kam tundaga wannan rana yakasa Xuwa gidan Inna,Ba lafy kullum yana cikin ciwo da rashin Hafsa a rayuwar sa".

Sai da aka watse kusan Kwanan Hafsa Sha hudu sannan ya iya xuwa Gidan Inna,wanda ganin Hasile yasa Shi cuno masa dogon famin xiciyar sa,tabbas kaman Hafsatu tayi kaki ne ta aje".

Don kaman su ya baci".

Haka xai xauna ya tasa Ta yy ta kuka...sai Inna ta shigo dakin tayi ta rarrashin sa hadi da masa nasiha.

A haka Hasile ta fara girma,Inna na bata madara,dom Ammie ne ta dauki nauyin komai....Shikam Aliyou maganar Karatu ya jingine gyefe..kullum bayi da aiki sai raino.

A haka Hasile ta kai kusan shekara biyu,bb wanda ta sani sai nurry dad din ta,da Uncle Farouq,sai inna don daga baya ne tasan Ammie...

Mahaofin Aliyoune ya sama masa Admission a Uk.wanda badon yasoba yaya fara shirin tfy karatu can.

A inda xai karatan medicine".

A kwanakin da Haidat baya nan,Inna bata da sukuni,Kullum Hasile tana kukan rashun Nurr Dad din ta .idan Ammien Haidar taxo,tayi shirru tana jirar shigowar sa,abuka ga yarinta idan taga Shiru
bau shigo ba,sai ta kuma saka masu ihu tana tsalamasu,ahaka xasuyi ta rigi
da ita,suna rainon ta...A haka Aliyou yy Wata uku acan yagasa sukuni sai da yadawo ganin Hafsan nashi".

A ranar da yadawo shiru sukeji,don sai murna takeyi,shima kam sosai yaji dadin yanda yaga Su Ammie na Kula masa da Amanar sa...a hakayy sati guda sanan ya koma".

Dawowan da xaiyi na buyu ne,ya tadda Inna Da su Farouq duka basa gidan,da yatmbyi mai hayan,sai yace masa ai kwanan su Shida kenan da tfy Rugar su,har yau basu dawo ba.

Acan ko Ruga tun da suka je ne,Macido ya kyekyeshe ido,shikawai abashi Hafsa...abar masa diyarsa...Zuciya irin na Omar nan yace"Sai Inna ta bashi yar shi...Kuma su da rugar Hunkuyi harabada,sun barta...Haka inna ke kuka ta baima maccido Hafsatu da suke kirar ta da Hasile,amma da yake shi kafaffafen mutum ne haka yasa hannu ya amsa.

Tun bayan da suka bai masa Hasile,aranar Omar ya ce subar Ruga haka kam akayi,wanda a hanya ne Inna tace"BazTaxata iya xaman kd ba.

Ahaka suka nufo xaria.

Tun daganan inna bata kara komawa kaduna ba...tabbas tasan mutuwa yankan kauna ce,ra rabu da Diyarta kuma wanda take gani taji sanyi yanxu itama an rabata da ita..tayi kuka kuma ta fammala ma Allah komai.

A haka suka cigaba da ryuwar su a Zaria,inda Omar ya samu aikin soja...ya fara karatun sojan..Aliyou kam da Ammie kullum suna saka ran Dawowar Inna da Omar da diyar su Hafsa,duk shiru har shekaru biyar a haka suka cire rai da dawowan su".
Chapter 17 · 0% Book details