← Book details Gidan Kwarata Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Gidan Kwarata Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

Na taba yi maka Wasa ne,yy mganar kaman shine gaba da Lukman din,Ina sonta,kuma ni tun a jiya na fadi ma Ammie,na samu matar da zan Aura!

Ohh Allah!

Aliyou na fahimci haukar yarita ke damunka".

Wacece matar Auren naka?

Wancen Yarinyar da kk Age mate ne xaka Aura?

Nan deen ya amshi damgnar Lukman yana cewa" Rabu dai Da Aliyou,kila Ma Kamin yy Aure ita tayi har ta haihu da Jikoki".

Nan kaji sun kwashe da Driiya...wanda yabata ran Aliyou Haidar".

Tom se mene?

Ni Ita din nakeso,kuma mgnar agemate dina,ai Atarihi ma yaxo mana dashi,Annabin mu Ya auri Nana khadija da ta girme masa,bare kuma ni da take aagemate dina, Inna Aureta sai Ku Hana!.

Jin yanda ya bude masu witar Fada yasa su jahn bakunan su sukayi shiru,Deen zo muje wurin Hafsa,na fada mata ina sonta!

Aliyou ka tsaya muyi tunani".

Baxan tsaya ba,idan xakaxo muje malam kaxo mu wuce,idan baxaka...aa muje tom".

Deen yayi saurin katse sa yana takawa hadi da nufar inda Su Hauwa suke a zaune".

Kirjin Hafsa ne ya buga,ganin Aliyoun da Aminin shi Wato Deen,babu Fara'a ko kadan saman fuskar shi ...

Deen ne yayi mawa Hauwa mgna da cewa"Hauwa'u Muna son mgna da Hafsa".

Kallon su Hauwa tayi cike da mmki,sai kuma tace"Tom me zakuyi mata?

Murmushi Deen yayi kamin yace"Boss ne ke Son mgna da ita
. ieem nan ta yatsina baki kamin tace"Ok Hafsa ina jirar ki a kofan Class...ta mike tabar Hafsa da ta tagaxa cewa komao,Hankalin ta ya dan tashi,don ta lura Haidar baya da mutunci sam".

Mikewa tayi daga tsaye kaman yanda yake".

Kamin tace"Ina jinka".

Hmmm shiru yayi na en seconnni,kana yakalleta ido cikin ido,bb kunya yace da ita" Hafsa Ina sonki,Inason zana Aure ki..kefah?

Mamaki gami da haushi Ne duka suka rufeta,lallai wannan yaron ya raina ta,abun da take cewa"kenan A xuciyarta da take wani irin tafasa,wanda kamin ya ankare Yaji saukar ya tsunta biyar a saman kuncin shi".

Tasssss...

Wannan marin yasaka Gabaki daya ilahirin daliban Side din suka juyo da hankslin su a kan Aliyou da Hafsa".

Amaimakon yayi wani abu,ko bata ranshi kawai sai yy murmushi yana shafa saman kuncin sa,kana ya kuma maimata mata,I really luv u".

Ba da wasa ba,Zan Aureki kod...Kuma wanka masa wani bahagon marin tayi,kamin ta fara mgna a zafafe,don itama batasan ta iyashi ba,Kai wani irin yaro ne,ni sa'ar kace?

Kana kanin bayana kaxo kana cemun Kanaso na!

Hauka kakeyi ne?

Mgnar take jero su dika a one sentence,kamin Hauwa taxo tayi saurin jan Ta suka nufi Class...

Taana mmkin Tsaurin hali irin na hafsa da har ta iya marin Aliyou Haidar".

Sukam abokansa,wani iri kiyayayyan Hafsane ya lullubesu,duk da basa da Halin nunawa sbd Gaba dya idon Aliyou Haidar ya rufe a sonta".

Tun daga wannan Rana Baki daya Class din suka chanja mata banda Hauwa bb mai kallon ta,run da ta taba Shalelen su abunso Aliyou Haidar".

Kowa Tsaksnin ta dashi sai harara da yada mgna".

A wannan satin kam su Rufaida har a salinta sai da Suka kwakwulo dabata san ta inda suka sani ba...

Kinsan mene Ne Naima?

Aa sai kin fada rufaida,wlh Shi idan akace maka mutum
an kauyen Bafulkatani ne,tom baya taba wayewa har ya mutu,don sai yy shekara arbain a binni kamin nan".

Nan suka kwashe Da dariya har suna tuntsirawa...shiru Hafsat tayi kana ta wuce su batare da tace"Komai ba".

Tundaga Ranan Kaman ance Aliyou Haidar ya kuma takura mata da damu ne,Don Tun tana marin shi har ta daina tabarsa da halinsa don ta lura shi irin mutanen nan ne idan suna son abu,idon su rufewa yake sukoma kaman mahaukata".

Hakan yasata rabuwa dashi duk wacce hanya da xai hada su bata son haduwar tasu".

A haka dai yau dadi gobe akasin hakan....a haka take ta gungurawa tana kokarin kauce mawa Aliyou da nacin shi".

Ammie Kin san ina son Hafsan sosai kuwa?

Allah dai Haidar?

Ehhh Ammie yabata amsa tana kokarin Hada masa Ruwar wanka....Ammie Tom tayaya Daddy Zai amince mun na Aureta?

Tofah Aliyou Wannan wani irin mgna ce haka?

Na dauka dai Kawai Abun na ka schl friend ship ne...

Aa Ammie nifah Auren ta xanyi.

Ganin Abun nashi yana shirin samata Rigima,yasata cewa"Tom shikenan Haidar,allah ya nuna mun lokaci...Sosai yaji dadin mgnar Ammien nashi,Don haka ne A washegari Har ita hafsan sai da ya samu ya fade mata abun da Ammien shi tace,amma sai ta mayar dashi Sakarai".

Ana haka sukayi hutu,wanda sosai Hafsa taji dadin hakan,don ta huta Da damun Haidar....Sai dai Hauwa da take zuwa gida suna taba zumunci".
****************************
Hafsa...Hafsa....

Inna ce tayo kirar diyar nata,wanda yasa Hafsa Saurin fitowa tana amsa kirar Innan nata daga wajen soron gidan nasu".

Kicibus sukayi da Shi hannun ta dauke da manjan da Inna ta aiketa sayowa....aiko sam bata san lokacin da Ta juye masa manjan a jikin shi ba".

Gaba daya yar farar shaddan tasa ta rine da manja dama ana kafulle an shigo binni daga ruga".

A zuciye ya daga hannun shi yana shirin wanketa da mari,aiko nan Yy saurin rike hannun nasa,kana suka hau kallon kallo".

Cike da xafin murya Maccido ya kalli Aliyou Haidar yana cewa"kai wanene?

Da xan hukunta kanwata kaxo ka rike ni".
.murmushi Aliyu yy kana yace mai sonta!

Mene?

Ehh yanda kaji".

Zaro ido hafsa tayi,tana ta'ajibi yaakayi Ya taho gidan su,har ya sani....muryar Umar ne taji yana cewa"Aliyou yayan mu ne,xo mu tafi laifi tayi masa,shigo ka gaida inna!

Jin ance ya taho ya gaida inna yasa shi kutsa kansa cikin soron gidan nasu da yakasance tun daga farkon sa har karshen sa ginin jar kasa.

Tab dijammm Hafsa,yaudara takkyi dama?

Budan bakin maccido abun da yace mata kenan,wanda cikin sauri tayi wajen gidan don tsoron xuciya irin na Maccido".

Mmn teddy
[10/6, 12:59 PM] Maman Teddy
: *Loading......*
GDN KWARATA!

Na Maman teddy
84-85
*@Alheri Writer's asso.

Ban yarda ki karantamun lbri ba tare da kin biyani Kudin sa ba,domun kuwa lbrn na kudi ne idan kina bukatan cigaban Lbrn zaki yi mgna ta wannan number 08081202932 .

Vip payment #500 mtn card,Normal #200.

Idan har kika karanta baki baya ba keda Allah!

Bismillahir rahmanur rahim".
______________________________
"Shikam Omar nufa da Aliyou yy wurin Inna dake kitchen hayaki ya cika tun daga farkon gida har karshe".

Inna Ga Haidar din da nake maki mgn".

Omar yy mgnar yana nuna Aliyou Wanda ya dan risina ya gaida Inna dake ta fama da Hayakin Ice".

Cike da harka Inna ta amshe aa Wannan Ne Aliyoun Hafsatun nawa?

Tom maza kai shi daki,ka barshi daga Waje?

Inna tayi mgnar hadi da Sauke idanun ta da sukayi jah sbd icen damunan dake damun ta akan na Omar...Tom Inna yy maganar yana juyawa hadi da nufah da Aliyou Dakin Innan da kwakkwarar Leda babu".

Wata fatakakkakkiyar Tabarma ya shimfida ma Aliyou kamin Ya zauna,shima ya jah ya zauna.

Itakam inna Bayan Wucewan su da ido takebin Aliyoun da lokaci daya tayaba da natsuwar sa,yaron kirki,sam baya da fahari da Girman kai irin na Yaran masu dashi".

Murmushi tayi tuno da mgnar Omar da sukayi da yake cewa"Inna fah Shi Aliyou da gaske yakeyi Aurar Hafsatu zaiyi".

Nan Inna tayi dariya a xuciyar ta tana fadin" Inbanda Yarinta ina Aliyou Ina Hafsatu?

Dukan su nawa suke,takitaki basu fi shekaru Sha shida ba".

Fitowa tayi daga madafin da take tana nufar Dakin Ta...da yake ba ginin Zamani ba,gini ne ta kasa,kasan ma jar kasa ta yambo,sai kofan lagye
n ta".

Da shigarta tahau tsokanan Aliyou don ita macace mai harka da barkwanci sosai....Zama tayi tana debo masa ruwa a kwanon sha,sannan suka cigaba da fira,wanda duk da Haidar ba gwanin Fira bane,amma sun taba da Inna...koda Hafsatu ta dawo,tun a tsakar gidan take jiyio firar Inna da Aliyou hakan yasata Yin tsaki,tana mmkin tayaya Aliyou yasan Yayan ta Omar?.

A haka ta yi shirin islamiya sai dai muryar ta daga kofa sukajiyo tana cewa"_Inna Sai na dawo!

Tom Auta na Adawo lfy?.

Da hakan ta fice".

Shikam Aliyou bai bar gidan ba sai wuraren Biyar na yamma,kamin nan ya fahimci labr da tarihin Hafsatun duka,don mahaifin ta Allah yy masa Rasuwa tun bata da wayo,batafi shekaru biyu ba Ya rasu,Dama shi sana'arsa Sai da Manshanu a kasuwa,don a salin sa bafullatani ne na Zaria garin hunkuyi".

Har Halakar ta Da maccido sai da ya juyo,duk da Inna bata fade masa Wani Abun dake boye tsakanin Maccidon Da Hafsatun ba!

Da mahafin Maccido Wato Hardo da Baban Hafsatu Uwa daya Uba daya ne.Hakan yasa shi Yana xuwa Kawo masu Inna Ziyara,duk da itama Innan yar Asalin Hunkuyin ce".

Wannan kenan!

Tun daga wannan rana,ba'a kwana biyu Aliyou baizo gidan Inna ba,duk xuwan da yakeyi don yaga Hafsatu ne,wanda har yanxu kallon shi batayi,Duk da tana tsoron Yah Omar".

Tsakanin Aliyou ko da Maccido sai harara,babu maj kallon wani da sunan Gaisuwar mutuntawa.

Hakan yasa Hankalin maccido tashi,ahaka dai ya koma Rugar hunkuyi,su kuma su Aliyou Aka cigaba da Zuwa Makaranta,don hutun mako biyu aka masu takare".

Haka xaita shishshige ma Hafsa tana yarfa shi,bai damuwa har ta gaji ta dawo daga rakiyar shi,Yazama na idan Ammien Aliyou taxo daukar shi sai ta dauki Hafsatu takaita gida,sannan su dawo da Aliyoun,A haka har Ammie da Inna aka saba,sosai suke mutumci,Don Itakan ta Ammie Sosai takejin son Hafsatu a xuciyarta,duk da tasan Auren ta Da Aliyiun ba mai yiwuba ne ba".

A haka har suka shiga ajina biyu,aliyou kullum mgnar sa da xarar sun shiga ajin karshe xa'a tsaida mgnar Auren su,Tun Hafsatu na damuwa takoma rabuwa dashi bata cemasa Komai,don idan tabi tanashi xatayi ta marin sa a banxa,don bashi xai hana mgn yataso ya fada ba...kullum firar shi Hafsatu".

A ranar Laraba ne sam baiga Hafsatu a makaranta ba,sosai ya kasance baya da Walwala...ahaka yake saran Ganin ta gobe nan ma bai ga xuwanta ba...Da ya tambayi Hauwa sai ce masa tayi ai tana lfy,gobe friday xata zo".

A washe garin juma'a nan mababu Hafsatu babu hauwan don duka basu xoba!

Hakan yasa Aliyou yakomakaman majinyaci".

A natashin su ya koma gida,Anan ya tadda Ammien shi tana shirin ta tsaf daalama fita xatayi".

Ammie ina xakije?

Inaso ki kaini gidan su Hafsa yau?
Chapter 16 · 0% Book details